Showing 156001 words to 159000 words out of 180493 words

Chapter 53 - Nurul-Huda Complete by 0mmer Farouk.txt

30 Aug 2025

4097

Ta gyada kai tace "Um haka su Umma ke kirana" Anty Maryam tace "Sbda me?" Murmushi tayi tace "Sbda am now a muslim" Anty Maryam ta buda ido tace "Kai daughter" tace "Wllh Anty" shiru Anty Maryam tayi tana kallonta can a hankali tace "Toh a wani dalilin kika yrda kika yi converting, in ji ba don Aliyu ba, ba kuma don yaran ki ba?" Girgixa kai Noor tayi tace "A'a, ai lkcn ban haife su ba, har ynxu kuma bbu wanda yasan nayi converting banda su Umma da kika gani daxu" Anty Maryam tace "To su suka ce kiyi converting din?" Tace "A'a i have my reasons" Anty Maryam tace "Toh ko xa ki iya gaya min reasons din" tana son sanin dalilin conversion din nata ne don bata son ya kasance don wani tayi hakan, Noor ta d'an yi murmushi nan ta shiga ba ma Aunt din tata dalilanta na komawa musulunci kmr yanda ta fadi ma Umma, banda Murmushi bbu abinda Anty Maryam take, can ta rungumeta tace "That's it daughter, gwara da kika fahimce hakan da kanki, Muslims are always their brother's keeper, infact ba ma brothers dinsu kadai ba, har wanda addininsu ya sha bam bam in most cases, am happy for you dear, Allah ubangiji ya sa Abbanki ma ya gano hakan da wuri daughter" a hankali Noor tace "Hadda Ummata" murmushi Anty Maryam tayi ta shafa kanta a xuciyarta kuwa cewa tayi da kamar wuya, a fili kuwa tace "Toh Allah ubangiji yasa hakan, na kira Abbanki nace you re back with ur babies, he was very happy, yace anjima da daddare kila ya shigo" Noor da ta ji wani mugun dadi har ranta tace "Anty da gaske xai xo?" Anty Maryam tace "Yace kila" ta girgixa kai tace "Noo plss ya xo don Allah ina son in gansa" Anty Maryam tace "Toh xai xo idan Allah ya yrda, one more thing daughter" Noor ta kalleta tana jiran jin me xata ce, Anty Maryam ta dafata tana kallonta tace "Ke bafulatana ce gaba da baya, a al'adar fulani kuma an san mu da kunya da kauda kai, mijin ki ma bafulatani ne gabansa da baya, kar kuma ki mance gidan surkan ki kike yanxu daughter, abinda nake so da ke bana son ki sake taba yaran nn sai an daukesu an baki su, ko kuma anyi insisting ki dauke su, na lura shegen son yara ke gare ki, kuma ban yi mamaki da yanda kika fito da hakan baro baro ba don haka mamarki ma take" ita dai Noor kallonta kawai take, ta ci gaba tace "Duk kukan da xa su yi idan ba gun ki suke ba bbu ruwanki kin ji daughter, kar a dinga ganin rashin kunyar ki" Sunkuyar da kai tayi cikin sanyin murya tace "Toh" Anty Maryam tayi murmushi ta ja hancinta tace "Yauwa maman biyu" murmushi ita ma tayi ta boye fuskarta jikinta. Bayan Magrib Noor na xaune dakin ta sa pepper soup din da wata k'awar Mami ta kawo mata gaba ta kasa ci sbda yajin da yyi mata yawa, Hajiya Mariya ma na dakin da Mami suna jera uban kayan twins dake xube kasa kamar baxa su girma ba don kayan da Hajiya Mariya ta siyo masu tare da Abuturrab ma yawan su ba a cewa komai, ta kashe ma Col yafi dubu dari biyu duk a kayan yara, shi dai bai ce mata komai ba ta ajiye atm ta kara gaba, lkci lkci Noor kan kalli yaran da suke kwance kan gado sai motsi suke da ta kallesu kuma maganganun da Anty Maryam tayi mata sai ya fado mata, hakan yasa har suka fara kuka bata yi yunkurin daukarsu ba, sai Hajiya Mariya ce tace "Jariran nn sun cika son hannu naga alama" daga haka ta nufe su, Anty Maryam ce ta shigo dakin da sallama tayi masu sannu da aiki, tana kallon Noor tace "Har ynxu baki gama ba, to rufe ki xi ku gaisa da Abbanki" mikewa tayi da sauri tace "Abbana" Bayi ta shiga da sauri ta wanke hannunta ta fito, ta nufi kofa, Mami da Hajiya Mariya suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Anty Maryam kam murmushi tayi ta juya ta bi bayanta, Noor na sauka kasa taga Abbanta xaune parlorn, da Abuturrab da Col, ae bata san lkcn da ta taho da gudu ba ta fada jikinsa tace "Abbana!" murmushi yyi yana kallonta yace "Samantha...." Rungumesa tayi hawaye ya cika idonta tace "I missed you Abbana, i missed you" har lkcn yana murmushi yace "I missed you more daughter" hawaye na sakko mata tace "Abba Mumy fah?" Yace "She is home" tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "I wish i can see her" Abuturrab dai sai kallonsu yake, yaji wani iri har cikin ransa, Col ma dai kallonsu yake shi ma, Hajiya Mariya ce ta shigo parlon rike da Hussain, Ramla kuma na rike da Hassan suka nufo su, yana ganin haka ya janyeta jikinsa, Hajiya Mariya ta mika masa yaron tana murmushi ya karbesa, Ramla ta mika masa dayan ma, kallon yaran kawai yake, can yyi murmushi ya kalli Noor yace "Are you sure babies din ki ne wnn daughter" turo baki tayi tace "Nawa ne fa Abba" ya girgixa kai yace "A'a ba naki bane" tace "Abba wllh nawa ne" yace "Noo" kamar xata yi kuka tace "Da gaske Abba nawa ne" ya ja hancinta yace "You are nt saying the truth" kamar xata yi kuka tace "Am nt lying, they re my babies" yace "Hw will i believe they re urs, gashi ba su yi kama da ke ba?" juyawa Hajiya Mariya kar dariya ya subuce mata, Abuturrab ya sunkuyar da kansa yana murmushi, Hawaye har ya fara cika idonta ta kalli Abuturrab, Col ya d'an yi murmushi shi ma, kuka ta fara yi ta rufe kanta jikin Abbanta, Anty Maryam dai sai kallon ikon Allah take, Hajiya Mariya tace "Ki bar daddy daughter, yaran ki sun yi kama da ke kin ji" Murmushi kawai Abban nata ke yi ya kai bakinsa kunnenta yace "Yea, sun yi kama dake My daughter, they are beautiful just as you, i love them just as i love you...." A hankali ta dago kanta tana d'an murmushi tace "Thanks Abbana," yace "Yea my Samantha" turo baki tayi tace "Abba am nt Samantha any longer" ya d'an bude ido yace "Who are you then?" Lumshe ido tayi tace "Noor..." Yace "Ohh really? Noorul Islam?" Daga Abuturrab har Abbansa kallonsu kawai suke, ta girgixa kai tace "Rather, *Noorul Huda*" Gyada kai Abbanta ya dinga yi yace "Light of Guidance you mean" ta wara ido ta rungumesa tace "Yes Abba, i want to be just as my grandpa" Murmushi ya dinga yi yace "All the best daughter" Noor ji tayi kamar kada Abbanta ya tafi duk da ya kusa minti talatin a gidan, ana kiran isha yace xai wuce, Dad din Abuturrab ya rakasa suka fita. Abuturrab sai kallonta yake ganin ynda take hawaye, ta galla masa harara ta mike ta bar parlorn tana share hawayenta, mikewa yyi ya bi bayanta bedroom din Mami xata shiga ya jawota xuwa nasa bedroom din ya rufe kofa ta fashe da kuka, rungumeta yyi yace "Ae tun da kina nan kullum xai dinga xuwa fa wife" lamo tayi jikinsa tana sheshsheka, ya lumshe ido yace "Yaushe kika dawo Noor wife, you re getting me confused" bata ce komai ba, ya ja ta xuwa gefen gado ya xaunar da ita yace "Kin ji dear" tace "Ba ruwan ka" shiru yyi yana kallonta, can ya d'an yi murmushi yana kallon dogon hancinta yace "Ohk" hannu ya kai hancin nata yace "Ta nn kadai twins suka maki kara, ba don kuma nima nawa bashi da kyau ba.... Amma bakinsu, idonsu, fuskarsu, infact komai nasu nawa ne" yana magana ne yana mata wani irin kallo, ta tabe baki irin kan ka ake ji din nan, dariya yyi ya rungumeta yana kiss din wuyarta yace "There is always reason for everything baby" lumshe ido tayi bata ce komai ba. Haka Noor ta dinga samun kulawa yanda ya kamata gidansu Abuturrab, babu abinda aka raga mata ita da yaranta biyu, shi dai Col har lkcn an kasa gane inda ya dosa don haka yake bbu yabo bbu fallasa, ana gobe suna Anty Maryam ta dawo gidan da sassafe, irin shirye shiryen da ake yi gidan sai ka rantse biki xa ayi, bikin ma mai aji, da rana misalin karfe biyu Ahmad ya aiko da raguna biyu, hakan ya ba Abuturrab mamaki har su Mami, nan Mami ta kira Ummarsa tayi mata godiya sosai, a ranan da yamma Abban Noor shi ma ya aika nasa ragunan biyu, Abuturrab na waje tare da old time frnds dinsa da suka xo ganin babies kiran Sadeeq ya shigo wayarsa, ya dauka suka gaisa Sadeeq yace "Ya boys dina?" Abuturrab yace "Sunan nn, growing fast, suna kuma missing rugged dad nasu Sadeeq" Sadeeq yyi dariya yace "Awwwnn, am missing dem more, in'sha Allah gobe xan shigo Nigeria just because of them, xan ma transfer ynxu ka tashi ka shiga kasuwa ka samo masu biggest of rams biyu plss...." Abuturrab yace "Ohh i knw they will be grateful Abbakar, buh an siyo masu raguna da yawa, just get dem something different" Sadeeq yace "Alryt then, till i cum, a shafa min kansu, a kuma gaida min mai jego" Abuturrab yace "Alryt frnd, thanks much" karfe shidda na yamma Ummi ta iso a ranan, Mami ta ji dadin ganinta don abubuwa sun fara shan kansu, aiki yyi yawa sosai, lafiyayyen dinkin atamfar English biyu tayi ma Noor sai jewelries masu kyau, su Mami suka dinga godiya, ta bude jakarta ta fiddo wani box din earrings ta bude ta ciro dankunnen zinari me kyau a ciki ta mika ma Noor tace "Gashi daughter naki ne wnn" ta kalli su Mami dake kallonta da mamaki tayi dariya tace "A'a ba ni na siya mata ba, sadakinta ne dubu hamsin da Aliyu ya ban da dadewa, naga wnn xai fi dacewa shi yasa na siyo mata" Mami tayi murmushi tace "Allah sarki, to mun gode Hajiya, Allahu ya bar xumunci" ita ma tana murmushin tace "Amin" bayan Magrib aka shigo da babban cow gidan da kayan abinci me yawa, Abuturrab ya riga ya san Abbansa ne ya siya kuma hakan ne shi ya siya, sai bayan da ya bari ya tafi part dinsa snn ya bi sa, xaunawa yyi a kasa yana kallonsa a hankali yace "Abba Allah kara budi, mun gode sosai" Hade rai yyi yace "Godiya na me?" D'an murmushi Abuturrab yyi bai ce komai ba, Abba yace "Leave now before i kick you outttt" mikewa yyi yana murmushi ya fita daga dakin, Abba ya ciro wayarsa ya nemo number yayarsa, a hankali yyi dialing number tana dagawa tace "Ahmad" yayi kasa da kai yace "Na'am yaya kuna lafiya" tace "Toh lafiya lau kenan xa ace, ya gidan, da yara?" Yace "Alhmdllh" tace "Toh Allah yyi albarka, har yau Ali shiru ko Ahmad!" Shiru yyi don ko yaushe xai kirata sai tayi maganan Abuturrab, tace "Kana ji na Ahmad" yace "Ina ji yaya, Aliyu ya dawo" da karfi tace "Ya dawo??" Yace "Ehh" wani kabbara tayi tace "Yaushe?" Col yace "Kwanan nn" tace "Toh madallah, gari na wayewa xan dau hanyar kano idan Allah ya yrda," yace "Ba shi daya ya dawo ba yaya" ta tsuke fuska tace "Shi da wa?" Yace "Shi da yarinyar da yan biyu maza, gobe ne sunan yaran ma" bude baki tayi tace "Har da 'ya ya? Wato aurenta dai yyi koh Ahmad" yace "Ehh yaya" tace "Toh xa mu gani, ina nan xuwa jibi da sassafe in sha Allah ayi ta ta kare" daga haka ta katse wayar, ya mike ya isa window yana kallon waje ya rungume hannayensa.

*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫

By khaleesat Haiydar📚✍🏻

94.....

A daren ranan Abuturrab ya ishi Noor ta fadi sunan da take son a sa ma babies din tace ita bata sani ba, ya langwabar da kai yace "You mean baki da sunan da kike so a ran ki?" Nan ma ta girgixa masa kai, murmushi yyi yace "Toh shknn" gun Maminsa ya tafi yyi shawara da ita sunan da yake son rada ma babies din tace Allah ya raya su amma ya samu Abbansa dai tukun, ko da ya sanar da Abbansa xai yi masa takwara girgixa kai yyi yace "A'a na yafe" Abuturrab yyi shiru yana kallonsa, can Abba yace "Yea sbda mahaifinta hakan baxai yiwu ba, ka rada masu wani sunan daban, there is next time" Daga haka Abba ya mike ya dau wayarsa dake ring ya nufi kofa, Abuturrab bai iya yace komai ba don shi ma da farko yyi wnn tunanin bai mata adalci ba idan yasa nasa mahaifin, an dai san baxai kama ya sa ma d'ansa David ba, Washegari da ya kama friday aka rada ma twins sunansu, Hassan ya ci sunan Ahmad d'an Umma, Hussain kuma aka rada masa Abbakar Sadeeq, ya ci sunan Sadeeq, don wa ennan mutanen ne Abuturrab bai jin xai iya mance su a rayuwa, duk da ba wai Ahmad ya taka wani rawa bane amma tunda har shi ya kuma hada sa da Noor dinsa baxai mance sa ba, wannan suna dai ya samu halartar mutane da dama har da abokan col, har hakan ya dinga ba Hajiya Mariya da Mami mamaki, idan ka ga Noor a wnn rana sai kayi xaton amarya ce tsabar kyau da haduwar da tayi, sosai Mami suka kashe kudi gun ganin sun fito da ita, irin yanda mutane daga nisa da kusa suka cika gidan Col bbu masaka tsinke abun ba a magana, da gani kasan Abuturrab ba karamin d'an gata bane ko daga kan cimar da aka yi domin sunan, ni kam nace to da an gaya maku baban nawa na wasa ne ko don kun gansa a banxa yana wantagalili a gombe da maraba? to dai tillon d'a ne ga Colonel guda, sake baki da idanuwa nayi ganin members na Khaleesat Haiydar Novels su Maman Shakur, Ummu ilham, chamo, Anty Fyn, Ashmaad, Fiddo s dangi, Mimic, Fa'ee, Zuhoorah, Ummu Zainab, Ummu Amana, Humainah, Jamila.... kaiiii ni kam ina xan iya lissafo su... zaxxaune na hangosu kan kujeru ko wannensu ya cakare cikin ankon da suka yi na wani ubansun lace kalan sea green sai head jaa, sai daukar ido suke, ga abinci kala kala an ajiye ma kowa a kan table din gabansa daga gefensu kuma tulin gifts din yan biyu da suka yi wrapping a wrapping paper iri daya ne, Hajiya Mariya da Anty Maryam suka dinga bi suna gaisawa da su, ni ko na rike baki nace "Ohhhh wa yaga gayyar sodi😜" don ni dai nasan banda phatiemarkh bbu warce na gayyata wnn sunan, ae fa ban sake bakin da na rike ba na hango wata tawagar guda na 'yan haske writers💡su ma suna xaxxaune nace "Toh fahhh" su Ummy Shatu ne, Fatyma Zahrah, sweet sis Asmy B Aliyu, Billy Galadanci, Mom Ihsaan, faxy, Safiyya Huguma, Ayusher, feedohm.... kai gaskiya suna da yawa, su ma sun cakare cikin ankonsu na holland da suka yi ko wannensu sanye da siririn glass na 'yan gayu su ma ga uban gifts dinsu ajiye a gefe, Ummi sai bi take tana gaisawa da su, cannnn cikin jama'ar asali da aka gayyata aka basu pass din shigowa gate din Colonel na hango Iqram Mujaheed tana ta rawan kan kwaso drinks da ruwa tana raba ma mutane uwa an sa ta, ita a dole k'anwar khaleesat Haiydar bakin nn yaki rufuwa, na kyabe baki nace wa yaga karere🙄, kai na bai gama daurewa ba sai da nasamu lbrin ae fa akwai wani canopy da aka kafa a waje na gayun😎 Khlst Hydr Nvls su ma sun sha anko cikin shadda fari tas irin na Abuturrab da Sadeeq dake bi yana gaisawa da su, nace cabdi abun na yi ne oo.... Noor kam duk wnn budurin da ake bata da walwala, da ta tuna Anty Maryam da yaranta kadai ne nata a gidan sai hawaye ya cika idonta, ko ba a fadi ma Anty Maryam ba tasan me ke damun yar tata, ita ma duk sai ta ji wani iri. A can gidan Mr David kuwa yau kwana biyu knn Rachael ke fama da ciwon kan dake sa ta fita hayyacinta idan ta fara shi, duk asibitin da xa su bbu sauki sai don kansa yake tafiya, da yake ta kwana biyu bata yi ciwon ba sai take jin sa kamar sabo, abincin da mai aikin gidan ta girka Mr David ya kai mata har daki, tana durkushe bakin gado Bible a kusa da ita, ta rataye rosary a wuya, ya ajiye xai fita, cikin sanyin murya tace "Yanxu da Samantha tana kusa dani ciwon nn baxae kada ni haka ba, for heaven sake sai yaushe 'ya ta zata dawo garen, yaushe ne wnn rana da xan ga samantha" tana magana ne zar tausayi idon nn cike da kwalla, ya dawo dakin ya xauna jin tausayin matar tasa, glass din idonsa ya cire yace "Ke ce Rachael fadan ki ya fi karfin ki, nasan Samantha na son xuwa gun ki amma tana tsoro" Kallonsa take tace "Ya baxa ta ji tsoro ba bayan ta cuce ni, haka kawai ta mayar da ni barren din karfi da yaji kamar ban taba haihuwa ba, yanxu sai dai in ga wasu da 'ya ya ni bani da, ta fiffita namiji a kai na" tana kai wa nn ta fashe da kuka sosai, shiru yyi yana kallonta, can yace "Yanxu da xa ki ga samantha tsakanin ki da Allah ya xa ki yi Rachael" mikewa tayi tana share hawayen idonta tace "I know it, nasani dama, David ka san inda Samantha take shi yasa baka damu ba, nasan kai da kanuwarka kun san komai, kun san inda 'ya ta take, munafurtata kawai kuke" ta fashe da matsanancin kuka tace "Me nayi maku David da xa ku bar ni da kadaicin 'ya ta haka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login