Showing 12001 words to 15000 words out of 21076 words

Chapter 5 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

09 Sep 2025

2273

wallahi,”
“To in da ce shi ba dan Sarki bane fa?”



Wannan maganganu na yawo cikin masarautar, musamman daga matan sarki da sauran dangin sarauta. Amma Baby ba ta ma sanin hakan gaba ɗaya — MJ ya ɓoye mata komai. Kullum sai ya saka dariya a fuskarta, ya boye mata gaskiyar wuta da take ƙone masa zuciya.


---


Wata rana, Hajiya rasheeda ta kira MJ da Baby. Sun zauna a ƙaramin daki, wuri mai kamshi da natsuwa.

“Baby,” ta ce da ita cikin tausayi, “zaki fara shiga duniya mai wahala. Wannan masarauta ba gidan ƙauna ba ne — idan ba da zuciya ba, zaki ɓata rai. Amma karki taɓa jin kanki ƙarama ce. Kin fi kowa a nan, saboda kana da wanda ya tsaya miki fiye da zuriya — ƙauna.”



Baby ta juya, ta kalli MJ. MJ kuwa ya ce:

“Idan duniya bata karɓi ki ba, ni zan yi mata dole.”


Hajiya rasheeda tayi murmushi a zuciyar ta tace "yaro kenan ,lallai har yanzu bakasan bakasan makirci gidan sarautar sauba ba.

---

Zuciyar Sarki Tana Da Ganuwa

Sarki Umar na lura da wannan raino da MJ ke yi da kulawa ta musamman, wanda duk masarautar ta lura da shi.


Yau ma kamar kullum sarki ya kirawo MJ domin ya kara fahimtar dashi akan jabaya da baby ,tun da dai watara na dolene. Baby zatayi aure su rabu,

Kallon sa yayi cike da nuna alamun damuwa yace

“Ina so ka fahimta, abee,” sarkin ya faɗa masa a wata tattaunawa ta sirri, “kamar yadda ka kula da ita yanzu, haka za ka dinga kare martabar masarauta idan wani abu ya same ta.”



MJ ya sunkuyar da kai.

“I know, Abba. Kuma zan ci gaba da kare ta — ko da kuwa hakan zai haifi hatsari.”



Sarki ya ɗan murmusa da gefen baki.

“To yanzu, daga yau, Baby zata koma makarantar gwamnati tare da jami’an tsaro — domin ta koyi rayuwar talaka da kima. Idan ta girma, zata dawo ta karanci tsarin masarauta.”



MJ ya kasa amincewa da maganar abban sa, duk da zuciyarsa na ɗan cika da fargaba,wai yau babynsa ake wulakanta wa?


---"Abba kayimin aikin alfarma ,Dan Allah ina rokonka ka bar baby TA cigaba da zama Dani"

Shiru mai martaba yayi kafin daga bisani Kuma yace " shikkenan kaje zanyi ruanni".


***************
To Shekaru biyu sun shige. Baby yanzu yarinya ce mai wayo, mai nutsuwa. Tana karatu sosai, tana samun lambobin yabo. MJ kullum na zuwa makaranta ya dauko ta, ya yi mata nasiha, ya sayo mata ice cream ko juice. Idan dare ya zo, suna karatu tare.

Wani dare MJ ya ce mata:

“One day, you’ll understand everything. But for now, just promise me this...” “Wane abu ne, daddy?” ta tambaya tana dariya.



Ya ce:

“Just promise me you’ll never stop learning. Never stop dreaming.”



Ta ce:

“I promise, Daddy.”


---hannun ta ta dago ya kawo nasa hannun Sannan tayi murmushi tace " inama kowa zai samu mahaifi kamarka " murmushi MJ yayi batare da ya sake cewa komai ba


---Daren ya lafa. Hasken fitilar dakin karatu yana dumi kamar zuciyar MJ. Baby ta kwanta bisa kujera, kanta a kafadarsa, hannunta sanye da zoben roba da MJ ya saya mata ranar ta ci nasarar farko.

MJ ya shafa kanta a hankali, yana jin wani abu da ba zai iya fassara ba. Ƙauna ce — ba irin soyayyar masoya ba, amma irin wacce take zamewa fatalwar rayuwa.

Ya ce da ita a hankali, yana kallon wata daga tagar dakin:

“Someday... you’ll be everything you dream of. And more.”



Baby ta ce da ƙasa da murya:

“As long as you’re here to see it.”



MJ ya lumshe ido. Bai ce komai ba. Amma zuciyarsa na magana: "Ko ba ni da damar rayuwa, zan bar miki mafarkin da zai tashi da safe."


---

RANAR KARRAMAWA —

Washe gari, masarauta ta cika da jama’a. Wani babban wuri an kawata shi da tutocin masarautar. Muryar masu watsa shirye-shirye na yawo a cikin rediyo da talabijin.

Kafin Baby ta fito, MJ ya taimaka mata da gyaran rigarta — rigar royal blue, mai ado da zinariya. Ya saka mata ɗan karamin sarkar wuya da rubutun "Shine Bright."

Ya ce: “Today, you speak for every girl that ever felt invisible.”



Ta ce da nutsuwa:

“I’ll speak for me… and for you.”



Suna isa wajen taron, ido ya koma kansu. Baby da MJ — mahaifi da 'ya — wanda ba jini ya haɗa su ba, amma zuciya.ta hadasu

Wajen jawabinta, Baby ta tsaya gaban jama’a. Ta ɗan girgiza kafadarta. Ta kalli MJ a gefe — wanda ke murmushi, yana daga yatsarsa alamar "Na yarda dake."

Sannan ta ce, da ƙarfin murya mai natsuwa:

“Ni ba jini na sarauta bane. Amma ina da zuciya kamar kowacce ‘ya mace. Ina da mafarki kamar kowanne ɗan adam. Kuma yau na tsaya anan... saboda wani mutum ya yarda da ni kafin na yarda da kaina.”



Jama’a suka yi shiru. Sai ta cigaba:

“Wanda ya ce min ilimi ne garkuwata. Wanda ya ce min ƙauna ba takalmi ba ce da ake cirewa — ita ne hanya. Kuma yau... na zo ne in ce: ‘A ƙaunaci yara, a koya musu mafarki. Su ne masarautarmu ta gobe.’”



Ƙarshen jawabin ya jawo tsit. Sai kuma tafi — tafi mai ƙarfi, har da hawayen wasu, musamman daga mahaifiyar MJ da ke zaune a bayan kujerar sarki.


---



Bayan an gama taro, MJ ya zo ya rungume Baby sosai. Ya ce da ita:

“You made me proud. You made me... complete.”



Ta ce da murmushi:

“Because you made me possible.”




---Tunda Baby ta kammala jawabin nata a wancan rana, abubuwa sun fara sauyawa a cikin masarauta. Ana girmama ta a bainar jama'a, amma a bayan-gida, kalamai masu zafi na yawo kamar iska mai ɗauke da ƙura.

Zuwaira da ‘yan uwanta mata guda biyu — — su ne aka fi shirya wa MJ tun shekaru da suka wuce. Amma yanzu, gashi Baby tana ja da MJ cikin kulawa da girmamawa, sai dai wannan ba karɓa ba ne a idanunsu — zubar da daraja ne.

Zuwaira ta ce wata rana cikin ɓacin rai, yayin da suke zaune a gefen harabar masarauta:

“Ke da aka dauko daga titi, ke za ki zo ki tsaya gabanmu a dakin sarauta? Wallahi duniya ba ta da adalci.”



Nafisa ta ɗan hara baki:

“Ai ba kowa ne ya san ainihin asalinta ba. Su dai suna gani kawai MJ na kula da ita. Amma mu muna ganin bakin ciki ne — ya mayar da masarauta gidan reno.”



Yagana ta ce da dariya mai cike da cin fuska:

“Kuma idan ta girma fa? Me zai hana ya ce zai aure ta? Sai ace ita ce aka tanada tun daga haihuwa — ciki da goyo — a matsayin matar sarki!”



Suka yi dariya, amma babu dariya a zukatansu. Tsana da kishi ne ke cin su.


---
Ita dai baby batace musu komai ba, sai da ta shiga dakin Sannan ta shiga goge hawaye.

Wasu lokuta idan Baby ta yi wani kuskure, ko da ƙanana ne, to gori zai biyo ta kamar guguwa.

Wata rana, tana gefen wani katafaren bangon makarantarsu a cikin masarauta, tana karanta littafi, sai Nafisa ta zo da wasu ‘yan mata biyu, suka tsaya suka kalleta.

“Hmm… ke da ya Mujahid ke muku wa'azi kullum. Ashe duk wannan wayon sai kike rubuta answer a jikin tafin hannu?” ai kamata yayi ki rubuta a kokon zuciyar ki shine Zamu tabbatar da soyayyar ta Kai soyayya ".



Baby ta ɗago kai cikin nutsuwa, ba ta ce komai ba.

Sai Yagana ta ƙara da karfi:

“Mu mun san irin ki. Kuma ba girma ko lambobin yabo ne zasu mayar da ke yar masarauta ba. Ke dai rainon ya Mujahid ke miki — ba ƙima ba ce hakan, Ton da yanzu har TA Kai takawo daki Daya han yanzu kuke kwana".



Zuwaira ta karɓa da sakin baki:

“To i ai, kamar yadda aka gina ta da kulawa, haka za a rushe ta da haƙiƙa. Wannan masarauta ce fa, ba gidan yara marasa gata ba.”



Baby ta ja numfashi. Ta mike. Ta ce cikin kwanciyar hankali, amma da ƙarfi mai tasiri:

“Kuna ganin raino ne. Amma ni ina ganin gini ne. Wanda ake yi da so, da hakuri, da tarbiyya. Kuma ko kun raina ni, ban raina kaina ba.”



Sannan ta juyo ta tafi, zuciyarta na cike da bakin ciki, amma tana ɗauke da darajar kalmomin MJ da mahaifiyarsa:
“Never stop learning. Never stop dreaming. Kuma kada ki taɓa barin su su rushe ki da kalmomi.”


---



Daga nesa MJ ya gan ta tana dawowa daga wannan fushin. Ya tare ta a tsakar hanya. Ya kalli idanunta.

“Waye ya taɓa miki zuciya?”



Ta ce da murmushi mai rauni:

“No one, Daddy. They can’t touch what they can’t reach.”



Ya janye wata goge tears daga gefen idanunta.

“Don’t let anyone measure your worth by your roots. You are not what they think — you are who you decide to be.”


Zuwaira ta ɗauki alkawari a zuciyarta: “Zan gano asalin wannan yarinyar. Ko da sai na dauki rana da dare, zan tona sirrin da zai kifar da ita.”
Kuma wallahi Indai ina raye sainaga bayan baby

Ta fara tuntubar tsofaffin bayin masarauta. Wata rana ta je dakin tsohuwa Halimatu — wata tsohuwa mai zane, wadda take zaune tun zamanin Sarki Balarabe, kakansu MJ. A cikin shakku da kishi, ta ce:

“Tsohuwa, kin san wata yarinya da aka kawo masarauta fiye da shekaru bakwai da suka wuce? Wadda MJ ya rike kamar nasa?”



Tsohuwa Halimatu ta tabe baki, sannan ta zuba mata ido. Da wata murya mai cike da hikima da zafi, ta ce:

“Ke da baki san asalin ki ba, kina son sanin asalin wata? Ki farka daga mafarki, ‘yar sarki. Wannan yarinyar da kike tsana, ita ce silar zaman lafiya a cikin zuciyar MJ. Kuma gaskiyar haihuwarta... na da nauyi fiye da abin da kike tunani.”



Zuwaira ta kurma ido, zuciyarta na dukan tamkar ana bugunta da tabarya.

“Tsohuwa... kina nufin akwai sirri?”



“Akwai. Amma sirrin nan, idan ya fito, ba ke kadai zai jefa cikin duhu ba. Masarauta ma ba za ta tsira ba.”



Zuwaira ta fita a ruɗe, amma zuciyarta na ƙonewa da son sani da kuma ƙoƙarin ganin Baby ta faɗi.


---

A BANGAREN BABY...

Baby ta fara fahimtar kishi, zagi, da gorin da ake mata. Amma ba ta daina daraja MJ ba. Ta fara tambaya a zuciyarta:

“Me yasa mutane basa son na? Me na yi musu?”



Sai MJ ya kama hannunta wata rana, bayan ya kawo ta daga makaranta, suka zauna a bayan falo.

Ya ce:

“Baby, kin san wani abu? Akwai mutane da ba sa son haske saboda yana nuna inuwa a gare su. Amma ke... kina haskaka.”



Ta ce da dariya mai ɗan ɗaci:

“To idan ina haskaka, me ya sa suke so su kashe fitilata?”



Ya ce:

“Saboda suna jin tsoro. Tsoron wanda suka raina, ya wuce su da gaskiya.”



Sannan ya ce mata:

“You don’t have to fight them. Just grow. Haske ba ya takura — yana tsage duhu ne kawai.”


"Uhm wataran daddy idan kana magana kana bani kwarin gywa sainaji kamar nagama dacewa a rayuwata"

"Kidaina kokonta baby kinma dace da dacewar ubangiji insha Allah kinfiso dole su kyleki, ayanzu kinsoma zama mace Kuma suna son suga suncutar min dake sabi da ke basa,ar su bace kaunata

---🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂🫂


---
Shekara na 14 kenan da MJ ke rainon Baby. Yanzu tana da shekaru 15,kyawunta yana ƙara bayyana fiye da kullum. Idan ta wuce, idanu na bisarta. Koda kuwa mutane suna ƙoƙarin ɓoye sha’awar su, murmushinta da ɗabi’arta na jan hankalin duk wanda ya kalle ta.

A makaranta, ƙawaye sun fara fadin: cewar wanna yarinyar idan sukai wasa zata janyewa kowa saurayinsa ,basu da aiki kullum cikin gulmarta ,to yauma kamar kullum suna zaune suna cewa:

“Baby ke nan, wadda ko ɗan Minista ya kalle ta sau biyu!”

"Hmm kadai bari abin Yana batamin Rai ,daga gefansu sukaji wani saurayi na fadawa a bokin SA cewar :...



“Ni zan aika mata gift jibi, wallahi. Koda MJ zai ƙone!”


" Kai haba abokina wai da gaskiya kake? "

"Ina Maka wasane Daman" gaba kidaya su suka tafa lokaci guda.

To tafiya tatafi girman baby na daukar hankalin kowa a yanzu har takai ta kawo
Har ‘yan masarauta suna aika sako da kyaututtuka — iPads, zoben zinariya, katunan soyayya... Amma Baby tana karɓa da godiya kawai, ba ta amsawa da ƙauna. Domin ita aganina Babu Wanda zai sota a duniyarnan fiye da Daddynta.


******



Wani rana suna zaune a harabar gidan masarauta, MJ na gyara mata Dan kwali, tana dariya, tana zuba masa kwantar da hankali. Sai wayar Baby ta yi kara. Tana duba, sai murmushi ya bayyana a fuskarta.

“Wa ne ya turo miki?” MJ ya tambaya, da murya mai sanyi.



Ta ce, “Yayan wani classmate ɗina ne... ya turo min poem wai saboda birthday dina.”



MJ ya yi shiru na dan lokaci. Ya kalli hannunta, sai ya ce da ƙasa-ƙasa:

“Ni ban iya rubuta poem ba. Amma nasan duk poem da za a rubuta, ba zai iya bayyana yadda nake ji ba idan kika tafi da wani, Kuma ta itana har yasan kwanan watan haihuwarki?"



Baby ta dubeshi. Zuciyarta ta buga da sauri. Amma kafin ta yi magana, MJ ya sake murmushi — murmushin ɓoye gaskiya.

“Ke fa karatu, ba soyayya. Ko kin manta?”

"Ban mantaba daddy kayi hakuri insha Allah bazan sakeba" daga haka ya kwantaeda kanta kan cinyarsa ya shiga duba kunnenta Yana cire mata datti.

*******




Sarki Umar.......

Sarki ya fara lura. Wani dare, ya kira MJ cikin ɗakin karatu. Tana kwance, MJ na shirin fita daga dakin ta.

Sarki Umar ya ce masa:

“Abee… kana rainonta sosai. Kana kyauta mata sosai. Kana duba ta fiye da yadda uba ke duban ’ya.”



MJ ya lumshe ido. Ya ce:

“Abba, ita ce farin cikin zuciyata. Amma na sani, babu aure tsakanina da ita. Na ɗauke ta tamkar ’yata ne.”



Sarki ya girgiza kai:

“Ba ina cewa kana son ka aure ta ba. Amma ita tana girma. Kuma idan wani ya so ta — ya fi ka dacewa da ita — kada ka tsaya a gabanta. Ka tuna da sharadin da aka yi, abee.”



MJ ya lumshe ido. “Na tuna. Amma zuciyata... tana da wahala ta yarda da hakan.”

Sarki ya yi ajiyar zuciya, ya ce:

“Kayi ƙoƙari ka yanke kanka daga zuciyarta kafin lokaci ya kure. Ko kuma ka bar zuciyarta ta yanke ka.”


Kai kawai MJ ya nunnar kana yadan Yi murmushin karfin hali yace "in sha allah Abba, za a kiyaye. Daga haka sarki Umar yayi gaba Mujahid ya koma cikin dakin.



🕊️ RAINON YARO

Chapter 7,





---
Babyna zaune a daki
ta fara jin wasu raɗaɗi a zuciya. Tana tambaya:

“Me yasa duk abinda nake jin game da daddy... ba irin na ɗa da uba bane?”




Kullum cikin wanan tambayar takewa kanta

Amma tana ɓoye komai a fuskarta — sai dariya, sai ladabi, sai kwanciyar hankali.



MJ kuma yana ƙara fuska, amma zuciyarsa na ƙonewa a hankali. Yana tare da ita, amma kamar an raba su da wani bango da ba a iya gani.


WATARANA.....


Wata rana a makaranta, wata sabuwar mota ta tsaya — black SUV mai tinting da tambarin jami’an gwamnati. Kowa ya tsaya kallon wanda zai fito.

YARO NE. Tsawo, fari, sanye da school uniform, amma yana da salon shigowa irin na manya. Yana da karsashi da walwala. Sunansa: HAFID.

Hafid ya kasance ɗa ne ga wani sanannen dan siyasa a garin, kuma ya canja makaranta zuwa inda Baby take karatu.

Bayan sati biyu kacal… kowa ya lura da yadda yake kulawa da Baby. Yana kokarin zama kusa da ita a dakin karatu. Yana rike mata littattafai. Wani lokaci yana dan raira mata waka idan suna kan break.

MJ YA LURA DA HAKAN A RANAR TARON YABO.

Ranar da Baby ta samu Award na Best Student, MJ ya shirya sosai — ya sa blue shirt da hula mai mutunci. Ya zauna a bango yana kallonta tana karɓar kyautarta.

Hafid yana gefenta, ya sa mata zobe na gem-stone da cake mai rubutun "To the best mind I know."

MJ ya matso kusa da ita, yana murmushi, ya ce:

“Wow, look at you. Kina haskaka kamar rana yau.”



Ta ce, “Nagode Daddy.”

Ya ce, “Ki zo mu tafi gida.”

Sai Hafid ya ce da dariya, “Uncle, zamu je café ɗin makaranta kafin su tafi.”

MJ ya lumshe ido. Ya ce da nutsuwa:

“Ita yarinya ce. Ni ne ke da alhakin ta.”



Sai ya juya ya kalli Baby, yana ce mata:

“Let’s go. You’ve done enough celebration today.”



Ta amsa da “Okay Daddy…”
Amma kafin ta tafi, ta kalli Hafid tana dariya. Hafid ya ce:

“Zan aiko miki da notes dinnan da kika tambaya.”



MJ bai ce komai ba. Amma zuciyarsa ta fara girgiza. Yana jin wani abu yana tashi a cikinsa — kishin da ba ya iya furtawa.


---

ZUWA GA SARKI…

Sarki ya kira MJ, yana zaune cikin natsuwa. Ya ce:

“Kana jin haushi ne yanzu?”



MJ ya ce:

“A’a, kawai bana son wani ya kawo mata rudani a karatu.”



Sarki ya kalle shi.

“ayanzu baby ta Kai matakin da bazaka iya hanata kula samariba tun da dai ita macece dole gidan wani za a kaita a matsayinka na mahaifinta farinciki yakamata kayi 'yarka tana da farinjinin da za a sota har a aureta"


"Abba gidan wani fa?" Ya fada idonsa ya kada yayi jajur .


"Eh ko Kai zaka aureta ne? Yayi maganar cikin tuhuma.


"A,ah Abba Amma .....


"Amma me tashi ka bani guri Abee kafin ranka ya baci."



Babu musu MJ ya mike jiki Babu kwari ya fita Yana fita ya huce lanbun masarauta sabi da yau su Baby suna picnic na makaranta a cikin masarauta.

Sarkin masarauta ya bada izini, don haka an ware wuri na musamman ga dalibai masu hazaka da iyayensu ko guardians su taru.

Baby ta saka farin rigar ‘flower gown’, kanta ya sha tsaf da kitso mai kwalliya. MJ ne ya taimaka mata kwana biyu da suka wuce wajen gyaran sumar kanta.

MJ ya zo daukarta . Yana sanye da kayan casual masu kyau — t-shirt da wando, gashinsa yana sheƙi, kamar bai da damuwa, amma a zuciya, mamaki da fargaba sun hade.





Yayin da picnic ya fara, dalibai na rawa, wasu na wasanni, wasu suna cin abinci. Hafid ya zo cikin sabuwar kaya, ya karaso wajen Baby da MJ. Yana dariya yana sanye da hular gwaninta.

"Look who’s glowing today — you again," ya ce yana kallon Baby.



MJ ya zuba masa ido. Bai ce komai ba.

Hafid ya ce da MJ:

"Uncle, zamu ɗan ɗauki hoto tare da Baby mana… group picture ne."



Baby ta dubi MJ, kamar tana neman izini. MJ ya ce da murya mai laushi:

"Go ahead."



Sun ɗauki hoto. Amma MJ yana gefe, yana karanta motsin Baby da na Hafid fiye da hoton kansa. Zuciyarsa na harbawa da tausayi, da kishin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login