Showing 1 words to 3000 words out of 20139 words
Chapter 1 - KUNDIN AL'AJABI Book 1 Free COMPLETE BY MANSUR USMAN SUFI .txt
KUDIN AL'AJABI
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071
Littattafan Marubucin:-
TAFARKIN TSIRA
JARUMAN DUNIYA
KOGON ANNOBA
KANGIN BAUTA
FATAUCIN BAYI
SARAUTAR MUTUWA
TAKOBIN ƊAUKAKA
SARKIN SADAUKAI
GOGA SHA FAMA
KARYA DA GASKIYA
ƘARNI UKU
ƘARSHEN ZALUNCI
KUNDIN AL'AJABI
GWARAZAN JIYA
BABI NA ƊAYA
Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta.
Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!.
Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu.
Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne,
Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi.
Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi,
Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa,
Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi,
Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa.
Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba,
Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske,
Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya,
Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa,
Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi ba.
Yana cikin wannan hali ne idanuwanshi suka kai kan wannan akwatin baƙin karfe da ta faɗo daga cikin keken dokin,
Cikin matukar farin ciki ya taka da ƙafafuwanshu zuwa wajen da akwatun take ya tsugunna ƙasa ya sanya hannunshu ya buɗe murfin akwatun sa'dda ya yi arba da abin da ke cikin ta sai ya miƙe tsaye zumbur cikin matukar kaɗuwa.
Bakomai ne ya firgita shi ba face arba da yayi da wata tsaleliyar jariiriya,
Wacce tunda yazo duniya bai taɓa gani ko jin labarin mai tsananin kyawun ta ba.
Ita dai jaririyar an lullluɓeta da mayafi na alhariri a gefen ta kuma an ajiye wani kambu na damtse da aka yi shi zallar zinariya da jauhari,
Mafaraucin ya ƙurawa jaririyar idanu wacce take kwance ta na sharar barcin bata san abin da ke gudana ba,
Abin tambaya anan shi ne daga ina wannan jaririya ta fito? Kuma mene ne dalilin da ya sanya aka sakata a cikin wannan akwatu?
Amsar tambayoyin da mafaraucin ya kasa bawa kansa kenan.
An ya kuwa badan a tseratar da rayuwar wannan jaririya ba ne yasa aka sakata a cikin akwatin?
Koda ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya durƙusa ƙasa a karo na biyu ya sanya hannuwanshi ya rufe murfin akwatun sannan ya cicciɓeta ya ɗora akan kafaɗarshi ya juya ya cigaba da tafiya yana mai kunna kai izuwa cikin dajin,
Jim kaɗan da tafiyar shi sai ga waɗansu ZARATAN DAKARU sun iso wajen,
Dakarun suna ɗauke da miyagun makamai dangin gatari, Sungumi, Takobi, Al'amudi da takobi, adadin su ya kai dubu da ɗoriya wasu akan dawakai wasu a ƙafa, Sai muzurai suke yi suna dube-dube a dajin tamkar zasu ci babu.
Ko da bayyanar su sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna nazarin takun sawayen keken dokin,
Kaico Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan yayi arna da mayaƙan dole ne ya firgice.
A lokaci guda su ka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak, suka shiga haska takun sawayen keken dokin da fitilar ice tsawon waɗansu daƙiƙu.
Daga bisani shugaban dakarun ya dawo zuwa inda dokinshi ke tsaye ya dubi sauran dakarun cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce " Ya ku 'yan uwana dakaru kuyi sani cewa binciken da na gudanar a yanzu ya tabbatar msni da cewa keken dokin da ke ɗauke da jaririyar Hunaisat ya faɗa izuwa cikin wannan rami dake gaban mu, Kenan kanan ya nuna cewa jaririyar bata raye a halin yanzu.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban sai wani saurayi daga cikin dakarun yayi gyaran murya ya dube shi cikin ladabi ya ce " Ya shugabana shin wata shaida ka ke da ita da ya tabbatar da cewa keken dokin da ya faɗa wannan rami shine ke ɗauke da jaririyar Hunaisat? Kasan fa masu iya magana na cewa "kaɗa Mage ba yankawa ba ne".
Ko da jin wannan tambaya daga bakin saurayin sai shugaban dakarun ya bushe da dariyar mugunta tamkar ba zai daina ba daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da sakon mutuwa ya shafi gemunshi mai tsawon kamu huɗu tamkar an tufka igiyar ya ce " Ya kai Hamsil ka yi sani cewa ai "Komai gudun kare baya ƙure daji" ina da tabbacin cewa jaririyar Hunaisat bazata taɓa kuɓuta daga tarko na ba, kada ka manta cewa fiye da shekaru sha uku nine ke kula da dawakan da ke ɓangaren gimbiya Hunaisat.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban sai dakarun suka ƙaure da shewa da ihun murna , muryoyin su su ka amsa kuwwa izuwa cikin dajin su na masu ɗaga makamansu izuwa sama.
Tsawon daƙika goma su na cikin wannan hali sai daga bisani ne suka kaɗa linzamin dawakansu suka koma izuwa cikin dajin.
Abin tambaya a nan shi ne mene ne ne dalilin da sanya waɗannan dabaru ke farautar jaririyar?
Daga ina keken dokin ya ɗauko jaririyar kuma wane ne ya sanya ta a cikin wannan akwati?.
Dalilin faruwar hakan kuwa shine.
Babi na biyu
A ƙarni na biyu a yankin ƙasashen yammacin duniya anyi wani ƙasaitaccen birni da ake yiwa laƙabi da Madinatul-kusuf.
Birnin Madinatul-kusuf ya bunƙasa a noma, kiwo kasuwanci da tarin al'umma, Daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan mayaƙa masu juriya a filin daga.
Sarkin da ke riƙe da sarautar birnin yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa DANDAZON JARUMI a filin fama, Yana da tarin dukiya, kuma ya shahara ainun a fagen sanin ilimin tsafi,
Bisa wannan dalili ya sanya ya zamo gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu a tsakanin sarakunan nahiyar.
Ana yi ma shi laƙabi da Sabrul-Marhut, Ya na da matar aure guda ɗaya wata kyakkyawar gaske mai suna Hunaisat.
Sun kai shekara goma da yin aure amma Allah bai basu Haihuwa ba, Al'amarin da yake matukar dugunzuma hankalin sarki Sabrul-Marhut kenan, Duk sa'adda ya gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi sai ya ga cewa tabbas zai samu haihuwa amma sai a nan gaba.
Shin yaushe zan samu wannan haihuwa bayan cewa a ko da yaushe shekaruna na daɗuwa girma na kamani?
Anya kuwa halarar tsafina gaskiya ta faɗi cewa zan samu Haihuwa?
Tambayoyin da sarki Sabrul-Marhut ke kasa bawa zuciyarshi kenan.
Wata rana sarki Sabrul-Marhut na zaune a cikin ƙasaitacciyar turakarsa bisa kujera ta alfarma sanye da tufafin barci marasa nauyi, A wannan lokaci dare ya tsala babu abin da kunne keji face haushi karnuka da kukan gyare tsilli-tsilli.
Duk da kasancewar akwai gajiya a tare da Sabrul-Marhut yana buƙatar rintsawa, Amma sai ya ji ko da gyangyaɗi bai yi ba sai dai ya saƙa wannan ya warware waccan.
Yana cikin wannan hali ne sai ya ji alamun motsi a harabar turakarshi, kawai sai ya miƙe tsaye zumbur ya fita zuwa wajen amma sai yaga wayam bai ga komai ba, kuma gaba ɗaya dakarun dake ɓangaren sun ɓingire ƙasa suna sharar barci, Al'amarin da yayi matuƙar ɗaure mashi kai Kenan kuma ya bashi mamaki.
Nan take ya fahimci cewa tabbas akwai aikin wani Ma'abocin sihiri a wannan al'amari, Nan fa ya sha jinin jikinshi har ya buɗi baki da nufin ya furta waɗansu ɗalasiman tsafi.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wani Dattijo ya bayyana gareshi ma'abocin ƙaurin jiki, ya na da ƙirar mutanen birnin Sin, gashin kansa, Gemu da ƙasumba farare ne sol ko da ɗigon baƙi ɗaya babu, yana sanye da tufafi na jemammiyar fatar damisa tun daga ƙasa har sama, a hannunsa yana riƙe da wani ƙwagiri na sihiri.
Kallo ɗaya za ka yiwa masa ka tabbatar da cewa ya yi shura a halarar tsafi,
Sa'adda sarki Sabrul-Marhut ya yi arba da mutumin sai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi tsoro ya kama sa ainun, amma saboda ƙi faɗi irin ta manyan sarakai sai basar ya dubi mutumin ya daka masa tsawa ya ce "Shin wane ne kai kuma mene ne nufin ka a gare ni?.
Ko da jin wannan batu daga bakin Sarki Sabrul-Marhut sai mutumin ya taƙarƙare ya bushe da dariya mai kama da haniniyar doki, sai daga bisani ya turɓune fuska tamkar an aiko ma shi da wasiƙar mutuwa ya buɗi baki cikin kakkausar murya "Yakai Sabrul-Marhut ibn saiban ka yi sani cewa ba na zo gare ka domin na cutar da kai ba sai domin na taimaki rayuwarka.
Amma kafin hakan akwai buƙatar na sanar da kai wane ne ni kamar yadda ka buƙata.
Babi na uku
Kimanin shekaru ɗari biyu da ɗoriya a birnin Romaniya mahaifinmu sarki Raziban shi ne ke riƙe da Sarautar birnin,
Sarki Raziban yakasance gwarzon mayaƙi kuma JARUMIN JARUMAI gawutaccen matsafi wanda masu bincike da hasashe suka tabbatar da cewa a ƘARSHEN ƘARNI na uku bayan shuɗewar boka Shuyuɗan mai taskar ANNOBA DARI ba a samu wanda ya kai mahaifinmu ƙarfin sihirin tsafi,
Bisa wannan dalili ya sanya sarakunan nahiyar ke yi masa mubaya'a bisa dole,
Wasu ma na kiran mahaifinmu da Amirul-Sihir ma'ana Sarkin bokaye.
Duk da irin ƙasaitar mulki da mahaifin mu ke da shi amma giyar mulki ba ta ja shi ba yakasance mutum adali ma'abocin tausayi da afuwa,
Mahaifinmu ya na da 'ya'ya guda bakwai, Yarima Zafiyar shi ne babba dai gimbiya Rumailat, Yarima Hasanul-Mausur, Sumaiyat, Laswil, Rukaisu, Zaidar sannan kuma ni Matawus na cikon bakwai ɗin su.
Kowannen mu na samun kulawa daga soyayyar mahaifinmu, duk da irin matsananciyar gaba da ƙiyayyar da ke tsakanin mu wacce ba kowa ba ne ya haddasa hakan ba face bakin kishin da ke tsakanin iyayen mu mata.
Wata rana mahaifin mu na zaune a fadarshi bisa karagar mulki, fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har da ma abin da idanu ba su taɓa gani,
Fadar ta cika maƙil duk inda mutum ya kalla babu abin da zai gani face kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke.
'Yan majalissar sarki na zaune bisa ƙayatattun kujeru na alfarma
A kowa ce kusurwa a fadar dakaru ne na jinsin MUTUM DA ALJAN shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar gwarjini da ban tsoro ɗauke da miyagun makamai suna kai komo domin tabbatar da cikekken tsaro.
A wannan lokaci idan ka ɗauke iskar da ke kaɗawa a fadar babu abin da kunne ke ji face sautin fitar numfashin ɗaruruwan jama'ar fadar.
A na cikin wannan hali ne kwatsam sai a ka ga sarki ya faɗo daga kan karagar mulki yana amai na jini kuma tari mai tsanani ya turnuƙe shi,
Cikin kaɗuwa gaba ɗaya 'yan majalissa suka yi ca akan mahaifina, da hanzari dakaru suka shigo fadar ɗauke da wani ƙayataccen gado suka ɗauki sarki suka fice da shi kai tsaye suka kai shi turakar shi suka shimfiɗe shi bisa gadon sarauta suka shiga ƙoƙarin ceto rayuwar shi.
A can gidan sarauta kuwa labarin abin da ya faru da sarki ya riske mu don haka ni da 'yan uwana sai muka ɗunguma muka nufi turakar shi hankulan mu a tashe,
Ya yin da muka iso ne sai dakarun da ke tsaron ƙofa suka dakatar da mu cewa sarki ya ce kada a kyale kowa ya shiga har sai ya yi umarni.
Ko da jin wannan batu daga bakin dakarun sai yarima Zafiyar ya fusata ainun ya daka masu tsawa ya dube su ya ce "Shin mene ne matsayin ku da har zaku hana mu ganawa da abbanmu ina so ku gaggauta buɗe mana ƙofar tun kafin KAIFIN TAKOBI na ya tsara ruhikan ku".
Da jin hakan daga bakin yarima sai hankalin dakarun ya dugunzuma ainun, daƙyar aka samu wani mai dakakkiyar zuciya ya buɗi baki da nufin ya furta wani abu, kawai sai aka ji ƙarar zare sakatun dake dake kofar, jim kaɗan sai ƙofar ta buɗe sai ga boka Jauwad ibn Ramli ya bayyana a gare su.
Boka Jauwad yakasance dattijo mai kimanin shekaru saba'in dogo ne kakkaura yana da gashin gemu da ƙasumba farare sol ko ɗigon baki babu, fuskarshi doguwa ce mai ɗauke da dara-daran idanu jajajur! tamkar garwashin, yana da faffaɗan hanci mai ɗauke da ƙofofi tamkar mazirari, bakinshi tafkeke ne tamkar bakin rijiya mai ɗauke da wargatsattsun haƙora marasa kyawun gani, yana sanye da baƙaƙen tufafi tare da guraye da layu na sihiri tamkar wani tsohon mahaukaci, kallo ɗaya za ka yi boka Jauwad ka tabbatar da cewa ya cika hatsabibi a fagen sarrafa alƙalumman sihiri.
Duk da kasancewar mahaifinmu mashahurin matsafi da babu tamkar shi a nahiyar amma bisa al'adar masarautar mu akwai bokan da ya ke gudanar da dukkan wani sha'ani na lafiyar iyalan masarauta, da kuma jagorancin abin bauta.
Ya yin da muka yi arba da boka Jauwad sai dukkanin mu muka risina gare shi muka kwashi gaisuwa cikin girmamawa, boka Jauwad ya dube mu ɗaya-bayan-ɗaya, sannan daga bisani ya buɗe tafkeken bakinshi cikin kakkausar murya mai kama da haushin kare ya ce
"Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa wannan jinya da ta samu mai martaba cuta ce mai matuƙar haɗarin gaske, wacce za ta iya zamowa ajalin shi baki ɗaya,
Ba wani abu ba ne ya haddasa mashi cutar ba face wani sihiri da abokin gabar shi boka Bazzagul-Nadiyar ya yi mashi, an binne sihirin ne a cikin wata tsohuwar rijiya dake cikin fadar sarkin bokayen aljanu na duniya,
Kafin mutum ya isa inda fadar sarki bokayen take akwai haɗdura masu yawa gami da miyagun dazuka.
A halin yanzu bincike ya tabbatar mani da cewa a kaf duniya yanzu babu wani waje mai tattare da haɗari tamkar shi,
Daga nan zuwa can ɗin tafiyar shekaru huɗu ce amma bisa Saurayin aljani mai tashen balaga za a iya isa cikin watanni shida.
Sa'adda boka Jauwad yazo nan a jawabin shi sai hankulanmu ya dugunzuma ainun, wasu daga cikin'yan uwana cikinsu ya ɗuru ruwa, saboda fargabar kada sarki ya rasa rayuwar shi a halin yanzu ba tare da ya sanar da su mabuɗin taskar dukiya ba.
Boka Jauwad ya katse shirun da ya wanzu tsakanin su ta hanyar buɗe baki a karo na biyu ya ce " Ya ku 'ya'yan mai girma Raziwan ku yi sani cewa a halin yanzu
babu abin da ya ke gaban ku face shiga duniya domin ku isa fadar sarkin bokaye ku karya sihirin da aka yi wa sarki,
Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan har kuka yi jinkiri sarki ya rasa rayuwar shi tamkar kun rushe birnin ku da hannayenku ne, domin abokin gabar abban ku boka Bazzagul-Nadiyar zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA na wannan birni, kun ga kenan shi ne zai gaji KARAGAR MULKI ta mahaifin ku.
Jawabi na ƙarshe a gare ku shi ne mai martaba sarki ya ce na faɗa maku cewa dukkanin wanda ya samu nasarar tone sihirin da aka yi masa shi ne zai samu nasarar mallakar KAMBUN SARAUTA.
Ko da boka Jauwad yazo nan a zancen shi sai ya rikiɗa zuwa wani baƙin hayaƙi ya ɓace ɓat! tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Jiki a sanyaye ni da sauran 'yan uwana kuma juya muka fice daga harabar turakar mai martaba.
Kamar yadda boka Jauwad ya faɗa haka al'amarin yakasance bayan kwanaki biyu da kwanciyar mai martaba jinyar rashin lafiya sai dukkan 'ya'yan tare da ni mu ka hallara a fada domin gudanar da tafiya karya sihirin tsafin da aka yiwa mahaifinmu, lokacin da mu ka shigo fadar sai mu ka tarar ta cika maƙil da jama'ar gari tare da 'yan majalissar sarki a gefe guda boka Jauwad ne tare da magajin gari mai suna Shuraih wanda yakasance ɗan uwa a wajen sarki uwa ɗaya uba ɗaya, bisa dokar masarautar duk sa'adda sarki ya kwanta jinya ko kuma wani uzuri ya same shi sai a damƙa sarauta ga magajin gari,
A iya sanin da nayi wa magajin gari shuraih nasan babu wata matsala tsakanin shi da sarki don haka koda wannan jinya ta sarki ta faru ban zarge shi da wani abu ba,
Bayan kowa ya hallara a fadar kuma an samu nutsuwa sai sarki Jauwad ya miƙe tsaye daga kan kujerarshi ya fuskanci al'umma ya yi gyaran murya ya ce "Ya ku jama'ar wannan faɗa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne 'ya'yan mai martaba sarkinmu za su tafi izuwa fadar sarkin bokayen duniya domin su tone sihirin tsafin da aka yiwa sarki wanda abokin gabar shi kuma maƙiyin wannan ƙasa tamu ya yi mashi wato sarki Bazzagul-Nadiyar.
Bisa Wasiyyar da sarki ya bayar cewa dukkanin wanda ya tone wannan sihirin tsafi ya zo da shi nan shi ne zai gaji karagar shi ya mulki.
Sa'adda boka Jauwad yazo nan azancen shi sai fadar ta kaure da cece kuce kowa na