Showing 9001 words to 12000 words out of 20139 words
Chapter 4 - KUNDIN AL'AJABI Book 1 Free COMPLETE BY MANSUR USMAN SUFI .txt
ya ɗago da kanshi cikin ladabi ya ce "ya shugabana na rantse da ƙabarin kakana Marganun-uƙub ba zan dawo gare ka ba face na samu nasara shiga fadar bokaye.
Koda gama faɗin hakan sai Jauharul-Layal ya shimfiɗe gadon bayanshi,
Nan take Raudatul-Abyad ta ruga izuwa inda mahaifinta yake ta faɗa kan ƙirjinshi tana mai fashe da kuka, Abu-Raudat ya rungume ta, na wani lokaci daga bisani ta janye jikinta daga nashi ta dube shi cikin alamun matuƙar tausayi lokacin da idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta ce "ya abbana haƙiƙa na shaƙu da kai ainun tsawon shekaru tun ina yarinya ƙarama, ban san kowa ba sai kai, yau ga shi zan tafi nayi nesa da kai inda bana da tabbacin zamu sake saduwa da juna ba";
Koda jin wannan batu daga bakin Raudatul-Abyad sai mahaifinta ya dube ta lokacin da ƙwalla ta cika mashi idanu ya dube ta ya ce "ya farin cikin rayuwata kuma sanyin idaniyata kiyi sani cewa na fi ki jin zafi da raɗaɗin rabuwa dake, domin a halin yanzu na rasa komai na jin daɗin rayuwa, dukiya, mulki da SADAUKANTAKA.
A halin yanzu yanzu shekaru na sun ja a Kowa ne lokaci ajali zai iya riskata, domin koda a halin yanzu bamu rabu ba, tabbas akwai mutuwa. Kin ga dole na zaɓa miki abin da zai inganta rayuwarki kuma ya ba ki farin ciki.
Wasiyya ta a gare ki ita ce duk sa'adda rai da rabo suka kai ki izuwa birnin Madinatul-Aswaj ki cika burin zuri'armu na ɗaukar fansa akan sarauniya Jauharat.
Lokacin da tsoho Abu-Raudat ya zo nan azancen shi sai duk biyun suka fashe da kuka mai tsuma zuciya suka sake ƙanƙame juna.
Al'amarin da ya sanya na ji ƙwallar tausayi ta zubo min, domin rabuwa da masoyi babu daɗi, duk da dake War zuciya irin ta aljani Jauharul-Layal sai da ƙwalla ta zubo mashi.
Tsawon daƙiƙa hamsin suna cikin wannan hali sai daga bisani ne Raudatul-Abyad ta janye jikinta daga na mahaifinta ta nufi inda nake, ba tare da wani ɓata lokaci ba ni da ita muka hau bisa Jauharul-Layal muka zauna.
Jauharul-Layal ya yunƙura cikin zafin nama irin na GWARAZAN JIYA ya buɗe manyan fuka-fukan shi ya tashi izuwa sararin samaniya ya fara keta giza-gizai. Tun Abu-Raudat na iya hangen mu har muka ɓace mashi da gani, ana fara wannan tafiya sai na cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin matsanancin gudun da Jauharul-Layal ke yi, domin a iya tsawon rayuwata ko a tarihi ban taɓa jin aljani mai matuƙar gudu a sararin samaniya tamkar shi ba.
Sai da muka shafe tsawon sa'a bakwai a sararin samaniya muna tafiya babu sassauci ba tare da mun yada zango ba, lokacin da sa'a ɗaya ta sake shuɗewa ne, Jauharul-Layal ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a bisa turba.
Inda aka saukar ya kasance daji mai tattare da dogwayen bishiyu, duwatsu, ƙoromu da sarƙaƙiya. Ko iya shirun da ya wanzu a dajin ya isa ya jefa razani a zukatan duk wata halitta.
Cikin alamun matuƙar damuwa na dubi Raudatul-Abyad na ce "ya sarauniyar kyawawa shin bakya ganin cewa yada zango a wannan daji a haɗari sosai, ki duba ga ki ga yadda yanayin shi yake ?
Har Raudat ta buɗi baki da nufin ta furta wani abu sai sarkin matasan aljanu ya yi caraf na tari numfashin ta ya ce "ai an kare zai yi cizo ake siyo shi a kiwata. Domin koda akwai abubuwa masu cutar a wannan daji dole ne mu yada zango domin mu samu ƙwarin jikin da zamu tunkari fadar Sarkin bokaye".
Raudatul-Abyad ta ce "kwarai kuwa zancen ka dutse ya sarkin matasa, domin haka sai mu kasance cikin shirin ko ta kwana".
Koda gama faɗin hakan sai muka nufi wata itaciya, bayan mun zauna a ƙarƙashin ta sai muka fito da abin guzuri muka shiga kimtsa cikinmu, bayan mun kammala ne sai muka kishingiɗa domin mu huce gajiyar dake tattare, shi kuwa Jauharul-Layal sai ya shiga yin rangadi a wajen domin tabbatar da cikekken tsaro.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata kyakkyawar budurwa ta bayyana a wajen.
Budurwar ta kasance doguwa mai kyawun diri da sura.
Hancinta dogo ne mai lankwasa da kyawu a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur, wuyanta mai kyawu ne dogo tamkar na barewa, kirjinta cike yake kuna a tsaye ƙyam! Ba su ranƙwafa ba, sai sheƙi suke tamkar nunanniyar gwanda, gwanin ban sha'awa, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya buɗe ya yi tudu ta yadda koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi da fatar su ta kasance luwai-luwai tamkar ta jaririya sabuwar haihuwa, sanye take cikin tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama da suka kama jikinta ainun duk wata sura da zata ja hankalin namiji ta bayyana.
Wohoho! Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kwaɗaitu da sha'awarta
Sa'adda muka yi arbda da wannan kyakkyawar sura sai muka miƙe tsaye zumbur! Aka fara kallon-kallo tsakaninmu, a iya tsawon rayuwata ban taɓa ganiko jin wata 'ya mace mai kyawu tamkar budurwar ba. Duk da irin kyawun diri na Raudatul-Abyad amma budurwar ta zarce ta matuƙa ainun.
Tsawon daƙiƙa hamsin muna cikin wannan hali sai daga bisani ne kyakkyawar budurwa ta buɗi cikin wata irin zazzaƙar murya tamkar ana busa sarewa ta ce "yakai Matawus ibn Raziwan tare da Raudatul-Abyad bintu Abu-Raudat ku yi sani cewa tsawon shekaru huɗu ina jiran dakon samun ku domin na mallaki taswirar fadar sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar domin cimma burina na ɗaukar fansar ran mahaifina a hannun sarakunan duniya huɗu na kuma mulki duniya baki ɗaya. Fatana na cikawa abbana burinshi na mulkar duniya baki ɗaya,
Saboda haka kira na a gare ku ku gaggauta damƙa min taswirar fadar cikin ruwan sanyi, idan kuwa kuka ƙi ta lumana azabar KAIFIN TAKOBI na zata tabbata a gare ku".
Koda jin wannan batu daga bakin kyakkyawar budurwar sai na dube ta cikin matuƙar fushi na ce "ya ke wannan AZZALUMA kiyi sani cewa haƙiƙa rafkananniyar zuciyarki ta yaudare ki da ta bayyana maki cewa za ki iya yi mana fashi da makami, wato ƙura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi.
Kuma ina so kiyi sani cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne, ko ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza" kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Zamu ga yadda za ki karɓe taswirar daga hannunmu."
Koda jin wannan daga bakina sai kyakkyawar budurwar ta fusata ainun, idanuwanta suka kaɗa suka yi jajur, har ƙwalla ta zubo mata ta dube mu ta ce "haƙiƙa rashin sani ne ya sanya har ka amba ce ni da azzaluma, amma akwai buƙatar na sanar da ku labarina a takaice.
Babi na biyar
A da can baya kimanin shekaru dubu ɗaya da ɗoriya da suka gabata, lokacin da Ƙarfin sihiri da na jarumataka suka zamto jari hujja, zalunci gami da yaudara suka yi katutu a zukatan bil'adama, kowanne sarki burin shi ya kai farmaki zuwa ɗan uwanshi ya mamaye ƙasar shi ta dawo izuwa ƙarƙashin masarautarshi.
A wannan lokaci akwai manyan biranen duniya da suka shura, waɗanda gaba ɗaya sune ke tafiyar da mulkin duniya baki ɗaya. Biranen sun haɗar da birnin Sin, Rum, Misra da birnin Hindu.
Birnin Sin na ƙarƙashin mulkin sarki Abul-uyum. Abul-uyum ya kasance gwarzon mayaƙi mai dakawa maza gumba a hannu, an ce saboda Jarumtakarshi yana iya shafe tsawon kwana uku yana yaƙi ba tare ya ci ko ya sha ba ballantana gajiya, batun ƙarfin sihiri, dukiya da rundunar mayaƙa kuwa ya yiwa gaba ɗaya sarakunan yammacin duniya zarra. Bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu ga sarakunan nahiyar.
Birnin Rum yana bisa jagorancin sarki Fitinatul-muluk ibnu Larab,
Fitinatul-muluk ya kasance hatsabibin matsafi, gwarzon jarumi ma'abocin tarin dukiya dangin lu'ulu'u da dabbobin ni'ima, masu hasashe da bincike sun tabbatar da cewa a iya fadar shi akwai dakarun aljanu da na bil'adama guda miliyan ɗaya, bayan waɗanda aka tanade su domin kai farmaki izuwa birane da ƙasashe domin FATAUCIN BAYI, kusan komai dake fadar shi an samar da shi ne da ƙarfin sihirin tsafi.
Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan ke yi mashi laƙabi ya da ANNOBAR SARAKAI.
Sarki Hubaizu ibnu Shardas kuwa shine ke riƙe da Kambun birnin Hindu.
Hubaizu mutum ma'abocin sadaukantaka ta gaban kwatance, sanin alƙalumman sihiri, gami da tarin dukiya. A jerin sarakunan da aka yi a birnin Hindu shine sarki na saba'in, ya hau karagar mulki tun yana matashi ɗan shekara sha biyar, kuma a halin yanzu yana da shekaru saba'in cif a duniya, bisa binciken bokaye da masu hasashe sun gano cewa a kowacce rana sarki Hubaizu yana samun sabbin sirrikan tsafi guda miliyan ɗaya, yana samun sirrikan ne a duk sa'adda da sadu da wata kuyangarshi. Bokayen sun gano cewa duk sa'adda da hakan ta faru ƙarfin damtsenshi yana ƙaruwa sau hamsin cin ɗari.
Bisa wannan dalili ya sanya ya zamto wa sarakunan nahiyar ANNOBA ƊARI.
Birnin Misra na bisa jagorancin wani gwarzon mayaƙi ne da ake yiwa laƙabi da Ayumul-barƙas ibnu Zairul.
Sarki Ayumul-barƙas mutum mai tattare da abubuwan al'ajabi ba ya tsafi kuma sihiri ba ya tasiri akan shi, komai yawan sirrikan tsafinka idan kayi arba da shi take za su daina amfani.
Gaba ɗaya sarakunan biranen huɗu, Abul-uyum, Hubaizu, Fitinatul-muluk da sarki Ayumul-barƙas sun kasance basa ga muciji da juna, burin kowannen su shine ya kawar da abokan gabar shi domin ya zamto sarkin SARAKAI na duniya.
Bisa binciken da sarakunan suka gudanar shine ɗyan su ba zau iya cimma wannan buri na shi ba face ya mallaki wani kundi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI dake ajiye a kogon GARUL-SHAMMAR.
shi dai KUNDIN AL'AJABI na ɗauke da sirrikan tsafi guda miliyan dubu hamsin, babu wani mahaluki a doron ƙasa walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin face ya zamtowa duniya gagarabadau kuma ANNOBA ƊARI.
Koda mutum ya mallaki KUNDIN AL'AJABI ba zai iya sarrafa shi ba face ya mallaki wata kuba da ake yiwa laƙabi da Miftahul-sihir, a halin yanzu kubar Miftahul-sihir ta rabu kaso huɗu, kowanne sarki daga cikin sarakunan huɗu yana ɗauke da ɓari guda, dukkaninsu sun mallaki ɓarin kubar a hannun mahaifan su.
Sa'adda sarakunan huɗu suka ga wannan al'amari a cikin halarar tsafin su sai hankulansu suka dugunzuma ainun, abu na farko da ya dugunzuma hankulan su shine. Ta ya ya ɗayan su zai yaƙi sauran abokan gabar shi har ya raba su da sassan kubar guda uku, bayan cewa fiye da shekaru goma suna kwabza yaƙi tsakanin su amma babu nasara, sai dai a samu asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa.
Abu na biyu da yafi tayar masu da hankali shine a cikin su babu wanda yake da ikon shiga kogon GARUL-SHAMMAR har ya ɗauko KUNDIN AL'AJABI face wani barde da ake yiwa laƙabi da Yasiran jin Taufid.
Yasiran ya kasance mafarauci, fiye da rabin rayuwarshi ya yi ta je a daji tare da iyalan shi.
Abun tambaya anan shine ta ya ya ɗayan su zai mallaki mafarauci Yasiran?
Bisa dogon nazari da sarakunan suka yi sai suka samu mafita tsakanin su.
Mafitar kuwa ita ce kowannen su zai bayar da ɓarin kubarshi a haɗe waje guda, sannan a nemi taimakon mafarauci Yasiran, idan ya so bayan ya samu nasarar ɗauko KUNDIN AL'AJABI sai a kwabza yaƙi tsakanin su, duk wanda ya yi nasara sai ya mallaki kundi da kuba.
Kamar yadda sarakunan suka tsara haka al'amarin ya kasance, wata rana da la'asar sakaliya mafarauci Yasiran da matarshi Zarilat sai ni 'yarsu Sulaiza muna zaune a cikin bukka muna fira cikin nishaɗi sai kawai muka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai sun cika dajin baki ɗaya.
Cikin matuƙar kaɗuwa abbana na miƙe tsaye zumbur yana mai ɗaukar KWARI DA BAKAN shi ya yunƙura ya durfafi ƙofar fita, har na yunƙura zan bi shi a baya sai ya dakatar da ni ta hanyar dafa kafaɗuna ya dube mu ni da mahaifiyata ya ce "ya farin cikin rayuwata bana so wani abu ya ɗaga maku hankali kawai ku zauna naje na duba domin naga mene ne ke faruwa".
Koda jin wannan batu daga bakin abbana, sai idanun mahaifiyata suka ciko da ƙwalla kuma ta janyo ni ta rungume ni a ƙirjinta, sannan ta dube shi muryar ta cike damuwa ta ce " ya muradin zuciyata kayi sani cewa yau tsawon shekaru ashirin muna zaune a wannan daji ba a taɓa samun wata muguwar dabba, ko dakarun sumame sun kawo mana farmaki ba sai a yau, jikina ya bani cewa babu alheri a tare wannan fita taka".
Koda jin wannan batu daga bakin mahaifiyata sai ya dube mu cikin alamun matuƙar tausayi ya ce "ya abar kaunata ki kwantar da hankalinki da yardar abun bauta zan dawo gare ku cikin ƙoshin lafiya".
Koda gama faɗin hakan sai mahaifina ya juya ya fice daga turakar yana mai kunna kai izuwa ɓangaren da yake jin takun sawayen, yana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mahaifina ya yi arba da waɗansu zaratan mayaƙa su huɗu zaune a bisa ingarmun dawakai, dukkanin su suna shirye cikin gagarumar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro sun rufe fusakunsu idanunsu kaɗai ake gani.
Kafin abbana ya yi wani yunƙuri sun yi mashi ƙawanya suna masu kewaye shi,
cikin dakewar zuciya mahaifina ya dubi mayaƙan cikin matuƙar fushi ya ce "ya ku waɗannan mayaƙa shin mene ne nufin ku a gare ni? Koda jin wannan tambaya sai kowannen su ya ɗora hannunshi a kanshi ya cire hular ƙarfenshi take fusakunsu suka bayyana a fili ƙarara.
Sa'adda mafarauci Yasiran ya yi arba da fusakun na su sai hankulanshi ya dugunzuma ainun tsoro ya kama shi,
Domin a iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin sadaukai masu matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar mayaƙan ba.
Daga can sai wani daga cikin mayaƙan mai ƙirar samudawan farko fuskarshi a murtuke take babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta,
ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ya ce "ya kai Yasiran ibnu Taufid ka yi sani cewa bamu zo gare ka domin cutar da kai ba sai domin mu taimaki juna tsakaninmu, don haka sai ka tsaya ka saurari bayanin da zan yi maka da idanun basira. Ya kai Yasiran kayi sani cewa bakomai ne ke tafe damu izuwa gare ka ba, face muna so ka tafi izuwa tekun Bahar-rum ka shiga kogon GARUL-SHAMMAR domin ka ɗauko mana wani littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN AL'AJABI, domin mu tseratar da al'ummar ƙasashenmu daga annobar fari da junya dake addabar su, ka yi sani cewa matsawar ka cika mana wannan buri namu, ni Ayumul-barƙas da sauran 'yan uwana Fitinatul-muluk, Hubaizu, da sarki Abul-uyum zamu baka ladan dukiya mai tarin yawa wacce kai da zuri'arka ba su taɓa cinye ta har tattaɓa kunnen ka, sannan kai da kan ka zaka zaɓi inda kake don ka zauna tare da iyalan ka a ɗaya daga cikin biranen mu huɗu".
Lokacin da sarki Ayumul-barƙas na birnin Hindu ya zo dai-dai nan a zancen shi sai sauran sarakunan suka gyaɗa kai dake nuni da tabbatar da maganar da ɗan uwansu ya faɗa, suna masu cewa a ransu haƙiƙa sarki Ayumul-barƙas ba ƙaramar hikima ya yi ba da ya ɓoyewa Yasiran gaskiyar batun KUDNIN AL'AJABI ba, amma a ɓangare guda zukatansu cike suke da mugun tanadi.
Tsawon daƙiƙa hamsin mafarauci Yasiran yana nazarin maganar da sarki Ayumul-barƙas ya yi mashi. Abu na farko da ya faɗo mashi a rai shine, mene ne ya sanya waɗannan sarakuna suka zaɓe shi a matsayin wanda zai ɗauko masu KUNDIN AL'AJABI bayan cewa dukkanin su manyan jarumai ne da za su iya aiwatar da hakan? Sannan ma shin wane tabbaci kake da shi cewa zaka dawo ka tarar da iyalanka cikin ƙoshin lafiya, wani ɓangaren a zuciyarshi kuma na cewa da shi ka tuna asarar miliyoyin rayukan jama'ar da zaka ceto idan ka ɗauko KUNDIN AL'AJABI.
Sa'adda mahaifina yazo nan a tunanin shi, sai kawai ya cire kai ya dubi sarki Ayumul-barƙas, sannan ya yi gyaran murya ya ce "na amince zan biya maku wannan muhimmiyar buƙata amma ina buƙatar ku bani lokaci na yi nazari".
Koda jin wannan batu daga bakin abbana sai sarakunan suka sake duban juna gami da yiwa juna murmushi mai tattare da tsantsar mugun tanadi.
A can dajin Harbul-zawat kuwa ina zaune tare da mahaifiyata cikin tashin hankali, sai mu kaji abbana ya yi gyaran murya ya tura ƙofar hujjar, koda muka yi arba da shi sai muka riga izuwa inda yake suka faɗa kan ƙirjinshi ya rungume mu, muna masu fashewa da kuka.
Sai daga bisani ne ya janye jikinshi daga namu ya dube mu fuskarshi cike da annuri, nan take ya zayyane mana abin da ya wakana tsakanin shi da sarakunan tun daga farko har ƙarshe.
Koda jin wannan jawabi sai mahaifiyata ta cika da matuƙar farin ciki, amma kuma sai hankalinta ya dugunzuma ainun, abin da ya dugunzuma hankalin nata shine shin akwai tabbacin cewa abbana ba zai rasa rayuwarshi wajen shiga tekun Bahar-rum ba?
Sannan wata shaida gare shi dake tabbatar da cewa sarakunan ba su ci amanar shi ba?
Cikin alamun matuƙar damuwa mahaifiyata ta dubi abbana ta ce "haƙiƙa nayi matuƙar farin ciki bisa jin wannan gagarumin aikin ceton al'umma da zaka yi,
sai dai ina matuƙar tsoron ka rasa rayuwarka a wannan hali, sannan kar mutanen da ka aminta da su suci amanarka".
Koda jin wannan batu daga bakin ummina sai mahaifina ya yi murmushi a gare ta ya ce "ki kwantar da hankalinki babu wani sharri da zai same ni,