Showing 6001 words to 8033 words out of 8033 words
Chapter 3 - Fatalwar Budurwar Mijina Complete Hausa Novels by Mujaheeda.txt
hatta window d'in nata tana cikin duka Gardiner yanzu haka bud'e take iska Mai sanyi nashiga kuma tana iya hangar Wannan iccen dama kabarin Zeeza Saidai inba Wanda yasani ba, bazaka tab'a cewa Anyi tonon k'asa wurin ba, Saida tafara waya dasu Zahra sannan tashiga toilet, tagama wankan duka tafito harta shirya taji Kamar Ana Kiran sunanta da wata irin murya cikin kuka,
"Falmata!!!! Kitaimake Ni,"?
Kalmar da taji tana fitowa Kenan ta window d'in,
Cikin k'arfin hali tanufe window d'in talek'a bakowa Amma wani irin duhu yagame wurin
Iska tasoma kad'awa da k'arfi take labulayen d'akin suka Soma fira sama kamar zasu cire, wutar d'akin ta d'auke take d'akin ya game da wani matsanancin duhu wanda ko hannunka baka iya gani, tsoro taji da sauri tajuya ganin meya kashe hasken, kawai taji Anshak'o wuyanta tabayan Anyi sama da ita Ana k'ok'arin fidda kanta cikin Wannan k'aramar window d'in.............................
_TO FANSSSS MUN FARA KABARIN KO MEZAI FARU DA FALMATA A YANZU??? MUJE NEXT PAGE ZAMU SANI KUMA K'ARSHEN FREE PAGE IN SHA ALLAH_
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617
Or
07068956952
*FATALWAR☠️ BUDURWAR MIJINA*
_PAID BOOK #300 ONLY_
*MAY 5/2023*
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._
```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK..
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱```
_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *FATALWAR☠️ BUDURWAR MIJINA!!! PAID BOOK #300 ONLY* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_
*INAYIN LITTAFAINA DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*
*FREE 🅿️26 to 30*
_Last free page in Sha Allah, Wannan shine k'arshen free page so idan kinason Ayi tafiyar dake kibiya 300 D'inki....._
.....gashi Anrufe mata baki Sam takasa ihu, neman k'wacewa take Amma kasa A Yanzu Sam batada ma wani saurin kuzarin kwantar Kanta idanuwan ta sunfito suna neman kafewa,
Jin shurun yayi yawa Bata dawowa ba yasa yamik'e ya nufe d'akin nata, rufe ya tarda k'ofar nocking yafara"Wifey yadai shurun Lafiya kuwa ki bud'emin k'ofar Mana kizo ga Abinci"
Nanma shuru sake murd'a handles d'in k'ofar Yayi kuma saiya bud'e, shiga yayi yanata magana
Kan gado ya hangeta kwance tarufa da blanket ga Alama dai bacci take,
"Bacci kuma soulmate bakici Abinci ba? Kuma ko sallah bakiyi ba," ya k'arasa in Yana Hawa Kan gadon yana tashin ta,
"Wayyo zan mutu wuya na," shine Abunda tafad'a tana falkawa
Rik'eta Yayi "kinga natsu Soulmate nine fa, waye zai kasheki kuma,"
Jin muryasa yasa tabud'e idanuwanta kalle kalle tafara Amma komai Yana normal wuyanta ta tab'a shima lafiya da sauri ta sauka Kan gadon tadube wuyanta cikin madubin Amma ba Alamar komai,
Cikin mamaki tace"Wllh my soul shak'emin wuya Akayi harda d'agani sama sannnan Ana k'ok'arin fita dakan nawa cikin Wannan window d'in,"? Nuna Masa tagar tayi
"Hahahaha Kai soulmate kina Neman zautar da kanki Yanzu Haka saboda wad'annan magunguna ne ke Neman haukatamin ke, wazai iya d'agaki sama ta hanyar shak'ar wuyanki? Saikace A film ko labari,? Hahaha wllh wifey kinada Abun dariya yanzu Haka mafalki ne kike ba kina bacci na tarar dake ba,"
Shuru tayi Alamar tinani itadai tasan Anshak'o wuyanta tabayan Anyi sama da ita har tana neman mutuwa amma Yanzu tana bacci kuma bawata Alama hakan na nuna gaskiya mustapha ya fad'a,.
"Kada kisawa kanki dogon tinani zo muje yanzu Haka harda yunwa nadamunki,"
Tagama gasgata Maganar sa Kan mafalki ne, Dan Haka tabishi kawai Saida sukayi sallah sannan sukaci Take Away d'in da ya tura sani ya siyomusu,
Kwantawa sukayi daganan suka Lula sabuwar duniya........
Washe gari Tinda safe suka tashi tare sukayi wanka kitchen d'in tashiga tasoma girka musu Abinci
Saidai tagama takirashi yaci yabawa su Sani sannan Yawuce gun Aiki,
Zaune take ita k'ad'ai sai TV data kunna wayar ta nagefenta Bata jima da Gama waya da Zahra ba,
Nocking k'ofa taji Anayi, "Waye," ta tanbaya?
Amma shuru ba ansa Saidai Anata buga k'ofar
Tsaki taja taje tabud'e saidai bakowa Anan cike da mamaki tarufe tadawo ta zauna sake buga k'ofar Akayi Wannan karon da k'arfi kamar za'a k'arya k'ofar irin Mai bugun yagaji ba'a bud'e masa ba,
Tsoro yasoma kamata dakuma Jin haushin waye Wannan
Cikin masifa taje tabud'e har tana shirin fad'a da kowaye Amma nanma bakowa fitowa tayi duka taduba bakowa can ta hange Joseph Yana Aikinsa kwada masa Kira tayi yazo Yana fad'in"Sannu madam"
"Da kwai Wanda yazo gidan Nan ne,? Ma'ana wani ya shigo bayan fitar maigidan,"?
"A'a madam ba kowa Ni kaina Ina Nan ba Wanda ya shigo Sam,"
Shuru tayi tana mamaki
"Da matsala ne madam,"? Joseph ya jofo mata tanbayar
"A'a ba Komai koma Kan Aikinka kawai"
Komawa tayi ciki Had'ida barin k'ofar A bud'e,
Tana Zama taji Anshafi gefen fuskar ta,
Cikin tsoro ta waiga Amma ba kowa, zuciyar ta tafara dukan Tara Tara Bata Yi Aune ba taji Anja gashin kanta da k'arfi Anyi bedroom d'in ta da ita, jifa Akayi da ita daidai madubin d'akin,
Sam takasa Ihu Saidai kawai tanajin zafin buguwar da tayi da mirror d'in har wasu kayan saman sun zube k'asa, ga zafin Jan gashin da Akayi nata,
Da k'yar ta mik'e tsaye tana duban mirror d'in
Abunda tagani cikine yasata wartsakewa daga Jin zafin buguwar,
Jaaaa baya tafara tsoro tashin hankali duk suka mata dirar Mikiya
Fuskar wata mummunar halitta tagani cikin madubin tabbas Macce ce Amma kuma FATALWA☠️ Mai ban tsoro bakinta sai jini ke zuba halshenta har yana tab'a kasa gashi duk ya barbazu Kan fuskar ta,
Cikin wata irin murya Mara dad'in sauti tace"Yau na bayyana gareki Falmata, Ina son d'aukar ranki, kina son ganin Ainahin fuskata," tak'arasa Maganar tana babbaka wata irin ma haukaciyar dariya wadda take d'akin yafara rawa Haske ya d'auke,
Tamkar gunki saboda tsabar tsoro Haka Falmata tadawo tanaja baya,
Daina dariyar tayi tadawo kuka"Zan kasheki inason kasheki na rabaki da mijinki," tana gama fad'in hakan tazalo dogon hannunta tashak'o wuyanta tasoma gaurata Agini, Saida tasuma sannnan tabarta watsa Mata ruwa tayi tasake farfad'o FATALWAR ☠️ tasake makata Agini, gigitacciyar k'ara tasaki Saboda wahala tasake suma....
Sai Kusan k'arfe 6:00 yadawo yanata sauri ganin yabarta ita kad'ai
Tinda Ya shigo yaketa Sallama Amma shuru, d'akin ta yanufa kwance take tana bacci
Tashin ta yafara" Yana fad'in soulmate bacci yanzu, Kinga magunguna Nan na Neman haukataki nidai gobe zamuje Asibiti Asake Dubaki,"
Harta bud'e Baki dariyar bashi labarin Komai amma saita kasa bawai ta manta bane a'a kawai bakinta ya mata nauyi ne,
"Baki dafa Komai ba,"?
"Bari na dafa yanzu koda taliya ce,"
"Zaki iya,"
"Eh"
"Shikenan zanje masallaci"
_____________
Zaune take ita k'ad'ai tinani take Wai kodai tadawo mahaukaciya ne? Kwana biyu da batasha maganin ba tasoma jinta wani iri, tashi tayi tasoma binciken kayanta ta ya mutsa Komai can taga ragowar maganin d'auka tayi tana k'ok'arin sha, saiga Mustapha cikin sauri yazo ya fisge maganin
Cikin b'acin Rai ya Fara magana"Ashe dama Baki daina Shan Wannan mugun Abunba,"
"Taya zandaina bayan shine kawai maganin damuwata,"
"Ta Ina ya Zama magani Abu Yana Neman cutar dake da lafiyar ki,"?
"Au kana son Lafiya ta kasani cikin damuwar,"?
"Oh Falmata kada kikaini bango fa,"
"Sakina zakayi,"? Tayi tanbayar tana kafeshi da Ido,
Baice komai ba yajuya yabar d'akin
Cikin d'aga murya tace"Kadawomin da maganina fa,"
Bai nemeta ba ya rufe d'akinsa yayi Kwanciyar sa,
Kwance take Amma bacci yakasa zuwa mata
Kiranta taji Anfara
"Falmata!!!! Falmata!!!
Hannu kawai tagani ba jiki Yana Neman kamota, Jada baya tafara Kan gadon tana rawar Baki saboda takasa Aikata komai
Hannun cigaba da biyota yayi tincikin window d'in har cikin d'akin inda take,
Garin ja baya har ta fad'o Kan gadon, Dariya taji amma ba kowa "Bazaki tab'a tseremin ba," janyota Akayi da k'arfi Aka fita da ita waje,
Bata sake sanin meke faruwa ba Saida safe taganta ya she cikin Gardiner d'in
Inda take kwance taji wani Abu Koda ta duba D'an Kunne Macce tagani ya tsufa Sosai Dan harya fara tsatsa hakan ke nuni yajima cikin k'asar,
K'ura Masa Ido tayi kamar ta tab'a ganinsa Amma takasa Tina inane,
"Soulmate meya kawo ki Nan yashe haka," muryar mustapha taji,
"Bansani ba kawai nima na ganni Nan ne Wllhi, Gidan Nan wllahi Yanada Aljanu Nidai nagaji ka maidani Abuja kawai," tak'arasa Maganar tana kuka Had'ida barin wurin,
"Aljanu kuma,"? Ya tanbaye kansa,"?
Idanuwansa suka fad'a Kan D'an kunnen gabansa ya buga da k'arfi take yatina komai, Afili yafurta "kodai *FATALWAR ☠️ BUDURWAR TAWA ZEEZA* Itace ke wahalar da matata,? Wata Zuciyar tace masa A'a Wanda ya mutu baya dawowa," sauke Ajiyar zuciya yayi kafin yakoma ciki, lallashinta ya hauyi da k'yar yasamu ta sauka,
Saida ya fita tayi waya da Zahra ta fad'a Mata Komai Nan take cemata suna Nan tafe gobe ma sa ida Maganar,
Hakan kuwa Akayi bayan zuwansu suka keb'e sukayi maganar
Zahra tace," Indai kece keda Iskan ko Nan gidan masani ne ta hanya d'aya"
"Wace hanya,"
"Inada k'awa Anan Sajida ita zankira tasan malaman Nan garin,
"Kibari idan sunfita maje inda take kawai,"
Hakan kuwa Akayi daganan Sajida ta kaisu inda wani d'an duba, yabata wani turare yace "indai gidanki da FATALWA ☠️ to zata bayyana gareki Kuma kada kiji tsoro ki tanbayeta wacece ita, wannan kawai Zaki nema"
"To nagode,"
Komawa sukayi cikin sa'a kuwa su mustapha basu dawo ba,
"Falmata Zaki iya kuwa? Yin magana da FATALWA ☠️ Kuma sai cikin dare,"?
"Kada ki damu Zahra A Yanzu Zuciyata tabushe bana tsoron komai zan iya kodan Samun mafita ga Rayuwata,"
"Allah yabaki sa'a"
"Ameen"
Fira sukayi sosai Saida dare yayi sannnan su Abbas suka wuce nasu d'akin, Saida ta tabbatar mustapha yayi bacci sannan ta barshi takoma d'akin ta, tarufe k'ofa takashe hasken sannnan tazuba turaren hayak'i yafara tashi
Giegiza d'akin ya Fara k'aramar fitalar da ta kunna take ta d'auke dubu ya maye d'akin
Iska Mai k'arfi ta taso window d'in d'akin ta bud'e
Tagama tsorata A wurin Amma tadake ranta burinta kawai tasan wacece Kamar yarda Mlm yace tayi,
D'ago kanda zatayi taga Abu maimugun tsawo cikin farin nad'i tsawon sa baida iyaka Domin harya fice daga cikin Celine d'in d'akin dogon hannunta tayi sama dashi taciro kanta daketa zubda jini da bakin ta rik'e A hannu inda za'a ganshi,
Falmata kuwa Kamar taruga tsabar Tsoro da firgici Amma Mlm yamata gargad'in kada ta gudu idan tayi niyar guduwa to zata Ida nufinta Anan zata kashe ta gaba d'aya, dole ta tsaya jikinta na rawa tana kallon ikon Allah, da Ace Bata bushe zuciyar ta hakan ba data gudu,..
Cikin b'acin Rai na tadota daga makwancinta sama da Shekara d'aya FATALWAR ☠️ Tace........................
*KO ME FATALWAR☠️ ZATACE? SHIN FALMATA ZATA IYA MAGANA DA ITA KUWA? IDAN TAYI MAGANA DA ITA ZATA FAD'A MATA KO ITA WACE? SHIN RIGIMAR ZATA K'ARE ANAN NE? FATALWAR ☠️ ZATAYI NASARAR HALLAKA FALMATA? WAI ME ZAI FARU AGABA?????? SANIN DUKA TARIN WAD'ANNAN TANBAYOYIN TO KU KASANCE DANI NI MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN 👸 OF WRITER 📝 CHAMBER 300 NE KAWAI NUMBER TA ITACE 07064904617 AMMA KUSANI YANZU ZAMU FARA WASAN YANZU LABARIN ZAI D'AUKI ZAFI, FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA!!!!!*
*25/5/2023 Thursday may*
_BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_
WhatsApp number 07064904617
Or
07068956952