Showing 3001 words to 6000 words out of 20139 words
Chapter 2 - KUNDIN AL'AJABI Book 1 Free COMPLETE BY MANSUR USMAN SUFI .txt
faɗin albarkacin bakinshi, tsawon daƙiƙa ashirin ana cikin wannan hali sai daga bisani Jauwad ya ɗaga hannunshi sama fadar ta yi tsit a karo na biyu sannan ya cigaba da cewa "Yanzu dukkan wani abu na guzuri da abin hawa an tanadar masu abin da ya rage yanzu shi ne za a ɗora Magajin gari a bisa KARAGAR MULKI, sannan bayan 'ya'yan mai martaba sun yi bankwana da mahaifinsu mata za'a yi masu rakiya izuwa bakin ƙofar gari.
Lokacin da boka Jauwad yazo nan azancen shi sai wani badakare ya matso daf da shi ɗauke da wata akwatun baƙin ƙarfe ya ajiye a gaban shi ya buɗe ta ya ɗauko wani kambun Sarauta ya miƙa mashi shi kuma ya ɗora kambun a bisa kan magajin gari da ke zaune a daf dashi a kan kujerarshi, badakaren ya sake zira hannunshi a cikin akwatun ya ɗauko wata sharbebiyar takobi a cikin kubenta ya risina cikin ladabi ya miƙa wa Boka Jauwad shi kuma sai ya damƙa a hannun magajin gari,
Sannan shuraih ya miƙe tsaye ya je ya zauna a bisa KARAGAR MULKI take jama'ar dake fadar suka risina da kawunansu a gare shi dake nuna mubaya'a a gare shi.
Koda kammala bada riƙon sarauta sai ni da 'yan uwana muka shiga zuwa gidan sarauta domin yin bankwana da mahaifanmu kamar yadda boka Jauwad ya tsara,
Lokacin da na Kaɗaita da mahaifiyata a cikin turakarta sai na dube ta cikin alamun matuƙar damuwa na ce "Ya ummina na ji a jikina cewa wannan gasa da aka sanya mana ita babu tabbacin zan yi nasara domin duk abin da zai kai ga a samu nasarar 'yan uwa sun ɗara ni wato jarumtaka da ƙarfin sihiri".
Koda jin wannan batu daga bakina sai murmushi mai taushi ya suɓucewa mahaifiyata al'amarin da ya yi matuƙar bani mamaki kenan na dube ta nace "Ya ummina shin ina dalilin wannan murmushi na ki?.
Dajin wannan tambaya sai mahaifiyata ta yi buɗe baki ta ƙura mani idanu ko kiftawa bata yi ta fara magana a karo na farko "Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa haƙiƙa bani da wani buri da huce naga cewa kai ne ka gaji sarki ba 'yan uwanka ba, kuma dukkan maganar da ka faɗa tana kan gaskiya,
Abin da ya sanya ni murmushi kuwa shi ne kana tare da abin da yafi na 'yan uwanka kuma matsawar ka yi riƙo da shi zai zaka samu nasarar cinye wannan gasa",
Cikin matuƙar mamaki na dubi ummina na ce "Ya ummina shin ina dalilin wannan furuci na ki kuma wane abubuwa ne nake d su wanda idan na riƙe su zan samu nasara?,
Ummina ta ce "Ya ɗana ka yi sani cewa tun da na mahaife ka na tabbatar da cewa na haifi yaro nagari kuma mai nasara a rayuwa, tun kana yaro ƙarami na fahimci halayen ka masu kyaune saɓanin 'yan uwanka,
Ka yi sani cewa a halin yanzu a duniya komai kake taƙama da shi akwai wanda ya huce ka domin masu iya magana na cewa "Kamai sammakon ka wani a hanya ya kwana"
Wato idan jarumta, sihirin tsafi ko ƙarfin mulki kake taƙama da su cewa sune zasu bada nasara a cikin 'yan uwanka akwai waɗanda suka shafe ka,
Abin da kake da shi wanda 'yan uwanka basu da shi da idan ka rike su zaka samu nasara su ne kamar haka,
Gaskiya, Tausayi, Amana da hakuri waɗannan sune halaye mafi daraja da dukkan wanda ya riƙe su zai cimma nasara a rayuwar shi kuma babu wani abu da zai sanya a gaban shi face ya samu nasara,
Gaskiya dai zata ƙara maka daraja da ɗaukaka a cikin dukkanin harkokin rayuwa kuma ita ce ke bayyanawa jama'a darajar da mutumtakar ɗan Adam,
Tausayi kuwa na sanya soyayyarka a cikin zukatan al'umma har da maƙiyan ka,
Amana kuwa na ƙara wa maka ƙima da daraja a cikin kowacce irin al'umma ka shiga,Hakuri kuwa zai sanya ka cimma nasara a dukkan abin da ka sanya a gaba, domin duk kyawun abu idan baka yi hakuri ka cimma karshen shi ba to abu biyu zai faru,
Da farko shi ne zaka rasa wannan abun, sannan ka yi asarar lokaci da lafiyar da ka ɓata a kan shi,
Ya farin cikin rayuwata ka yi sani cewa waɗannan halaye sune sinadaran shaharar duk wani tauraro a duniya, Na so a celokaci bai kure ba da baka tsakure daga hikayar jarumi Masnur ibn Abdullah da wani fasihin marubucin hikayoyin wannan ƙarni wato Sufi ya tattara kuma ya sanya littafin suna KUNDIN HIKAYA,
Tabbas da zaka ƙara tabbatar da batu na kuma ka ƙara ƙanƙame halayen da kyau".
Lokacin da na ji wannan dogon jawabi daga bakin ummina sai na cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ban sa'adda na rungume ta ba ina mai cewa haƙiƙa na aminta da ke ummina ɗari-bisa-ɗari, da yardar abin bauta ba zan ketare wannan wasiyya ta ki ba, kuma zan samu nasara bisa abin da na fita nema fatana na dawo na same ki cikin ƙoshin Lafiya".
Sa'adda da na zo nan azance na sai mu duka biyun muka fashe da kukan farin ciki, dakyar da siɗin goshi muka rabu da juna suna masu zubar da hawayen baƙin ciki na shaƙuwa da juna.
Lokacin da na isa fada sai na tarar dukkan 'yan uwana sun hallara ni kaɗai ake jira domin haka ina isowa sai aka ɗunguma izuwa wajen fada muka kama dawakai muka haye dake dauke da abin guzuri, kai tsaye boka Jauwad tare da magajin gari Shuraih haɗe da sauran mutanen gari suka yi mana rakiya har zuwa bakin iyakar gari suna masu yi mana fatan samun nasara,
Lokacin da muka nausa zuwa cikin daji sai muka cigaba da tsala gudu a bisa dawakai sai da muka shafe tsawon sa'a ɗaya muna tafiya babu sassauci lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta cika a dai-dai wannan lokaci ne mu ka iso wata mararraba a dajin da ta kasu gida huɗu,
Sai yarima Zafiyar ya durfafi hanyar yamma, Laswil kudu, Rumailat arewa sai ni kuma na yi gabas, dukkan 'yan suna kallon juna cikin matuƙar ƙiyayya amma ni sai na dunga sakar masu tattausan murmushi a haka har mu ka ɓacewa juna da gani.
Lokacin da cigaba da tafiya a cikin dajin sai na wanzu ina tsala azababban gudu a bisa dokina ta hanyar ratsa duwatsu, ƙoramu, bishiyu da sarƙakiya,
Sai da na shafe tsawon sa'a biyar ina wannan tafiya a dai-dai lokacin ne na fahimci cewa dokina ƙarfin gudun shi ya ƙaru ainun domin haka sai na ja linzamin shi na tsaya cak! na sauka ƙasa na zauna a ƙarƙashin wata itaciya na fito da abin guzuri na domin na yi kalaci shi kuma dokina ya shiga yin kiwo yana cin ciyayin da ke dajin,
Ina cikin yin kalacin ne kwatsam bazato babu tsammani sai na ji kwantsama wata tsawa gami walƙiya cikin ƙankanin lokaci sararin samaniya ta canza launi izuwa baƙi,
Cikin wani irin baƙin zafin nama na miƙe tsaye zumbur gami da mayar da abin kalacin izuwa cikin jakar guzuri na gami da zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayana,
Kwatsam sai na ga dokina ya faɗi ƙasa ƙasa yana shure-shuren mutuwa, Cikin kaɗuwa na ruga zuwa inda ya ke kafin na isa har rai ya yi halin shi, cikin matuƙar takaici na tsugunna a gaban shi cikin alhini a lokacin ne na lura cewa wani irin baƙin ruwa mai yauƙi na fitowa daga bakin shi, koda na shin-shina ruwan sai na ji alamun akwai guba a cikin shi hakan ya sanya na fahimci cewa tabbas ciyawar da ke dajin ita ce ke ɗauke da wannan guba,
Cikin matuƙar fushi na miƙe tsaye zumbur gami da kwarara wawan ihu, faruwar hakan ke da wuya sai duhun da ke sararin samaniya ya washe tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Kwatsam! sai wani ƙaton kai mai ɗauke da kawo biyu da fala-falan kunnuwa irin na Zomo haɗi baki irin na jemage ya faɗo tim, sannan hannaye, kafafuwa, gangar jiki suka biyo baya, ko da ganin hakan sai na ƙara riƙon takobina ina zuba idanun,
Sannu a hankali sai sassan jikin suka dunga haɗuwa da 'yan uwan su har sai da halittar surar ta kammala, kafin na ƙarewa surar kallo wani sulken yaƙi da makamai sun bayyana a gare ta,
A lokacin ne na fahimci cewa tabbas surar aljani ne ba bil'adama ba saboda waɗansu fuka-fukai da suka bayyana a gwiɓin hammatarsa guda biyu,
Tsawon rayuwa ta ban taɓa ganin halitta mai kwarjini da ban tsoro tamkar halittar ba domin haka sai yanayin tsoro ya kama ni har gumi ya fara tsattsafo mani a fuska amma saboda ƙi faɗi Irin ta 'ya'yan sarakai sai na basar.
Ko da aljanin ya lura da hakan sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, Sai da ya yi dariyar ta ishe shi sannan ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da Saƙon mutuwa,
Kawai sai ya zare wani makami a jikinshi mai kama da lauje ya yi ɗauki izuwa Kai na yana ihu da kururuwa mai firgitarwa,
Ko da ganin hakan sai nima na ruga gare shi domin tarar juna muna haɗuwa muka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
Muka wanzu muna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta irin ta MAZAN JIYA masu juriya a filin fama, Idan ka ɗauke sautin kaɗawar iskar dake sanya rassan bishiyu rangaji babu abin da kunne ke ji face ƙarar karafniyar makaman yaƙin mu da ke haddasa tartsatsin wuta gami da ƙara mara daɗin saurare,
Sai da muka shafe tsawon rabin sa'a muna wannan baƙin artabu babu sassauci a lokacin ne na fahimci cewa tabbas na gamu da gamo na, Domin ƙarfin saran aljanin ya nunka nawa sau uku,
A wasu lokutan idan ya kawo mani hari idan na kare da takobina sai na durƙushe ƙasa sannan na taso sama na mayar da martani,
A cikin wannan artabu ne aljanin ya kawo mani wani nagartaccen sara da nufin ya tsinke mani wuya, cikin zafin nama na sunkuya makaminshi ya sari iska, Kafin ya sake wani yunƙuri ya sake kawo mani wani harin a kwaɓin cinyata ta hagu duk ƙoƙarin da nayi domin naga na kaure amma sai da makamin ya yanke ni a cinya jini ya yi tsartuwa na kurma ihu sakamakon raɗaɗi da zugin da na ji.
Kafin cikar daƙiƙa ashirin ya samu nasarar yi mani raunuka biyar ɗaya a cinya biyu a kafaɗata ta dama sauran biyun a damtsen hannuna na hagu kowanne rauni na zubar da jini,
Nan fa wani irin zazzaɓi mai matuƙar zafi ya kama ni, jiri ya fara ɗiba ta ina faɗuwa ƙasa, amma saboda da JURIYA DA JARUMTA irin ta MAZAN JIYA sai na miƙe tsaye a haka na ci gaba da kare kaina ba tare da mayar da martani ba.
Lokacin da rabin sa'a da daƙiƙa ɗari biyu da hamsin ta shuɗe ana wannan artabu kwatsam! Bazato babu tsammani sai na wata hikima ta faɗo mani a rai, koda jin hakan sai na yi wuf na dunƙule hannuna ya kirɓawa aljanin naushi a kwiɓin hammatarshi saboda ƙarfin naushin sai da ƙashin hannun ya karye ya yi ƙara ruƙus! Aljanin ya kurma ihu sakamakon zafi da raɗaɗin da ya ji.
Koda na fahimci cewa ashe sam makami ba ya tasiri akan shi nan take na yi jifa da takobina na shiga kai mashi bugu da naushi hannu da ƙafa.
Wohoho haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ta canja, nan fa yazamana cewa cikin ƙanƙanin lokaci na yi mashi jini-jina baya iya mayar da martani, kawai sai na yi wuf na kama wuyan shi na murɗe da ƙarfin tsiya, nan take na jefar da gawarshi gefe guda ko shurawa bai yi ba.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai na cika da matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa na ɗauki takobina na ci-gaba da tafiya ina takawa daƙyar bisa ƙafafuna na durfafi wata hanya, tafiyar daƙiƙa ɗari kacal nayi na iso wata ƙorama da ruwan cikinta yakasance garai-garai gwanin ban sha'awa, cikin matuƙar farin ciki na tsugunna ƙasa ya sanya hannayena biyu ina kamfatar ruwan ciki ina sha. Sannan na miƙe tsaye na durfafi wata bishiyar tuffa na tsinka na ci na ƙoshi.
A sannanne na ji ƙarfin jikina ya dawo kuma sanyi da zazzaɓin da nake ji sun rabu da ni.
Nan take na ci gaba da tafiya ina sake kunna kai izuwa cikin dajin ina tafiya cikin hanzari.
Tsawon kwanaki uku na shafe ina tafiya a ranar kwana na ukun ne na iso izuwa gabar wani ƙaramin tsibiri mai ɗauke da bukka guda ɗaya jal, a gaɓar tsibirin wani makeken kogi ne mai tsawon gaske da ba a iya hango ƙarshen shi. Nan take na fahimci cewa ba zai yiwu na iya ƙetare wannan kogi ba face na ha samu kwale-kwale, don haka sai na isa izuwa bakin wannan bukka na yi gyaran murya har sau uku. Jim kaɗan sai ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wani dattijo dogo mai matsakaicin kaurin jiki ma'abocin kamala da haiba sanye da jajayen tufafi a hannun shi yana dogare da wani kwagiri. Sannu a hankali ya tako da ƙafafuwanshi har yazamana ya iso daf da ni ya ƙura min idanu.
Fuska ta cike da annuri na dube shi na yi gyaran murya na ce "ya kai wannan dattijo ma'abocin kamala ni matafiya ne hanya ta biyo da ni domin nemo wani abu mai matuƙar alfanu gare ni, ina so ka taimake ni da jirgin ruwan da zan iya ƙetare wannan kogi, kasancewar na rasa abin hawa na?
Koda jin wannan tambaya sai dattijon ya buɗi baki ya yi gyaran murya cikin kakkausar murya ya ce "ya kai wannan matashi ka yi sani cewa idan har ka amince da wasu sharuɗɗa da zan gindaya maka to zan ƙetarar da kai daga wannan kogi.
Sharaɗi na farko shine zaka zauna da ni na tsawon mako takwas domin ka taya 'yata noma da kiwo.
Sharaɗi na biyu kai ne zaka dinga nemo mana abin kalaci na nau'in dabbobi,
Sharaɗi na ƙarshe shine duk kaine zaka bamu tsaro a duk lokacin da muke barci.
Waɗannan su ne sharuɗɗan kuma ka yi aiki bisa amana to ina mai tabbatar maka da cewa zan haurar da kai akan wannan teku kuma zaka cimma nasara akan abin da ka fito nema.
Sa'adda na ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin dattijon sai nayi shiru ina mai zurfafa cikin kogin tunani.
Abu na farko da ya faɗo min a rai shi ne "shin yanzun kana ganin cewa idan ka ɓata tsawon mako huɗu 'yan uwanka ba za su cimma nasara ba.
To amma kuwa shin akwai wata hanya da mutum zai iya isa gidan boka Bazzagul-Nadiyar batare da ya ƙetare wannan kogi ba,
Kenan hakan ya tabbatar cewa dukkanin 'yan uwana sun iso wannan waje ko kuma za su iso anan gaba.
Kaga kenan a cikin su babu wanda zai iya amincewa da sharuɗɗan dattijon".
Lokacin da nazo dai-dai nan a tununi na sai na dubi dattijon na ce da shi na amince da dukkan sharuɗɗan ka kuma ina mai tabbatar maka da cewa ba za ka same ni mai cin amana ba";
Koda jin wannan batu sai dattijon ya yi murmushi mai taushi ya ce "zuwa gobe da safe bayan ka huce gajiyar dake tattare da kai.
Daga wannan batu ne dattijon ya juya ya kunna kai izuwa cikin bukkar yana mai yafito ni da hannu yana nuni da na biyo bayan shi.
Lokacin da muka shiga izuwa cikin bukkar sai na tarar ta kasance mai girma da faɗi kuma tana ɗauke da ababan more rayuwa abin da ya haɗar da gadaje biyu, shimfiɗu da sauransu, bayan na zauna a bisa shimfiɗar sai dattijon ya yi gyaran murya da ƙarfi jim kaɗan sai ga ƙofar bukkar ta buɗe sai ga wata budurwa ta shigo ɗauke da Alhaji da salkar ruwa, budurwar takasance mai matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ne ba gajere ba, fatar jikinta takasance mai tsantsi luwai-luwai tamkar ta jariri sabon haihuwa, ƙugunta mai faɗi ne da tudu ta yadda koda kofin lemo aka ɗora zai zauna daram daga gaba kuma ya tsuke, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, fuskarta rufe take da baƙin yanki idanunwanta kaɗai ake gani waɗanda suka kasance dara-dara farare ƙal masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu baƙin cikinsu yakasance ɓaƙi siɗik, gashin kanta baƙi ne mai sheƙi ya zuba har izuwa kan kwankwasonta. Sanye take cikin tufafi masu yalwa na fatun dabbobi.
Koda na haɗa idanu da budurwar sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi wani abu ya ɗarsu a zuciyata.
Budurwar tana takawa a hankali cikin ƙasaita irinta JININ SARAKAI ta iso daf da ni ta tsugunna ta ajiye wannan akushi da salkar ruwa sannan ta juya ta nufi ƙofar fita har ya sanya ƙafarta ɗaya a waje sai dattijon ya dube ta ya yi gyaran murya ya ce "ya sha'afa ban faɗa miki sunan baƙonmu ba da abin da ke tafe dashi, amma magana a bakin mai ita tafi daɗi bari ki ji daga gare shi.
Koda jin hakan sai na buɗi baki na ce da farko dai suna Matawus ibnu Sahibul-Sihir, kuma na fito ne tare da 'yan uwana domin zuwa fadar Sarkin bokaye Bazzagul-Nadiyar duk wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yiwa mahaifinmu shine zai gaji karagar mulki. A wannan tafiya tawa ne hanya ta biyo da ni ta nan, kuma zan zauna tare da ku wani lokaci kafin na samu damar haye kogin dake gaɓar wannan tsibiri.
Sa'adda nazo nan a jawabi na sai kyakkyawar budurwar ta juyo ta dube ni tare da ƙura min idanu ko ƙiftawa ba