Showing 21001 words to 24000 words out of 37413 words

Chapter 8 - DUBAI PART ONE BY UMMUH HAIRAN.txt

14 Jan 2025

3791

biyayya.










Ranar da suka gama abinda ya kawosu suka fara shirin tafiya, kwana biyu suka qara suka daga zuwa Dubai tafiya ce irinta kurame babu me cewa da wani qala.
Nanma gidansa yakaita ya ajiyeta kashedi na tashin hankali yayiwa masu gadin gdan akan bayason Koda ya tafi abar wani ya shigo gdan, kudi ya ajiye mata sosai ana i gobe zai tafi da dare ta samesa a parlour yana kallo ta nemi guri ta zauna “bai ko dago ya kalleta ba har tagaji da zamanta ta miqe zatabar gurin ya riqo hannunta.
Fadowa tayi jikinsa ya riqeta tare da dafa cikinta yace “da magana a bakinki maman twins me kikeso?" Kukan da take hadiyewa ne ya kubce mata yayi saurin dora bakinsa akan nata ya rufe mashi ruf yana tsotsarta yana shafa cikinta.










Janyewa tayi a hankali tace “yanzu kuma idan ka tafi yaushe zaka dawo?" Murmushi yayi yace “zanje nayiwa Mom albishir ne takusa daukan jika..."
Da sauri ta zuba masa manyan idanunta tace “na shiga ukuna don Allah kada ka fada musu Taheer me zance da Addata idan taji wannan baqin lbrn bayan karuwancin da nakeyi ma har cikin shege nay...."
Wani gigitaccen mari ya dauketa dashi ya miqe yana huci ya sake dauketa da mari ta zube kanta ya daki glass ya fashe kuwa jini yayi tsartuwa.
A masifar zafafe yace “ke wacce irin jahilar qwaqwalwa ce dake sau nawa zance miki ki daina sheganta min babena Amma kinqi ganewa"...........










*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[7/23, 9:23 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️








*_22/7/2020_*










_Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200 VIP da nake posting sau uku a rana 600_












_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_




_Account number_
👇🏻
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_


_GTB_


_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
👇🏻
_09013718241_


_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_
👇🏻
_09013718241_








*Episode 16*






Cikin mugun tashin hankali ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta ta bude idonta a galabaice ta shafa fuskarsa tace “ad... Adda..na ta mut... Shi...shikenan ba...ni da sauran me fadamin gsk..." Amaine ya turnuqo Mata ta fara tureshi tanajin yanda qirjinta yake wani mugun zafi a fara sheqa amai.
Tsoro ya cika zuciyar Taheer ganin zallan jini takeyi amansa guda guda, ya qanqameta a qirjinsa yana danna Mata qirjinta yana cewa “zaki mutu ki barni kike nufi Habeey aa bazai yuwu ba bazaki mutu ba don Allah kada kice zaki mutu nima mutuwa zanyi, ki bari muyi aure sai mu mutu tare..."








Jikinta yana wani mugun tsuma hakanne yasashi surarta ya fice da ita a guje yasata a mota ya nufi asibitin data taba kwanciya da ita cikin fitar hayyaci sai aman jini takeyi.
Ikon ilahi ne kawai yakaisu asibitin ya sunkuceta suka shiga ciki ya kwantar da ita a saman wani gado yaje ya finciko wani likita ya kawoshi gaban gadon kawai ya zube a gurin.
Suma sosai abin ya firgitasu suka turata suka nufi heart attacks ward da ita suka fara qoqarin ceto rayuwarta, sun raba ranar kafin su samu numfashinta ya daidaita likitar ta fito ta tarar dashi a zaune ya hade kai da gwiwa yanata sharar gumi yana duba agogo tun 3:00 na dare gashi har 1:00pm sannan suka fito.








Tararsu yayi yana tambayarsu “ya take? Ya baben Amma dai babu abinda ya samesu ko?" Share gumi likitar tayi ta miqa masa takardun hannunta tace “akwai abinda yake damun matarka da take boyewa Wanda ya haifar mata da kumburin zuciya, yakamata ka bincika kasan matsalarta ku kawo qarshenta idan ba hakaba rayuwarta tana barazanar yankewa"
Sakin baki yayi yana kallon likitan a sanyaye zuciyarsa ta tafi tunanin matsalar dake danqare a zuciyar sahibar tasa shikam wannan karon duk me yuwuwa zaiyi yaga yaji matsalarta domin ya kawo qarshen koma menene course rashinta rashin tashi rayuwarsa ne"










Duk wani abu da aka rubuta masa Saida yaje ya nemosa ya kawo, sannan ya tafi gida ya zube a parlourn yana tunanin ta inda zai fara tunkarar iyayensa da mgnr haihuwar da zaayi masa.
Bayason dauko dalar sai yaje gabansu zaifijin dadin nada gammon dauka, shima yini yayi bashida lfyr saboda zuciyarsa batada lfy ko abinci ya kasaci sai ruwan tea kawai da yakesha.
Daqyar yayi wanka ya koma asibitin yayi saa ya tarar da ita ta farka ya ajiye kayan hannunsa ya matsa gabanta da sauri ya rungumeta yace “sannu wifey don Allah kada ki mutu ki barni zuciyata nima gaf take da bugawa"
Lumshe idonta tayi wasu hawaye masu dumi suka zubo mata tace cikin kasalalliyar wahalalliyar murya “shikenan Taheer Addana ta mutu shikenan ta tafi ta barmu shikenan tabarwa duniya mu, Taheer Adda ta mutu da baqin cikina ta mutu da baqin cikin wannan qazamar rayuwar da mukeyi"








Sai yanzu ya fahimci abinda ya sabbaba mata ciwon ya sake rungumeta cikin tsananin tausayinta da yakejin yana ratsa duk wata qofa ta shigar iska jikinsa.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo masa suka sauka akan dokin wuyanta ya dora habarsa cikin gashinta a hankali yace “ Innanillahi wa innah ilaihirraji'un Allah ya jiqan Adda Habeey" kukane ya sake kwace Mata ta rungumeshi sosai tace “shikenan fah na rasata har abada ko Taheer" shafa kanta yayi yace “dukkanmu a haka mukazo da daidai kuma a haka zamu koma mudaiyi fatan kyakkyawan qarshe"
Kukanta takeyi me quntata zuciyar me sauraro yayi rarrashin duniya taqi tayi shiru, a hankali ta dago tace masa “Adda tabar wasiyyar na koma 9ja nayi aure Taheer ya zanyi da Pappa da kullum yake cewa idan na dawo 9ja saiya tsinemin?"








Dagota yayi yace “meye asalin abinda ya kawo rikicin jumurdar dake faruwa tsakaninki da mahaifinki? Na roqeki badon kaina don Allah da Kuma darajar mahaifiyarki dake kwance cikin qasa tana sauraronki ki fadamin wani abu game dake"
Kwantar da kanta tayi a qirjinsa taci gaba da rera kukanta tace “banason tuna komai game dani Taheer lbrna bashi da dadin sauraro baudadden lamari ne me wuyar warwara Taheer nifa dama zaka sanya suyimin allurar da zan mutu da nafi farin ciki fiye da rayuwar da zanyi a gaba ta quncin da bansan adadinsa ba"
Rufe mata baki yayi yace “babu abinda bazai wucce ba Babe don Allah ki sanar dani inason taimakonki na mayar dake gda, hakan kuma bazai taba faruwa ba harsai kin sanar dani wacece ke"






Ajiyar zuciya tayi ta dago manyan idanunta da suka kada sukayi jawur tace “nayi maka alqawarin zan sanar dakai abinda ka dade kana tambayata.
Sake mayar da kanta tayi qirjinsa tace








_____________Hajara Liman Ɓillire shine cikakken sunan mahaifiyata amma muna kiranta da Adda, mahaifinta shine limamin masallacin jumma'a na ƙauyen ɓillire yaransa shidda hudu maza biyu mata, mahaifiyarmu macece kyakkyawar gaske me cikar zati hakan yaja Mata masoya daga lungu da saqo na garuruwan gombe.
Abinka da yayan malamai Hajara bata kulasu sai sun nemi izini gurin mahaifinta, ana haka wani mutumin Ganjuwa wanda ya kasance qabilar tangale shima ya shigo cikin maneman aurenta.








Cikin qudura ta ubangiji da Kuma rabo sai Allah ya cusawa Hajar qaunar Dalson Damuna Iro, zuwansa na farko gidan Liman da zummar neman aurenta sai Liman ya kirashi ya sanar dashi yayi hqr babu aure tsakaninsa da Hajar.
Aikuwa Hajar ta shiga tashin hankali ita da masoyinta kullum cikin kuka take shikuma ya rinqa zugeta yana qara cusa Mata qaunarsa a zuciyarta ita kuwa ta saki jiki wutar qaunarsa sai ruruwa takeyi a zuciyarta.
A dabi'ar qauyukan da suke da cakudin addinai ba wani abu bane don auratayya ta shiga tsakanin ahlil kitab maza da mata musulmi duk da abin ya kasance haramtacce a jadawalin dokokin addininmu.








Wannan dalilin yasa Liman ya kafe yace bazaayi wannan abin kunyar dashi ba, qarshe ma da yaga Hajar tana qoqarin bijire masa sai ya zaba Mata miji cikin almajiransa hakanan Liman ya hada auren nan aka ganganda akayisa.
Amma Kuma sai zama yaqi dadi duk wani haqqoqi na aure hajar ta hana Salihu mijin da Liman mahaifinta ya zaba mata sai cin mutunci da tujara kullum cikin sulhu suke amma idan ta koma gdan jiya zaa koma.
Daqyar Hajar ta iya yin wata biyar a gdan Salihu suka hada baki da Dalson sukayi masa kurciyya yabar garin lkcn tana dauke da ciki watanni biyu, ya akayi ya akayi baa sani ba wasu dai sunce kwantar dashi sukayi.
Tsayin sati uku da batan Salihu sai gashi ya aiko da takardar sakinta, murna kamar Hajar ta zuba ruwa a qasa tasha hakanan tayi idda a daddafe Dalson ya dawo sahun maneman aurenta.








Lkcn daya dawo yazowa Hajar da albishir din ya karbi kalmar shahada tayi murna sosai hakanan yazo ya shiga cikin almajiran Liman yana daukar darasi,a gefe guda kuma yana gyara kansa gurin Liman.
Shidai Liman har lkcn zuciyarsa bata kwanta da Dalson daya koma Haroon ba, amma Kuma yaga Hajar ta mutu akansa, har takai lkcn daya kirata yanayi Mata nasiha akan aurenta da Haroon ta fito tace masa itafa yanzu ya qyaleta ta auri abinda takeso.
Hakanan da yaga abin zai zama matsala ya kira Haroon ya fada masa ya kawo sadaki a daura musu aure da Hajar" cikin sati daya akayi biki aka gama amarya ta tare a gdanta.










Farkon zaman Hajar da masoyinta Haroon abin gwanin gwasama amma da zama ya fara nisa sai hali ya fara bambamta Haroon baya sallah azumi ma sai yaga dama yakeyi Haroon bai damu da bawa Hajar abinci ba.
Ana cikin wannan murdadden zaman ne cikin da suka kwantar ya tashi, nan fa sabuwar rigima ta tashi yace shifa saidai a zubar da wannan ciki saboda baya qaunar duk abinda ya shafi Salihu, itakuma tace bai isaba ai shine yace su kwantar dashi tun farko.
Shikuwa ya hanata abinci saidai tayi surfau da dakau da wankau ta samu abinda zataci har cikinta ya isa haihuwa cikin dare naquda ta kamata daqyar ya taso mata wata Mata da suke haya tare Cristian ce sunanta Alheri itace ta karbi haihuwar cikin hikima ta ubangiji Hajar ta haifo sunkuceciyar yarta mace kyakkyawar gaske.








Alheri ce tayiwa Haroon albishir na kyakkyawar yarinyar da suka haifa da farko qin zuwa yayi amma da yaji anata zuzuta kyawun yarinyar sai yazo yaganta kamarta daya da Salihu amma saboda idanunta da hancinta na Hajar ne sai kamar ta buya amma har kalar fatar yarinyar irinta Salihu ce wato chocolate colour.
Yana ganin yarinyar nandanan Allah ya dasa masa qaunarta a zuciyarsa ya daukita yayi Mata huduba da Anitah Nan fah Hajar tayi tsalle ta dire tace aa ita Habibatullah sunan yarta nan ma an samu rikici me yawa kafin kowa ya zabi sunan da zaike kiran yarinyar dashi shi yana kirana da Anitah Addana tana kirana da Habibatullah.........












*UMMUH HAIRAN CE...✍🏻*
[7/23, 9:24 AM] OPEN AYES MULTIMEDIA: ✈️ *DUBAI*✈️






*_22/7/2020_*






_Page 15 shine last Free Page, ga wadanda suke buqatar jin qarshen wannan labari zasu biya kudinsu ta wadannan hanyoyin dake qasa single section da nake posting sau daya a rana 200 VIP da nake posting sau uku a rana 600_












_Idan kinada interested zaki iya biyan kudinki ta wadannan hanyoyin_




_Account number_
👇🏻
_0255526235_
_Fauziyya Tasi'u Umar_


_GTB_


_Ko katin waya MTN ta wannan number a WhatsApp_
👇🏻
_09013718241_


_Saiki tura avidance of payment dinki ta wannan number_
👇🏻
_09013718241_


*Episode 17*






Haka Addah take rainona ta dauki son duniya ta doramin tun Ina shan nono Addah takeda tarin buruka a kaina, babban burinta shine nayi karatun addinin muslumci me zurfi sannan nayi na boko.
Watanni na goma sha bakwai Addah ta haifi Ibrahim wato Sunday sunan da Pappa yake kiransa dashi kenan, tsakaninmu da Pappa kullum naira biyu da ficika ce nida Ibrahim itace abincin rananmu itace ta darenmu gashi kamar ya kafe Hajar bata iya fadawa kowa matsalarta saidai tayi surfau dakau wankau ta sama mana abinda zamuci.








Taheer tunda nake a rayuwata idan ka dauke kayan jarirantaka zan iya rantse maka baa tabayi mana sabon dinki ba saidai abamu saqabu musaka wasu ma sunyimin yawa haka zanta bunjim bunjim a ciki gani Masha Allah ta ko Ina Allah ya qerani baiyimin qirar wasa ba amma babu kulawa.
Duk da mahaifiyarmu tana iyakar bakin qoqarinta abinne yafi qarfinta ci sha sutura omon wanki sabulun wanka man shafawa duk Addah keyi mana, a haka ta haifi Aishatu wato Hellin.
Nan fa dangantaka ta fara tsami tsakanin Addah da Pappa takai ta kawo Pappa sai yayi wata biyu yana cikin garin gombe amma baizo inda muke ba Amma hakan bazaisa idan yazo Addah ta canza masa kallo ba.








Gashi Allah yayiwa addanmu baiwar aihuwa data tashi sake haihuwa sai tayi biyu Fatima da Idris Wato Ritah da Jumson lkcn inada shekara hudu yar kyakkyawa dani, sanda na fara tasawa ne al'amura suka qara quntata.
Wani dare da bazan taba mantawa dashi ba a rayuwata daren dana fara fahimtar me rayuwar gidanmu take cewa, Taheer na fito tsakar gida fitsari ya kamani na shiga bandaki na fito kawai sai na tarar da Addah zaune kan kujera yar tsugunno tanata rera kukanta.
Nan na matsa gabanta na zauna na riqo hannunta kawai sai naji jikinta da zafi, Ina Shirin yi Mata mgn naga Pappa ya fito rungume da wata mace a jikinsa yana shafata yana cewa “madam yau kinyi sugar dubu uku zan baki"








Mamaki ya kamani da naga ya sanya qafa ya hankade addana yace “shashasha da kin dauka ni dan iskane da zan tsaya Ina wahalar sallah azumi sannan insha wahala na tara dukiya ace nayi zakkah to bari kiji Hajar wannan addinin naku na wahalallu yayimin tsauri bazan iyaba Kuma giya da neman Mata yanzu na fara, Hajar bakida wani dadi ni'imarki Habeey ta kwashe da ganin wannan dundubusar yarinyar ruwazata tara bana wasa ba.
Amma dake abin naki son kaine baki bawa yayana ba sai kika bawa yar tsohon mijinki da mota ta niqeshi, to ko ruwana da aka diva aka wanke wannan yarinyar idan ta girma saita biyani da hannunta saboda ni ba bawan wani shege ko shigiya bane"










Nidai sakin baki nayi bata da ina gane ko kalma dayaba Ina kallonsu suka fice Addah ta dago ta kalleni tace “kije ki kwanta Habbatullah kada ki makara zuwa makaranta kinga gobe akwai tahfiz"
Banyi Mata musuba na miqe naje na kwanta amma zuciyata cunkushe da tunanin abubuwa da yawa, abin mamaki Dana tashi da safe banga alamun wata damuwa a fuskar Addah ba tanata aikinta na dauki tsintsiya nayi Mata shara nayi wanke wanke na taso Fatima da Idris nayi musu wanka naja hannunsu zamu tafi Tahfiz amma sai naji Pappa ya kirani da sunan dana tsana wato Anitah.
Babu yanda zanyi haka na juya na kalleshi yace “sakesu dan ubanki kedai da kika gaji wahala kije kiyi amma yayana bazasuyi wannan wahalar ba"








Tatar qullin kunun da Addah takeyi ta bari tace “wai da gaske kakeyi maigida kayi riddah?" Batare da tunanin komai ba yace “Ni dama ban musulumta ba balle nayi riddah sani nayi wannan daqiqin uban naki meci da buguzun bazai bani aurenki ba sai nayi masa basaja bakisan wani abuba yanzu haka church gudace a hannuna saboda haka Hellin Sunday Ritah da Jumson Yaya nane bana buqatar ki qara dangantasu da addininki"








Duk da ba komai nake fahimta ba amma kalaman na qarshe sunfi komai girgizani ina tsaye kamar dashe yazo ya janye qannen nawa ya mayar dasu ciki nikuma addah ta kalleni tace “jeki makarantarki kinji Habbatullah" hakanan natafi tahfiz din ni kadai.
Tundaga wannan ranar su Aisha suka daina zuwa makarantar islamiyya saida Adda ta koya musu, ana haka sai Dalson ya tsiro da wata tsiya wai lallai sai Addah ta rinq binsa church, itakuma tace Allah kasheta bazata ba nanfa dangataka ta qara tsami kullum sai Dalson yayiwa Addah dukan mutuwa sannan yaje ya shawo giyarsa yazo yayita sheqa Mata amai hakanan zata wanke kuma ya jibgeta.










Nikam dukan yana damuna amma ban isa na fadaba sai Addah tacemin Ina ruwana ai laifi takeyi masa shiyasa yake jibgarta, ana haka labari ya ishe liman na cewa Haroon yayi riddah ya koma kafircinsa.
Nan fa kakanmu yayo tattaki har zuwa garin Ganjuwa yazo domin qwatarwa Addah yancinta amma fir tace itafa a qyaleta da mijinta zata zauna dashi a haka saboda idan ta tafi bazai bar mata yayanta ba kuma tasan canza musu addini zaiyi.
Taheer duk yanda Liman zaiyi yayi amma Hajar taqi basa hadin kai har cewa yayi zai bata gidan zama anan cikin birnin gombe da jari me tsoka sannan zai shigo da hukuma ta qwatar mata yayanta amma taqi yarda wai ita idan ta rabu da Dalson mutuwa zatayi.








Wannan bacin ranne ya sanya Liman tattara kan zuri'arsa yace ya sallamawa Dalson Hajar ko mutuwa yayi bayason tazo kan gawarsa.
Tun daga wannan ranar komai ya qara lalace mana duk cikin yaran gidanmu mu biyar ni kadai nakeyin karatu shima wani Alh ne ya dauki nauyi na saboda nidin qawar yarsa ce Zainurah amma sauran qannena duk basa arabi basa boko sai tallan burkutu da Pappa yake dora musu sukai church.
Haka rayuwar tayita tafiya cikin qunci talauci da qangin rayuwa, a zahirance Pappa bayada mahaukacin talauci amma ya rantse daidai da ransa indai Addah batayi riddah ba to bazata qara samun tallafi daga gareshi ba itakuma tace ya riqe tallafinsa bata buqata.








Daqyar Addah tasamu ta dorani akan tarbiyyar islama saboda tanayi ne Pappa na warwarewa duk cikin yayan Addah ni da Aisha ne kawai mukebin addinin muslumci sai Ibrahim da naji lbrn shima ya musulumta yanzu.
Girma nakeyi sosai bana wasaba shekaruna goma sha uku duk wasu halittuna suka gama bayyana komai nawa na musamman ne, tun a lkcn samarin maza yayan masu halin garinmu suka rinqa kawomin caffa amma naqi domin zaman gidanmu ya dasamin tsoro da tsanar da namiji cikin zuciyata gani nakeyi duk wani namiji irin halin Pappa ne dashi sai gashi a hankali Taheer ka tabbatar min da zatona gsky ne ko babu bambamcin addini akwai zalumci tsakanin namiji da mace.








Komai ya fara lalacewa Pappa takai ta kawo an qwace church din dake hannunsa saboda neman matansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login