Showing 15001 words to 17050 words out of 17050 words

Chapter 6 - YANCIN BAYI Book Complete Document .txt

None   

13 Dec 2024

2106






*STORY WRITTEN BY*✍🏻


*SURAYYERH B.ABDUL*


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






Page d'innan kyauta ne gareki *MUNAYAH* ta Kainuwa fitatttu,ina ganin comments d'inki kuma yana sani nishad'i,godiya tik'a tik'a.








*PAGE 12*






Wata kuyanga ce tayi sallama ta shigo parlour'n,cikn girmamawa ta zube a k'asa ta ce "Ranka shi dad'e yarima Yusufu ne ya ce yana so a mashi iso wajen ka",sai da ya b'ata lokaci kamar ba zaiyi magana ba sannan ya ce "A shigo da shi",godiya kuyangar ta yi sannan ta fice.




Da sallama yarima Yusufu ya shigo fuskarsa d'auke da murmushin da ya zame masa jiki, tasowa yarima Sameer yayi sukayi hugging juna cikn farin ciki,zama sukayi a had'ad'd'un kujerun da suka yiwa parlour'n k'awanya, yarima Yusufu ne ya kalli wajen da gimbiya Jalila take tana cin abinci,cikn tsokanarsa ya ce "Ahhh matar prince don kar na ce zan ci abincin ne ya sa aka k'i yimin magana?,tab'e baki ta d'anyi kafin ta yamutsa fuska,murya k'asa² ta ce "ya kake?, ba yarima Yusufu kad'ai ba kaf d'insu sun ga abin da tayi,amma dayake me sanyin hali ne shi kawai sai ya basar ya ce "ina lpy",.




Mik'ewa tayi tareda k'arasawa kusa da yarima Sameer tana wani iyayi ta ce "My prince zan je gidansu yarinyar can ynz",ta fad'a tana nuna Muwadda wacce ta juya bayanta tana kwashe kayan abinci, ba'a ganin fuskarta ta b'angaren da su yarima Yusufu suke,shiyasa ma sam bai ganta ba.


Yarima Sameer ya ji haushi da tayi masa maganar a gaban yarima yusufu amma ganin yarima yusufu'n ya sa ya gyad'a mata kai kawai alamun to,peck tai masa a kumatu kafin ta fice.




Juyowa Muwadda tayi da niyyar kai kaya kitchen, karaf suka had'a ido da yarima Yusufu,ta d'an tsorata da ganin shi don tana tsoron ya ja mata fitina,shiyasa tayi saurin kauda kanta ta fara tafiya,yarima yusufu da gabad'aya ya d'imauce da ganin Muwadda,wani irin abu yake ji yana fuzgarsa da k'arfin gaske game da ita,zuwa ynz ya tabbatarwa kansa zuciyarsa son Muwadda take yi,kuma da k'arfin gaske,shiyasa ya d'aura d'amarar d'auka tare da rungumar duk wani tashin hankali da zai tunkareshi a hanyarsa ta mallakar ta ,saboda ya riga ya sani ba k'aramin tashin hankali za'a yiba da mahaifan shi a matsayinsa na yarima yace wai zai auri baiwa,tab'osa d'in da yarima Sameer yayi ne ya sashi juyowa da sauri yana murmushi,shi ma yarima Sameer d'in murmushi yayi cikin k'aunar k'anin nasa ya ce "yadai?",sosa k'eya yarima Yusufu yayi kafin ya d'aga ido sama cikin shaukin soyayya ya ce "Wlh ina matuk'ar k'aunar ta",da sauri yarima Sameer yace "Wa kenan?",batare da ya bashi amsa ba ya juyo ya rik'e hannuwansa duka biyun ckn raunin murya yace "Wlh komai zan iya a kanta shiyasa nake tausayawa kaina,ban san cewa haka zafin so yake ba sai a kanta,don Allah yayana inason idan lokaci yayi ka taimake ni ka jajirce wajen ganin na mallake ta, shi ne mafi girman so da za ka nunamin a rayuwata saboda ita ce rayuwata".


Cikin tsokana yarima Sameer ya ce "Tabd'ijan!,wace ce wannan k'atuwar b'arauniyar da take neman rikitamin k'ani haka?,kuma y'ar wani sarki ce da kake tunanin aurenta zai zo maka da matsala?.


Mikewa yarima Yusufu yayi tare da riko hannun yarima Sameer ya mik'ar da shi sannan ya ce "za ka santa yayana da zarar lokaci yayi,sai dai abu d'aya da zan fad'a maka shi ne yarinyar ba y'ar gidan kowa bace face y'ar talakawa,talakwan ma fitik,shiyasa nakeson ka tsayamin akan aurenta,wani irin kallon tausayi da mamaki yarima Sameer yakebin yarima yusufu dashi,kafin yace "Amma dai k'ani na da wasa kakeyi ko?,y'ar talakawa fa kace?,Shiru yarima yusufu yayi,sbd haka yarima Sameer yaci gaba da magana,"a gaskiya kusan zan iya cewa zuciyar ka batai maka adalci ba da tarasa wadda zataso sai y'ar talakawa,meye haka?kana hauka ne?,to wlh kayi gaggawar cireta a rai saboda sanin kanka ne me martaba da umma bazasu tab'a yadda ka auri y'ar talakawa ba,me zakayi da ita?,ga y'ay'an sarakuna nan da dama wad'anda suke sonka amma zaka ce kana son wata y'ar talakawa?.




Zuciyar yarima yusufu ce takai kololuwa wajen b'aci,har wani tafarfasa k'irjinsa yake,lokaci d'aya ya harzuk'a,a fusace yace "y'ay'an sarakunan da kake magana akansu wlh babu wacce takama yatsan y'ar talakawar a daraja da Kama kai,banda tak'ama da rashin kunya me y'ay'an sarakunan suka ajiye?,murmushin takaici yayi kafin yace "Nariga nayi d'amarar duk wani tashin hankali dazai tunkare ni a kanta,kasa ido kayi kallo",yak'arasa a fusace yana k'ok'arin barin d'akin,muryar yarima Sameer yaji yana fad'in"Tabbas zaka jawa yarinyar babban bala'i a garin nan kuwa", dasauri yajuyo idonsa yayi jajir,ckn b'acin rai matsananci yace "Wlh matuk'ar hakan ta faru kusa a ranku kun rasa ni!!!,yana gama fad'in haka yabar d'akin a fusace.




Jagwab yarima Sameer yazauna a kujera tareda dafe kansa,ya Salam!,ya furta a fili tareda fuzgar da zazzafar iska,tabbas ya tabbatarwa kansa yarima yusufu yayi nisa,tashin hankalin da zai riskeshi kawai yake jiyemasa,yasan halin me martaba ciki da bai,shikam yarasa ta inda zai b'ullowa matsalar,yasan yarima yusufu yanada matuk'ar sanyin hali amma idan ranshi ya b'aci yanada kafiya da taurin kai sosai,Sam baya tsoron koma mene,tausayin k'anin nashi ne yakamashi sosai sbd Allah yasani yana matuk'ar k'aunar shi,jingina kansa yayi da kujera yana tunanin ta inda zai b'ullowa matsalar, gabad'aya yama manta da gimbiya jalila ta tafi gidansu muwadda.




Muwadda kuwa tana kwashe kayan abincin takai kitchen bata dawo ba tabi ta k'ofar baya,gurin tsaunin da ta saba zama ta nufa,tana tafe tana tunanin yarima yusufu yaushe rabon taganshi,muryar ubaida tajiyo tana Kiran muwadda!muwadda!!,juyowa tayi fuskarta d'auke da murmushi,k'arasowa ubaida tayi tana haki tace "Way..yo Allah na gsky nasha gudu,Kai muwadda Kinga yanda kikai kyau kuwa?,dungure kan ubaida muwadda tayi tana murmushi tace "Zaki fara surutun naki ko?",dariya ubaida tayi tace "wlh dgsk,gsky India ta karb'eki,kinsanme?,gyad'a Kai muwadda tayi alamun a'a,jan hannunta ubaida tayi tace muje muzauna kiji,nan suka nufi kan tsaunin suka zauna suna fuskantar juna,ckn dariya ubaida tace "Kee wlh wani mafarki nayi Wai kina zaune akan wata tamfatsetsiyar kujera me tsananin kyawun gaske wadda nidai idan nace zan kwatanta miki yanzu wlh nayi k'arya,kina sanye da wasu irin kaya na sarauta masu tsananin kyawu,alkyabbar ki sai zuba kyalli take,kyakykyawar fuskarki tana fidda wani irin annuri,fad'in kyaun da kikayi k'arya ne,wata yarinya nagani me tsananin kyau babu inda ta baro kamarki ko kad'an ta taho da gudu ckn gwarancinta na yara tana fad'in Ammi!Ammi Kinga Abbu zai kwace min sweet yaba boy ko?,sai Kika d'aga yarinyar dasauri sama kina dariya,dai²lkcn kyakykyawan mutumin da nake tunanin mahaifinta ne yashigo hannunsa d'auke da wani kyakykyawan yaro shima me masifar Kama dashi sak,gyara zama ubaida tayi tana murmushi tace ga mamaki na sai naga ashe mahaifin yaran nan ba kowa bane bace......dasauri muwadda ta katse ubaida ta hanyar cewa "Don Allah ubaida karki fad'amin,mafarki ai ba gaskiya ba ne, ni ubaida abinda ke damuna wlh yau tunda na tashi kirjina yake wani irin mugun fad'uwa,Allah dai yasa ba wani abu mara kyau ne zai faru da ni ba😞,ckn lallashi ubaida ta dafa kafad'arta tace "Kar kisa wannan a ranki muwadda inshallah babu komai kinji?",gyad'a kai tayi tace ameen,haka suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin d'ora girkin rana yayi ubaida taiwa muwadda sallama don ita ynz tunda an y'anta ta aikin kud'i takeyi sab'anin muwadda,har suka rabu muwadda bata ji bugun k'irjinta yadaina ba.








A b'angaren gimbiya jalila kuwa tana fita takira Jakadiya tasa aka had'amata bayi guda biyar,ita kad'ai tashiga mota sai me tuk'i, yayinda bayin suke tafiya a k'asa tunda motar a hankali² take tafiya,basu jimaba suka isa gdnsu muwadda tunda dama basuda nisa sosai tsakanin su.


Kamar kullum iya na zaune a d'akin ta tana tunanin duniya da gudaliyar y'arta taga shigowar bayi guda biyu da k'atuwar dadduma sun shimfid'a a tsakar gidan,bata tsinke da lamarinsu ba saida taga sun d'auko turare sun shiga feshe gidan dashi,sannan suka d'auko na tsinke suka kunna suka saka,ganin suna Shirin fita ne yasa ta d'aga murya tace "Bayin Allah lpy?,suwaye ku?,basu tsaya bata amsa ba suka fice,ckn matsanancin mamaki tace "Me kenan hakan?",sukuma wad'annan fa?.


Gimbiya jalila ce tashigo cikin takun k'asaita da isa ,tana wani yatsina fuska kamar wacce taga kashi,bayinta na take mata baya,yayinda mutum biyu ke rik'e da wata had'ad'd'iyar kujera,ganin gimbiya jalila ba k'aramin firgita iya yayi ba,don kad'an yarage fitsari ya kwace mata saboda tashin hankalin da ta shiga,duk a zatonta wani abu ne yasamu muwadda,da ace k'afafunta lafiyarsu k'alau ta tabbata saita mike a zabure,ckn kula ta fara fad'in "Don Allah karku cemin wani abu yasamu d'iyata.




K'arasowa gimbiya jalila tayi ckn d'akin bayan ansa mata kujera ta kame tareda d'ora k'afa d'aya kan d'aya,da ido tayiwa kuyangin alamun subasu waje,a take suka fice.


Juyowa tayi ta kalli iya tana wani irin murmushin mugunta tace "Yadai daga gani na sai tsorata?,to ni ba wani abu zanyi miki ba umarni kawai nazo baki,ckn kuka iya tace "Umarnin me?,Murmushi tasakeyi karo na biyu sannan tace "Daga yau inaso kisani y'arki muwadda tadawo da zama a hannu na nawani lokaci,ba ina nufin narik'eta har abada kenan ba,dukda hakanma idan naso zanyi,amma bana buk'atar hakan,a b'angaren kula da ke Kuma zankawo masu miki komai,ke hatta wannan k'azamar cimar taku zaki rabu da ita,idan tagama min aiki na tadawo kisani tadawo kenan don a lokacin zan y'anta ta,Kuma zanmata kyauta badon ta isa ba sai don ganin dama ta,karkiga nazo sanar miki da kaina kiyi tunanin kin isa ne,a'a nazo ne saboda maganar nan sirri ce banason kowa yasani,idan har kikaimin gardama to zakisha wuya ne sannan Kuma narik'e y'arki ko bakyaso,gwarama karki b'atawa kanki lokaci ki amince kisawa kanki hakuri don ni banda niyyar cutar da y'arki,zata dawo lpy amma fa idan kinso.


Tunda gimbiya jalila tafara magana iya take wani irin kuka me tab'a zuciya,tasan su gimbiya jalila basuda imani,abinda tafad'a zata aikata harma wanda bata fad'a ba,shiyasa tayi saurin bawa zuciyarta hakuri sbd batason wani abu yasami y'arta,tana fatan Allah yabasu dangana har zuwa lokacin da zasu sake ganawa,ckn kuka tace "Na amince!!,Amma kiji tsoron Allah karki cutar da ita,kallon wulakanci gimbiya jalila taiwa iya tareda fad'in "Sanin kanki ne inda zan cutar da ita kinyi kad'an na b'oye miki ai,dasauri iya tace "Allah ya huci zuciyar ki tuba nake",mik'ewa gimbiya jalila tayi tace "da anjima masu kula da ke zasuzo tare da kayan abincin,gdy iya tayi sannan gimbiya jalila tafita bayan tasake jawa iya kunne akan karta kuskura tayi gangancin fad'awa wani.




Suna tafiya iya tafashe da kuka tana wasu irin surutai,addu'a takeyi akan Allah ya tsare Mata y'arta a kowani irin aiki need da zatayi,har gimbiya jalila takoma gida ta turo masu kula da iya,manyan mata guda 2,ga tulin kayan abinci na zamani,amma har lokacin kuka take.






Muwadda na tsaye a dinning tana shirya abincin dare datayi gimbiya jalila tazo,dasauri ta durk'usa ta gaisheta,batare da ta amsa ba tace biyoni,ba musu tabi bayanta,sunyi y'ar tafiya me nisa kafin suzo wani d'aki, gimbiya jalila ce tabud'e tashiga sannan muwadda tabi bayanta.


D'aki ne madaidaici me kyau tareda band'aki da kitchen a ciki,babu wasu tarkace,gado ne sai sif sai wani k'aramin fridge da fankar k'asa,sai wata katifa sabuwa a gefe,d'akin gwanin burgewa,juyowa gimbiya jalila tayi takalli muwadda wadda ta sunkuyar da kai k'asa tana jiran taji umarnin da gimbiya zata bata,kamar daga sama tajiyo muryar gimbiya jalila tana fad'in "Daga yau wannan shi ne d'akin da zaki dinga kwana,saboda kindawo kwana a gdnnan zuwa wani lokaci!!".


Dasauri muwadda ta d'ago cikin tashin hankalin da ya wuce misali tace "Nadawo kwana a gdnnan fa kikace??mahaifiya ta fa??,ckn halin ko inkula gimbiya jalila tace "Natura me kula da ita,don a k'alla zaki shafe kusan shekara a gdnnan batare da kinfita kinganta ba,ke ko harabar gidannan sai naso zaki fita.




Wani irin mugun kuka muwadda tasaki ckn tashin hankali take fad'in "Wai ku wani irin muta ne ne da kanku kad'ai kuka sani?,mahaifi na yarasu ta sanadiyyar kula da ku,mahaifiya ta ta nakasa ta sanadiyyar kula da ku,nima haka kukeso nak'are rayuwata cikin kula da ku?,shikenan banda lokacin mahaifiya ta?,karku manta bafa siyo mu kuka....maganar ce ta mak'ale sakamakon d'auke war da numfashinta yake k'ok'arin yi,lokaci guda tayi baya zata zube,dasauri gimbiya jalila tarik'ota tafad'o jikinta a sume.




*WAI SHIN MENE NE TARIHIN SU MUWADDA A MASARAUTAR ZINARI?,WANI DALILI NE YAI SANADIN MUTUWAR MAHAIFINTA?,MENE SANADIN CIWON K'AFAR MAHAIFIYARTA?*



```Ku biyo ni a shafi nagaba domin jin answer wannan tambaya.```

4
5
6

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login