Showing 9001 words to 12000 words out of 14963 words

Chapter 4 - Man Of The World Book 3 end Writing by Real Eesho .txt

09 Jan 2025

2712

sallama ya tafi abunsa miƙewa Ummih tayi zata tafi Abbah yayi saurin riƙe haɓar hijabinta tare da cewa"ina kuma zaki tafi ki barni ".
ba tare da Ummih ta juyo ba wani kuka ya suɓucemata tare da cewa"ɗaki zankoma kaifa kacemun ka tsanemu sekaga bayana ni da ƴaƴana kaifa kace idan nasake matsowa kusa dakai seka kasheni kaifa kace sekaga ƙarshena zaman mezanyi a kusa dakai yazama dole in nisanceka".
a zabure Abbah yamiƙe tare da rungumeta suka fashe da kuka nan ya buɗewa su Inteesar hannu ba musu suka rungume mahaifinsu suka fashe da wani matsanancin kuka sosai suka bama Hauwah da Rahama tausayi seda sukayi me isarsu sannan suka zauna Khadija uwar azagwaigwai tashiga bashi labarin abunda yayiyyimusu wani mugun tausayinsu ne yayi mugun kamashi yayita kuka kamar ƙaramin yaro nan yabasu haƙuri suka yafemasa sannan suka shiga hirar duniya .


Suna shiga ɗaki Uwar Gwarama ta fashe da wani matsanancin kuka tare da nuna Jameelah da yatsa tace"shikenan kin cuceni kingama dani kin lalatamun komai hankalinki ya kwanta ƴar iska tsinanniya wallahi sede ke ki haukace badai ni ba jaka kawai kin lalatamun aikin shekara da shekaru garin sakarcinki ".
tasowa Uwar Gwarama Jameelah tayi a hassale tace"yakamata kibarni inji da rashin lafiyar dake damuna".
"iyeee wato dan ubanki har kinada bakin magana to wallahi bari kiji infaɗamiki tun wuri kije kinemo uban cikin dake jikinki ko jikinki yayi tsami".
"ki kira su Bahijja suzo muji yadda za'ah ɓullowa abunnan ingurin bokan zanu koma musa tayi tunda wuri domin wannan abun dake faruwa bekamata a tsaya sanya akanshi ba".
cewar Dagauta furzar da numfashi Uwar Gwarama tayi tare da cewa"toh".
nantashiga dialing number ƴaƴanta.


9:00pm
Aje wayar dake hannunta tayi ta buɗe plate ɗin dake gabanta ta ɗauki spoon ɗebi faten wake kenan zatakai bakinta taji an!!!!!!


Votes and Comments


_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow


_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 3


7⃣5⃣➡7⃣6⃣


Kaɓar da spoon ɗin hannunta yayi sanadiyyar haka abincikan dake gabanta suka tarwatse gabaki ɗayansu hankalin kowa na gurinne yadawo kansu murya naɗan rawa alamun firgici taji muryar Namijin duniya yace"haba Baby meyasa idan na hanaki abu bakyaji ne kinsan idan kikasha faten wake cikinki baya zama lafiya meyasa bazaki guji duk abinda kesaki cikin trouble bane".
sosai kalamansa sukayi matuƙar bawa Inteesar mamaki sosai ranta yakai ƙololuwar ɓaci ita aganinta wani sabon muzantata zeyi ta miƙe a fusace da niyyar barin gurin zuciyarta na tafarfasa wani santsi ya kwasheta zuuu ta tafi zata faɗi saurin rife lulu eyes ɗinta tayi domin tagama sadaƙarwa zatajita a ƙasa seji tayi tafaɗa jikin mutum koda bata buɗe lulu eyes ɗinta tasan jikin wanda tafaɗa ƙamshin daddaɗan turarensa ne yaƙara tabbatarmata da shine sakin wata ajiyar zuciya tayi me ƙarfi a hankali tashiga buɗe lulu eyes ɗinta dake manne da zara-zaran eye lashes ta saukesu akan kyakyawar fuskar Namijin duniya daya kafeta da manya-manyan idanunsa da suke kamar name bacci ko ƙiftawa bayayi iska ce tashiga kaɗawa abunka da garin damuna lokaci ɗaya suka shiga wani yanayi iskar dake kaɗawa ce tasanya dogon gashinta rifemata fuska bazato taji yasa lallausan hannunsa yayi baya dashi a zuciyarta tace"kai Allah ya zuba halitta anan gurin ashe da ni duk kallon tsoro nakemishi".
wata zuciyar ce tace"wannan wanne irin kallo kikemishi ne karfa kija yaƙara rainaki yazata mutuwa kikayi akansa yadda ƴammata keyi yaji daɗin takaki dolene kiyi controling ɗin kanki agun wannan ɗan rainin hankalin inba hakaba yadaɗa rainaki".
saurin kauda idonta tayi daka garesa tashiga mutsu-mutsu alamun ya saketa hannunta tasa akan nashi daya ɗora a ƙugunta tare saurin zame jikinta a nashi a kunya ce sakamakon haɗa ido da sukayi a da Ammih da shigowarta kenan ta dawo daka unguwa saurin ƙasa tayi da kanta tare da satar kallon dining ɗin gani tayi wayam bakowa hakan yabata tabbacin ganin yadda suka rungume juna ne yasa kowa na gurin barin gurin a kunyace tace"sannu da dawowa Ammih".
"yauwa ƴar albarka".
nan ta anshi jakarta da wata leda data shigo da ita ta tafi kaimata su bedroom ɗinta.


Murza hannunshi yayi dayasa a ƙugunta tare da sakin murmushin dabe shirya yinsa ba shinshina rigar jikinsa yayi yaji ƙamshin mayen turarenta yazauna kamar a jikinsa aka fesa karon farko dayaji yanason kara kasancewa da ita domin a wannan lokacin da suke tare jiyake dama su dawwama a haka da baze taɓa gajiya ba sauke ajiyar zuciya yayi tare da fara tafiya ɗaga idonnan dazeyi sukayi ido huɗu da Ammih sosa ƙeya yayi alamun jin kunya tare da cewa"barka dai Ammih mu yaushe kika dawo aida naɗauka zaki kirani in ɗakkoki ".
"ina zakasan da wata Ammih meɗan ido baɗan ciki kana can kana tsinko fure".
"hhhh kinji Ammih ni bara na wuce inaso inkwanta da wuri saboda 9 insha Allahu muntafi".
"hakane kam gwara kayi maza ka kwanta bara inje nima insa takwarata takwanta da wuri kar azo ana jiranta".
"toh seda safe".
"Allah ya tashemu lafiya".
nanya wuce ɓangarensa itakuma ta wuce bedroom ɗinta bata jimaba tafito hannunta riƙe da ledar da Inteesar tashigarmata ta nufi bedroom ɗin su Inteesar.





Kwance take akan gadonsu ba abinda take se aikin tinanin meyasa Namijin duniya ze kaɓarmata da abincinta zuciyarta ce tace da ita" ƙila wani sabon faifan rashin mutuncin ne wannan kai gaskiya akwai dalili tunda hakanan Namijin duniya baze firgita ba babu dalili gaskiya akwai dalili".
tana nan tana saƙe-saƙenta akan gado taji sallamar Ammih tashi tayi zaune tare da yin ƙasa da kanta tace"sannu da shigowa Ammih".
"yauwa ke kaɗai kike zaune ina Rahaman kuma?".
"tashiga toilet".
"toh".
"Rahama kiyi…".
"kyaleta kawai dama ai gurinki nazo ".
"toh Ammih Allah dai yasa lafiya".
"lafiya ƙlau ingo wannan ki shanye shi tas".
taƙarasa zancenta tana mai miƙawa Inteesar roba cike da tsumi ansa tayu babu musu ta buɗe robar ta shanyeshi tas sannan ta miƙamata wani abu data dama da madara a cup ta ansa ta shanye shima tas tana yamutsa fuska nan tayita bata magunguna kala-kala tana shanyewa sannan suka ɗan taɓa hira Ammih tayimata sallama ta tafi itakuma ta kwanta.


"Meemah anyako wani bega lokacin da kika zuba maganin nan ba kuwa yasanarwa da Abdallah nifa gaskiya ina zargin lokacin dakike zubawa wani yaganki batare da kingashi ba inba haka ba babu tayarda za'ayi Abdallah yayi reaction ɗin da yayi ɗazu".
"kewai Mummy meyasa kika cika nacin abu ɗaya ne nacemiki babu wanda yaganni kekuma kin nace nafi zargin ƙila ya hanata shan faten waken".
sauke numfashi Mummy tayi tare da cewa"hakane kuma hakan zata iya faruwa anyako wannan yarinyar ba wani abun suka yiwa Namijin duniya ba kuwa yake wannan rawar ɗuwawun akanta gaskiya da zancen ji".
"gashi narigada na juye maganin duka sede idan gobe muyi sammako gurin boka da wuri kinga idan muka samu taci maganin kinga shikenan ze tsaneta sekuma muyi wanda za'ah juyo da hankalinshi kaina".
"aiko dai gwara muje da wuri har na hangoki a spain ɗiyata".
nan suka shirya zasu tafi da wuri saboda Inteesar taci maganin kafin su tafi yafasa tafiya da ita.


Washe gari misalin ƙarfe takwas da rabi jirgin su Namijin duniya ya dira a!!!!!!!
MAN OF THE WORLD BOOK 3


Book 3


7⃣7⃣➡7⃣8⃣


Airport ɗin Spain suna sauka wasu haɗaɗɗun motoci masu tambarin MAN OF THE WORLD a jikin lambarsu suka kwashesu basu zame dasu ko inaba se unguwar My one tafiya kaɗan sukayi suka isa gaban wani tamfatsetsen gini me tsayi da alamu dai estate ne horn sukayi wasu kitika-kitikan majiya ƙarfine suka wangale ƙofar haɗaɗɗen get ɗin nan suka kutsa hancin motocinsu ciki seda sukayi tafiya me nisa sannan suka kewaya wani round about me photon butterfly yana zubar da ruwa a bakinsa sannan suka isa gaban wannan tanƙamemen ginin wanda ke liƙi da sunan Namijin duniya da farin haske yana juyawa liƙe da sunan parking motocin sukai a wadataccen parking space ɗin gurin sannan driver yajuya cikin girmamawa yace"Oga mun iso".
"okay".
nan drivern yafita yazagaya ya buɗewa Namijin duniya tare nufar ƙofar da Inteesar ke zaune ze buɗe muryar Namijin duniya yaji yace"kyaleta nizan buɗemata dakaina".
cikin ladabi yace"okay Sir".
nanya matsa tare da maida ƙofar da Namijin duniya ya fito ya rife cikin takun ƙasaita yazagaya ƙofar da take zaune yasa lallausan hannunsa ya buɗe handle ɗin haɗaɗɗiyar motar kawai bazato yaji yamiƙamata hannu batare data shirya ba ta miƙamasa hannunta nanta fito suka jera kamar wasu taurari suka nufi ƙofar katafaren estate ɗin batare da sun jira su Ahmad ba.


Ahmad dake liƙe da matarsa ne yayi gyaran murya Adam yajuya ya kallesa nuni yayimasa da Abdallah da Inteesar yace"Namijin duniya fa yariga da yagama zurmawa ba tare daya sani ba jibifa amma tsabar girman kai yakasa gane yana son matarshi ya tsaya yanata wani rainamana hankali".
"aini tun yaushe nagane yana sonta tun ranar daya hana kowa ya taɓa jikinta a Comphany nagane yana mugun sonta kana ganin yadda ya harzuƙa dakazo zaka taɓata zaka tabbatar da kishinta ne yasashi yin haka shiyasa tunda na lura nadena shiga tsakaninsu domin dukkansu suna matuƙar son junansu tsabar girman kaine yahanasu sanarwa da junansu saboda kowanne cikinsu ji yake da kanshi gani yake idan ya furtawa ɗan uwansa kamar ajinsa yagama zubewa".
"hmmm zama su sauke domin ƙila kafin mukoma gida ƙila sunzama romeo da juliet".
"Allah yasa idanfa suka jone suka tino abubuwan da suka riƙayiwa junansu kowanne cikinsu seya yiwa kansa dariya domin kowanne cikinsu girman kai ke ɗawainiya dashi".
nan suna tafiya suna magana har suka isa ƙofar dasu Inteesar suka shiga kowanne ya nufi ɓangarensa.


Suna shiga haɗaɗɗen falon part ɗin da suka shiga ta zube akan kujera sakamakon wani irin mugun sanyin dataji tanaji wucewa yayi gaban ɗaya daka cikin ƙofofin dake falon ya murza key ɗin dake jikin ƙofar ya buɗe ya kutsa kanshi cikin ɗakin wani haɗaɗɗen bedroom ne ya bayyana tsayawa faɗin tsaruwa dakin bata lokaci ne domin se inƙare labarinnan bangama ba komai na ɗakin fari ne tas hattana furnitures ɗin ɗakin farare ne aje system ɗinsa yayi akan bedside drower yashiga rage kayan jikinsa zuwa yayi gurin wardrobe ya buɗe yazari sabon towel ya tuɓe kayan jikinsa yashiga toilet ya sakarwa kansa ruwan zafi .


Tashi tayi daka kan kujerar da take domin harta fara gyan-gyaɗi ta nufi ƙofar dataga yashiga ta buɗe tashiga ta mayar ta rife aje handbag ɗinta tayi domin basu tafi da kayaba a cewarsa bazasu ɗakko komai ba ya siyamusu wani mugun fitsari taji tanaji ya matseta da sauri ta nufi ƙofar data gani a ɗakin ta tura ba tare datayi knocking ba tafaɗa da gudu sakamakon jin datayi kamar fitsarin ze zubomata cin karo tayi da Namijin duniya dake tsaye gaban shower yana wankansa ba kaya a jikinsa kwalla ƙara tayi tsabar gigicewar datayi sakamakon bata taɓa ganin babba mutum kamarshi ba tsirara a tamanin ta juya zata koma jikinta se rawa yakeyi kamar mazari taku ɗaya yayi ana biyu ya cafkota tafaɗa jikinsa murmushin gefan baki yayi tare da cewa"ina zaki bakiga abinda kikazo gani ba bari in nunamiki badai wannan kikazo gani ba".
yaƙarasa zancensa tare da juyo da ita suna fuskantar juna saurin rintse ido tayi jikinta na tsuma bakinta na ɓari tace"dan Allah kayi haƙuri wallahi bansan kana ciki ba naɗauka kafice shiyasa na shigo kaina tsaye ba tare danayi knocking ba dan Allah kayimun rai wallahi bazan sakeba".
taƙarasa zancenta bakinta na rawa murmushin ƙeta Abdallah yayi me sauti tare da cewa"aiko yarinya ba inda zaki sekinga abinda kikazo gani atoh gwarama ki tsaya ki kalla domin ba inda zaki".
haƙuri tayita bashi saboda tsabar tsoratar datayi jikinta ko ina rawa yakeyi ƙuramata sexy eyes ɗinta yayi yaga yadda dukta tsure se jikinta ke ɓari gani yayi rigar jikinta dukta ɗameta har ana ganin nipple ɗinta dake babu braziyya jikinta kafe tsayyayun breast ɗinta yayi da ido tare da cewa"idan kinaso inkyaleki sede ki haɗani da friends ɗina".
"faɗamun suwaye inhaɗaka dasu ko su waye nidai fatana kabarni intafi dan Allah Yah Abdallah".
jin wani abu yayi tundaka tsakiyar kansa har ƙafarsa ya tsirgarmasa lokaci ɗaya yaji tsigar jikinsa tashi wata irin muguwar sha'awarsa ta motsa sakamakon jin yadda takira sunanshi jiyayi kamar duk duniya ba wanda yakaita iya faɗar sunan matseta yayi a faffaɗan kirjinsa dake yalwace da kwantaccen gashi wata uwar ajiyar zuciya suka sauke a tare hannunsa yasa ta tsakankanin ƙirjinsu yashiga ɓaɓɓale bottle ɗin jikin rigarta ya ɓallesu duk yayi wurgi da rigar gefe tare da janta jikinsa yaƙara matseta a ƙirjinsa yashiga sauke ajiyar zuciya akai-akai wani mugun tsoronsa ne ya dirarmata murya na rawa alamun yana tsananin buƙace yake da ita ya shafa boob ɗinta guda ɗaya tare da cewa"kingansu nan sune friend ɗin nawa kina haɗani dasu mukaɗan gaisa zan sakeki".
"nidai a'ah dan Allah kayi haƙuri Allah nason masu yafiya wallahi bazan sake ba ka kyaleni banaso fitsari nakeji sosai wallahi kafita dan Allah zezubo".
taƙarasa zancenta tanamai fashewa da wani matsanancin kuka tana kakkare jikinta da hannunta murmushin ƙeta Abdallah yaƙarayi tare da cewa"kiyi fitsarinki man na hanaki ne?".
"to kafita inyi babu kyau mutum yakalli tsiraicin wanifa".
"hmm sekuma akacemiki harda miji da mata ne bakyau ɗin ba inda zani aini kika tarar bani na sameki ba".
yaƙarasa zancensa yana mai shafa hips ɗinta shiru tayi ta lamfacesa ta duƙa kamar zata tsugunna ta kwasa a guje ta buɗe ƙofa tafice a tamanin jiyayi wata uwar dariya ta kuɓucemasa yayitayi seda yayi me isarsa sannan yayi wankan tsarki sannan yafara wankan sabulu.


Bata tsaya ko inaba se a cikin ɗayan bedroom ɗin tana shiga ta murza key ta nufi toilet a tamanin tayi fitsari tafito tazauna akan gado tare da cewa"wash Allah na kajini daɗan duniyar mutumi da Allah anyako Namijin duniya ba ɗan iska bane anyako Namijin duniyar dana sanine me baƙin girman kan tsiyarnan ne kuwa gaskiya da sakal dole indena fitowa muhaɗu dashi tunda dai shi bashi da kamun kai ko ba'ah kulashi ba shi seya kula mutum haba ina dalili gaskiya wannan matarshi tashiga uku da ƙunata irinsune basa ɗagawa matansu ƙafa".
zuciyarta ce tabata amsa da"ai kece matarsan dakike cewa".
a zabure ta miƙe tare da cewa a fili "Allah ya kyauta inzama matar wannan kwazababben mutumin".
rashin me bata amsa yasata tayita tufka da warwara domin al'amarin Namijin duniya baƙaramin tsoro yabawa Inteesar ba ta yanke hukuncin bazata sake yadda su haɗu dashi ba ko abinci ne se bayanan zata fito taci.


12:00am
Sanye da burmemen hijabi tafito tana sanɗa ta zauna akan kujera ta jawo center table ɗin dataga ledar restuarant akai ta buɗe gani tayi friedrice tayi da kaza sekuma spoon da pork nantashiga ci seda ta cinye tas domin baƙaramin yunwa takeji ba sakamakon taƙi fitowa taci abinci saboda jin motsin Namijin duniya datayi a gidan tana gamawa ta ɗauki ledar da take away ɗin tasaka a dustbin sannan ta buɗe wata ƙofa da take tinanin kitchen ne tashiga gani tayi shiɗinne gani tayi ko ina fes-fes dashi ba ƙura taɓe baki tayi tare da cewa"kamar gidan mutumin arziƙi mutum se ɗacin ran tsiya".
sannan ta wuce ta buɗe deap freezer wow tafurta domin maƙare yake da kayan alatu ruwa taɗauka sekuma inibi data zuba a cikin plate ta maida pridge ɗin ta rife ta leƙa store ɗin jikin kitchen nanma ta girgiza kai tare da cewa"Allah mungodemaka jibi komai na gidannan kamar baza'ah mutu ba".
nan tayita santinta domin komai na gidan ya burgeta tana juyawa yiff aka ɗauke wuta duhu ne gabaki ɗaya ya kauraye gurin lokaci ɗaya wani mugun tsoro ya dirarmata da lalube ta buɗe ƙofa ta fita a tsorace tana laɗube harta isa tsakiyar babban falon taji wani abu ya zubomata a jiki ɗaga idonnan da zatayi tayi arba da!!!!!!!


Votes and Comments


_*Daga Alƙalamun ƴar Mutanen Gwarzo.*_# Real eeshow


_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 3


7⃣9⃣➡8⃣0⃣


Wani jan haske ya haskamata mutum a duƙe yayi kneel down a mugun tsorace ta wurgar da kas ɗin data zubo inibi zata zura da gudu taji an riƙe hannunta gani tayi wani haske me colours ya bayyana juyawa tayi dan ganin wanene arba tayi da kyakyawar fuskar Namijin duniya hannunsa ɗaya riƙe da jar flower mamaki ne ya mugun kamata bata gama mamakin da takeyi ba taji yace"Inteesar ina sonki ina ƙaunarki tun ranar dana fara ɗora idona akanki na tabbatar da nasamu mahaɗin rayuwata uwar ƴaƴana inasonki so na haƙiƙa akanki nafara so akanki na rifeshi akanki nafara tinanin wata ɗiya mace akanki na rifeshi kidaure kisoni koda rabin son da nakemiki My 100% sure I love you with all my heart".
yaƙarasa zancensa tare da miƙamata rose flower dake hannunsa wasu zafafan hawayene suka shiga zarya a kumatunta ta rasa dalilin yin kukan domin ko a mafarki bata taɓa tinanin mutum me dukiya da daraja da muƙami irin Namijin duniya ze iya duƙamata ba har ƙasa ba tarasa gane kukan me takeyi kukan farinciki ko na baƙin ciki .


Murya a raunane yace"idan bakya sona Aishatu karki takurawa kanki kifaɗamun insha Allahu kamar yadda nayiwa zuciyata alƙawarin nemowa taki zuciyar farinciki to a wannan karonma zanyi ƙoƙarin nemomata koda zan rasa raina saboda sonki tun kina ƙarama nake dakon sonki dan Allah karki ce bakya sona".
bazato yaji tafaɗa jikinsa ta fashe da wani matsanancin kuka ruɗewa Namijin duniya yayi sakamakon kukanta da yakeji har cikin zuciyarsa be hanata kukan da takeyi ba saboda shima da ze samu hawaye su zubomasa dazeji daɗi saboda seda tayi me isarta yana ɗan bubbuga bayanta alamun rarrashi sannan tayi shiru murya a dishe tace"duk duniya Yah Abdallah ba macen da zata ganka tace batasonka ina sonka nima so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login