Showing 9001 words to 12000 words out of 85780 words

Chapter 4 - LAUJE CIKIN NADI COMPLETE BOOK BY Mrs Suleiman .pdf

28 Apr 2025

6650

kira mama dake zaune gefen Abba Æ™ tana
yanka mishi apples a plate wayar ta tayi ringing

Seda ta kammala tukun ta kira shi

yana É—agawa yace


"Mama yau akwai kunun gyaÉ—ar nan kuwa?"


Murmushi mama tayi tana gyara zamanta kafin tace

"So sorry yaro na, na mance shaf ba'a kawo maka ba"

Kafin yace a ba mumtaz ta kawo mishi, mama tayi saurin faÉ—in


"Bari mumtaz ta kawo maka yanzun nan"


Godiya yayi mata suka aje wayar


Number mumtaz mama tayi dialing, bugu biyu ta ɗaga tana wani shaƙe murya kamar me ciwon
gaske, a tunanin ta wani aikin mamar zata saka ta


Ilai kuwa mama tace

"Ki duba kan dinnig flask É—in yayan ku na nan ki É—auka ki kai mishi yanzu"

Da sauri mumtaz ta wuntsulo daga kan kujerar da take kwance tace

"mama kuma kince nice zan kawo mishi?"


Tsaki mama ta ja tace

"in sakko inga baki kai mishi ba, zan baki mamaki ke da baki son a more ki sam"

Ta tsinka wayar ta, tana ci gaba da mammatsa wa Abba ƙ ƙafar shi.




Cikin marairaicewa mumtaz ta kalli sakina dake waya da saurayin tace

"Dan Allah sakina ki kaima ya faruk kunun shi"

Mumtaz bata gama rufe baki ba sakina tace


"caɓ, wallahi ba zani ba, salon inje ya rinƙa mun kallon wulaƙancin nan da ya saba"


Kamar mumtaz zatayi kuka tace

"Baki fahimce shi bane, haka yake shi, ni wlh jiwa nake gani shiyasa nace ki kai mishi"


Tsaki sakina ta sake yi, seda ta gyara kwanciyar ta tkun tace

"Haka nan zaki daddafa ki kai malama, thank God ba'a gidan nan nake ba da za'a kwashi Æ´an
kallo dani"

Ta maida wayar ta a kunne taci gaba sa firar ta.



A zuciye mumtaz ta yayimi hijabin ta tasaka tukun ta ɗauki flask ɗin kamar shine me laifin, ƙiris
ya hana shi suɓucewa daga hannun ta tasamu ta taro shi

Tafi minti goma a tsaye tana jiran taga ko zata ga wani daga cikin yaran gidan ta bashi ya kai,
haka nan ta gaji da tsayuwar ta tayi shahada kawai ta nufi É—akin



Ya faruk na zaune a gaban laptop É—in shi, vedion mumtaz wanda ta É—auki agogon nan ya kafa
ma ido yana kallo,
har yanzu ya kasa yarda da abun, se yake gani kamar ba nutsatstsiyar mumtaz É—in da ya sani
bace


Knocking ɗin ƙofar da tayi ne yasa yayi maza yayi pausing vedion ya juyar da laptop ɗin zuwa
ɗayan ɓangaren da ba lale wanda ze shigo ya gani ba


Seda ya kimtsa tukun yace

"Come in"

A hankali mumtaz ta tura ƙofar kamar warce ƙwai ya fashe ma a ciki


Tunda ta shigo ya kafe ta da manyan idanun shi yana kallon ta,

Gaba ɗaya wani mugun tausayin Abba ƙ da mama ne suka lulluɓe shi, for the first time da yaji
kamar ya fashe da kuka tun bayan ya mallaki hankalin shi.


Tana sunkuyawa zata ajiye flask É—in ya faruk yayi saurin tashi ya rufe É—akin da key


Tana ganin haka ta juyo a tsorace tana niyar kware baki ta kurma ihu


Kamar yasan me take da shirin yi kuwa, manyan idanun shi ya zazzaro waje ya É—ora yatsar shi
ɗaya a kan laɓɓan shi yace

"shiii, kina fasa ihun nan zan sauya miki kamanni wlh"


Ƙut mumtaz ta haɗiye ihun ta, taci gaba da rarraba nata manyan idanun

Belt ɗin jikin shi ya zaro, tana ganin haka ta tsugunna ta dunƙule waje ɗaya tana ɓarin jiki



Rufe ida ya faruk yayi ya zambaÉ—a mata É—aya a jikin ta

Kuma ya hana ta ihu


Sosai mumtaz ta tsorata da yarda taga ya faruk ɗin, a iya tsawon rayuwar ta bata yaɓa gani ya
É—aga hannu ya daki wani a cikin gidan nan ba se yanzu, yanzun kuma a kanta



Cikin tsananin tsoro mumtaz tace

"Dan Allah ya faruk kayi haƙuri, wallahi mantawa nayi ranar da kace inzo in same ka ba da
gangan naƙi zuwa ba"


Bayan hannun shi yasa ya make bakin ta da ƙarfi, cikin fushi yace


"Rufe min baki maƙaryaciya, bayan sata har ƙarya kika koya kenan?"


Ƙwalalo manya idanun ta tayi waje, a lokaci ɗaya kuma kukan da take ya ɗauke ɗif


Jiki a sanyaye ta sauke kanta ƙasa tana sauraron yarda gaban ta ke dukan uku-uku



Sosai ya faruk ke kallo da nazartar yanayin ta,


Farko yaso yazo mata da mugun zafi, amma haka nan yaji zuciyar shi bata aminta da hakan ba


Unexpected muntaz taji murya ya faruk a kanta cikin nutsuwa yace


"Bayan ni akwai wanda ya taɓa kamaki?"

Shiru tayi bata ce komi ba, seda ya buÉ—e murya yayi kamar ze sake shauÉ—a mata belt É—in tukun
ta girgiza mishi kai da sauri


Rai a ɓace yace "buɗe bakin ki kiyi min magana kamar yarda kika ji inayi"


Kanta a ƙasa tace "a'a"


Kallon ta kawai ya faruk yake, sam ya rasa ta ina ma ze fara, sosai yake jin É—acin abun a ranshi


Can dai ya daure yace


"Me kika rasa da kika saka rayuwar ki a cikin wannan ƙazamar ɗabi'ar?"


Bata ce komi ba se sheshshekar kuka da take


Shima be buƙaci da yajin ba ya ɗora da


"Yanzu kina ganin kinyi wa Abba Æ™ da mama adalci kenan? kina ganin suka san wannan abun
ba ze zama musu mugun tashin hankali ba?
Ashe baki da tausayi? imanin ki ragagge ne?
Baki jin kunyar Allah balle ace kunyar da zaki shiga duk ranar da aka kama ki?"


Kuka kawai mumtaz take, maganganun ya faruk nayi mata raga raga da zuciya


A tsawace yace

"ki min shiru, wannn kukan munafurci ne ai, gaya min tun yauahe kika fara satar"?


Kasa cewa komi tayi, banda aukin share hawaye

Wata tambayar ya faruk ya sake wurgo mata

"In kin saci kayan me kike da su?"


Kanta a ƙasa tace

"Ban taɓa ɗaukar ma kowa ba ai"

Bayan hannun shi ya saka ya make mata baki tukun ya waigo mata da screen É—in laptop É—in shi
yace


"Wannan wacece?"


Baki sake mumtaz ke kallon vedion kanta da kanta, da dai ta san ta kamu kawai se ta fashe da
kuka me taɓa zuciya


Cikin muryar kuka tace,

"wallahi wannan shine karo na farko da na fara É—auka, nasha ganin abubuwa zan É—auka amma
bana samun dama, kuma kaima yanzu zanje in É—akko maka kayan ka"


Da mamaki ya faruk ke kallon ta,jin tace "tasha gani abu amma bata samun É—auka"


"Da kika É—auki wannan me zakiyi da shi da?"

"bakomai" tace cikin kuka


Da sauri ya faruk yace

"Ƙarya kike, kodai kina da saurayin dake saka ki ɗauke-ɗauke?"


Da sauri ta karkaÉ—a kanta, tana ci gaba da share hawayen ta da bayan hannun ta

Shiru ya faruk yayi, can dai yace "tashi kije"


Sosai tayi mamakin furucin shi


Tsaye tayi taƙi fita,


Da ƙarfi yace

"I said get out!!"

Da gudu ta fice tana ƙumshe kukan da ya tawo mata da mugun ƙarfi.


ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

LAUJE CIKIN NAÆŠI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA👹
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAÆŠI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

pg8

Memakon ta wuce side É—in su kai tsaye se ta wuce can back yard É—in side É—in su

Suna ajiye kujeru haka a wajen dan hutawa wani lokacin
Zama tayi dirshen a ƙasa ta haɗe kai da gwiwa

Tunda ta shigo wajen mus'ab yaga shigowar ta,
Ya jima yana kallon ta bece komi ba, sema faÉ—uwa da gaban shi ke yi tunda yaji sautin kukan ta


A hankali ya taso daga inda yake ya matso kusa da ita

Dafatan da yayi ne yayi matuƙar razana ta, ƙiris ya hana ta kurma ihu, Allah yasa yayi saurin yin
magana


Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta saka hannun tana share hawayen fuskar ta


Sam taƙi yarda ta kalli mus'ab da ta san shima kallon ta yake

Abubuwa take na irin wanda suke a tsarge É—in nan


Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace


"me ke damun ki? waye ya saka ki kuka?"


Muryar ta na rawa tace

'Bakowa ya mus'ab, kawai bana jin daÉ—in komi ne"


A hankali, yarda ba lale tajishi ba ya ce

"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!


Jin bece komi ba yasa tace


"Kai me kake yi a ban ya mus'ab?"


Ƙirƙirar murmushi yayi tukun yace

"Zafi ne ya fito dani"

Da sauri mumtaz ta ware manyan idanun ta da mamaki tace

"Zafi fa kace? Air con É—in É—akin ka fa?"


Shiru mus'ab yayi ya dafe kanshi, shi sam ya manta da wata aba wai air con,
Sam baya jin daÉ—i ji yake kamar ana iza mishi wuta a zuciyar shi, azalzala kawai yake ji, sam ya
rasa nutsuwa ko kaÉ—an
Bugu da ƙari ga abunda ya faru ɗazu, wanda shi kanshi seda ya bar wajen tukun yake tuna
rashin É—a'ar da yayi"


Still bece komi É—in ba,
Miƙewa yayi sannan yace


"Ki rinƙa addu'a ne, kuma kar in sake ganin dan abu ya dameki ki rinƙa fitowa wajen nan da
daddare, tashi ki wuce ciki"


Tashi tayi ta wuce jiki a sanyaye,

Seda mus'ab yadena hangen ta tukun ya koma ya zauna a wajen memakon É—aki da yayi niyar
tafiya


Zabga tagumi yayi hannu bibbiyu yana maganar zuci da be san ta fito fili ba

"Allah na roƙeka kasa ba abinda nake ji bane yake damun mumtaz, Allah ka tsayar a iyakacin
kaina kar ka É—ora musu ya rabb, nima ka yaye min ya Allah".




Sanda mumtaz ta shiga side É—in su kowa ya kama gaban shi dan har an kashe wutar ko'ina
ÆŠaki ta wuce itama kai tsaye tunani kala-kala a cikin ranta


Abunda ya bata mamaki shine, titsiyen da ya faruk yayi mata ya sa taji tsanar kayan kowa,
amma tunda ta saka ƙafarta a side ɗin su taji damuwar ta ragun mata, tana ƙara jin kwaɗaituwar
sake tattara duk wani abu da yazo gaban ta koda kuwa na Abba ne ko mama

Murmushi tayi bayan ta sake yin ido biyu da agogunan ya faruk da sam ta gama ƙudirtar
salwantar da su ta ko wani irin hali a goben nan


A hankali ta saka hannu ta shafi laɓɓan ta inda tasha masga ɗazu

Jin sun É—an tasa kaÉ—an yasa ta murguÉ—a baki tace

"Allah ya isa na".



2am

Karo na kusan biyar kenan yana fitowa daga wanka,

In ka kalli idon shi kamar an zazzago su tsabar azabar raÉ—aÉ—in da yake ji a cikin zuviyar shi

A daddafe ya samu yayi sallar isha da se yanzu ya samu zarafin yin ta


Tunda ya idar ya janyo biro da takardar da ya ajiye tun É—azu

Hannun shi na rawa idanun shu na zubar da rywa ya fara rubutu .....



Seda ya gama, ya ninke takardar tukun ya ajiye a gefe


Jeans da riga ne a jikin shi, se baƙar jacket da ya ɗora akai


Ya jima a tsaye kanshi jingine da bango kafin ya É—auki takardar nan

Seda ya kalli agogo yaga huÉ—u saura, lokacin da yawa wasu sun tashi sahur


Fitowa yayi daga É—akin ya wuce part É—in su kai tsaye

Knocking biyu yayi Altine ta buÉ—e mishi ya shiga


Kallon stairs yayi yaga alamun mama bata sakko ba, dan ko hasken corridor É—in ba'a kunna ba


Ɗakin mumtaz ya ɗan ƙonƙosa, tashin ta kenan dama taji knocking ɗin, ta aza mama ce ma,
shiyasa tayi saurin sakkowa ta buÉ—e É—akin


Tana buɗewa taga mus'ab tsaye a bakin ƙofar


"lafia ya mus'ab?"


Muryar shi a dishe yace


"mama bata sakko bane?"


GyaÉ—a kai kawai tayi tana ci gaba da kallon shi


Be sake cewa komi ba ya saka hannun shi a aljihun jacket ɗin shi ya ciro takardar ɗazu ya miƙa
mata


Hannu tasa ta karɓa

Kafin ma ta nemi ƙarin bayani yace


"Ki ba mama in ta fito, ni ba zan samu damar shigowa ba anjima, kice mata list É—in data ce
akawo mata ne"

Yana gama faÉ—ar haka ya juya ze fice


Da sauri mumtaz tace

"ya mus'ab"

Waigowa yayi yana ya kalle ta da jajayen idanuwan shi


Jiki a sanyaye tace

"Baka da lafia ne?"


Murmushi yayi mata tukun yace

"lafia lau nake, kawai ban samu enough bacci bane"


Yana gama faɗin haka ya ƙarasa ficewa.


Anan kan mirrow ta ajiye takardar ta shige toilet.





Wajen sha É—aya da rabi na safe, Mama na zaune tana nuna ma Altine kayayyakin sallah da
za'a kai gidan marayu tana haÉ—e su a babban kwali


Dogon list ne a hannun ta na sunayen jama'a, sannu a hankali sukai ta fitar da na kowa, hatta
altine an cire mata nata rabon


Rabon yazo ya caɓe mata, ga shirin tafiya umara da zasuyi jibi shiyasa take so ta sallami kowa
da kowa dan ta tafi cikin kwanciyar rai



Mumtaz na zaune a gefe tana auna sarkar wuyan mama da tun fitowar ta take tsole mata idanu,
ta tuna da takardar da mus'ab ya bata É—azu da asubah, kamar ba zata tashi ba can dai tace


"Akwai fa sauran ki mama, É—azu ya mus'ab ya kawo wani list É—in fa"

Bata jira cewar mama ba tayi É—aki.


Hankalin ta na kab wayar da take daddanawa ta miƙa wa mama takardar har tana ƙoƙarin tsole
mata idanu



Daga mama har Altine sakato sukayi suna kallon Mumtaz da bata ma san me takeyi ba


Rai a ɓace mama tace

"Ki cire min idon se ki huta"


ÆŠago kanta tayi, memakon ta gane abinda tayi sema dariya datayi tace

"Da abun yayi mana yawa ai mama, ga makanta ga kuma faÉ—a"


Da sauri Altine ta sauke kanta ƙasa tana ƙunshe dariyar dake cinta


Mumtaz kam ganin kallon da mama ke mata yasa tace


"Allah baki haƙuri, ni wasa nake miki" ta aje mata takardar a table ɗin gaban ta.



Seda mama ta gama da gaba É—aya na hannun ta tukun ta É—auki warda mumtaz ta ajiye mata


Haka kurin taji gaban ta na dukan uku-uku


A hankali ta warware, memakon taga sunaye ko gidauniyoyi se kawai taga an fara da

"Dear mamana da kuma Abba na"


Dummmm, haka gaban ta ya bata wani mugun sauti, ji tayi miyan bakin ta ya É—auke, numfashin

ta na ƙoƙarin fin ƙarfin ta

Ido a waje take karanta takardar, gaba É—aya hannun ta rawa yake


Tana kaiwa ƙarshe ta hau nanata kalmar "innalillahi wa'inna ilaihirrahi'un! da ikacin ƙarfin ta



Mumtaz da Altine sukayi kanta da gudu suna auna ma sunan ta kira


Dai-dai shigowar Ahmad kenan ya iske su a haka

Shima da sauri ya ƙarasa inda suke ƙoƙarin ganin sun tare mama bata kai ƙasa ba
Amma inaa jikin ta ya riga da ya gama saki ba wani alamun numfashi a tattare da ita.


ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

LAUJE CIKIN NAÆŠI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA👹
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAÆŠI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 9-10

Ganin yarda Ahmad ke girgiza ta da ƙarfi yana kiran sunan ta yasa Mumtaz ficewa da gudu
tana faÉ—in

"Innalillahi mama bata numfashi, bala ka fito da mota".

Cikin bacci ya faruk ke jiwo kururuwar ta, kasaƙe yayi dan yaji me take faɗi


Jin muryoyi daban daban ciki harda na Umma ƙarama(kishiyar umma b)
Yasa shi saurin miƙewa yana lalubar jallabiyar shi

Da sauri ya fito, jin furucin Umma babba da tace

"Wannan gawa ce ai, ba wani alamun rai a tattare da ita"


A sukwane ya faruk ya ƙarasa palon sunyi cirko-cirko, mummy da umma b na faɗin ta mutu,
Aunty da umma ƙarama na faɗin a tafi hospital dai.


Gaba É—aya ihun mumtaz yasa ba'a jin komi, seda ya faruk ya waiga ya daka mata tsawa tukun
ta lafa da iface ifacen,

Jiki a sanyaye Amal ta rungume ta itama tana ta É—igar da hawaye


Kutsawa wajen yayi gaban shi na dukan uku uku hannun shi ya saka a wuyan mama, jin da
alamun numfashi a tattare da ita yasa ya cicciɓe ta yayi waje da gudu yana faɗin


"Fito da mota Ahmad, tana numfashi"


ÆŠiii, haka suka biyo shi harabar gidan


Kafin Ahmad ya É—akko motar har bala driver ya fito da ita


A bayan motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login