Showing 78001 words to 81000 words out of 122957 words

Chapter 27 - Dr Esha Book Complete by J Hajara.txt

J Hajara   

26 Nov 2024

5040

baka wuceba?


Aliyu ya susa Kai yace" uhum uhm Ammi ni tare zamu shiga"


Ammi ta rike kai tasaki takai mishi duka wasa ya goce Yana dariya, itama tayi murmushi taja hannu Essha zuwa ciki.


Kana shiga palace din kamshi turare ne Kota ina, Girma palace din na da girma sosai, Royal couch furnitures ne aka tsagaya parlor dashi gwani kyau, sai kujera da Marmataba yake zaune shima kanshi abun kallone, yanda aka tsara Fada ikai bako ne sai ma kamata da abunda ya kawo ka ka shagala da kallo. A decorating palace din in a royal way.Marmataba dake zaune yasha rawani ga fadawa da dogarai gefe da gefeshi fuskarsu daya da Tycoon sai dai shi yafi Tycoon kwari jiki. Gabadaya family a hade a palace din ana jira isowarsu Aliyu


Suna Shiga Essha ta daga Kai a hankali tana bin Yan fada da kallo . Ba cika sosai ba, su daddy ne dan Yan fada sai su bestie dasu Haydar da kanne Aliyu
Essha ta Soma ji kirari na tashi a gefeta ta kalli guri taga Aliyu ne ke kwasa gaisuwa a gaba Mai martaba dogarai ke masa kirari" **Takawa ka* *lafiya Yarima,* *Makiyaka fadawaka** *Sarki ya amsa gaisuwarka* *rankashidade* "


Taga ya Mike ya koma gefe ya zauna yana kallota sun hada Ido sai kunya ya kamata, Taji Ammi ta rike Mata hannu takai ta har gaba Mai martaba suka Gaisa a kunyace. Itama Tasha nata kirari. Ammi ta mikar da ita tanemi guri gefe Bestie ta rakube.


Mai martaba yayi gyara murya nan Fada kaji tsit. Yace ma liman dake gefeshi ya bude musu taro da addu'a. Nan kuwa liman yashiga sharoro addu'a Yana Kai karshe aka shafa.
Baya nan
Tycoon ne yasoma magana yabada labari haduwar Aliyu da Essha Nan Yan fada suka Shiga mamaki waensu harda guntu kwallasu yabasu labari tass.


Kowa yan fada ayi tsit ana saurarashi yakai Aya labari cike da murna yace" am so happy, Allah na yayi ikoshi a inda bamu taba zato ba, Yan kungiyar na Allah yamusu albarka, da ace zangasu yanzu zamu su Kyauta da bazu taba mancewa dashi ba" duk suka fashe da dariya.


Duk ya fada suka jijina ma Daddy Essha iri kokari da yayi. Daddy har Yana kuka. Gaskiya yayi namiji kokari he's a strong Dad.


Baya a natsu duka agama sani juna Mai martaba ya kalli liman yace" Mall liman haryanzu da aure tsakanisu ko babu?


Daddy yace" Nima abunda nakeso nasani kenan dun Kar mushiga hakki"


Liman yace" da Hadi auresu zuwa yanzu shekara nawa kenan?


Idrees ya amsa da" shekara bakwai kenan mallam"


Liman yace"toh madala, a addinace dai idai mace tayi Wana shekaru batare da mijitaba toh babu aure ko da kuwa a gida daya suke zaune in wani suna kwana a gado daya, na aurataya baishiga tsakanisu ba har zuwa kawo Wana lokaci hakika babu aure ko da kuwa bai furta Mata saki ba, ama in miji na da bukatar matarsa sai an sake daura aure( πŸ™ Sisters inda gyara somebody should help outπŸ™‡)




Liman na fadi haka Aliyu Nan take gabashi ya Soma faduwa liman zaiyi magana Aliyu ya katseshi" walahi inason matarta na Amince ku daura mana aure please liman ka taimaka an daura" ya ciki murya tausayi.


Essha daji haka ta Soma kuka Mara sauti ta kwanta a cinye Siyama,






Duk akayi tsit ana jira anji Mai Daddy ko Tycoon za su ce, duk cikisu Babu Wanda ya bude baki dun yayi magana sai kallo juna sukeyi, shi Tycoon kam ya kasa maganane saboda Yana shakkar Daddy daji nauyi. Daddy kam shi bai da dalili dun yamafi son a daura dun yasomaji tausayi Aliyu.


Can duk anyi shiru Daddy yaga shiru yayi yawa ya kalli Liman yace" Mallam ba damuwa an daura Allah yasa haka yazama mafi alkhari"




Duk suka kalleshi cike da mamaki iri kyau hali iri na bawa Allah na da wuya ansamu kamarshi..


Ammi ta kalli Essha taga yanda take kuka sai bataji Dadi ba ta kallesu tace" gaskiya haka baizuyu ba, Essha dai ba yariya bace, ku fara tambaya ta ita Amince toh, ama andaura.aure batare da yarda ta ba, toh Wana ba adalci bane" ta juya ga Daddy ta hada hannuwata Alama roko tace" da Allah Alhaji Kar kace zakasa ta ta Amince na Dole ku bar ta , ta Amince da kanta, Aliyu Dana ne nasa Yana sonta, tun haduwarsu na fari, so baza Amince amanta na Dole kamar yanda Yan kungiya suka Mata ba saboda mu ba jahilai bane"


Ta juya ga Aliyu da fuskar yagama yi ja saboda tashi hankali tace" Aliyu...


Wai hajiya maikike shiri yi ne" Daddy ya katseta.


Ammi ta juyo tace" inaso Kare ma Essha hakkita ne da kuke neman danemata shi "


Liman yace" eh Hajiya tayi gaskiya bara munji daga yariya ta Amince ko Bata Amince ba"


"Aishatu ki Amince a sake daura Aure ki da Aliyu eh ko aa?




Essha duk jikita ya hau Bari gashi duk ido akanta harwani zufa take hadawa. Aliyu idoshi na kanta so yake su hada ido ama Taki dagowa wani hawaye tashi hankali ne ke siyaya a idonshi . Bakita har wani rawa yakeyi ta bada amsa takasa. Bataya tsaya wani tunani ba ta bude baki a hankali zatace aa Bata Amince ba Sadik ya shigo shi dasu Sofia ya fada akan cinyar ta Yana" Mummy na koshi na koshi sosai"


Essha ta rugumeshi ta fashe da kuka, duka guri an tausaya musu daga ita har Aliyu ba Wanda zaka kalleni idoshi ka ga ba kwalla aciki saboda tausayi.


Essha ta gyada Kai kawai ta Mike ta fice a palace din rike da Sadik tana kuka.....






WassssshhhπŸ₯΅πŸ₯΅πŸ₯΅Nima nayi nawa😭😭
Kai DOCTOR ESSHA fans group Kuna da Amana nagode sosai Allah yabar zumunci daga yanzu zaku riga samu update kullum 😁πŸ₯° nagode da kulawarku Wana page naku ne kuyi yanda kukeso dashi πŸ₯°πŸ₯°


Ya Allah sisters daughters frieds namu Wanda suke zana WAEC ubangiji Allah yabasu sa'a yasa sufito da 9credit Ameen ya Allah πŸ™β˜ΊοΈπŸ™πŸ™πŸ™β€οΈ






More comment πŸ™β€οΈmore typing β€οΈπŸ™β€οΈ
Love you guys πŸ₯°






πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ




*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ


*M. W. A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da masoya ta.πŸ€™πŸ»
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________


7️⃣7️⃣&7️⃣8️⃣


Tana ficewa Aliyu ya Mike da himma zai bin bayata, Mami ta dakatar dashi. Ammi ta kallesu tace" da Allah kuyi hakuri abata Nan da sati kafi anji na bakita"


Ta juya ga Daddy tace" da Allah Kar ka takura Mata kan Aliyu. Yanzu addu'a mu suke bukata, Allah ya zabe mafi alkhari"


Duk suka amsa da ameen sukayi na'am da zance Ammi. Tycoon yasa Siyama ta dubata. Mami da Siyama suka fice wuri dubota. Suna fita koina su duduba har ciki gida su duba Bata. Suka fito compound suna tambaya dogarai. Dogarai suka Basu amsa da yanzu yanzu ta fice Tana kuka.


Mami ciki tsawa tacemusu"maza maza ku bi bayata"


Dogarai ciki sauri suka bi bayata. Suna kaiwa baki hanya su duba koina Bata ba alamata ciki sauri suka koma suka sanar ma Mami. Mami ta juyo ciki palace din ciki tashi hankali ta sanar masu Tycoon.


Aliyu ya Mike a razane har jikishi na rawa yace"Ma..mi i...na tabi? Ya fada a rarabe.


Mami tace"Boy ina za sani, Allah yas...


Daddy yayi murmushi ya katseta yace" ku kwantar da hankali ku, Essha daga na baida zataje sai gida. Ina da tabbaci tana gida"


Aliyu daji haka ya ajiya numfashi Mai karfi Yana lumshe ido, shi kadai yasa maiyakeji. Fatashi daya Allah yasa Essha ta Amince da maganar Mai da auresu. Cus he can't bear losing her for the second time.


Nan aka fara Kira Sallah Asr. Duk suka mike. Su Ammi zasu shiga ciki suyi sallah Tycoon ya dakatar dasu da cewa in su idar da sallah su fito zasuje gidasu Essha ba Bata lokaci.


Mami ta amsa" da toh shikena sai mu fito"


Duk maza suka wuce zuwa masjid.




Essha lokaci da ta fita napep ta tare kamar Daddy ta yasani gida tasa Mai napep ya kaita. Suna zuwa baki gate nasu ta ciro kudi da ita kanta batasan nawa bane ta biya Mai napep ta ja hannu Sadik, haweye ke sauka a fuskata shabe shabe Kamar a bale famfo. Sadik sai tambaya yakeyi"Mummy what's wrong with you? Why are you crying?


Takasa bashi amsa taja hannushi kawai suka Shiga ciki. Ta tarda su Mummy dukasu hardasu Amir, Walid, Daddy karami da hajiya a baki kofa sunyi zugum Kamar a musu mutuwa. Duka fuskakokisu yanuna tsatsa tashi hankali da suke ciki.


Essha ta karaso gabasu takara tsanata kuka ta. A rikece duka suka nufo ta.


Hajiya ta dafata tace" Essha aina ku ka ganshi? Inashi Abbanaki?


Essha Bata amsa ba takara karfi kuka nata Kai wanan karon na shagwaba ne.


Mummy ta juyar da inta suna kallo juna tace"bakijine ba tambaya ki akeyi ba? Ina Daddy ki?


Essha Bata amsaba tasaki hannu Sadik tayi ciki direct dakita ta wuce ta fada gado tana Tana Kara tsanata kukata.


Mummy cike da mamaki suke bin bayata dukasu.


Daddy karami ya kalli Hajiya yace" hajiya Wana kuka da takeyi ya nuna alamu ba lafiya"


Hajiya ta zuba tagumi. Mummy ta nemi guri ta zauna gefe gadon ta daura kan Essha a cinyarta ta Soma share Mata haweye ciki murya lalashi tace" Essha gayamin maiye sameki? Ina kika baro Daddy ki? Ko dai wani Abu yasamaikune?


Essha still Bata amsa ba, kuka ta tsaida ta riga sauke numfashi tana shesheka.


Mummy tace" Essha kince wani Abu Mana ko hankali mu ya kwanta musan mataki da zamu dauko. Rashi maganakifa bashi ne mafita ba you have to talk kinji"


Essha ta Saida shesheka tana kallo Sadik.


Amir ya ja hannu Sadik ya daurashi a cinyarshi yace" Boy where is your grandpa?


Sadik ya amsa da" he is with my Dad"


Dukasu suka dago suna kallo Sadik da mamaki a fuskokisu. Daddy karami ya nantata" Daddy shi fa toh ai'na suka hadu!


Bai gama rufe baki ba suka Soma ji horn da jiniyar mototoci natashi a kofar gida.


Basu tsaya wani tunani ba duk suka mike suka fito. Essha ko motsawa batayiba Dan tasa su Daddy tane. Kara makewa tayi karshe gado ta na zance zuci.


Walid ya bude gate din, motoci suka sa Kai ciki gidan.


Su Daddy karami Mamaki ma ya hanasu magana sai bi motoci suke da ido har motoci suka gama parking.


Securities nandai suka sake fitowa suka bude motoci. Daddy da Tycoon suka fito lokaci guda. Saura ma duk suka firfito.


Aliyu ne karshe fitowa Hajiya ciki firgici ta matso gabashi ta Soma ta tabashi Nanda idonta ya cika da kwalla bakita na rawa ta kalli Daddy Tace"Ahmadu wa nake gani gabana, Kamar dai Aliyu nake gani Miji Essha da Yan kungiya su ka aura mata ko dai idona gizo yake min kuwa?


Hajiya takai hannu Tana shafa fuskarshi kwalla na zuba. Aliyu ya riko hannu ta Yana murmushi yace" kaka idonki ba gizo yake minki ba ni ne"




Hajiya ta fashe da kuka tace"dama kana raye?


Daddy yazo yaja ta yace"hajiya zo mushiga ciki magana bana nabane"




Suna Shiga su Mummy suka musu tarba na mutuci . Aliyu yasoma baza Ido Yana neman Essha, baiga gatanba sai wansu yanmata biyu yagani masu Kama da ita . Wato khairat da Mufeedat kenan. Sai yaji jikishi yayi sanyi yakasan dago Kai. Yanaji Daddy na basu Mummy labari haduwar su har shirya magana auresu da dagawa ana jira Essha, ya kwashe Tass yanda akayi ya shaida musu.



Daddy karami yace"kaji wani ikon Allah ko. Kai gaskiya Nima naji dadi haka. Ke mufeedat je ki kirawota"


Ammi tace" aa ku barta ta huta. Kar ku sake daga Mata hankali"


Hajiya tace" aa kunji wani daura ma karya gindi, tundama Saboda Wana magana ne yasa ta shigo gida da kuka kamar ace Mata na mutu"


Ji magana hajiya yasa duk suka fashe da dariya.


Hajiya Tasha mur ta kalli Aliyu tace" yaro Sha kurumika Kamar ka mayar da mataka ka gama bi'izinilahi"


Aliyu haryashi sanyi a ranshi ciki sansayar murya yace" nagode hajiya Allah ya Kara girma"


Tace" Bari godemin Dana ni kadai nasan wahala da Yan kungiya suka baka ga jinya so ai Dole ta koma gidaka"


Tycoon yaji Dadi haka nan aka Shiga hira kamar a Saba da juna.


Ciki daki Essha kuwa. Ita dasu Bestie ne da su Siyama su Santa a gaba tun Bata magana hartazo ta sake dasu. Yanmata su shiga ranta. Bestie kam sai kallota takeyi tanason tamata magana akan Aliyu ama tana tsora kartasake tsokolo wani tsuliya dodo taja bakita tayi shiru tana ta Mata dariya kasa kasa.


Essha ta kalleta ta tura baki tace" munafuka shine harda min dariya ko? Ta halbeta da pillow.


Bestie ta cabke ta fashe da dariya tace" da Allah siyama kunji nace wani abun? Kawai dai kice min ki tsargu ne"


Siyama tayi dariya tace" karfa ki Bata Mata Rai dun zaiya Kai karaki guri Ya Aliyu" ta fada ciki wasa.


Bestie ta rike kirji tace" ni wa da Allah ku rufa min asiri maza su binne ni ba mataba"


Duk suka fashe da dariya ama Banda Essha. Tayi shiru tana kallo gefe daya. Rahma ta tapping nata a hankali tace" Anty yadai ana hira ke kiyi shiru?


Essha tayi murmushi kawai tace" bakomai dr"




Sukacigaba da hira sai wurare 6 na yamma family din Tycoon suka shirya zasu koma. Tycoon Yama Daddy sha Tara na arziki da farko Daddy ki karba yayi sanda Tycoon yariga hadashi Allah da Annabi Sana ya karba Yana godiya.


Suka rakasu har baki motar, Aliyu ba haka yasoba shi da za a barshi ma kwana zaiyi. Sai kumbere kumbere fuska yake tayi su Haydar na mishi. Yana kallo su Rahma sun fito suna rike da hannu Sadik tare zasu wuce, Still ba Essha cikisu ya ja karami tsaki yaji sanyi kadan yau zai kwana da danshi na cikishi. Sai binshi kawai yake da idon, suzo za sushiga motar ya saki Hannu Rahma zai koma ciki tace" hey boy where are you going?


Sadik Yana tafiya ya na" sorry aunt, one minute, i want to say goodbye to my mum"


Siyama tayi murmushi tace" yawa Dan albarka toh sai ka dawo munjiraka"


Aliyu ya zagaya ciki sauri ya bi baya Sadik bawanda ya lura dashi. Yaga Sadik yashiga wani Daki dake gefe hannu haggu na parlor shima yashiga da sauri. Yana shiga yaji wani kamshi ya mamayeshi ya lumshe idon a hankali. Ya ji a rike Mai hannu. Ya bude idon a firgice yaga Ashe ma Sadik ne.


Sadik yayi murmushi yace ciki harshe turaci yace" la Papa kaji tsoro"


Aliyu shima yayi murmushi a hankali yace" where's your mum?




Sadik yace" nashigo ba gantaba Killa tana toilet, papa mu zauna munjirata ko?


Aliyu ya daga mishi Kai yana murmushi.


Sadik ya kalleshi shiru can yace" did wanna say goodbye to her too?


Aliyu yace" shsssh reduce your voice"


Sadik yasake rage murya kamar Mai rada yasake nantamishi tambaya.


Aliyu Yana dariya ya amsa da yap.


Ba'afi second goma sukaji Kara bude kofar toilet din.


Sadik ya Mike yace" papa gata zata fito"


Aliyu ya zuba ma kofar toilet din na mujiya, na yafara cin karo da farare dumaduma cinyoyita, sanda ya hade wata shegiya iyau kutt ya wuce. Ya dago Kai ciki sauri yaga daure take da towel fari sol, Dakar towel din ya rufe Mata mazaunata, sai fama share wet hair nata take da karami towel dake hannuta da alama dai wanka tayi, batasan da waesu mutani a daki ba. Ta sauke karami towel din kenan zata shara fuska taci karo da shi a tsaye Yana binta da wani iri kallo Kamar maye, zata saka Kara Sadik ya matso ya rike Mata Hannu Kamar Yana whispering yace" sssshhss Mummy don't scream we just wanna say goodbye to you"


Essha tasoma kame kame ciki ranta tace"tabdijam tare ma suke"


Sadik ya katse ta yace" Mummy zamuwuce bye" ya kalli Daddy shi yace" papa baka ce Mata good bye ba"


Aliyu Yana murmushi bai dauke idosa daga kallota ba ya matso daf da ita Kamar sai ta bata kaiwa yasa hannu ya sukuci Sadik, Essha hartaji tsoro .


Sadik na kafada Daddy shi yasa dariya yace" ye mummy kema kinji tsoro"


Essha ta baka mishi harara ta Kara takurewa a kofa toilet tana Kare kirjita, Aliyu kuwa Kara matsowa yakeyi har ya naiyaji sauti bugu zuciya ta. Yayi murmushi gefe baki yana kashe Mata Ido daya har zai juya sai yasake matsowa yace" Boy close ur eyes"


Sadik ya kulle idoshi gam.yace" okay papa"


Aliyu ya zuba Mata lumsasu Ido sa. Batasan gani kwaya idonshi ciki sauri ta runtse nata gam gam ciki haka kawai taji ya sumbaci kumatuta da gashi kanta.


Tanason ta tureshi tana tsoro tawul dinta Kar ya fadi. Haka ta zuba ma saurauta Allah idon.


Yace" good boy open your eyes"


Sadik ya bude a hankali.


Aliyu yace" Babyyy Bye mu salameki"


Sadik yay sauri yabata peck a goshi yace" Bye mum"


Essha Ido kawai taiya binshi dashi Bata amsaba. Aliyu yayi murmushi zasu fita Sadik ya dakatar dashi.


Aliyu ya tambeyeshi yadai?


Yanuna Mummy shi yace" Bata mishi peck ba" ya fada a shagwabe


Aliyu yayi murmushi mugunta ya karaso gabata Sadik ya juya Mata gefe fuska shi, baya da taiya ta mishi peck, Aliyu daidai saiti kunneta ya Mata rada da Bye bye Dream about me" ya Dora mata light kiss a gefe kunne ya juya suka fice Yana murmushi he feels Happy now.


Essha baki kawai tasake tana binsu da kallo. Takasa motsawa.


Aliyu kam suna fita yaga duk an zuba musu ido dagashi har Danshi mamaki suke basu.




Bawanda yace musu kala, haydar ne ya matso kusadashi Yana dariya kasa kasa yace" Buddy maikaje yi ciki?


Aliyu yace" bansaniba, wuce muje"


Duk suka shiga motar suka fice, Sadik na daga masu hajiya hannu.


Washegari..










More comment πŸ™ More typing πŸ₯°
Love you guys πŸ₯°






πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ
*DOCTOR ESSHA*
πŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈπŸ‘©β€βš•οΈ




*WRITING BY*
*J Hajara*




🌍 *MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“š πŸ–ŠοΈ


*M. W. A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login