Showing 42001 words to 45000 words out of 69262 words

Chapter 15 - KUN MAKARO COMPLETE HAERMEEBRAEEH.docx

26 Oct 2025

557

komai kare qaryar da kikai ne ta farko ba wani abu ba'

"Kin kwanta ne?"

"A'a na dai koma dakina, kai fa?"

'Wayyooo Ummana what is wrong with me?'

"Ni na kwanta ke kawai nake son kasancewa da, amma an nuna min ban isa ba da iyalina an dauke min ke,"

Wani abu ta ji ya ratsa ta, wanda bata san meye shi ba,qanqame wayar tayi,tana sauraran sautin nimfashin shi, gaba daya ya saukar mata da kasala,

"Hello? Ki na jina kuwa?"

"Ina jin ka,"

"Bakice komai ba"

"Yah Khaleefa kayi hakuri, ba laifina bane, da da yanda zan dana zo gare ka, kasan koda bamu son juna ba zan taba hana ka abinda Allah ya yi naka bane, bana daga cikin matan da suke sanya kan su cikin fushin Allah da sanen su, sai a bisa kuskure,"

'Sarkin wa'azi,oho miki yau dake nake son na kauda kwadayi na ta wayar nan,bari nai amfani da wa'azin naki nima' ya faɗa a ran shi.

"Indai kin san haka ne to ya kamata ki ban haqqi na yanzu,"

"Yah Khaleefa ta yaya?"

"Baki sani ba?

"Eh tinda baka kusa bana kusa, ya zan na baka haqqin ka?"

Idon ta ne ya kawo hawaye,' Oh mutumin nan yana buqata ta kuma an faɗa mana in miji ya nemi matar shi bata biya masa buqatar shi ba Allah da mala'ikun shi na fushi da ita, yanzu ya zan yi?'

"Kina jina ba?"

"Eh ina jin ka,"

"Yauwa tashi ki rufe qofa sosai da key,ki dawo,ki saka rigar baccin ki mai kyau a jikin ki, ki jira ni zan sake kiran ki, amma ta whatsapp ai naga kina yi ko?"

"Eh ina yi"

Kashe wayar yayi, ita kuma ta tashi ta leqa parlour ta ga ba kowa, an kashe wuta, komawa tai tana jin kunya, dan ta san Hajja ta gano dawa take waya, umarnin Khaleefa ba wanda bata aikata ba, tana tinanin to zuwa zai ko ya abun yake?

Khaleefa kuwa d'aki ya koma ya cire kaya, ya bar boxern shi, ya haye gado, ya kunna laptop, nan ya shiga whatsapp, ya lalubo ta, video call ya kira ya ji shiru, daya duba sai yaga bata online,tsaki yayi ya kira ta, yace ta kunna data, kunnawa tai ta kwanta, a zaton ta chatting zasuyi, sai mamakin su take, ohhh wato dan an raba su shine yanzu yake son ya na kula ta, yaushe magana mai daɗi ta taba shiga tsakanin su?

Yana ganin ta online har wani lashe harshe yake, kamar tsohon maye.

"Hey"

"Assalamu alaikum"

🙄

"Wa'alaikumussalam"

"Bari na kira ki video call, "

"Ok"

Hijab din ta ta dakko da sauri ta saka, aiko yana kira ta aje wayar yanda zai dinga ganin ta.

Khaleefa kafin ta amsa har ya zare boxern shi, yana jiran ta dauka, aiko tana dauka tai arba da Khaleefa hannun ta na rawa ta kashe, qirjin ta na bugawa, ko da suna tare ai bata taba ganin shi a haka ba tin ganin da ta masa a gidan su tana aikin sabon shi.

Meye hakan yake son yi,

Message ya turo mata yana ta zabga masifa, wai ta wulaqanta shi, yau sai ta kwana cikin fushin Allah, ya kira dan ya samu su yi abun su ta waya tinda an dauke ta, amma take neman wulaqantashi, to yanda ta wulaqanta shi itama sai Allah ya wulaqanta ta.

Kuka kawai take, tana karantawa, amma ai aikata hakan zai iya jawowa su aikata haramun, tinda in suka fara hirar da zata tada masu sha'awa dole zasu biyawa kan su buqata da hannayen su ne,hakan kuma haramun ne sosai to ya zata yi ne? Ga shi can sai fushi yake da ita harda kira mata wulaqanta a wajen Allah,

"Kije ki riqe abin ki, zan kira wasu su ban abinda kk hana min"

Dummmm gaban ta ya yi muguwar faduwa, kiran shi ta dinga yi amma yaqi dagawa, daga qarshe ya kashe wayar shi, message ta yi ta turawa ta whatsapp tana bashi hakuri yaqi dubawa ma kuma tana ganin shi ya sake hawa online, ina zata saka kan ta yau tinani tai tinda yaqi saurarar uzirin ta shikenan, gwanda ta barshi ai ba yau ya saba ba dama.

"Ka ji tsoron Allah a dik abinda kk aikatawa yana ganin ka,"

"Da tsoron ki zan ji, kar ki kawon raini dan kinga na nemi wani abu wajen ki, haqqina ne ba dan haka ba ke baki isa na tsaya ina maki magana ba ma,"

Kashe data tayi, ta kwanta, can ta tashi, ta kunna, still yana online, shiga contact din ta tayi, tana duba numbers da take da, tana cikin dubawa taga Hadiza ma na whatsapp ashe, murmushi tayi, tana shiga contact din hadizan sai ta ga tana online,murmushi ta sake yi,

"Ohh Hadixa ko dawa ake hira da tsohon daren nan?"

Sallama ta mata, Hadiza ta gani taqi amsawa, can ba a jima ba sai taga message daga Khaleefa, da sauri ta duba,

"Ke sauka online, in kuma da wani qaton kike hira sai naji,"

Baki bude cike da mamaki ta sauka, wai ita ke magana da wani qaton, to a ina?lallai Khaleefa ba dama, to ita da bata kula shi ba ya akai yasan tana online? Ko kuma duba wa yayi yagan ta? Oho dai yaje yaci kan shi ta sauka.

Addu'a tayi ta kwanta, bacci ne mai nauyi cike da mafarke2 kala2 na ban tsoro da kuma nishadi ya mamayi baccin ta.

Allah ya tabbatar mana d alkhairi kedai Aeeshaa.

***********************

Tinda Aeeshaa ta tafi khaleefa bai je gidan ba, yau cikin Aeesha ya shiga wata na tara kenan, iyakar shi yaje wajen Rebecca ko ya dau Hadiza su faki idon mutane su shige gidan su sheqe ayar su, ta fita,ko suje inda suka saba zuwa.

A hankali son kasancewar ta matar Khaleefa ke shigar ta, da kawai so take suna debema juna kewa, amma yanzu auren shi take son yi dan ta dandana daula itama.

Wani babban abin haushin kullum sai sunyi waya ko chatting da Aesshaa, ta ji lafiyar ta wai da babyn ta, tayi2 taji cikin Aeeshaa akan zaman su da mijin ta taqi sanar da ita komai, sai tayi ta tambayar ta khaleefa ya je kuwa? Aeeshaa kullum sai tace mata me yasa take tambaya, taqi dai bata takamaimai amsa.

*********************

"Kasan Allah yau in baka zo gidannan ba sai ka ci Uban ka, kar ka ga ina daga maka qafa kana kiramin aiki in ka dawo ka gaji, kuma kana waya da ita, na gaji da jin uzirirn ka,kazo yau dinnan, dan matar ka ta wuni naquda, anjima in mun daidaici abin yazo gadan2 zamu kai ta asibiti"

"Haihuwa kuma Hajja? Wace irin haihuwa? Ko dai bari?"

"A'uzubillahi min kulli sharrin dan uban ka, wanne irin bari? Ciki wata tara cif ana xancen haihuwa, dan ka ja mana mugun baki kk kiran bari; sai dai ka barar da abincin ranar ka shegen yaro mai mugun fata,ga babar ka nan tin safe take sintiri akan yarinyar nan, tinda uwar ta ta zama baqauyiya taqi zuwa, in baka zo ba nan da minti 10 zaka isko mana a asibiti"

"Kuje na taho,'

Hajja ta kashe waya tana ta masifa,

"Dik iskancin dake kan ka ka gama, bari ta haihu lfy hankalina ya nutsu waje daya, ai na gano inda kk zuwa yanzu daga wajen aiki, ba wajen karuwa ba ko wajen magajiyar karuwai ne sai na sa an kulle ta an kulle gidan nata, 'yan iskaa marasa tsoron Allah, ba abin tausayi irin Baban ka da General, sun aminta da kai matuqa kana nan kana iskanci,ita ma sallamammiyar matar taka ba zata iya faɗa ba kamar wanda kaiwa asiri ka rufe mata baki, dik to zan iya daku dika, marasa mafadi kawai,"

(Dama alaqar su Hadiza aka hango tafi ban huashi ni fa😡)

Asibitin da take zuwa aka kai ta, likitan na ganin ta yaggguta sallamar wanda yake gani, ya miqata wajen daya Dr. Dan yana matuqar son taimakawa Aeeshaa.

"Sannu Aeeshaa, abin yazo kenan, ku shiga da ita, ina mijin naki? Ko har yanzu yana kan bakan shi na zubda cikin,"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, me nake ji haka?"

Da biyu yayi maganar, dan kamannin Aeeshaa da Khaleefa kamannin wannan dattijuwar, tabbas wata mata ce mai mahimmanci a rayuwar su, dole ya faɗi hakan dan ta sa ma ma'auratan ido, Aeeshaa kuwa bata son sirrin gidan ta ya bayyana, kullum addu'a take Allah ya gyara mata lamarin ta, bata son asirin Khaleefa ya tonu, ko da ba mijin ta bane zata so ya shiryu ba tare da kowa ya san meke faruwa ba, amma likitan nan ya sa Hajja zata matsa sai ta san komai.

An shiga da Aeeshaa Hajja da Maman Khaleefa hankalin su ya kasu kashi biyu, dama baya son haihuwa? Amma Aeeshaa taqi fadawa kowa? Lallai wannan yarinya a gaishe ta, sai tinanin haihuwar ta.

Hajja ce ta dauki waya ta kira Umman su Aeeshaa,

"To bafulatanar daji, tana dakin haihuwa sai ki mata addu'a"

Kit ta kashe wayar ta, dan ta san indai Khadeeja ce bazata samu kyakkyawar amsa ba.

Hassana da ummeen sabeer na gida suna aikin tarbar baqo ko baquwa, farfesun naman rago Ummeen Sabeer ke dafawa, Hassana ta dora ruwan wanka a bangaren Hajja, sai addu'a take Allah ya sauki Aeeshaa lfy.

Likita ne ya fiton yana washe baki,

"Mama a bani goron albishir gaskiya,kafin na fadi kinyi Amarya,"

"Alhamdu lilLAAHi ai ka riga ka faɗa, ga wanda yayi amarya nan, mu kam diya ce muka sake samu,ga uban yarinya kuma anan,"

"Baba General ne ke wannan maganar daidi lokacin da yake qarasowa, bai taho ba sai da ya biya office,din Baban Khaleefa ya dakko shi sannan ya taho da khaleefan, in ka gan shi da Baban khaleefa sai ka rantse abokai ne,babu ruwan shi da daukan kai ma yaran shi, yana jan su ajiki sosai, komai tare sukeyi musaman na family.

Khaleefa ba mai gane yanayin shi, fuskar nan kamar kullum cike da munafukin murmushi.

Hajja wani kallo ta watsa masa na zamu gaura da kai ne.

Dakin da aka gyara mai jego da baby suka shiga, nan kowa ya dinga yabawa yana ganin qoqarin Aeeshaa na haifar wannan narkekiyar yarinyar.

Khaleefa na rakub'e a gefe, ya rasa kallon mutuwar da Hajja take wurga masa.

Karambani ya kaishi daukar yarinya daga Hannun Baban shi bayan ya gama yi mata addu'a..............

*wayyooo cikina🤣🤣What do u think will happen guys?🤣*

KUN MAKARO

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 19

"In ka taɓa ta sai na sare hannayen ka da wannan silver din, dan uban ka ba b'arin ta kk son ayi ba? A zubar da cikin ko? Kar ta zo duniya, hummmm na maka murna a asibiti muke, da agida muke sai na maka dukan da zai tabbatar maka da sauran qarfina, shiyasa mutane ke cewa ni babar ka ce ba kaka ba, dan iska mara mutunci bar nan, ai ko ba kai za ta rayu, akwai uban ka akwai kakan ka, har suna dik zasu saka mata,ban taba sanin baka da mutunci har haka ba khaleef, ka fita nace ko? Ko kayi ajiya ne anan din?"

Kuka Aeeshaa take yi saboda a kwance take amma jiri take gani, jinin nan fa ya qi tsaiwa, Hajja ko a zaton ta korar da akao wa Khaleefa ne ya sata kuka,

"Kema taki uwar xanci in baki rifen baki ba,bari dik mu koma gida, in baki fadan asalin zaman da ku ke ba ni da ke ne, mun tattara mun miqa ki muna ganin shi mutumin kirki ne ashe dik rufemu yayi"

"Hajja bata numbashi,"

"Subhanallahi kira likita da sauri,"

Likita ne ya shigo da azamar shi, Khaleefa ba wanda ya san sanda ya bar wajen.

Ana ta qoqarin bata taimakon gaggawa, likita ya sanar da su Hajja jini ne bai tsaya ba,da sauri ta fita dan  komawa gida, driver ne ya maida ta gidan, sai azalzalar shi take yayi sauri, Hajja akan Aeeshaa bata da sauqi, wannan karon ba zata yi wa kowa da wasa ba, tinda aka d'ano ta sai tai harbi zata huce.

Tana isa gida, Hassana da Ummeen su sukai ta mata barka, hankalin ta tashe take amsawa, gyada ta debo danya, ta wanke ta jiqa sannan ta zuba gishiri kamar cokali daya da kaɗan, barin ta tayi kamar minti sha biyar, ta jiqu bayan ya fara kamar barewa da kan shi, ruwan yayi jawur, sai ta tsiyaye ta saka a gora, da azama ta shirya ta koma asibitin.

Ta je ta tarar da Aeeshaa ko motsawa bata iya yi tana nan kwance kamar Matacciya, an samu jinin ya rage zuba, dan haka ta bawa likita maganin da ta kawo, tace a bawa Aeeshaa zai tsaida jinin, musu ya tsaya mata akan ta hakura zuwa wani lokacin.

"Ina da 'yancin da zan bata da kaina, amma na baka, in wani abu ya samu jikata sai nai qarar ka, ni da ka ganni nan cikakkiyar 'yar boko ce ba 'yar gargajiya ba, balle kace zan mata wani abun da zai cuce ta,yanda nake son ta ko uwar ta bana so haka, maza amshi ku san ya zakuyi ku dura mata ta shanye,"

Amsa likita yayi, ya shiga ciki suka fara qoqarin ba ta Hajja na kallo, dan bata yarda ta barshi ba yaqi bata.

Suna nan zaune kamar awa daya, ta farka, tana jin yunwa, kowa sai murna yake,jini ya tsaya, ba wata matsala yanzu, sai satar kallo yarinyar take,

"Amshe ta ki riqe abin ki, ke kinfi kowa sanin ciwon nunawa yaro qiyayya, ke zaki bawa wani labari ma, amshe ta ki mata addu'a ki sa mata albarka, sannan ki tauna dabinon nan ki bata, a bata zamzam dinnan, Allah ya muku albarka, ya qara maki lfy ya yara mana ita da imani"

"Ameen Hajja na gode sosai, Allah ya ja mana da ranki,"

"Ameen Aeeshaa ta, maza bata kema ki ci abincin, hada mata shayi kai Muhammadu,"

Mugun kunya ne ya kama Aeeshaa da taga Baba da kan shi yana hada mata shayi cikin farin ciki da kuma son yin hakan.

Mama sai qoqarin amsa take amma ya dakatar da ita,

"Basshi kawai ke zuba mata abinci, ai ba wani abu bane, diyata ce fa, ko kin manta ne?"

Murmushi suka yi, ran Hajja yayi fari, a qalla Aeeshaa bata yi maraicin uba ba duk da baya nan  amma kuma ta na maraicin  Uwa duk da kasancewar ta a raye,tana kusa amma kamar itace ta mutu.

(Hajja bata da labari fa yanzu Umma tana zuwa wajen Aeesha a sace)

Waya ta dauka ta kira Khadeejan,

"Ta sauka an samu mace, in kinga dama kizo ko ki zauna, muna nan muna dik abinda ya dace uwa tayi, "

"Hajja dan Allah kiyi hakuri ina nan tafe in kun koma gida,"

"Kar ma kizo ki yi zaman ki ni kaɗai na ishi gayya,"

Kashe wayar tai tana ta mita, Baba General ya san an tabo masa mata, ya fi kowa sanin a wannan yanayin ya yi shiru ya mata biyayya shi yafi masa alkhairi.

************************

Khaleefa daya koma gida,kwanciyar shi yayi ya na baccin rana, ko a jikin shi, dan an hana shi daukan yarinya ai dama shi bai so aka haife ta bama, suje suyi ta dawainiya su suka ga zasu iya.

Bai farka ba sai wajen magrib, qamshin abinci yaji, kawai sai Aeeshaa ta fado masa a rai,

'Amma wannan ba irin girkin ta bane, girkin ta ai tada shi zai a barci tsabar daɗin qamshin shi, and ta haihu ya za ai tazo yi masa girki'

Sauka yayi a gadon yana murje idon shi, daga shi sai boxer, dan shi yana son zama haka, tafe yake kamar baccin bai ishe shi ba, ganin ta yayi a tsaye a bakin qofar shiga dakin, sanye da rigar shi, ta riqe ludayin motsa miya, ba ko dogon wando, ta daure gashin ta data qara a bayan kan ta, tana wani rausaya.

"Hadiza? Yaushe kk zo? Me kk yi haka? In wani ya shigo ya gan ki a haka fa?"

"Sai kace masu amaryar ka ce ni?"

Dan dariya yayi ta baki da hankali ya shige toilete, ita kuwa daɗi ne ya kashe ta tayi tsalle ta faɗa gado, tana wurwurga qafa tana murna, ita a dole Khaleefa yaji daɗi tace ita amaryar shi ce.

Bayan ya fito ya tarar da ta kammala shirya abinci,ba kunya ba tunanin komai suka zauna suka ci,shidai kwata2 ba zai ce ba daɗi ba, ba kuma zai yaba ba, sai jira take taji ya yaba, taji shiru, dake 'yar bariki ce sai cewa tai,

"Gaba daya yau ban ji daɗin abincin nan ba, banga maggi ba, haka nayi shi ina jin shi yasa bai daɗi ba sosai,"

Khaleefa a ran shi yace

'Gaskiya mana abu ba wani daɗi haka, ai na zaci iyakar kwarewar ki kenan'

"Ayyaa aiko yan nan baki kula bane, ba laifi ai za a iya ci haka,"

Kada ido tayi

"Dan ma renon Goggo ce,kasan tsoffin da suna girki ba maggi kuma yayi dadi,"

"Haka ne kam, kamar yanda kk da d*** ba,"

Anzo wajen, nan da nan ta washe baki, sauri2 suka gama ci, ko kwashe plates ba ta san ta yi ba, sai shi ya fara kwashewa dan baya son datti, yana shiga yaga kitchen kaca2 a aiki ɗaya ta maida shi kamar an dad'e ana aiki ba gyara, ledojin maggi ya gani ko ta ina sai kawai ya kad'a kai, maggi an tafka shi an gode Allah, ko a zaton ta maggi shike girki oho?

Gyara wajen ya fara tana taya shi, ita fa bata son aiki sam, haka suka kammala, a kitchen din ta d'afe shi,nan da nan suka fara aikin na su na rashin mafad'i,Khaleefa Aeeshaa kawai yake hangowa, inama zata zama romantic haka, ai da da ita zai wannan lamari a kitchen, haka dai sukai ta sabawa Allah hankalin su kwance.

**********************

Ranar suna, yarinya an rada mata suna Khadeeja, suna kiran ta da Ameerah, Umma kam ta aje kunya a gefe, dan ba dan Adam din da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login