Showing 6001 words to 9000 words out of 14963 words

Chapter 3 - Man Of The World Book 3 end Writing by Real Eesho .txt

09 Jan 2025

2809

dan Allah inma wasa kakemun Muhseen dan Allah na roƙeƙa kadena dan Allah kadenamun irin wannan wasan banaso insha Allahu bazakayi dana sanin sanina ba da izinin Allah".
juyawa Muhseen yayi ya wurga mishi wani banzan kallo cikin takaici yace"kanka zaka tambaya wannan kuma domin ni bani da lokacinka".
yana gama faɗar haka ya juya yafice da sauri a fusace binsa da kallo Zaid yayi ya zabura ya miƙe kamar wanda aka tsikara murya kamar zeyi kuka yace"Abbah menayiwa Muhseen ne haka yake tsananin fishi dani Mummy nakasa gane meke faruwa dan Allah ku sanar dani ko zuciyata tasamu salama ".
yaƙarasa zancensa hawaye na zarya a kumatunsa a taɓe baki Abbah yayi tare da cewa"inma zaka dena rainawa kanka hankali ka dena domin mu bamu kake rainawa ba kanka kake rainawa".
Abbah yana gama faɗar haka ya haye sama bin bayansa Mummy ma tayi itama domin gani sukeyi raina musu hankali kawai yakeyi gurin ya rage dagashi se Maryam da duk tsananin tausayinsa yakamata takasa koda kwakwaran motsi shiru ne ya biyo baya naɗan wani lokaci kowanne cikinsu yana sakawa da warwara ita tana tinanin tayadda zata fara ganar da iyayensu abinda ke faruwa shikuma yana tinanin meyayiwa babban amininsa da iyayensa da har sukayi fishi dashi haka jiki a sanyaye ya miƙe tsaye yafara tafiya yana haɗa hanya saboda har wani duhu-duhu yake gani sakamakon kukan da yakeyi kamar ƙaramin yaro sosai yabawa Maryam tausayi ta nufi ɓangaren mahaifiyarsu jiki a sanyaye.


Kamar wani ɗan shaye-shaye haka ya isa ɓangarensa yana zuwa ya zube akan 3seater tare da fashewa da wani matsanancin kuka bazato yaji anfaɗa jikinsa cikin ƙissa gami da shagwaɓa tashiga cewa"Babyna daka cewa yanzu zaka dawo shine kaje kayi zamanka ko idanba………".
batakai ga ƙarasa maganarta ba taji anɗauketa da wani gigitaccen mari wanda har seda tafara ganin taurari anyi wani wurgi da ita kanta ya bugu da center table ɗin ɗakin jini yafara zuba cikin kakkausar murya me nuna yana cikin tsananin ɓacin rai ya nunata da yatsa yace"kee wacce irin dabbace ne ke mara tinani da zaki faɗowa mutumin daba maharraminki ba a jiki sau nawa zanmiki warning ne kanki fita sabgata ne ko matan sunƙare bazan taɓa sonki ba ballagaza kawai mara kamunkai a haka za'ah sokin baki san darajar kanki ba ko tinkiya bazatayi abinda kike ba koda yake jahilci ke damunki kifitarmun a sashina tunkafin wani yaganki ƴar iska kawai mebin maza Inteesar ɗindai da kuka tsana ita nake so ita takwanta mun sede ku mutu idan mukayi aure ".
kuka Jameelah ta fashe dashi tare da ɗora hannu aka tace"wayyo Allah na wayyo ze kashe ni mejan kunne shikenan wannan tsinanniyar ta rabani da mijina ko kwanan wata ba'ayi ba ".
wani banzan kallo Zaid ya watsamata da rinanun idaninshi da suka canza kala cikin ɗaga murya yace"ubanki ne mijin naki tsinanniya bara inzo in sassaɓamiki kamani kya faɗi mijin naki tinkiya ko kunya bakwaji ke da uwar me siffar agwagwa ku rasa wadda zakuyiwa hassada se ƴar uwarki kunyi asara".
yayi kanta ganin ya nufi kanta gadan-gadan ze maƙureta ƙara ta kwanyara hakanne ya jawo hankalin Mummy tayo ɓangaren hankali tashe samun Zaid tayi ya maƙure Jameelah a bango ƙananun idanunta duk sun tutturo tanata hawaye saurin ƙarasawa tayi da gudu ta cire hannun Zaid tace"haba Zaid karka kashe Nisful-hayat ɗinka man matarka cefa Jameelah matar so wadda tasa ka rabu da kowa naka saboda tsananin son da kakemata karfa kamanta farincikinka ce wadda kakemun iƙirarin da zaka iya rabuwa da kowa kanta".
"bangane ba Mummy wai meyake faruwa ne ni kuna sani a duhu wallahi dan Allah ku sanar dani".
muryar Maryam yaji katsam tashiga zayyanomasa labarin duk abinda yafaru tun daka ranar da yace bayason Inteesar Jameelah yake so har zuwa ranar ba abinda Zaid keyi se aikin kuka murya a dishe yace"yanzu kenan Maryam kina so kicemun na wulaƙanta masoyiyita ta haƙiƙa farincikina abar alfaharina da kowa nawa kan waccan dabba ".
yaƙarasa zancensa tare da yin kukan kura ya cafki Jameelah yayi bedroom ɗinsa da ita ya kulle ƙofar yasa key yashiga jibgarta kamar Allah ya aikosa seda yayimata shegen duka sannan cikin daga murya yace"na sakeki saki 1 na sakeki saki 2 na sakeki saki 3 uku Allah ya isa tsakanina dake kin rabani da komai nawa wallahi sena kasheki kamar yadda kika rabani da farin cikina dan kutumar ubanki".
jin abinda yake ƙoƙarin yine yasa su Mummy tsurewa suka buɗe wata loka dake kusa dasu suka ɗauki spare key suka buɗe suna buɗewa Abbah ya ɗauke Zaid da wani wawan mari a hassale yace"kashe ta zakayi ne".
durƙushewa Zaid yayi a gurin yana kuka sosai yaba kowa na gurin tausayi domin Maryam ta sanar dasu komai nan Maryam ta ɗakko ruwa aka yayyafawa Jameelah datayi suman wucin gadi tana farfaɗowa tasaki wata uwar ƙara tare da cewa"wayyo ze kasheni Ummah na kizo ki temakeni dama seda kikace kar inbari wani yaga lokacin da zan yarfa maganin boka yabayar to gashi ya kwaɓemun mejan kunne na ƙoƙarin kasheni nashiga ukuna kizo ki temakeni Ummah……".
kasa ƙarasa maganarta tayi sakamakon jin muryar Mummy na cewa"Allah dai ya tsinemiki tsinanniyar yarinya ki cutarmun da rayuwar ɗana kin rabashi da farincikinsa Inteesar Allah ya isana bazan taɓa yafemiki sha Allahu sekunga ƙarshenku keda uwarki ".
Muhseen dake zubarwa da abokinsa hawayene ya rungume Zaid dake kuka kamar ƙaramin yaro yashiga bubbuga bayanshi alamun rarrashi a zabure Zaid ya zame jikinsa ana Muhseen yayi kan Jameelah da gudu ta nufi hanyar ƙofa mayafi babu ruga a guje tana haki tana kwara uban amai.


Ɓangaren Inteesar ko zaune take akan 1seater tana bin karatun alqur'ani megirma ƙira'ar Sudais cikin takun ƙasaita yake tafiya har ya ƙarasa shigowa falon murmushin ƙeta Namijin duniya yayi ganin yadda taci uban gayu tana jiranshi zama yayi akan kujerar dake passing ɗinta tare da!!!!!!


NOT EDITING


Votes and Comments


_*Daga Alƙalamun ƴar mutanen Gwarzo.*_r Mutanen Gw# Real eeshow


_*Paidbook,Amount Nml grp 300,Vip 800,pc 1k, Account Detail 2411022356 Aisha Umar Ibrahim Zenith Bank, or Vtu mtn or airtel ga ƴan Niger kuma zaku turo da katin Airtel na daidai kuɗin da kikeson shiga aiko da shedar biyanka/biyanki ta wannan number 08108362334.*_


Book 3


7⃣1⃣➡7⃣2⃣


Ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yayi tare da yasakin wani ƙasaitaccen murmushin ƙeta wayarshi dake kusa dashi ce tafara ringing dubawa yayi tare da ɗaga wayar yakaita kunnensa tare dayin shiru daga ɗaya ɓangaren akace"My man ina ka shigene tunɗazu muke kiranka wayarka a kashe ko dai amaryar ce ta ɓoyekane kanata kwasar gara dan nasan irinku muskilannan badai naci ba musamman da kuka kasance farin shiga a sabgar zakuyi zumuɗi sosai idan kuka lula duniyar ko ya kace Ahmad".
"gaskiya ne adaibi yarinyar mutane a hankali atoh kar ajimata ciwo".
cewar Ahmad dake kusa Adam sunawa Namijin duniya dariyar shaƙiyanci ta wutsiyar ido Namijin duniya yasaki kallon Inteesar data wani basar dashi kamar batasan yana gurin ba karaf sukayi four eyes da ita itama tana satar kallonshi a tare suka ɗauke kansu murmushin gefan baki Namijin duniya yasaki tare da yin ƙasa da murya yayi gutun tsaki kamar bayason yin magana yace"ku wannan abun ya dama dahar kuke zancenshi aini koyi zanyi bazanyi da ƴar shilar nanba domin tayimun ƙanƙanta kudai da zaku riƙa zubar da girmanku sekuyi tayi Allah ya shiryeku gemai-gemai daku kuriƙa zubarmana da mutunci a gurin ƴaƴan cikinmu ".
"Ameen ya Allah dama haka mukace bara mukiraka muji yadda tafiyar zata kasance idan da wuri zamu wuce mu sani dan muyi settling ɗin komai namu akan lokaci hmm My Man kenan bazaka gane bane se ranar da faɗa komar Intee zakaga muna zubar da girmanmu".
"eh da wuri zamu wuce kamar 11:00am haka ".
a hansfree yamaida wayar yashiga ɗaura tamfatsetsen agogonsa a hannu daga ɗaya ɓangaren Adam yace"okay zaka zo muɗanyi exercise ɗinne ko kuwa mun kwana biyu bamuyiba".
saurin kallonsa Inteesar tayi alamun tana son jin abinda zece karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna saurin ɗauke kansa yayi tare da sakin murmushin ƙeta yace"zani kujirani yanzu zan ƙaraso mutafi".
damm gaban Inteesar yabada a zuciyar tace"amma gaskiya idan bamuje gidannan nayi sallama ba bakayimun adalci ba taya seda na shirya na sanar da zanzo zakayimun haka ai wannan rashin sanin darajar ɗan adam ne".
nanta shiga tufka da warwara domin baƙaramun ɓatamata rai yayi ba lokaci ɗaya fuskarta ta canza alamun ɓacin rai suka bayyana shiko ganin yadda lokaci ɗaya yanayinta ya canza baƙaramun daɗi hakan yayimasa ba ranshi fes yasaki jiki suka ɗan taɓa hira har sukayi sallama batasani ba tana can tana zancen zuci.


Yana aje wayar Ammih da Rahama na sakkowa daga stairs suna ƙarasawa suka zauna akan kujera kallon inda Namijin duniya yake Ammih tayi tare da cewa"idan kunje da Allah kuce ana gaidasu dakyau dakyau anzuba kaya a cikin boot dasu zaku tafi".
miƙewa Namijin duniya yayi kamar gaske ya kalli agogon dake hanunsa tare da cewa"Ammih dama yanzu aka kirani daka comphany zamuyi wani meeting na gaggawa sannan zansa hannu akan wasu takardu yanzu nake shirin hawowa in sanar dake inba damuwa ko Shafi'uh driver yakaisu koda gobe da safe ne naje nayi musu sallama naso mutafi tare wallahi".
sakin baki Inteesar tayi tana kallonshi saboda uwar ƙaryar daya yanko a gabanta fakaitar idanunsu Ammih yayi ya kashemata ido ɗaya ya ɗagamata gira alamun yakika gani murmushi Ammih tayi tare da cewa"bakomai Allah yakaimu sesu tafin".
"yauwa Ammih sena dawo".
"toh muje nayimuku rakiya".
"toh ".
nan suka miƙe yayi gaba sukabi bayanshi har gurin mota suka rakasu dan aga yana tattalinta yayi saurin buɗemata mota mota tashiga yanata nan da ita yamayar da marfin motar ya rife tare da ɗagamata hannu kamar gaske be dena yimata bye-bye ba da sakarmata ƙasaitaccen mumrmushi ba har seda suka fice daka gidan sannan yayiwa Ammih sallama yashiga haɗaɗiyar motarsa ƙirar roice-roice yafice a tamananin.


Suna isa Shafi'uh driver yafio da sauri ya buɗemusu ƙofa cikin girmamawa yakira wasu yara da sukazo wucewa ya buɗe boot ɗin motar da sukazo da ita dake shaƙe da abun arziƙi yace"dan Allah kuɗan shigarmana da waɗannan kayan cikin gidannan yanzu wata motar ma zatazo dan Allah kuɗan shigarmana".
yaƙarasa zancensa yanamai nuna musu gidansu Inteesar dake buɗe nan yaran suka shiga ɗibar haɗaɗɗun super holland ƴan ubansu da shaddoji da materials,lesuka kala-kala suna shigarwa gidansu Inteesar.


Ummih na alola a wajan mazarariyar ruwa yara suka yi sallama suka fara shiga da kaya sosai mamaki yakamata cikin sanyin daya zamemata jiki tace"bayin Allah waya turoku da waɗannan kayan".
"wani mutumi ne a waje yace mu shigo dasu".
"gaskiya banan gidan bane ku koma ku ƙara tabbatarwa domin gaskiya banajin nan gidan aka aikoku".
"kai kawo su nan ɗan albarka lallai Amina wato dan kinsan ƴarki almajiri take aure shine sabosa mugu abu iri naki zakice a juya dasu nidai narasa wacce irin ƙiyayya kikemun nida ƴaƴana ƴar baƙinciki sede ki mutu to daka gidan Jameelah suke ya ranki ai indai wannan baƙin halin naki zaki cigaba dashi sha Allahu tun a duniya zaki riƙa ganin ƙarshenki keda ƴaƴan naki arziƙi sede ku kalla a wani gurin indai mugum abune cinikinki ayyiriri Dagauta ku fito kuga kaɓakin arziƙi daka gidan ƴar albarka wadda takai darajarta gidan mijinta".
nan tashiga kwakwazon buɗa tana rawa tana sakin habaici domin kaya bana wasa ba aka shishishigo dasu Uwar gwarama jikinta se tsuma yake taga kayan alatu se buɗa takeyi ita da ƴar korenta Dagauta .


Suna niyyar shiga gida Jameelah ta bungujesu a tamanin se waige-waige takeyi tanayi tana kuka saurin taɓata Inteesar tayi tare da cewa"Jameelah lafiya".
wata uwar harara ta bankawa Inteesar tare da wucewa fuuu Jameelah ta wuce ko takan Inteesar bata bi ba tayi wucewarta taɓa Inteesar Rahama tayi tare da cewa!!!!!!!
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels


WhatsApp Number: 08138873799




Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************






MAN OF THE WORLD BOOK 3


Book 3


7⃣3⃣➡7⃣4⃣


"Aunty anya ko wannan ba mahaukaciya bace naga kina mata magana ko kulaki batayi ba sema wurgamiki harara danaga tayi anya ko ba mahaukaciya bace ba kuwa dubi fa yadda ta bangajemu ko haƙuri bata tsaya tabamu ba sema harararki danaga tayi wacece itan wai wacece?".
cikin sanyin muryar daya zamemata jiki tace"ƙanwata ce ubanmu ɗaya sunanta Jameelah".
"Jameelah kuma badai wadda ta auri Zaid ɗin Abbah berister ba naga ko lulluɓi babu a jikinta anya ko ba wani abunne yake faru ba kuwa".
"nima abunda nake tinani kenan muje ciki muji".
"toh".
nan suka cigaba da tafiyarsu.


Jameelah nashiga ta faɗa jikin Uwar gwarama daketa gaɗa a tsakar gida ta fashe da wani matsanancin kuka hankali tashe Uwar gwarama da dagauta sukace"lafiya Jameelah kike wannan kukan ko duk kaɓakin arziƙin da mijinki yakawo manane yasaki yin kuka ne".
cikin muryar kuka Jameelah tace"nashiga uku na lalace mejan kunne yasakeni saki uku yayimun shegen duka dakyar na ƙaraso nan gidan Ummah".
"bangane ya sakeki ba lafiya".
"mijina ya sakeni Ummah dakyar aka kwaceni a hannunsa".
gaban Uwar gwarama ne ya yanke ya faɗi sakamakon tino da sharaɗin boka tashiga bin ko ina na jikin Jameelah da ido murza ido tayi ta buɗe tagadai dagaske abinda idanunta keganemata haka yake ta buɗe baki zatayi magana kenan su Inteesar sukayi sallama ɗaga idonnan da Uwar gwarama zatayi taga wasu kamar Inteesar kamar kuma wata balarabiya domin baƙaramin canzawa tayi ba hutu yazauna ga sanyin a.c dayafara zamemata jiki Hauwa'uh da Khadijah ne suka fito da gudu daka ɗaki suka rungume Inteesar tare da cewa"oyoyo oyoyo sannu da zuwa Inteenmu".


Daskarewa Uwar gwarama da Dagauta sukayi sakamakon jin abunda kunnuwansu ke jiyemusu kusan suman tsaye sukayi buɗa Hauwa'uh ta rangaɗa tare da yin dariyar shaƙiyanci tace"Allah yayarda raƙumi yaci ƙaya zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho seyayi duk wanda ya riƙe Allah da manzonsa baze taɓa taɓewa ba waiwai bahaushe yayi gaskiya daya ce me haƙuri shike dafa dutse ya nuna luguf har yasha romonsa Inteesar ɗin dai da kuka tsana itace dai a sama nagaba yayi gaba na baya se labari dama ban faɗamiki ba yau gashi ranar da ake gujemuku tazo wa'inda kuke ganin bakomai bane yanzu sune komai ga gara nan ankawo daka gidan almajirin da ake cewa".
muƙut Uwar gwarama ta haɗiyi wani abu daya zo ya tsayamata cikin masifa tace"abunda baze taɓa yiwuwa ba kenan wallahu nasan duk wannan kutunguilar da munafuncin yana gurin Umaru bari Malam yashigo duk wadda za'ayi sedai ayi domin wallahi aurennan se an rabashi sede ayi mutuwar kasko wallahi kowa ma ya rasa nasan wallahi jifana akayi dole a raba tsinanne aurennan dan banga amfani haɗa zuri'ah da irin rashin tarbiyya ba".
batakai ga ƙarasa magana ba Jameelah dake jikinta a lafe ta zame jikinta da sauri tashiga kwara amai kamar zata amayar da ƴan cikinta lokaci ɗaya fita hayyacinta ruwa Dagauta tabata ta kurkure bakinta dashi takoma gefe tana maida numfashi tsorone ƙarara ya bayyana a fuskar Uwar gwarama ta ƙure Jameelah da ido.


Dariya Khadija ta tintsire da ita tare da kama hannun Inteesar tace"muje ko Mrs Namijin duniya mun barku a tsaye muntsaya kallon manyan Malamai da suka yankewa tarbiyya cibiya ko dayake duk cikin tarbiyyar ce aka samun sakamakon ɗan dakan kuka".
"hhh result ne yafara fitowa aidama haka Allah yake ikonsa wani hanin ga Allah baiwa sunyi ƙulunbotonsu Intee ta rasa Zaid segashi Allah ya musanyamata da mafiyinshi a hayye ɗus mahassada sede su mutu kinji wai jifanta akayi".
"hhh aidama abinda mutum yakeyi gani yakeyi kowa ma shi yakeyi ansaba bin bokaye da ƴan tsubbu dole ayi tinanin muna shi mukeyi Allah yakawo Abban lafiya kun rigada kun makaro anrigada an ɗaura aure sede haƙuri Allah ne ya gwadamuku ikonsa ".
"kewai Khadija wanne irin kunnen ƙashi ne dake ne wallahi inbakiyi shiru nazo nan sena tattakaki ki tsaranki ne".
cewar Ummih dake fitowa daka ɗakinta bata kaiga rife baki ba sukaji sallamar wani mutumi ya riƙe kafaɗar Abbansu Inteesar amsa sallamar sukayi gabaki ɗaya bazato Ummih taji muryar Abbah yace"Aminatu ɗakko tabarma ki shimfiɗa".
baki buɗe Ummih ke kallon Abbah domin rabon daya yimata kallon arziƙi ko maganar arziƙi ta haɗata dashi har ta manta lokaci ɗaya wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri a kumatunta ta rasa kukan farinciki takeyi ko na baƙin ciki tsunduma tayi a duniyar tinani tana ko kwanton anya ko ita yake nufi kuwa tana tsaka da tinani taji ya sake cewa"kin barmu a tsaye Aminatu tinanin mekikeyi ne haka dahar kike lafiya".
saurin share hawaye Ummih tayi tare da cewa"toh bara inɗakko".
nan ta tafi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki tana tafiya tana tinane-tinane domin rabon data shiga ɗakinsa tin tanada cikin Khadija shima yana ƙarami kama ƙugu Uwar Gwarama tayi tana jijjige-jijjige alamun rashin mutunci cikin ɗaga murya menuni da bada umarni tace"Malam menake gani ne haka ina zata ne baka ganin abinda wannan baƙin munafunkin ɗan uwanaka ya……".
kasa ƙarasa maganarta tayi sakamakon ganin wani banzan kallon da Abbah ya watsamata ba tare daya ce da ita ƙala ba yaƙara tsare gida yadawo asalin Malam Ibrahim ɗinshi jikinta ne yafara ɓari sum-sum takama hannun Jameelah sukayi ɗaka .


Shimfiɗamusu tabarma Ummih tayi mutuminnan ya zaunar da Abbah tare da kallon su Ummih yace"mun idar da sallah ya tashi ze tafi akaga ya yanke jiki yafaɗi shine na rakoshi".
gaidashi Ummih tayi nan ya amsa yayimusu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login