Showing 51001 words to 54000 words out of 58555 words

Chapter 18 - EXILED PRINCE BOOK 3 by MEERAH.txt

17 Aug 2025

4367

da ga saman wuyan shi ta na fadin ' i'm sorry baby , kawai dai am so happy "

a hankali ya sauka da ga jikin ta ya koma bakin gadon ya zauna ya na fadin " da gaske ? na ji shikenan ina zuwa " ya fada ya na kokarin tashi

da sauri ta riko hannunshi ta marairaice fuska ta na fadin " baby ina kuma za ka je ? "

" kar ki damu , fruits ne zan je na dauko mana , na fara jin yunwa "
wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " baby dama ka na iya jin yunwa ? "
" no , robot ne ni ba na cin abincin , sake ni , ina zuwa "
ba musu ta sake mishi hannu ta na fadin " ni ma ina so tom "
" tasso mu tafi " ya fada ya na mika mata hannu
da sauri ta daura hannunta saman nashi , ta mike zaune ta sauko da ga saman gadon da allamun ta manta babu riga a jikin ta

a hankali ya juya ya dauki rigarta ya saki hannunta sannan ya saka mata ita , ya riko hannun ta su ka baro dakin
kai tsaye dining room ka nufa , da kan shi ya janyo mata chair ta zauna , sannan ya janyo ta geffenta ya janyo tray din fruits din a gaban su
a tare su ka fara shan fruits din nan , ta na ba shi a baki shi ma ya na ba ta , ta na zuba mishi shagwaba

sai da su ka ji sun koshi sannan su ka tashi su ka koma bedroom din su da ga nan kuma su ka shiga sabon aiki


▪WASHE GARI ⛅


a hankali ya ware idanun shi ya na karanto addu'ar tashi da ga barci , sannan ya mike zaune a hankali ya na sauke ajiyar zuciya
a hankali ya juya da kan shi , nan ya ga Inaya konce babu riga a jikin ta , sai duvet din da ya rufe ta zuwa kugu

tsayawa ya yi ya na kallon ta ya na tuno irin sambatun da ta zuba mishi daren jiya , ji ya yi kamar duk lokacin da su ka yi sex na jiya ya fi kowane dadi
a hankali ya daura hannun shi saman forehead din ta kafin ya sunkuyo da kan shi ya manna mata kiss murya kassa kassa ya ce " lokacin tashi da ga barci ya yi "
[25/10 à 15:51] MEERAH:



❤⚘E X I L E D P R I N C E⚘❤

( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊




【BOOK ________3 👑✌】





______________________⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘___________________




{ P A G E ………16 🌹🕊}






a hankali ya daura hannun shi saman forehead din ta kafin ya sunkuyo da kan shi ya manna mata kiss murya kassa kassa ya ce " lokacin tashi da ga barci ya yi "

cikin magagin barci ta ce mishi " Nesi ki kyale ni barci na ke ji " ta kai karshen ta na juya mishi baya
a hankali ya zagayo da hannunshi a kugunta ya janyo ta jikin shi ya na fadin " ba ita ba ce , bude ido ki gani "
ko jin shi ba ta yi da ga gani ta na jin dadin barcin ta

" ni fa ki na neman ki tsayar da ni fada na ke son mu tafi , amma ni na san maganin ki " ya kai karshen ya na fiddo tongue din shi ya sa cikin kunnenta ya fara juya ta a ciki

ba shiri ta ware idanun ta , ta janye kanta da sauri , ta juyo ta na kallon shi ta na dan kashe ido sai yamutse fuska ta ke
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " lafiya ki na min irin wannan kallon ? "
" why za ta tashe ni ? ina mafarki na mai dadi " ta fada ta na shagwabe fuska
a hankali ya kon ta ya juya su na fuskantar juna ya dago kan shi da hannu ya na fadin " uhm , mafarkin me ki ka yi , fada min na ji "

wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce " mafarki na yi mun sabu kyakyawan baby boy mai kama tak da kai , har wadanan Hazel eyes din naka , sai dai shi ya na murmushi ba kamar kai ba " ta kai karshen ta na wata yar karamar dariya

a hankali ya kai hannu saman kugun ta ya janyo ta jikin shi ya na fadin " uhm , ai ni ma ina murmushi , kawai dai yanzu ba lokacin yin murmushina ne ba "

" shikenan na ji , na fada maka sunan babyn mu ? "
gyada mata kai ya yi allamun Eh
" amma sai ka yi min alkawari idan mu ka haifi baby boy sunan za ka saka mishi " ta fada cike da shagwaba

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " shikenan , na yi miki alkawari "
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta ce mishi " Nayel "
Har wata muguwar faduwa gaban shi ya yi ya na zaro idanu ya na kallon ta
" baby , ko sunan bai yi maka ba ? " ta fada ta na marairaice mishi fuska

a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya kai lips din shi saman forehead din ta ya manna mata kiss ya na fadin " it's perfect , tashi mu je mu yi wanka "

turo dan bakin nan nata ta yi ta kara matsowa jikinsa , cike da shagwaba ta ce mishi " na fada maka wani abu ? gaskiya tsoron haihuwa na ke , na sha gani cikin film in mata na haihuwa wasu har mutuwa su ke "

a hankali ya riko hannunta ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss sannan ya ce mata " ba abun da zai faru , idan lokacin ya zo haka zan rike hannun ki , zan kasance tare da ke , in dai ina nan ba zan taba bari mutuwa ta raba ni da ke a lokacin da mu ka fi bukatar ki , specially babyn da za mu samu "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce mishi " da gaske babyna ? "
gyada mata kai ya yi allamun Eh
ba ta ce mishi komai ba ta ida shigewa jikinsa ta rungume shi tsam
haka shi ma rungume ta sosai ya yi duk da ya na jin zuciyar shi ba dadi , tabbas shi ma ya na jin tsoro a ce wajen haihuwa ya rasa ta , ya san ko ba karamar wuya za ta sha ba a lokacin saboda karancin shekarun ta , amma har cikin zuciyar shi ya na son ya medo Nayel cikin familyn shi , ya na son ya medowa Ammien shi babyn ta , shi ya sa ba ya hakura ya ce su samun babyn

( 👻👻👻 shi fa Malik tun lokacin da ya yi dis virgin din ta bai sake bari ya yi realizing a jikin ta ba , ba ya son ya takura mata ne a kan wata contraception shi ya sa bai damu ba da sauyawar nan da ta yi saboda ya san ba a jikin ta ba ya ke zubar da ruwan jarabar shi ba 👻👻👻👻👻👻👻👻👻👻 )

sai da su ka dauki lokaci a haka kafin ya ce mata " please , tashi mu je mu yi wanka "

gyada mishi kai kawai ta yi kafin ta sake shi , ta sauko da kafafun ta kassa ta mike ta fara takawa a hankali ta shige toilet
sai da ya bari ta shiga sannan ya kai hannu cikin duvet din ya fara neman short din shi ya saka sannan ya janye duvet din ya tashi ya shiga toilet din shi ma

a tare su ka yi wankan su , su ka fito su ka shirya a tare sannan su ka baro part din , amma ba su wuce fada kai tsaye ba , sai da su ka fara biyawa wajen MALIKAT AL'UMU , Malik ya ga mahaifiyarshi , ta na nan dai konce kamar gawa , ko motsi ba ta yi , ga shi doctor sun kasa gano abun da ke damun ta

a haka ya gama abun da zai yi , su ka baro Hospital din , har ya budewa Inaya kofar motar su kawai ya ga ta tsaya ta kurawa waje guda ido ta na sakin murmushi
a hankali ya juya ya kalli wajen da ta ke kallo
nan ya ga Shadow ya nufa su da mugun gudu , dogarai na biye da shi da gudu su na neman su kama shi amma ina ya tsere musu

a hankali Inaya ta yi taku biyu gaba dai-dai lokacin da Shadow ya karaso wajen ta , ya tsaya cak ya na kuka

wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " ni ma na yi kewar ka " ta kai karshen ta na daura hannun ta saman shi

a hankali ya juya ya dan rinsina allamun ta hau
a hankali ta juya ta Kalli Malik da ya tsare ta da idanu , a iya sannin shi , bayan mahaifinshi babu wanda ya taba hawan Shadow har shi kan shi

cikin sanyin murya ta ce mishi " baby , ya ce akwai abun da ya ke son ya gwada min zan iya tafiya ? " ta kai karshen ta na marairaice fuska

gyada mata kai kawai ya yi kafin ya shiga cikin motar shi , da sauri guard ya rufe kofar , driver ya tada su ka nufi Fada
su na barin wajen Inaya ta juya a hankali ta haye saman bayan Shadow murya kassa kassa ta ce mishi " yi a hankali , ka ji ? "

wani dan karamin kuka ya yi kafin ya fara gudu da ita , duk in da ta wuce sai an bi ta da kallo , kowa ya na mamakin yadda a ka yi Shadow ya yarda ta hau saman shi , dan duk wanda ya taso cikin masarautar ya san Shadow ba ya yarda da kowa sai Malik Hicham

ita kuwa Inaya ba su ma san su na yi ba , sai gudu Shadow ya ke yi da ita
kai tsaye cen bayan masarautar ya nufa da ita inda babu kowa , ko dogarai babu
sai da ya karaso wajen wata katuwar bishiya sannan ya tsaya , ya dan rinsina allamun ta sauka

ba musu Inaya ta sauka da ga saman bayan shi , ta na bin wajen da kallo kafin ta kalli Shadow ta ce mishi " me ya sa ka kawo ni nan ? "

shiru ya yi ya na kallon ta , a hankali Inaya ta fara bin wajen da kallo ta ga babu kowa a wajen sai ita da Shadow sai Allah

a hankali ta nufo bishiyar nan , ta fara zagayen ta , ta na kallon ta da ga sama har kassa
a hankali ta daura hannunta saman bishiyar , kamar wadda electric current ya kama haka ta janye hannunta , ta yi baya ta na kallon bishiyar zuciyar ta na duka uku uku

wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dago hannun a hankali ta na kokarin mayar da shi saman bishiyar
wannan karan ma haka ta janye shi , har da sakin wata yar karamar kara ta na yin baya
karewa bishiyar kallo da kyau ta yi kafin ta nufi Shadow ta Haye bayan shi ta na fadin " mu je ka kai ni Fada "
a hankali Shadow ya mike ya juya su ka bar wajen da mugun gudu ya nufi hanyar Fada da ita


▪MALIK


bakin shi da Sallama cen kassan makoshi ya shigo fadar , ta na cike ko da mutane sai tattaunawa su ke yi
su na ganin Malik wajen ya yi tsit ,
wani dan karamin tsaki Aymane ya yi ya na kauda kai gefe cikin zuciyar shi ya na cewa " kash , matsiyaci kawai , wlh sai na ga bayan ka "

da sauri Diya ya mike da ga saman sofar ya nufi Malik ya rungume shi murya kassa kassa ya ce " i'm really HAPPY to see you , why ka taho , ka bari har ka kara samun karfin jikin ka mana " ya kai karshen ya na raba jikin shi da na Malik

murya cen kassan makoshi ya ce " no , mu je kawai " ya fada ya na fara takawa
da sauri mutanan wajen kowa ya mike tsaye su na sunkuyar da kai allamun girmamawa
Malik kuwa kai bi ta kan su ba ya nufi chair din shi ya zauna , Diya ya koma geffen shi ya tsaya

ya na zama kowa ya koma ya zauna , su na mika sakon gaisuwar su , su na yi mishi ya jiki
gyada musu kai Malik ya ke yi
sai da su ka Kamala gaishe shi sannan ya juya ya kalli Diya ya ce " zaman me ku ke yi ? "

dan jinkirtawa Diya ya yi kafin ya ce " ranka shi dade dama a kan kokarin kashe da a ka yi ne , ina ga General Abdallah zai fi dacewa ya yi muku bayani " ya kai karshen ya na kallon General

a hankali General ya mike ya na fadin " ranka shi dade , wannan karan shi ne na biyu da a ka yi kokarin kashe ka , na farko marigayi Malik ne ya tafi a madadin ka , mun kuma kamo wanda su ka saka a yi aikin , kuma an ba su hukunci dai'dai abun da su ka aikata , yanzu kuma an sake kokarin kashe ka , hakan na nufin bayan Miram da Mohammed akwai wasu da ke son ganin bayan ka ranka shi dade "

gyada kan shi Malik ya yi a hankali kafin ya ce " and ? "

ci gaba da Magana General ya yi ya na fadin " ranka shi dade , mun fara investigation a kan wannan case din , a ranar fruits din da ka sha da ga part din MALIKAT AL'UMU ya fito , duk wasu bayi da ke kula da bangaran MALIKAT AL'UMU yanzu haka su na hannun mu , bayan mun yi wa wasu da ga cikin su tambayoyi , sun ce Gimbiya Tesnim ce ta ba da umarnin a shirya muku fruits din , duk yadda a ka yi wani ya yi anfani da wannan damar ce dan ya ga bayan ka "

shiru Malik ya yi ya na kallon shi ba tare da ya ce komai ba har sai da General ya gaji da tsayuwar shi

a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " ku saki bayin da ku ka kama , kowane ya koma bakin aikin aikin shi "

duk mutanan wajen sai da su ka zaro idanu jin abun da Malik ya ce
cike da rudu General ya ce " amma ranka shi dade........ "
bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi da cewa " General ba shawara na ke ba ka ba , umarni ne , duk wanda ya yi kokarin kashe ni ya je shi ya sani , kuma ai ka na gani , ga ni nan tsaye a gaban ka , ban mutu ba , ko na mutu ? "

a hankali General ya girgiza mishi kai ya na fadin " a'a ranka shi dade "

" okay , ka sa a sake su yau din nan " ya na gama fadar haka ya kauda kai gefe
a hankali General ya koma saman sofar shi ya zauna ya na kallon Malik ya na mamakin wane irin mutum ne shi , a yi kokarin kashe ka , amma ka ce a bar zancen kawai

ya na zama ko Inaya ta shigo fadar ta na sallama
a tare duk su ka juyo su na kallon ta , har shi kan shi Malik , har wani dan kashe ido ya ke kamar me maye , kawai so ya ke ya tashi ya rungume abun shi su bar wajen
a hankali ta fara takawa cikin fadar duk inda ta wuce sai sun dan sunkuyar da kai su na gaishe ta cikin girmamawa dan a yanzu a matsayin MALIKAT din su ta ke

ita kuwa ba ta bi ta kan su ba , ta nufi Malik da ya tsare ta da ido babu ko kiftawa
sai da ta karaso tsakiyar fadar sannan ta tsaya cak ta na kallon Malik

wani dan karamin murmushin geffen fuska ta yi kafin ta ce " ina mika gaisuwa ta ga shugaban wannan kassar mai Albarka " ta fada ta na dan rinsinar da kai

har cikin zuciyar shi maganar ba karamar dariya ta so ta bashi ba , amma sai ya danne
ba shi kadai ba duk mutanan wajen sai da su ka saki wani dan karamin murmushi su na kallon ta

shi kuwa Diya sai da ya yi murmushi mai dan sauti kafin ya ce " mai martaba na amsa gaisuwar uwar gidan shi , sarauniyar kassar Saudiya har shi kan shi mai Saudiyar "

ba shiri Malik ya juya ya kalli Diya da ke ta faman qumshe dariya dama da gangan ya fadi hakan
sarai Diya ya lura da irin kallon da Malik ke yi mishi amma bai kula shi ba sai ma ci gaba da maganar shi ya yi ya na fadin " me ke tafe da shugabar mu a yau ? "

dan jinkirtawa Inaya ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login