Showing 6001 words to 9000 words out of 21076 words

Chapter 3 - RAINON YARO BOOK 1 FARKO BY HAFSAT UMAR DANGORO.txt

09 Sep 2025

2272

daga dukan duniya.

MJ ya ɗauke ta, ya daura ta a goyo — kamar ya ƙudiri aniyar: duk wanda zai ƙi ta, to shi ma MJ ya ƙi.



suna fito daga zauren masarauta, suka fuskanci jerin mata da aka tanada domin a haɗa MJ aure da ɗaya daga cikinsu bayan ya gama karatu. Amma yau... ba gaisuwa, ba murmushi — sai kyama da surutu.

“Kalli ya Mujahid goyo fa yake wannan ai a bin kunya ne kamar matarsa ta haifi shege!”
“Wannan yarinyar, wani irin kazanta ne haka... ai ba daga gidan masu tarbiyya take ba.”
“Idan wannan ce amana tasa, to wallahi ni da shi ba zamu tab jutuwa ba!”



Wata daga cikinsu — Farida, wacce aka fi sa rai za a ɗaura MJ da ita — ta matso da wani irin kallon ƙyama, sannan ta ce da wata a bayanta:

“Gashi yana da kyau, amma wallahi zuciyarsa ba ta gari ba. Wanda zai zauna da shegiyar wata marainiya, me zai hana ya ji kunyar abin kunyar Dan ya aikata?”



Wasu daga cikinsu har suka danna Baby da yatsa, suna faɗin:

“Banza ce kawai... wallahi duk wannan kyau da kulawa sai ta gama cikin wulakanci. Ba daga zuriyar mu ba ce ba dai ya zabi ta zauna a cikin gidannan ba wallahi sai ta gwammaci shegiyar da ta haifita bata kawota duniya ba!”



Baby ta matse hannun MJ. Duk da ƙarancin shekarunta, tana fahimtar mugunta. MJ kuwa ya tsaya cak. Bakinshi ya bushe. Amma ba ya fushi — sai ka ce yana jiyo ƙara ne daga cikin zuciyarsa.

“You hate what you don’t understand,” ya furta a hankali.
“But I will raise her until you all bow to her greatness.”



Sai kawai ya juya — ya tafi ba tare da ya waiwaya ba.

Duniya na kallonsa da kallon raini, amma zuciyarsa ta fi kowace sarauta.
Ya ɗauki Baby ya tafi da ita — kamar wanda ya ɗauki addininsa.


---Daren ranar...
Siririn fitila guda daya ke kunnawa a dakin MJ. Dakin da ke bangaren nesa da sauran masarautar. Dakin da babu komai sai karamin gadon kwanciya, kujera daya, da kwandunan kayan wanka.

MJ yana zaune a bakin gadon, ya cire rigar rigimarsa, ya nade hannayensa, yana kallon Baby da ke zaune a tsakiyar tabarma. Tana murmushi masa, duk da irin maganganun da aka jefar da ita da su yau.

"Duniya ta fara koyar miki darasi, Baby," MJ ya furta da daddadɗar murya, yana jan ruwan zafi daga flask ya zuba cikin karamin bokiti.
"But don’t let them break you. I didn’t carry you this far just for you to bend."



Ya daga ta a hankali, ya cire mata karamin riga, sannan ya soma wanke kafarta da tawul.
Hannunsa da taushi kamar yana tabawa da so da tausayi.

"Sannu...sannu, kin ji?" ya ce, yana murza gashin kanta da yatsunsa.



Baby ta kalleshi da idanu masu launin rana. Kamar tana son tambayar: “Me yasa suke ƙi na?”

"They don’t hate you, Baby. They fear you. Saboda ke ba irin su bace," MJ ya ce yana murya kamar mai kiran sallah daga zuciya.



Ya ɗauke ta, ya nannade da zani, ya zauna da ita a cinyarsa. Ya sanya mata man shafawa, yana hura mata iska a kunne, tana dariya kaɗan-kaɗan.
Sai ya kalli kanta... ya lumshe ido.

"Na rantse da kaina, Baby... ba zan bar kowa ya taɓa ki ba. Even if I have to fight my own blood."



Sai kwatsam aka buga ƙofa.
MJ ya miƙe tsaye da Baby a goyo. Kamar sojan da aka tsinkayo daga mafarki.

"Waye ne?"
“It’s Zuwaira... open the door.”



Zuwaira — ɗaya daga cikin 'yan matan da aka tanada don MJ. Ita ce wacce ba ta cewa komai yau lokacin aka zagi Baby, amma tana kallon MJ da idanu masu ƙuna.

MJ ya buɗe ƙofar.

Zuwaira ta tsaya tana kallonsa. Sai kallon Baby.

“I didn’t come to insult her like the others,” ta furta da ƙarfin zuciya.
“But I came to ask — me ya sa ita? Me ya sa wannan marainiyar ta kai matsayin da duk mu ba mu kai ba?”



MJ ya kalleta. Sai yayi shiru.

“Saboda ina da zuciyar da ba ta neman fari, ba ta tsoron baƙi. Ina so ne, ba domin ta cancanta — sai domin ta cancanta.”



Zuwaira ta nisa. Sai ta juya, tace:

“Then may your love protect you both. Amma ka sani... ba kowacce ƙauna ake sakawa ba da hura wuta — wasu ƙaunuka na cin wuta ne har abada.”



Ta juya, ta barshi a tsaye da Baby a bayansa —
Daya mai ƙauna, ɗaya mara tsoro.


---Safiyar fari, rana ta biyu da MJ da Baby suka dawo masarauta…

MJ na tsaye gaban madubi, yana daura agogon hannu, yana sanye da farar shadda mai tsabta da hula riga ɗaya, da takalmin fata na sarauta. Baby kuwa tana zaune a gaban kofar ɗaki, tana wasa da ƙaramar jar-takar da ya siyo mata jiya — sabuwar motar roba mai launin ja.

MJ ya kalleta ta madubi, sannan ya juya ya durƙusa gabanta.

"Yau zaki fara makaranta, Baby. Karki ji tsoro. Komai zai dai-daita, okay?"



Baby ta kallesa, sai ta yi murmushin da ke haskaka zuciyarsa fiye da fitilar dakin.
Ya ɗauketa, ya goya a baya — ta lumshe ido tana jin dumin fatarsa da ƙamshin man shafansa.


---

Bayan ƴan mintoci... a kofar makarantar da ke cikin masarautar:

Yara da dama suna fitowa daga motoci, wasu daga cikin dangin masu fada aji, wasu 'ya'yan sarauta. Wasu daga cikinsu sun tsaya suna kallo da mamaki lokacin da suka ga MJ ya sauka daga motar sarauta da goyo a bayansa.

"Waye wannan kuma? MJ ne da baby?!"
"Wato har yanzu yana riƙe wannan yarinyar?"
"Ko da girmansa, da bai samu matar aure ba, sai marainiya?"



Zuwaira da wasu 'yan mata biyu daga cikin waɗanda aka tanada domin MJ sun tsaya gefe suna kallon sa.
Zuwaira ta runtse ido, tace a hankali:

"He’s really not letting go..."
Ɗayarta ta ce da ɗan gajiya:
"To idan har Baby zata girma a masarauta, mu fa? Auren da muka zata...?"
"Yanzu duk za mu zama masu kallon soyayya kenan?"



Wani daga cikin malamai ya ƙaraso wajen MJ.

"Ranka ya daɗe, ka kawo yarinyar kenan?"



MJ ya gyaɗa kai.

"Eh, I want her to be raised with knowledge. Ku koya mata — amma kada ku ci mata mutunci. She's a child. And she's my child."



Malamin ya ɗan kaɗa kai da ladabi — amma mamaki bai ɓoye a fuskarsa ba.


---

Lokacin break... a makarantar:

Baby tana zaune cikin yara a gefe, amma wasu daga cikinsu suna harararta.

"Ke daga wace gida kike?"
"Me yasa na ganki da MJ?"
"Ko ke ce yarinyar da suke cewa ba jinin sarki bace?"



Baby ta ɗan lumshe ido. Duk da ƙarancin shekaru, zuciyarta na gane bambanci tsakanin tambaya da tsana. Ta miƙe, ta ja littafinta ta koma gefe.

Daga nesa, MJ na kallonta ta cikin gilashin ofishin malamai.

Ya dafe fuska, yana tunanin...

"I’m trying... amma me zai hana wannan duniya ta daina cutar da mai rauni?"



Sai aka ji murya daga bayansa:

“Za ka rasa komai saboda ita.”
MJ ya juyo — Sarki Umar ne ya tsaya a bayan ofishin, yana kallon Baby.



“Na riga na rasa abin da ba na so. Idan ita ce komai — I am ready to lose the world.”



****************



Dare ya rufe masarauta. Fitilu na haskakawa, iska na busa cikin sassanyar ƙamshi na tsiron jajjaye.

MJ yana tsaye a zauren barandar sashen sa, yana duba wayarsa. Jikin sa yana ɗaure da gajiya, amma zuciyarsa cike take da damuwa. Baby tana cikin ɗaki, tana bacci, bayan kuka da ya daɗe kafin ta lallaɓa ta kwanta.

Sai ga Uncle Faruq, ɗan’uwan Abba, wanda aka fi sani da dattijon fada, ya ƙaraso da takalman fata masu amo.

“MJ, akwai abin da nake son na fada maka. Ka shirya ranka.”



MJ ya ɗago kai.

“Uncle, lafiya?”



Uncle Faruq ya gyaɗa kai, yana jan kujera ya zauna kusa da shi.

“Akwai wani tsarin da 'yan mata uku daga cikin gidan sarauta suka fara. Sun fara ƙoƙarin ganin an hana Baby shiga makaranta gaba ɗaya.”



MJ ya dafe kansa.

“Me suka yi ne?”



“Sun yi ƙaryar cewa tana janyo rikici a cikin aji. Wata daga cikin su ta sa yaronta ya tura Baby, har ta fāɗi, sai aka ɗauki hoto aka nuna kamar ita ce ta fara faɗa.”



MJ ya miƙe tsaye. Idanunsa sun canza launi.

“Why would they do that to a child?”
“Wani kuskure ne a rayuwa da yasa mutane ke jin haushin wanda bai taɓa cutar da su ba?”



Uncle Faruq ya juyo da ido mai nuni:

“Wannan ba cuta ba ce ta zuciya kawai — kishin duniya ne. Sun fi tsoron yadda kake ƙaunar Baby fiye da yadda kake ƙin su.”



MJ ya ɗaga wayarsa, ya kira principal ɗin makaranta.

“Gobe da safe, zan zo da lawyer. A buɗe min cctv footage na makarantar. Ina son ganin komai.”




---

Washegari da safe...
MJ ya sauka cikin makarantar da manyan jami’an tsaro biyu. Baby na goye a bayansa, amma yau ta saki jiki kamar ta saba da waje. Sai dai idanun ta suna kallon kowa da tausayi.

Principal ya fito cikin girmamawa.

“Ranka ya daɗe, ga footage din.”



A gaban kwamfuta suka kunna bidiyon. A can aka ga ɗaya daga cikin yara ya ture Baby. Ta faɗi. Sannan wata yarinya ta kira wata da suna:

"Kira hoto! Ce mata ita ce ta fara!"



MJ ya dafe ƙirji.

“So that’s it…”



Ya juyo ga principal:

“You will issue an apology letter to my daughter. And you’ll suspend the students who lied.”



Principal ya lumshe ido:

“Yes, Your Highness. I apologize.”




---

Wajen ‘yan matan masarauta…

Zuwaira na zaune da su Sa’ada da Fa’izah. Sun samu labari cewa MJ ya gano duk abinda suka shirya.

“Yanzu fa... he’ll hate us,” Sa’ada ta ce tana shafa gashin kanta.
Zuwaira ta tashi tsaye, ta ce:
“Sai ya tsani mu kenan saboda waccan yarinyar?”



Fa’izah ta ce:

“Ba saboda ita ba. Saboda yadda muke ƙi wanda MJ yake so.”



“Well,” Zuwaira ta fadi da zafin rai,
“Let’s see how long this love will last. She’s just a child. But she’s living a queen’s life.”



Hakadai aka gama kashe wanan matsalar daker MJ ya hakaru ya kylesu , a hakanma Saida mai martaba ya saka baki a maganar.



•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••




Wata rana da safe, rana na fito da dumin ta, iska na kadawa cikin furanni a cikin masarautar. Baby na zaune a gaban teburin MJ, tana riƙe da fensir, tana ƙoƙarin rubuta sunanta.
MJ na zaune a gabanta, yana kallonta da murmushin da bai daina haskawa ba tun daga lokacin da ya ɗauki rainonta.

“Write it again, sweetheart. Slowly this time. B...A...B...Y.”



Baby ta lumshe ido, ta ce da harshenta mai rauni:
“Baby MJ.”



MJ ya bushe da dariya, ya ɗago ta ya rungume.

“No, sweetheart. Just Baby. You’re enough on your own.”



Kallon da suka yi wa juna ya cika da soyayya irin ta jini da rai — ba sai an furta uba da ɗiya ba, zuciya ta riga ta furta fiye da haka.


---

Cikin masarauta...

A wani bangare na fadar da aka fi kira "Zauren Shawara", wasu dattijai daga cikin gidan sarauta sun zauna suna tattaunawa.
Wani dattijo, Alhaji Kaura, ya ce:

“Wannan ƙaunar da MJ ke nuna wa waccan yarinyar zata iya dagula tsarin masarauta gaba ɗaya. Ya kamata a sa dokar hana ta shiga ayyukan masarauta gaba ɗaya.”



Wani ya ce:

“Amma fa yaron nan yana da ƙarfin zuciya. Ya fi mahaifinsa darewa daga sama ba tare da faduwa ba.”



Sai wani tsoho ya girgiza kai:

“Mu bar su suyi wasa, amma mu sa ido. Saboda idan wuta ta samo asali daga soyayya, tana ƙonewa fiye da wutar fushi.”




---

Daren ranar...

Baby ta dawo daga makaranta. A yau ta zo da 'report card'. MJ ya zauna a tsakar gida yana shan shayi, lokacin da ta karaso da takarda a hannunta.

“Daddy , see!”



Ya karɓa, ya karanta — tana da 'A' a kan karatu, da kyau sosai a tarbiyya da halayyar aiki tare da yara.

Ya ɗago ido da murmushi mai dumi:

“You are the best daughter anyone could ask for.”



Ya ɗago ta sama yana juyawa da ita, suna dariya. Har lokacin Zuwaira na tsaye daga nesa tana kallo, zuciyarta cike da wani abu mai kama da kishi, da kuma rashin fahimta.

“Why is it so easy for her to have him all to herself?”



To Washegari da safe, lokacin rana na sosa fuska da haske, MJ ya zauna a wani ɗan gindin mango a fadar gida. Ya ajiye Baby a jikin sa tana cin dankali mai zafi. Sai kuma wata mace ta fito daga cikin gida, ta zauna a gefensa cikin kulawa.

Hajiya Rasheeda, mahaifiyar MJ — mace ce mai tsafta, dattaku da natsuwa. Idonta yana da zurfin gani, kamar mace da ta rayu da hikima. Ta kalli MJ, sannan ta dora hannunta a kafaɗarsa.

Hajiya Rasheeda: “Ka girma, ɗana. Amma zuciyarka bata fasa kasancewa tamkar ta yaro ba. Wannan yarinya... ba kawai karamin sakamako bane. Ita ce kaddara da zuciyar ka ta karɓa tun kafin ka gane.”



MJ ya ɗan juyo ya kalli mahaifiyar tasa, idanunsa sun cika da godiya.

MJ: “momy, na san duniya zata yi mini tambayoyi da yawa. Zasu ce ‘ta wacece ita?’ Ko ‘me yasa ba waiyanda suka haife ni suka haife ta ba?’ Amma bana da amsar komai... sai dai: ina son ta.”



Hajiya Rasheeda: (ta shaƙi gashin Baby)
“To ka ci gaba da ƙaunarta. Akwai yara da yawa da iyaye suka haifa amma basu raina su ba. Amma kai... kai ka ɗauki yaro ba naka ba, ka saka a zuciyarka, ka saka a shiryayyen makomarka.”



Sannan ta matsa kusa da Baby, ta ce da dariya:

“Yanzu dai Baby zata san tana da ‘granny’ mai son ta sosai.”



Baby ta ce da ƙanana murya:

“Gwanny...”



MJ ya sa dariya har da hawaye. Ya kalli mahaifiyarsa, ya ce:

“Kina bani kwarin gwiwa,Momy. Wannan yarinyar — ita ce tsintuwa ta. Na tsinta aljanna daga cikin rikici.”



Hajiya Rasheeda:
“To ka kula da aljannarka. Domin irin wannan baiwar, idan aka raina — duniya ba zata sake kawo maka irinta ba.”





🕊️ RAINON YARO

Chapter 5




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
A cikin babban lambun masarauta, inda furanni ke sheƙi kamar zinariya, an shirya wani taron ‘yan mata na fada. Ana nan ana hira, ana dariya, wasu suna kallon MJ daga nesa yayin da Baby ke wasa a kusa da shi, ta zura riga ta ja wando, tana dariya da ɗan fashi.

Kallon da ake musu ba na ƙauna ba ne — na ƙyashi ne, tsana, da hassada.
Sai Zuwaira, ɗaya daga cikin kyawawan ‘yan mata da aka tanada domin MJ, ta juyo ga wata daga cikin kawayenta ta ce da murya mai ɗaci:

Zuwaira:
“To ai ba komai bane. Kamar yana raina mu ne — yaro ya dawo da shegiya a bayansa ya goya, ya mayar da ita ‘yar gida!”



Kawarta:
“Ai kuwa da ni ne, da na ce ko dai su fita daga fada, ko mu fita. Ba za mu yarda da haka ba.”



Suna cikin maganganu, sai Hajiya Rasheeda ta iso. Tana cikin kaya na kamala, murya nata cike da nutsuwa, amma tana ɗauke da ƙarfi da izza da ba’a sabawa da ita.

Hajiya Rasheeda:
“Ina jinku. Kuma ban zo don jin abinda kuke faɗa ba. Na zo in faɗa muku cewa — idan har zuciyarku na iya jin hassada akan jaririya, to ku sani ba ku da matsayi a cikin gidan nan.”



Zuwaira:
“Umm... Hajiya, ba komai, muna hira ne kawai…”





Hajiya Rasheeda: (ta ɗaga hannu)
“Kada ki ƙara ɓata lokaci da ƙarya. Na haifi abee da rainonsa. Kuma duk wanda zai masa mummuna — to shi ne ya ɓata ran sarki da uwar sarki. Ku saurara da kunnuwanku, Baby da kuke zagi — ita ce jininki da ke shigowa cikin masarauta da rahama.”



Kawarta:
“To amma ai ba ta da gata ko asali...”



Hajiya Rasheeda:
“Gata ba daga jininka yake ba — daga zuciyarka yake. Idan Baby ta sami gata a zuciyar abee da kuma a zuciyata — to ku manta da kowane masarauta. Ita ce masarauta.”



MJ ya nufo wajen, ya tsaya yana sauraron mahaifiyarsa, sannan ya ce:

MJ:
“Wannan ita ce mahaifiyata. Idan kuka ƙi Baby, ku sani — kun ƙi ni. Idan kuka ƙi ni, to kun ƙi gata. Kuma ba zan zabi gata akan amana ba.”



Zuwaira ta ja hancinta, suka juya cikin kunyarsu.

Baby ta zo da gudu, ta riƙe gwiwar MJ, sannan ta ce da murya:

“Daddy, I love you.”



MJ ya durƙusa, ya rungume ta.

MJ:
“And I will protect you, even if the whole world turns against us.”


After one day

A cikin zauren majalisar sarauta, ana ta jira Sarki ya fito. Kowane dattijo da mace mai mukami ta zauna cikin natsuwa, amma zuciyarsu na yawo. Ganin MJ da goyo a baya — ya tayar da kura. Amma jin bayanin mahaifiyarsa, Hajiya Rasheeda, ya ɗan kashe wutar – ko da kuwa wutar tana ƙasa tana ci.

Sarki Umar ya shigo cikin shigar zanna bukar mai masarautar Kano, sandarsa a hannunsa, idonsa yana haska kowa.

Sarki:
“Na ji dukkan maganganun ku. Na karanta yadda murya ke ƙasa tana ƙona zuciya. A yau, muna da batu guda: Shin wannan yarinya – Baby – tana da wuri a gidan sarauta ko a’a?”



Wasu suka yi murmushin mugunta, wasu suka yi shiru. Sai MJ ya tashi ya tsaya gaban su, da kwanciyar hankali, yana goye da Baby. Sai ya ce:

MJ:
“Babu wata rigima idan masarauta ta ƙi karɓar Baby. Amma ku sani — idan Baby ba ta da matsayi a nan, to Mujahid ma bai da matsayi.”



Kukan ƙasa-ƙasa ya cika zauren.

Wani dattijo: ya kalleshi yace
“Amma yaro… dokar sarauta bata amince da wannan aikinba. Wannan yarinya bata fito daga cikin hantar masarauta ba.”



MJ: ne yace
“Sai dai zuciya. Kuma idan akwai masarauta da bata iya jin tausayi — to wace irin sarauta ce hakan?”



Sarki ya danna sandarsa ƙasa. Duk suka yi shiru. Sai ya ce:

Sarki:
“Ina neman mahaifiyar abee — Rasheeda.”



Ta tashi da kamala.

Sarki:
“Kin goyi bayan wannan yaron akan rainon wannan yarinyar?”



Hajiya Rasheeda:
“Na goyi bayansa kamar yadda na goyeshi a bayana tun yana jariri. Idan har abee yana da matsayi — to Baby ma zata yi.”



Sarki:
“To ni ma zan yarda. Amma ku sani, “Na yarda a hukumance — cewa wannan yarinya, Baby, za ta zauna cikin masarauta. Za a bata kariya, za a bata matsayi. Za a raineta da mutunci. Kuma daga yau, duk wanda ya kalle ta da ƙyama, ya ci amanar masarauta.”



MJ ya lumshe ido — zuciyarsa cike da farin ciki da godiya. Ya durƙusa, yana jin kamar an rage nauyin da ke kansa.

Sai Sarki ya ɗan dakata. Idanunsa sun sauka kan MJ. Sai ya ƙara da cewa, da ƙarfin murya:

Sarki Umar:
“Amma Abee — kai ne ɗana, kai ne magajina. Kuma kai ma ka sani: masarauta bata rayu da ruɗani ba. Saboda haka, zan sa sharadi guda ɗaya...”



Zuciyar kowa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login