Showing 27001 words to 30000 words out of 85780 words

Chapter 10 - LAUJE CIKIN NADI COMPLETE BOOK BY Mrs Suleiman .pdf

28 Apr 2025

6651

Daga can ta jiyo Amal tace "ban sani ba umma Æ™"

Umma Æ™ tace "kamar ya baki sani ba?"

Da ɗan ƙosawa tace "da muka dawo a waje muka barta, nace tazo muje tayi banza dani, daga
nan ban san inda tayi ba"

Umma Æ™ na tsaye a É—akin su Amal, umma b ta shigo jin maganar su,

Ba yabo ba fallasa tace "hajiya sumayya lafia?"

Mama na jiyo su daga can, kafin umma Æ™ tabawa umma b amsa mama tace

"ko tana part É—ina ne?"

Umma Æ™ tace "bari inje can to"

Taɓe baki umma babba tayi ta juya tana faɗin

"Gulmamammu kawai, shishshigi babu kwarjini" ta ƙarashe ficewa.

Can ma wayam bata, nan ne fa hankalin mama ya fara tashi, farat É—aya tafiyar mus'ab ta dawo
mata kai

Cike da zullumi tace

"ko dai tana gidan Abbas ko ƙasim?"

Kafin umma Æ™ tayi magana, mama taga call É—in mumtaz na shigowa, da sauri tace "gashi tana

kirana bari naji".

Seda taji daga wajen ta tukun hankalin ta ya kwanta, duk da tayi mata faÉ—an rashin gaya mata
datayi.

Da suka gama wayar ta kira umma Æ™ ta gaya mata taje gidan ya junaid ne ashe.

*****KHALID

Daga yinin jiya zuwa na yau duk yabi ya susuce rashin ji daga wajen ta, msgs kam ya tura mata
su kamar me

Bashi da aiki se duba waya akai akai,

Bayan sallar isha haka ya sake wankar ƙafa ya koma hotel ɗin da suka sauka, haka yasha
zama kamar jiya amma bata da dalilin ta.

Zuwan shi na jiya dana yau duk akan idon ya faruk, yasan khalid farin sani tunda a ƙarƙashin su
yake aiki,

Yasan yana da kirki, amma ba ze iya cewa ga hallayyar shi ba, a fili yace

"Zanci gaba da sa maka ido naga dame kazo".

Mumtaz na kwance a É—akin data sauka, baka jin motsin kowa alamar dai dare ya ratsa

Juyi kawai take tana farfasa maganganun da ya mus'ab yayi mata É—azu,
Gaba É—aya kanta ya kulle ta rasa wani kalar tunani zata yi akan maganar, dama tacika damun
kanta taji ya fara sassara mata,

Haka ta tattara ta watsar da zancen, abu É—aya ne ta É—auka shine bazata bari kowa yaji ba har
sanda ya dace

Khalid ne ya faÉ—o mata a rai lokaci É—aya, sam ta mance da babin shi daga jiya zuwa yau, se
yanzu daya faÉ—o mata

Wayarta dake gefe ta janyo, kunna data tayi ta hau whatsapp, kan kice me saƙonnin shi suka

rinƙa antayowa

Tsuru tayi ta kafe wayar da ido

Seda suka gama shigowa tas tukun ta buɗe ta fara bin saƙonnin ɗaya bayan ɗaya tana dubawa

A karon farko tun jiya da tayi murmushi, ita kanta bata san sanda hakan ta kasance ba
Se tsintar kanta tayi da replying shi, ta rubuta "whats wrong"? akan saƙon shi da ya rubuta "ina
cikin wani hali" da manyan baƙi.

Khalid na ganin saƙon ta, hannun shi har rawa yake wajen danna mata kira

Tana É—aga wayar ta kara a kunne tayi shiru tana sauraren shi

"Baki da wani excuse da zaki bani, kina ina?"

Murmushi mumtaz tayi kafin tace "ina nan mana"

Cikin zaƙuwa yace "meyesa ban ganki a masallaci ba? har hotel ɗin da kika sauka naje nasha
jira amma banga ko me kama dake ba mumtaz" yaja sunan ta daga ƙarshe

Zumɓuro baki tayi kamar yana ganin ta kafin tace

"kai dai bari, Allah ne ya haɗamu da ɗan baƙin ciki yasa aka auno mu gida"

Yarda tayi maganar dole ya baka dariya, seda khalid ya dara kafin yace

"who was that person?"

Seda ta taɓe baki again kafin tace "a dangi yake, ataiƙaice dai ina ƙasarmu ta gado"

Duk da khalid beji daÉ—i ba, amma ya samu relief ko yayane, nan suka raba kusan daren gaba
É—aya suna fira,
Abun mamaki sosai mumtaz ta saki jiki da shi se gashi tana neman kunci da damuwar data
shiga sam ta raaa ta, ji tayi ma kamar kar ya kashe wayar su dauwama a haka.

A ranar daga khalid har mumtaz baccin farin ciki sukayi da alƙawarin haɗuwa a ranar sallar da
ze dawo da yamma,

Saɓanin wasu ƴan tsirarai masu mugun nufi da suke kwana da yini wajen tarwatsa rayuwar

bayin Allah da yawa wanda basu jiba basu gani ba, saboda tsabar son zuciya da rashin rabo!!!!.

SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

LAUJE CIKIN NAÆŠI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA👹
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAÆŠI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 31-32

BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU

Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a É—aki, duk da sun tashi amma
suna zazzaune

Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa

Da sallama umma b ta shiga É—akin,
Stool É—in gaban mudubi taja ta zauna,

Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo

Amal ma juyowa tayi gaba É—aya sukai shiru suna kallon ta.

Seda ta mula da kallon su tukun tace

"Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?"

Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba

ÆŠan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da
idanu itama

Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma

Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace

"Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?"

Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir É—in dai umma"

Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir
sau biyar umma"

Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi"

Da sauri Umma ta É—aga masu hannu haÉ—e da faÉ—in "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna
kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau
zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da
wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba"
Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa

Cike da zumuÉ—i hafsat tace

"umma wai maganar ta taso ne?"

Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace

"Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi,"

Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace

"Umma, to harda Æ´ar gaban goshin nashi ko mu kaÉ—ai?"

Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma"

Baki buÉ—e hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?"

Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na É—azu
Seda ta dara sosai tukun tace

"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta"
Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar.

Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace

"Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe"

Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama
tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu

Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima
da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna.

Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa
shirmen banza"

A fakaice hafsat ta murguÉ—a mata baki ta juya tana gunaguni.

Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk
da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma
Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye

Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba

jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa

"ya dai? ko akwai wani abunne?"

Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar
ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace

"nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama"

Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka Æ´a mace É—akin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki
kema kuma kina son shi ba shikenan ba?"

Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da
ita kaÉ—ai ke so.

******MUMTAZ

Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia
airport tarban Abba Æ™ da mama

"Gaskiya guy É—innan be iya zuwa ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?"

Sakina da ke É—aura É—ankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje
ya sauke mu ne?"

Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan
hau taxi"

Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan.

Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern,

Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik.

Agogo ta kalla taga befi awa É—aya ba su sauka,
Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina
ta fice.

Saboda traffic É—in hanyar, seda suka kai kusan minti talatin kafin suka kai

Daidai da zata shiga ciki call É—in khalid ya shigo wayar ta

Jin cewa tana airport ne yace ta jira shi yana ta wajen ze ƙaraso, taso ta hana shi zuwa amma
ya kafe se yazo, rabuwa tayi da shi ya zo É—in.

Bata jima a tsaye ba yayi parking a gaban ta,

Ganin da sauran time É—in saukar su mama yasa ta buÉ—e gaba ta shiga

Fuska cike da annuri khalid yace

"Da za ki min buƙulun gaisar da su Abba ko?"

Murmushi kawai tayi, can tace

"yanzun ma ba ganin su zaka yi ba malam, suna sauka zan sauka kai kuma ka kama gaban ka"

Gyara parking yayi da kyau, sannan ya waigo ya fuskance ta, ƙasa da murya yayi kafin yace

"Gani nake kamar bakya so na mumtaz"

ÆŠago manyan idanuwan ta tayi ta kalle shi sau É—aya ta kauda kai, sannan tace

"mene dalilin ka?"

"gashi kuwa bakya so na ga su Abba, ko gidan su sakina da ƙyar fa kika yarda naje"

Kallon agogon wayar ta tayi taga time É—in ya cika,

Cike da nutsuwa tace
"gobe ina gayyatar ka gidan mu to, Amma yau kam zanji kunya a Abba ya ganmu tare, in ma da
babban wanmu suka dawo wata maganar ce daban"

Marairaice fuska yayi, ba yarda ya iya dole ya haƙura,

Fita yayi da niyar ya buɗe mata ƙofa, yana fita idonta na kaiwa ga agogon shi dake ajiye, wuf
mumtaz tayi sama da shi, daidai ya buɗe mata ƙofar

Cikin ƙwarewa ta saƙe agogon nan tayi ciki wajen tarban matafiya, shi kuma ya shiga motar shi
ya tafi.

LAUJE CIKIN NAÆŠI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA👹
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAÆŠI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 31-32

BAYAN SALLAH DA KWANA BIYU

Tun safe da umma b ta fito daga wajen Abba b ta samu su Amal a É—aki, duk da sun tashi amma
suna zazzaune

Wayace a kunnen hafsa, while Amal kuma handouts ne a gaban ta tana dubawa

Da sallama umma b ta shiga É—akin,
Stool É—in gaban mudubi taja ta zauna,

Sallama hafsa tayi da wanda suke wayar ta maido da hankalin ga umma b dake binsu da kallo

Amal ma juyowa tayi gaba É—aya sukai shiru suna kallon ta.

Seda ta mula da kallon su tukun tace

"Dake zan fara Amal, Amir da faisal wanne yafi gwaɓi a cikin su?"

Bin ta da kallo Amal tayi, dan har ga Allah bata fahimci kalmar "gwaɓi" da umma tace ba

ÆŠan shirun da Amal tayi tana nazarin kalmar, umma ta sake maimaita tambayar tana kafe ta da
idanu itama

Da gaske Amal tace "wallahi ban gane me kike nufi ba umma

Ƙafa ɗaya kan ɗaya umma ta ɗora sannan tace

"Bari nayi maki dalla dalla, ina nufin Amir da faisal wanne yafi wani a cikin su?"

Murmushi Amal tayi kafin tace "Amir É—in dai umma"

Karaf hafsat tace "billahillazi ƙarya take, ko motar da faisal ke zuwa gidannan zata siya ta Amir
sau biyar umma"

Murtike fuska Amal tayi, cike da tsiwa tace "ba ruwanki a cikin maganar nan wallahi"

Da sauri Umma ta É—aga masu hannu haÉ—e da faÉ—in "Ku dakata min" duka sukayi shiru suna
kallon ta, idonta ta maida ga Amal sannan tace "na san kece zaki fi bani matsala, daga yau
zuwa jibin da Abban ku yace zasu tara ku suji zaɓin ku na wanda kuke so, ina so ki fitar da
wanda yafi rigar arziƙi a cikin su, kuma kar naga ba abinda nake so ba"
Sadda kai ƙatsa Amal tayi jin abinda umman ke faɗa

Cike da zumuÉ—i hafsat tace

"umma wai maganar ta taso ne?"

Seda ta ɗan taɓe baki tukun tace

"Tunda me ƙumbar susa ya bada umarni ai dole a bi,"

Zaro ido Hafsat tayi ta ɗan sake matsowa kusa tayi ƙasa da murya tace

"Umma, to harda Æ´ar gaban goshin nashi ko mu kaÉ—ai?"

Dariya umma b tayi sannan tace "hmmm, harda ita fa, da Bilkisu da Najwa ma"

Baki buÉ—e hafsat tace "jakar uba, to da wa za'ayi kenan?"

Wannan karon dariyar da umma b tayi tafi na É—azu
Seda ta dara sosai tukun tace

"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta"
Da ga nan tayi gaba ta ja musu ƙofar.

Umma na fita Amal ta kalli hafsat tace

"Mugunta fitsarin faƙƙo ce dai ya hafsa, har wani murna kike saboda wani dalilin ku mara tushe"

Kafin Amal ta rufe baki hafsat tayo kanta a mugun sukwane, dayake Amal ta san hali, dama
tayi readyn fita, aikuwa tana yunƙurowa ta kwasa tayi waje da gudu

Aikuwa hafsat kamar ta ari baki saboda masifa da take zazzagawa, seda ya fauza da basu jima
da zuwa gidan ba ita da khairi suka shiga tsakanin su tukunna.

Ya fauza da yake tana da faɗa sosai ta hau surfa musu bala'i, tace "kuna girma kuna cin ƙasa
shirmen banza"

A fakaice hafsat ta murguÉ—a mata baki ta juya tana gunaguni.

Kamar yarda umma b ta zaunar da yaran ta tasanar da su saƙon Abba b, haka ma mummy, duk
da Najwa ba ƴar cikin ta bace riƙonta take, hasali ma saboda son da take ma ƴa mace ne kuma
Allah be bata ba yasa yayan ta ya bata Najwa halak malak tun daga yaye

Najwa na kwance a kan doguwar kujera mummy ta sanar mata da umarnin su Abba

jin Najwa bata ce komi yasa mummyn cewa

"ya dai? ko akwai wani abunne?"

Can ƙasan zuciyar ta na zigata ta ce ya faruk take so, amma wani sashi na zuciyar yana ƙwaɓar
ta, murmushin dole ta ƙwaƙulo tukun tace

"nothing mummy, kawai naji maganar ne daga sama"

Shafa kanta tayi tace "mutuncin duka Æ´a mace É—akin mijin ta, tun da Allah yasa sadik na son ki
kema kuma kina son shi ba shikenan ba?"

Gyaɗa kai tayi, tana ƙara cire ya faruk daga cikin ranta dan har ga Allah bata son tayi auren da
ita kaÉ—ai ke so.

******MUMTAZ

Kicin-kicin mumtaz tayi da fuska, jin me sakina ke gaya mata, bayan sun gama shirin tafia
airport tarban Abba Æ™ da mama

"Gaskiya guy É—innan be iya zuwa ba, wai fisabilillahi baki gaya mishi fita zamuyi ba?"

Sakina da ke É—aura É—ankwali a gaban mudubi tace "shap na mance ban gaya mishi ba, ko muje
ya sauke mu ne?"

Da sauri mumtaz tace "no, bari nayi wa drivern ku magana, in kuma yana da abinda zeyi zan
hau taxi"

Sakina batace komi ba, looks like kamar da gangan ma tayi hakan.

Mumtaz na fita ta iske an aiki drivern,

Dama ba kowa a gidan, mama asiya taje unguwa, daga su se masu aik.

Agogo ta kalla taga befi awa É—aya ba su sauka,
Wayarta ta ɗauka ta kira bolt, minti biyar da kiran shi ya ƙaraso, "na wuce" kawai tace wa sakina
ta fice.

Saboda traffic É—in hanyar,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login