Showing 60001 words to 63000 words out of 122268 words
Chapter 21 - MATAR MAKAHO DOCUMENT BOOK COMPLETE by Rukayya Ibrahim Lawal.txt
harkan science"
Kai Aunty tsadane fa da school in kuma ga kudin registration mai yawa gashi wai sai anye Attitude test kafun abawa mutum gurbin karatu.
Khadija kenan indai kin yarda da kanki Attitude test bazai baki tsoro ba maganan tsadan registration, kuma ai kyaunsa yasa kudin yayi yawa, duk da makarantar goverment ne"?
Gaskiya ne sumayya kinsan koh lokacin mu ba makarantar da ta kaita inganci kyau da doka kuma sai wane da wane ne a ciki a kaf Taraba daga goverment har private Amma yanzun xamani ya chanja saidai a sata a lissafin goverment school mafi inganci
"Yauwa bara na tashi in shirya kaima sai muje dakai yayan khadija zan bude account a bank da voter's card naka"
Nikam gaskiya ba inda zani tunda khadija tazo da National ID card nata sai a bude miki babban Account kawai.
"Kace kawai bazaka ba shikenan"sumayya tace tana mikewa,kaya ta fitar zata saka ganin haka yasa khadija fita a d'akin ta bata waje
Nifa kawai zuwanne banji shiyasa nace kije da khadija
"Toh zamuje daga nan saina wuce bank in, nama manta ban fad'a maka ba nayi posted na vedio n make-up da lalle harda photos yanzun haka next week za'ayi bikin yar kanwar Deputy Govnor an bani kwangilan musu lalle da make-up kawaye kawai da Amarya"
Duk sunzo gidan nan?Al'ameen ya tambaya da mamaki
"Ah ah a online fa muka gama kome har balance na fad'a musu yanzun ma jiran Amaryar take na tura mata account numbar na"
Wow Allah abin godiya Amma dai sunan ki da suka ganine yasaka su baki aikin hala?
"Wani irin suna kuma?toh ni ban ma saka sunana ba wani sunan na saka"
Wani suna kenan?
"Basai kaji ba" tace tana yafa gyalenda ta d'auko sai jaka da takalmi data rike a hannu zata fita a d'akin sai kuma ta sake juyowa ta kallesa jin tambayar da ya mata
Sumayya baki bani bluetooth in ba?
"Ikon Allah"tace hade da nufar cikin kayanta, Allah yasa ma tayi charge insa, makala masa tayi a kunne ta saita da wayanta," waka zan saka maka koh wa'azi"?
Waka....
Wakar ta kunna masa"ga wajen da zaka taba ta gefe in zaka danna next koh back koh stop koh play"tana fad'a tana kama hannunsa tana nuna masa gun
Eh na fahimta, saikin dawo
"Allah yasa zanbi kasuwa duka me zan saya maka"?
Kasuwa kuma sumayya?
"Eh mana koh bakason naje? na saima khadija uniform ne da kuma d'an cefene nakeso na mana na sati uku kafun a fara azumi"
Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya
"Ameen baka fad'a mini abinda zan sai maka ba"
Am waken Gembu(Red beans)nakeso inkin iyya dafawa yanda suke innan asa tarugun Gembu(yellow pepper) da ice fish, irin dafin.
"Hhhh eyeee kaima har kasan hadin dadi haka bansani ba"
Allah inason abincin sosai...
"Shikenan zan saya maka sai mun dawo"
Allah yasa...
Ameen, sumayya tace tana fita a d'aki, suka nufi kofar gidan da khadija
Sunje makarantan kuma Alhamdulilah khadija ta samu gurbin karatu a makarantar science bayan interview da aka mata don an riga anyi Attitude test tun bayan sati uku, sun bawa khadija class, sumayya ta biya kudin kome atake aka mata registration aka bata su textbook, notebook , da tarkacen kayan makaranta su rigan sanyi rigan house socks vaji da sauran abubuwa
Bayan sun bar makarantar yau kam duk wanda yaga khadija koh ba'a fad'a masa ba yasan tana cikin farin ciki sosai bank sukaje sumayya tasa aka budewa khadija Account .
Kasuwa suka wuce tasai ma khadija uniform jaka da takalmi don sune kawai ba'a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d'inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta.
Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks, doya, dankalin hausa, harda na turawa, vegetables, kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d'an abinda baza'a rasa ba
Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d'aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi
Wa'alaikumus sallam, sannun ku da hanya Al'ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa
"Yauwa yayan khadija" sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi
Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita
Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawaπ
, tana fad'a tana kamo hannun yayanta ta d'aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi
Shima karan kansa Al'ameen yayi mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka.
"Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d'aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan"
Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa
Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti
Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin.
"Shikenan monday zaki fara zuwa jibi, kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge, gata sai school"π
Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa goggo kona barshi Anan?
"Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi"
Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita
Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al'ameen ya fad'a yana lalubar hannun sumayya ya kama
"Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji"
Allah yasa, kema Allah ya biyaki
"Ameen, na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna"
Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben
"Ameen", tace tana d'aukar wayanta dake neman agaji"Assalamu Alaikum"
Shuru tad'anyi sai kuma yaji tace "toh bara na tura miki ta WhatsApp"
"Ok shikenan", tace tana aje wayan
"Kasan waya kira"?
Ah ah ...
"Yar kanwar deputy ne waina tura account number"
Toh Allah ya bada sa'a
Ameen, bara na tura musu
Tashi Al'ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa
sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba'ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in.....
Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad'i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama'a na illalilahi keeee kalli gabanki
Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu.............
πππππππ *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* π
ππππ *Turare suna d'ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*
ππππ *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*
πππ *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*
πππ *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*
π *Na tsunguno(habil)*
π *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
π *Turaren turara jiki after birth* ,
π *Na d'aki(halud Al'oud)*
*UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* ππΌππΌ
πππ *Suna bada d'aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*
πππ *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*
Contact them vie
πͺ08028827241 or 09033791049
IG @umsadincense
πππππππππππ
π§βπ¦― *MATAR MAKAHO* π¨βπ¦―
~ Na ~
π *Rukayya* *Ibrahim* π
β¨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za'a ga mistake Koh typing error Amin afuwaπ
free book π€§
Page 4β£8β£&4β£9β£
Da karfi khadija ta watsar da kayan hannunta tsungunawa tayi jikinta na bari ta kama kai, gabaki d'aya ta gama sadakar wa yaukam sai Ta Allah
Cikin zafin nama da haushi mai motar ya fitoh da fad'a fad'a,kee wace irin wawuyace wai kina tafiya koh ganin gabanki bakyayi da yanzun na kadeki fa baki jawo mini matsala ba gashi yanzun kinsa na buge keke napep innan da sai dai me zan buge? nosense kawai stupid
Khadija kam har yanzun bata dawo daidai ba ga kuma tsawar da ake buga mata, d'aga kanta tayi tana kallon mutumin don Allah kayi hakuri wallahi bangan ka bane
Da mamaki mutumin ke kallon ta sai kuma yayi murmushi, ke bakece kanwar Al'ameen ba?
Eh.....eh..nice
Murmushi kawai yayi hade da dukawa a tsakar titin yana tattara mata kayanta,saiki taso ai inba so kike wani motar tabi ta kanki ba
Khadija kam cikin had'a fuska don sai yanzun takejin haushin zagin da ya mata, mikewa kawai tayi ta koma gefen titin
Kizo ki shiga mota na kaiki gida?
Bazan hauba, kuma ka bani kayana nikam.
Kinji haushine khadija?
Da mamaki take kallonsa toh a ina ya santa gashi itama tun d'azun sai tunanin inda tasan wannan fuskar take
Ke yar Kauye bar kallona
Naki dainawa kuma miko mini kayana, ta karasa maganar da kai hannu zata karbi laidodinta
Da sauri ya kauce hade da cewa, ke khadija nifa yau gidan yayanki zaki kaini yau kusan wata biyu ina sintiri a sintali kowa na tambaya Al'ameen mijin sumayya sai ace ba'a gane saba yau ma Allah ne yasa zamu hadu shiyasa na biyo ta bakin kasuwa.
Aikuwa bazan nuna maka ba, ba zagina kake ba
Yi hakuri haushi naji Shiyasa yanzun muje ki nuna mini gidan yayan naki
Gaskiya ni yanzun gida zan koma ba gidan yaya ba sauri nake
iyeee nace ki nunamin gidan da nafi wata biyu ina nema shine zaki wanice kina sauri
Kaga malam ni yanzun ma haka gidan na fitoh gaskiya bazan koma ba saidai nama kwatance
Toh shikenan yi mini, kuma ga kayanki karki shiga motar inkin ga dama
Oho maka dai, inka tsallaka titin nan sai ka mike kaga lungun shan kana shiga zakaga babban titi da yayi barade ka tambaye masu shagunan wajen, gidan Adara za'a nuna maka saika aike yaro kofar MAKAHO
Ok toh shikenan naji, yace yana komawa wajen mai keken biyansa yayi asaran da ya masa, ya shiga motarsa yaja
Khadija kam da ido ta bisa ta kasa tuna inda tasan bawan Allah nan Amma tabbas akwai inda ta sansa.
**************
"Yayan khadija gaskiya nifa yau bazanyi girki ba wallahi na gaji wanka zanyi na kwanta "
Kidaiyi wanka amma banda kwanciya kinsan bakyau bacci bayan la'asar koh?
"Gaskiya ne amma dai zan d'an taba kafun goshin mangariba saika tashe ni"
In ance abu ba kyau sumayya ki gujesa don Allah kidai kwantan koh waya koh TV ki kallah Amma banda bacci kam.
"Toh shikenan akwai kudi a purse nawa anjima ka sayo mana abinci"
Ah ah zan dafa...
"Zaka dafa kuma yayan khadija, kaji mini kaudi"π€
Nine mai kaudi?π³
"Eh man in ba kaudi ba ina kai ina girki, salon kaje ka kone koh ka yanke ba"
Amma dai wallahi sumayya kin gama raina mini wayo me kika maidani ne wai?
"Sorry toh me zaka iyya girkawa"
Oho.....
"Yi hakuri mana wasa fa nake maka"
Ba wani, ya karasa maganar yana zama a bakin dakalin
"Banace kayi hakuri ba, habba danejo Am heedee Am buddi Am yafannam lee"ta karasa wakar da kamo hannunsa ta nufi kitchen in dashi
Kinga sakeni nafa fasa girkin bara kiji karma ki kama mini wani waka wai ma tsaya ke bafulatana ne daman?
"Bororoje ce ba bafulatana ba, kuma girki sai kayi ehen"
Ke wai ana girkin dole ne?
"Yau sai kayi ai duk wanda yayi niyar aikin lada sayya karasa"
Toh nace na fasa koh
"Nikuma nace sai kayi" ta karasa maganar da dokarasa akan kujeran kitchen in
Kin zama yayi inta dosana sa saiya cije"wai kai kam menene haka kasan Allah yau saikayi girkin nan"
Zama yayi ba yanda ya iyya
"Me ka iyya girkawa"?
Me kikeso na girka miki?
"Iyeee lallai ma watoh am bani zabi kenan irin ga k'wareren nan"
Eh fad'a mini me zan girka miki?
"Waken gembun jiyan nan zaka girka"
Ah ah gaskiya banda shi don nidai ban iyya ba, don ni ba d'an gembu bane.
"Hhhhh bakar magana koh"?
Kema Aishi kika fad'amin
"Shikenan yanzun me ka iyya dafawa maganar gaskiya nafa gaji da tsayuwa kwanciya nake son nayi fa"
Doya na iyya soyawa da indomie, kwai, harda taliya dafa duka sai Tie
"Doya Da k'wai ka iyya soyawa ko daban daban"?
Soyayyen doya,kwai ma soyawa na iyya, da dafawa
"Ok sai ka soya mana doyan da salt daban saika soya kwai shima daban akwai yaji a roba ka hada mana da ruwan bunu"
Sannu hajiya,π yace yana kokarin lalubar bojuwa(tukunya)
"Waye hajiyan kadaiji dashi"bojuwan sumayya ta wanke ta d'aura akan hot plate tasa masa mai Amma bata kunna ba Albasa ta yanka a ciki, doya ta d'auko da kwai tarugu Albasa lawashi maggi gishiri ta aje masa a kusa dashi koh wanne a roba koh tire koh gwangwa ninsa ruwa ta iba a boket tasa kofi ta aje masa duka don ya huta da tashi koma ransa innan" ga kome a zaune Allah yasa yayi dadi"tace tana fita a kitchen in
Baiyi magana ba kawai wuka ya d'auka yafara feran doyan
Ruwa sumayya ta iba tayi wanka kaya tasa ta kwanta duk da Al'ameen ya hanata amma baccin tuni ya sace ta
Al'ameen na tsaka da feran doya yaji salaman yaro, amsa masa yayi
Wai ana sallama da MAKAHO
Inji wa?
Nima ban sansa ba yace dai in masa sallama dakai
Ok kaje kace masa ina zuwa
Toh, yace yana fita a kofar
Tashi Al'ameen yayi ya wanke hannun sa ya shiga d'akin, sumayya!ya kira sunanta jin shuru bata amsa ba sai numfashin ta dake sauka akai akai, girgiza kai kawai yayi ya d'auki sabon riga da wando da sumayya ta sai masa ya saka ya cire 3quiter dake jikinsa, waje ya fita yana mamakin waye yazo gunsa yau haka
Waje ya fita yana tattaba jikin ginin kofar gidan don jin ina mai sallama dashin ya tsaya jin baiji motsen saba ya sakasa, kara maimaita sallamar
Wa'alaikumu salam Al'ameen
Laiiiiii wana kejin muryarsa kamar Ammar?
Baka mantani ba Al'ameen ka rike sunana baka manta ba.
Habba Ammar wanda ya maka hallaci irin wanda kamin ai ba mutumin da zaka manta dashi bane
Hakane Ya mai jikin?
Da sauki sosai Ammar, ya aiki ya gida?
Lafiya kasan yau kusan wata biyu da dawowa na ina zuwa unguwan nan ban gane kaba wallahi har Hospital in na koma sukace ai an mata tiyata ma har an sallame ku tuntuni
Eh kam satin mu d'aya aka sallame muma tuni.
Allah sarki yamai jikin toh?
Da sauki fa sosai kamar ma ba'a taba yanka taba, na barka a tsaye muje bakin dakali
Ok toh in ba damuwa naga dakalin da rana kazo mu shiga cikin mota mana?
Tsakake Al'ameen yayi yana nazari kutt anya zai yarda ya shiga motar mutun da bai sansa ba(lokacin da ya taimake ka ka sansa ne) Am daman ina d'an aikine a gida nama manta na d'aura tukunya
Murmushi Ammar yayi watoh har yanzun Al'ameen bai yarda dashi ba kenan, toh ba kome nima bara na wuce naga yamma tayi sai na sake zuwa
Toh shikenan nagode da ziyara Ammar
Toh aje a cigaba da aiki mijin hajiya hhhhh
Hhh Ammar kenan, ya fad'a yana mikama Ammar hannu sukayi musabaha a karo na biyu
Bayan tafiyar Ammar cikin gida Al'ameen ya wuce yana tunane tunane sai kuma yaji bai kyauta ba da Ammar nason cutar dashi da randa ya d'auke sa da sumayya ya cuce su, ta wani bangaren kuma sai yaji gwara masa hakan babu ruwansa da mutanen duniya sai mutunci yanzun bai yarda da kowa ba haka zalika tsoron shiga mota ne dashi tunda masu mota suka makantar dashi, kauda tunanin yayi ya cigaba da aikinsa, daya ya gama fere doyan ya zuba a roba wankewa yayi ya tsame a kwando ya zuba gishiri kunna hot plate in yayi ya kama Aiki.
Bayan kammala girkin Al'ameen juyewa yayi a kula ruwan shayi koma a flask wanka yayi yashiga d'akin, har lokacin sumayya bacci take, hawa yayi kan gadon a hankali ya kamota d'agata yayi cak yayi waje da ita ajeta yayi a kan dakali
Ido sumayya ta ware jinta a sama kafun ma ta gama nazartar inda take taji an ajeta a dakali"menene haka"?
Mangariba ake kira baccin ya isa haka, watoh bakiji bakisan baccin mangariba akwai matsala bako
"Baccin kwasheni yayi ai"
Sai kiyi Alwala nikam na tafi masallaci, bai saurare abinda zatace ba ya fita abinsa
Itama samayya Alwala tayi ta shiga d'aki...
Bayan sallan isha Al'ameen ne ya shigo kofar su, kitchen ya wuce ya d'auko kulan da π½ ya shige d'aki
Sumayya dake kwance fuskarta sanye da glass ta d'aura system inta akan cikinta tana daddan nawa,d'ago kanta dake kan fillo tayi tana bin Al'ameen da kallo ganinsa d'auke da kula sosai tayi mamaki matuka, don ita harma ta manta da zancen zaiyi girki" ikon Allah wai da gaske kake kayi girki"?
Idanunki zai nuna miki, yana magana yana fita a d'akin bayan ya aje kulan hannun sa da plate da shukula, sai kuma gashi ya dawo dauke da flask da cups, ajewa yayi a hankali akan cafet ya zuzzuba doyan da kwai sai yaji a gefen plate ya tsiyaye tie a kofuna
Itakam sumayya sai ido kalala take kallonsa dashi"wai duk wannan kaika soya"?
Eh man bakin raina ni ba an gaya miki in mutum baida ido shikenan sai akace bazai iyya abinda masu ido keyi ba, ai harma yafi namasu ido muna iyyawa
"Ah ah kwadai kwatanta Amma badai yafi ba malam"
Au karya zan miki kenan?
"Bance ba,ina nawa doyan naga ka zuba plate d'aya"?
Eh namu ne yau tare zamuci a plate d'aya
Sumayya batayi magana ba sauka kawai tayi akan kujeran hannu kawai tasa ta fara cin doyan " kai maggi yayi yawa"
Kiji tsorin Allah fa sumayya
"Toh da tsoron ka zanji"
Amma dai k'wan nan babu maggin da yaji inba sharri ba
"Nikam naji, k'wan