Showing 60001 words to 63000 words out of 69262 words
mai dadi ta hada su.
Share hawayen shi yayi,ya miqa masa hannu suka gaisa John ma haka.
Aeeshaa ce ta fito tana amsa waya,
"Na'am Yah Sabeer ka iso? K gani nan zuwa, na aje masu abincin, ka dakko Ameerah? Dan na san rikicin ta yawa ne da shi, tin da akai yayen nan kamar wadda akai wa mugun abu,"
"Mugun abu akai mata mana,ke dai yi kixo mu koma gida, yau so nake mu dan je shoping, a siyo mata kayayyakin da zai debe mata kewar maman,"
Dariya Aeeshaa tayi sannan tace,
"Yah Sabeer kenan Abban Ameerah, bari na masu Hadizan Sallama kar su ga na tafi haka kawai,"
Juyawar nan da zata yi ta gan shi, cikn tsananin tsoro tayi baya, tare da zaro idanu waje, fuskar shi tayi jawur kamar garwashin wuta..........
*Kai kuma fushin me ye? Ko manja ka shafa a fuskar bamu da labari?😚*
KUN MAKARO
. WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 28
"Da uban wa kk waya har kk cewa 'yata 'yar shi?"
"Ban gane kana tambayata da wa nake waya ba, ina ruwan ka dani? Ohhhh sorry na manta ashe fa kai yayana ne, ina magana ne da Yah Sabeer, kuma uban Ameerah ne tinda ko kaqi ko kaso qanin ka ne shi,"
"Me ye a tsakanin ku da kk kashe murya kk magana kamar kina magana da mijin ki?"
"Inshaa Allahu mijina ne, Allah ya amsa maganar ka, kana da matsala akan hakan?"
"Baki da hankali ne? Da yarinyar tawa zaki wani auren? Kuma ma Sabeer a dik mutane?"
"Yarinyar ka auren ka ne akai na? Sabeer akan dik mutane ai gwanda shi akan ka ma ba mutane ba, kaga ba zan iya sa'in sa da kai ba a mutane, yanzu bakina ya bude, zan iya kwana kana fada ina fada, amma ba mutunci na bane, saboda haka in kana da magana ka zo gida bayan mun dawo daga shooopinggggg,"
Juyawa tai ta shige dakin da aka kwantar da Hadiza, zuciyar ta wasai ko haushin shi da take ji da babu, dan ta samu ta fidda abinda ke qulle a zuciyar ta ta, ya isa haka, haba, mutum kamar wani shaidan.
Sallama ta musu Hajja ta mata fatan alkhairi, ta ce ta gaida mata su Ameenaa, ita kuma ta bada saqon gaisuwa zuwa Baba General, ta wuce, Khaleefa na ganin fitar ta, yace shima gida zashi, su kai shi ya dakko diyar shi, ba zai bar ta a hannun su ba,
"Amma dai ka san ba wai umarnin ka muke bi ba ko? Kai kk bin umarnin mu, in kana so bi umarnin ka kaje ka nemi izini wajen Hajja,"
"Come on guys, yarinya ta ce fa wajen wani qato, ba zan taba yarda ta zauna wajen su ba,"
"Kaiii....zo nan,"
Bammm ta maida qofar ta rufe, kallon qofar yayi ya lumshe ido cikin bacin rai, wannan tsohuwar fa tana bashi matsala.
"Meye matsalar ka da Ameerah da kuma Aeeshaa da ba saka iya barin mu koma gida ba, a asibiti zaka zo kana sai da mana halin ka kowa na karba,"
"Hajja ba ki ji wai fita zasuyi da Sabeer da Ameerah ba?"
"In na ji sai na hana su? Ba diyar su bace suma, beside kace kai baka son yarinyar nan, ga wadda kk so nan kayi cikin shi ai ba aure ko? Kuma da alama ya shiga ran ka tinda yanda ma ka dauke shi daban ne, har suna ka rada masa, so kar na sake jin maganar Aeeshaa a bakin ka balle Ameerah da Sabeer,in zaka yi maganar su inji alkhairi, yarinyar nan sai in ta girma ta ga damar kula ka amatsayin uba, ba mai bata ka a idon ta amma ba wanda zai baka ita mahaukacin banza kawai,sai kayi kamar ka samu lfy, sai ka qara bazama,"
"Hajja kina nufin banda hankali kenan,"
"Kwarai da gaske, in kana da hankali wanda yake son naka kana da kamar shi ne, Sabeer dinnan da kk gani kwanan nan na san ya dad'e yana son Aeeshaa a sanadin an baka ita ya hakura, ba dan haka ba da Ameeran ma tashi ce, ka mata sakin hauka saboda kan ka na hayaqi ance ka sake ta, kuma naga dai ba son ta kk ba, tinda ka fada aura maka akai ba kai kace kana so ba,"
"Ni yaushe na taba cewa ban son ta, ni ba wanda ya taba jin nace bana son ta,in ma na fada nace na janye, kawai dan ba sona ake ba shi yasa komai nayi bana daidai, dik wani abu da ba ko son nayi ba na daina ba yanzu, kuma nace ina son a maida min mata ta da 'yata yanzu, ba shikenan ba a maidan ita shi ya samu wata,"
Hajja ba zata iya da wannan haukan ba, yi masa bayani ma baida amfani, saki uku a gidan uban wa aka taba maida shi?
"John ! Auwal ! Ku maida min shi gida,"
"Wai ya za a dinga min abu kamar wani barawo ko wani dan kidnapping? Ni to ba gida zani ba zanje na dakko mata ta da diyata,"
Ko kula shi basuyi ba suka sashi gaba, da kallon ka taka mu fita ko kasha na jaki kuma a ka zamu fidda ka, sarai ya san kallon, tinda ba yau yake tare da su ba almost a year now.
Ranshi bace ya fita yana zuba sauri, mota ya bude ya fada ya qame qam,sai muzurai yake yana tsaki,
Bayan sun isa gida ne ya shige dakin shi, in ya rufe ido Aeeshaa yake gani, yanda take waya take nishadi da annashuwa, bai taba sanin wannan side din nata ba, ashe mace ce mai cike da so da qauna a zuciyar ta, farin ciki da nishadi na baibaye da ita, ashe shi ne duhun daya disashe ta, bai san yana kuka ba sai da yaji sautin a kunnen shi, ya so ya riqe kukan amma inaa ba zai riqu ba, fashewa yayi da kuka sosai, yana sambatu,
"Aeeshaa ki yafe min, ki yafen dikkan munanan abubuwan da na maki, ban taba zatan zaki zama mace mai mahimmanci a rayuwa ta haka ba, a zatona jikin ki kawai nake so,ashe zuciyar ki ma ta shiga tawa, a daidai lokacin da NA MAKARO, dik abinda kk min a zaman mu mai daɗi ina fatan Allah ya dad'ad'a maki fiye da hakan kema, Allah ya sa ki farin ciki Aeeshaa, Allah ya raya Ameerah, Allah ya baku zaman lfy, dole na karbi qaddara ta ta auren Hadiza, ni na jawa kai na, Allah na gode maka daka nuna min gaskiya ka bani ikon bin ta, Ya Allah ka yafe min munanan aikin dana aikata a baya,Allah ka kare ni da aikata laifi a kan sani na a gaban rayuwa ta, inna aikata laifi a bisa kuskure Allah ka yafe min,"
Shessheqar kuka ya ji a bakin kofar shiga dakin nashi,sai ya juya daga durquson da yayi a qasa, mahaifiyar shi ce riqe da abincin shi kasancewar Hajja na asibiti bata dawo ba, yau dai tayi waya tace Maman shi ta kai masa, cikin murna kuwa ta debi abincin, ta kai masa, tana shiga taji yana kuka, yana addu'a, wani irin daɗi ne ya wanke zuciyar ta, d'a na gari abin so ne ga kowa, samun suruka kamar Hajja abin na da wahala a wannan zamani, wadda zata tsaya ta jajirce don ganin ta kare ahalin ta daga wuta, ta samu nasara sosai, ba abinda za su ce ma Hajja sai dai Allah ya mata kyakkyawan qarshe,ya qara mata shekaru masu albarka ta ci gaba da sa su a hanya.
"Son tashi ka ci abinci, inshaa Allahu Allah ya amsa dukkan abinda ka roqa, kai dai ka ci gaba da zama yaro na gari, in kayi haka ka gama komai a rayuwar ka, zo kaci abinci, kar yayi sanyi,"
"Mama kema ki yafen dik abinda na maki a rayuwa ta, inshaa Allahu na maki alqawarin zamowa yaro na gari abin alfaharin ku, na dau darasi, da girmana ana bani kulawar qananan yara, tarbiyya aka koma ban daga farko saboda watsi da nai da wadda aka min ina yaro, na gode wa Allah daya yo ni a cikn ahalin nan,"
"Sauran Baban ka da Baba General, ya kamata ka nemi gafar su, sannan ka samu Hajja ka mata godiya na musaman akan kulawa da lamarin ka da tayi,"
"Inshaa Allahu, ita na san me zan mata, su Baba kuwa yau yau dinnan zan nemi gafarar su,"
Abinci yaci yayi sallar Asr, yayi wanka da kyau, yana zabga qamshi yaje masjid ya dawo, a parlourn Hajja ya tadda iyayen nashi maza ya basu hakuri, kuma sun gamsu Khaleefa ya shiryu, dan haka sun yafe masa, sun kuma sanya masa albarka, Hajja ce ta fito cikin kwalliya kamar kullum, Khaleefa ne ya kalle ta, cikin zolaya yace,
"Gaskiya uwargida kin hadu, da zaki ban dama da yau mun fita on a date just me and u, dan na nuna maki irin yanda nake son ki a raina, kuma na nuna maki godiya ta a gare ki bata da iyaka,"
Cike da jin daɗi Hajja ta kada ido kamar wata budurwa tace,
"Why not?"
"Da izinin wa?"
"Ohhh dear don't be a jalouse husband,"
"K na bada izini amma a dawo da wuri,"
"Yes sir"
Mayafin ta ta dakko, suka jera, ya riqe hannun ta, Baba General yayi gyaran murya, juyawa sukai sika kalle shi,cikin daure fuska ya nuna da hannun shi alamar ya sake mata hannu, dariya aka dauka a wajen, Baban Khaleefa har yana kwallar farin ciki, suna fita su John suka taso,
"Not even today man, we ar going on a date, a date, bama buqatar kowa, na sauya ku kun sani, ba saida ta zan je nayi ba,"
"Kuje abun ku muma fita zamuyi, ina ruwan mu da kai?"
"Ba ku da ruwa tabbas amma kar ku ce zaku bi mu yau, i want to show her my appreciation thats all,"
"K man sai kun dawo, Allah ya kiyaye, u better watch it,dik inda ka shiga muna da ido a wajen,"
Hannun Auwal ya saka a gaban idanun shi, alamin muna ganin ka.
Budewa Hajja mota yayi wadda take ta dariya, wato kowa bai yarda da Khaleefa ba, ta yarda da fitar nan ne dan shima ya shaqata, ya dad'e a nade a gida, sannan hakan zai sake bata damar cusa mishi aqidar da take son ya kasance yana da ita.
Wani fancy restaurant suka je, ga kudi ga kyau, zama sukai, aka kawo masu abinci da abin sha, suna ci suna hira, mutane ana ta kallon su, ga tsohuwa ta sha gayu kamar amarya, ga yaro, matashi mai jini a jiki, kowa dai ya gan ta yaga kamilar dattijuwa, kamannin da suke ne ke korewa kowa shakku da zargi, dan mu ta nan wajejen hausawa ba kowa ke fita da matar shi ba, ko a je cin abinci ba da sauran irin dabi'un nan na turawa da larabawa.
Hajja tayi nasara wajen koyar da Khaleefa wasu abubuwan na rayuwa masu mahimmanci, yaji dadin fitar da sukai sosai, bayan sun fita ya kaita shoping, ta ji dadi kwarai, ashe Khaleefa is so sweet ba wanda ya san hakan, yanzu gashi yana ta nuna masu halin shi mai kyau.
Daf magrib suka isa gida, kusan sai da ya yi wa kowa siyayya, musamman Ameerah da Aeeshaa,sai Hadiza da yaron su, Hajja ta taya shi zaban kayayyakin wanda suka dace.
**********************
Yau wata hudu kenan da haihuwar Hadiza,Hadiza ta murmure, sai dai har yanzu bata dawo da hasken ta ba dan tayi alqawarin daina sabon Allah ta hanyar shafe2n mai da zasu qara mata fari, Goggo ta tsoratar da ita sosai, akan hukuncin masu sauya halittar Allah.
Parlourn Hajja a cike yake da baqi, Aeeshaa da Umman ta da su Ameena dik sun zo, Iyayen Ammar yau zasu zo, da wasu dangin Baban Hadiza dan saka ranar aure, abinci da abin sha ne cike a parlourn, sai raha ke tashi da hirarrakin iyayen nasu, Hassana kuka kawai take na farin ciki, wai yau ita za a sakawa rana, Aeeshaa na ta lallashin ta, can qasan ran ta tana tinani bata ji fa ance saka ranar harda nasu ba, ko dai ba yanzu su za a mallaka masu junan su ba ne? Gaskiya sun matsu su gan su a inuwa daya, ai ya kamata a hada dika a huta.
"Tinanin me kk?"
"Ummah ban ji ance za a saka rana har da mu ba, naji ance na Adda Hassana da Yah Ammar, Yah khaleefa da Hadiza,mu fa?"
"Aeeshaa qaniyar ki, wato kin matsu ki bar ni ko?"
Kwantawa tai a cinyar Umman nata cike da shagwaba ta dora habar ta kan kafadar ta,
"Ummaah u knw how much i love u,just curious to knw za a hada damu ne kk a'a,"
"To nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito muji,.....ke kuma ki daina mana kuka haka, ai murna zaki ba lokacin kuka bane wannan, ki godewa Allah, dama wani jinkirin alkhairi ne, gwanda ki aure a makare, akan ki auri wrong parson,"
"Haka ne Ummah, can't help it, kukan kawai ji nake yana zuwa,"
Ummeen ta da ta shigo dauke da abin sha ta zauna, tace,
"Yaran Ummee me ake tattaunawa ne?"
Da sauri Aeeshaa tace,
"Ba komai,"
Dariya suka sa dika, tabbas akwai wani abu kenan tinda take sauri kar a sani,
"Tambaya ta take wai da su za a saka rana ko ba su,"
"Su su wa?"
"Ita da Sabeer mana,"
"Ummaaaahhh,"
Tashi tayi ta bar wajen tana buga qafa irin na shagwaba, daidai lokacin Sabeer da Ammar suka shigo, Ammar baki har kunne, Sabeer fuskar shi a daure, kallon shi tai idon ta a waje, kar dai a ba sa rana da su ba...........😨😨😨😨😨😨
*Tabdi jamm aiko da na je na sake dasa sabon zama a gidannan, wa zai raka ni😡😡*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼
Da hannu ya mata alamar su je waje, ta kitchen suka je suka tsaya daga waje,
"Yah Sabeer me ya faru, naga fuskar ka babu walwla?"
Dan sosa kan shi yayi ya gyara tsaiwa,
"Na ji ana ta saka rana ba a kira sunan mu ba, sai daga baya wai naji Baba General na cewa mu in an tashi nasu an daura auren mu, kamar bamu da wani mahimmancin da za a mana yanda aka masu, cikin bayyana muma fa ranar mu za a sa, kamar yanda ake maganar nasu,"
Dan murmushi tayi, ta kai fuskar ta tana leqa tashi, wai da gaske fushi yake, qin kallon ta yayi da fari sai daga baya suka hada ido, nan da nan idon shi ya kawo haske saboda nutsuwar daya samu ta hanyar kallon fuskar ta.
(Ya ke 'yar uwata, kin san kuwa tasirin kallo? Kallo ya na da mabanbantan amfani, daya daga cikin amfanin kallo shine ki kwantar ma da mijin ki hankali ta hanyar kallo, in kina da zuciya mai kyau kallon ki xai tasiri a wajen dik wanda kk kalla da kyautatawa, amma zuciyar ki in ba alkhairi cikin ta kallon kwantar da hankali ba zai tasiri awajen ki ba,a lokuta da dama, ki gwada ki gani, komai fushin mijin ki, ki daure ku hada ido dashi, ki sakar masa murmushi mai qayatarwa, ki masa kallon da zai tafi direct zuwa zuciyar shi, inshaa Allahu zaki ga ya sassauta,koda so kk ya tausaya maki akan wani abun, kallo cike da fuskar tausayawa na tasiri, sai dia ina sake tinatar da mu ki kyauta ta zuciyar ki kafin kallon ki ya zama mai tasiri da isar d saqon ki inda ya dace)
"Yah Sabeer, Abban Ameerah, ko ka manta kai mijin bazawara ne wai? So kk a maka komai irin na samari ko? To ka qaro budurwa ka hada mu kaga in ba ai maka ba,"
Dariya take cike da sautin tsokana a ciki, shima dariya ya sake, sannan a hankali ya fara rage dariyar shi, yana kallon ta,tana dariya, cikin husky voice din shi ya furta mata,
"Ko a burwai ba za a samu budurwa da kamar ki ba a waje na, kin fi min 'yan mata kyawawa masu sarauta da mulki da kudi guda hudu, ko za a aura min su a rana daya dan gata in aka ha na ni ke an gama dani, so nake na raya sunnar auren bazawara nima,tinda wasu suna dabbaqa sunnanr auren budurwa, kinga ni harda kyauta mai girma ta diya na samu, Allah ya sanya mana albarka my love,"
"Ameen mine alone, ban hada son ka da kowa ba Yah Sabeer, sai yanzu nake tausaya maka, lokuta da dama har kuka nake, inna tina lokacin da ka dauka kana dakon so na, ka sha azaba matuqa, dan dik sanda na so ganin ka ban gan ka ba ina jin zuciya ta na zafi har sai na gan ka ko naji muryar ka nake jin dadi, ya Allah ka bamu rai d lafy ka mallaka mana junan mu da dikkan albarka d alkhairi,"
"Ameen my wife,"
Ba qaramin dad'i taji ba da kunya shige shi tai tana dariya, ganin su Umma still a parlour ne ya sa ta yin turus, kusan kowa na wajen har Hajja, ana ta hirar yanda biki zai kasance, domin Sati biyu kawai aka saka, sai dariya ake ma Sabeer yanda ya nuna rashin jin dadin shi dan kawai Baba General yace shida Aeeshaa an hada su da 'yan uwan su, kamar cewa akai ba za a aura masa Aeeshan ba.
"Ni fa na zaci daga nan gidan su suka wuce ma da naji shiru,"
"Yah Ammar dan kai ne xan kyale ka, amma da ba kai bane da nace ai gwanda mu, wasu kuma ji suke kamar su bar garin ma suje qasashen turawa dan shaqatawa,"
Dariya wajen ya dauka dan a fakaice dai ta rama kenan,
"Yarinya kin ci abinci, shi kk mayarwa da magana ko?"
"Soyayya ruwan zuma kar ku sata a gaba fa, ya isa haka,"
"Qaniyar ku, shin baku ganin mu ne a wajen?"
"Hajja tamu muko na Allah,"
"Laaaa