Showing 1 words to 3000 words out of 85780 words

Chapter 1 - LAUJE CIKIN NADI COMPLETE BOOK BY Mrs Suleiman .pdf

28 Apr 2025

6643

LAUJE CIKIN NAƊI.

NA


ZAINAB FALALU
(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU

Page 1

Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin, ganin ƙofar ta buɗe yasa ta sauke ajiyar zuciya me nauyi


Seda ta waiwaiga taga ba motsin kowa tukun ta saka kanta kai tsaye cikin É—akin


Seda ta gama ƙare ma ɗakin kallo ta lumshe ido tana shaƙar mayen ƙamshin turaren da ko a
bacci taji shi ta san na waye, tukun ta ƙarasa inda taga agogunan shi a jere


Tas ta gama ƙare musu kallo,
seda ta darje tukun ta ɗauki wanda suka fi ko wanne tsada a ciki, ta ɗaga rigar ta saƙa ta ɓoye
su


Motsin data ji ne ya sa bata kai ga taɓa sauran abubuwan ba ta fice da sauri


Tana fitowa daga É—akin ta hango shigowar shi gidan

Da sassarfa ta kwasa tayi hanyar part É—in su tana tallafe da agogunan data É—akko tana jin yarda
gaban ta ke dukan uku-uku a duk sanda tayi dafe



La haula wala ƙuwata illa billah! yanzu inda ban ankare dake ba da shikenan kin min illa kin sa

na yanke,
ki sabauta ni haka kurum mumtaz


Mumtaz da ake maganar domin ta tuni ta ƙule can cikin bedroom dan ko waiwayowa bata yi ba,
ballanta na tasan me tayi


Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi sannan ta murɗa key


Ta window taci gaba da leƙen ya Faruƙ dake tafe hankalin shin na ga wayar da yake,

Kamar walƙiya yaga giftawar mutum da gudu amma hankalin shi be kai ga kowaye ba, waya ce
me muhimmanci yake amsawa shiyasa be wani damu da ya san waye É—in ba.



Seda taga shigewar sa tukun ta sauke ajiyar zuciya tana komawa da baya ta zauna



Ɗaga rigarta tayi ta ciro agogon, ƙare mishi kallo tayi sosai sannan tace


"Daga gani zasuyi mugun tsada, Komi na ya Faruq me kyau ne wallahi,


Jakar islamiyar ta tajanyo ta saka agogon tukun ta rufe ta maida sannan ta fito palon inda
mama take



Zama kusa da Mama tayi ta zabga tagumi ta kafe ta da ido


Maman tana kallon ta tayi fuska kamar bata san da zaman ta a wajen ba taci gaba da yanke
farcen ta tana magana da atine dake kitchen tana haÉ—a kayan shan ruwa, da yake yamma ta
gabato ana gab da a kira sallar magriba.



Murya a sanyaye Mumtaz tace

"mama yau ba aikin da zan yi ne ni?"


ko kallon ta bata yi ba ballanta na ta saka ran amsa mata

Ganin ba amsa mata maman zatayi ba yasa ta miƙe jiki a sanyaye ta koma ɗaki tayi kwanciyar
ta dama ba ƙaramin jin azumin yau take ba,
ko gudun data yi É—azu shima dan ya zama dole ne dan in har ta kuskura ta shiga hannun yaya
faruƘ to tabbas se dai buzun ta dan tsaf se ya sauke mata waɗan nan yatsun nashi kamar itace
bama biyar É—in ba goman duka ze sauke mata


Juyi tayi ta gyara kwanciyar ta, tayi shiru tana tunanin wannan muguwar halayyar ta
É—auke-É—auke datake yi

kan kice me hawaye suka cika idanun ta kamar zasu zubo,

Da iyakacin ƙarfin ta tahanasu sauka ta maye gurbin su da murmushi, cikin zazzaƙar muryar ta
me daÉ—in sauraro tace


"Komi yana da lokaci, Allah ka yaye min wannan É—auke-É—auken da nake yi na ba gaira ba dalili'


kiran sallar magriba ne ya fito da ita palon inda aka jera komi da komi na buÉ—a baki

Dabino uku ta É—auka ta taci tukun ta wuce toilet É—in palon ta É—auro alwala


Seda ta gabatar da sallar magrib kafin ta ƙaraso ta zauna kamar yarda kowa da kowa ke zaune
ana shan ruwa.


Sama-sama ta tsakuri abincin, ita she ƙarshe zama kuma itace ta fara tashi


Ba wanda ya kula ta, kusan haka É—abi'ar ta take, bata fiya son cin abinci ba, tafi auki a kayan
ƙwalama, shiyasa gata nan bata da wani auki na azo a gani.



Gaba É—aya gidan suka hallara a babbar harabar gidan inda anan yaya faruÆ™ yake jan su sallar

asham in har yana gari


Manyan su da yaran su, kowa na wajen amma banda mumtaz, sakina ce dake zaune kusa da
mama kawai ta lura da rashin ta a wajen,

A hankali tace

"Mumtaz bata fito ba mama"

Kafin maman ta buÉ—e baki suka ga tawowar ta da sauri

Bawanda mumtaz ta kalla ta samu gefe ta shimfiÉ—a dardumar ta tabi sahu


Tunda suka ɗago daga sujjada ta ƙella ido akan carbin dake aje a gaban umma babba ta rasa
sukunin ta gaba É—aya,

Salla ake amma ita tunanin gaba É—aya ya tafi ta inda zata É—auke carbin

Har aka sake komawa sujjada mumtaz bata ankare ba


Can ƙasan zuciyar ta tace

"bari a tafi sujjadar ƙarshe, ai nasan ya faruƙ jimawa yake, har in ɗauke shi ma ba lale ne a
É—ago ba"


Haka tayi ta fakon wannan carbi har aka kai sujjadar ƙarshe


Cikin sanɗa ta janye jikin ta, ta matsa kusa da umma babba, cikin ƙwarewa a harkar ta saka
yatsar ta Æ´ar manuniya ta janyo carbin, seda taji shi gaba É—aya a hannun ta tukun ta juya a
hankali bayan ta cusa shi a cikin rigarta tkun ta koma kan dardumar ta tayi sujjada kamar yarda
taga kan kowa a ƙasa.


Sosai Umma babba tayi mamakin rashin ganin carbin ta, har Aunty dake gefen ta take
tambayar ta da "lafia umma babba?"

Da mamaki tace

"na rasa ina na wurga carbi na wlh, abun mamakin da shi na fito ba"


Kyaɓe baki aunty tayi, bata sake cewa komi ba taci gaba da tasbihin ta tana ɗan dudduba
wayar hannun ta sama-sama


Itama umma babban shiru tayi, taci gaba da mamakin ta ita kaÉ—ai a cikin ranta



Ɗaya bayan ɗaya ahalin gidan suka rinƙa watsewa kowa na kama gaban shi, kowa ya kama
hanyar part É—in su


Ya faruÆ™ na zaune be kai ga tashi ba, mumtaz na É—ago kai taga ya rage daga ita se ya faruÆ™ se
kuma ya Tk dake waya tayi saurin miƙewa da sauri zata bar wajen

Tsautsayi wannan carbin na umma babba data É—auka ya faÉ—o

Caraf akan idon ya faruÆ™ da ya kafe ta da kallon tuhuma yana kallon carbin yana kuma kallon ta
at thesame time



Wuri-wuri mumtaz tayi da idon ta tana kallon shi, gaba É—aya rashin gaskiya ya bayyana a tattare
da ita


A hankali ta saka hannun ta É—auke carbin sannan ta kwasa da gudu tayi hanyar part É—in su,
tana yi tana waiwayen shi ganin har lokacin be É—auke idon shi a kanta ba.


Seda ta ƙule ma ganin shi tukun ya kauda kan shi yana mamakin rashin nutsuwa sam na
mumtaz kusan so biyu kenan yana kama ta da makamancin abubuwa shigen wannan


Ƙwata ya ja tukun yace

"zan saka miki ido kuwa"

Tashi ya faruƙ yayi ya wuce ɗakin shi waya kare a kunnen shi yana sauraron saƙon da Abba
babba ke bashi akan rabon kayan masarufi da za'ayi ma bayin Allah saboda alfarmar watan
ramadana da ake ciki.


Mumtaz na shiga part É—in su ta wuce palon mama,

Tana shiga ta iske yayun ta da suke uwa É—aya uba É—aya zaune a palon suna fira mama na daga
gefe tana duba list ɗin sunayen ƴan'uwa da abokan arziƙi masu ƙaramin ƙarfi tana fidda list ɗin
wanda ya kamata ayi ma kayan salah


ÆŠago kai mama tayi ta kalli mumtaz da alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare ta

Cike da kulawa mama tace


"zo nan mumtaz"


A tsorace tace

"ina zuwa mama, futsari nake ji" ta yi hanyar ɗakin su da sauri tana ƙara damtse carbin hannun
ta.


Seda ta adana shi tukun ta fito ta zauna kusa da mama tace "gani"


Kafe ta da kallo mama tayi tace

"Anya akwai alamun gaskiya kuwa a tattare dake mumtaz, Æ´an watannin nan sam na kasa gane
ki, kwata-kwata baki da nutsuwa kullum in aka ganki a zabure kike, kodai basir É—inki ya tashi ne
mumtaz?"


Shiru mumtaz tayi tana kallon, ya Ahmad da yake dariyar basir da mama tace


Jiki a sanyaye ta girgiza kanta, sannn tace

"be tashi ba mama"

Sosai mama ta hauta da nasihar ita ƴa mace da nutsuwa aka santa, ba wai komi ta rinƙa yin shi
a hauka-hauka ba


Abinda mama bata sani ba shine duk maganar nan data ke ma mumtaz yana shiga ta kunnen
dama ne ta fice ta kunnen hagu, hankalin ta gaba É—aya na kan É—ayar wayar ya Ahmad da ya aje
a hannun kujera


Lissafin ta kawai yarda zata É—auki wayar ba tare da an samu matsala ba,


Ganin yarda mumtaz tayi shiru kamar tana sauraron abunda maman ke cewa yasa mama taci
gaba da kawo mata misalai da sauran Æ´ammatan gidan da suke sa'annin ta

Nuna mata take saboda tsabar rashin nutsuwar ta yasa ko saurayi yazo wajen ta baya sati uku
ze kama gaban shi, tun suna zuwa har sun dena zuwa



Murmushin ta me kyau mumtaz tayi, kallon mama tayi tace


"Saboda haka kenan suka dena zuwa waje na mama?"


Sosai mama ta buÉ—e ido akan ta, sannan tace


"ai duk É—a namiji yana sonbya samu mace nutsatstsiya me nutsuwa sosai, amma a yarda kike
yin abubuwa haka ai dole saurayi ya gudu"



Murmushi mumtaz tayi, bata sake cewa komi ba, sema kishingiÉ—a data yi tana jiran sa'ar ya
Ahmad akan wayar data ƙwallafa rai akan ta.


KAMAR YARDA NACE, IN SHA ALLAH NAN KUSA ZAN FARA SAKIN SHI,

SABODA MASU TAMBAYA NA DAN ALLAH IN ÆŠAN GUTSIRA MUSU KAÆŠAN DAGA CIKIN

LABARIN, TO GASHI NAN, INA MUKU FATAN ALKAIRI


ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

LAUJE CIKIN NAÆŠI

NA
ZAINAB FALALU
(MRS SULAIMAN)

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg2

Tana a nan zaune jiran tsammani bacci yayi awon gaba da ita, har su ya Ahmad suka tashi bata
sani ba


Wajajen goma mama ta tashe ta tawuce É—aki

Da wannan wayar ta farka, tunda ta buÉ—e ido taga wayam sun tashi ranta ya É—ugunzuma ya
ɓaci

Haka tayi ta zumɓure-zumɓurenta ta haƙura ta shige ɗaki.


WASHE GARI

Ƙarfe takwas da rabi na safiya ƴammatan gidan suka fito kusan a tare

Dukkan su sanye suke da blue dogayen hijabai


Su shida ne kyawawa da su ma sha Allah


Parcking lot suka wuce inda bala driver ke jiran su

Kowa ya shiga mota banda najwa data waiga ba ta ga mumtaz ba

Da sauri tace

"Ina zuwa mlm bala, bari in taso kira mumtaz

Bata jira cewar su ba ta juya da sauri har ta na haÉ—awa da É—an gudu-gudu

knocking ƙofar part ɗin su mumtaz da basu buɗe ba tayi cikin nutsuwa


Cikin bacci Altine me aiki taji knocking ɗin, da sauri ta taso ta zo ta buɗe ƙofar


A ladabce najwa ta gaishe da altine tukun ta shige ciki

Direct É—akin mumtaz ta wuce tana kiran sunan ta


Mumtaz na tsaye gaban mirrow tana saka nata hijabin najwa ta shigo


Ganin ta a tsaye yasa ta tsaya itama, tace

"nasha baki tashi ba ai"


Fuska a sake mumtaz tace

"Tun asuba ban koma ba, sam na kasa komawa se yanzu da lokacin islamiya yayi nake jin
baccin wallahi"


Dariya najwa tayi tace

"na saba jin wannan zancen naki malama, koya ya shiga mota fa, muje"


Tana gama faÉ—in haka ta juya ta fice


Jakar islamiyar ta dake ajiye gefe ta É—auka, seda ta buÉ—e jakar ta ga ajiyar ta na nan tukun ta
rufe ta sagala sannan ta janyo ƙofar


Ɗakin mama ta leƙa taga bata tashi ba ta wuce bayan ta sallami altine

Mumtaz tasan sarai jiran ta suke, tunda ta fito suka haÉ—a ido da hafsa taga yarda ta banko mata
harara yasa ta koma tafiya ɗai ɗai kamar bazata taka ba, ba dan komi ba se dan ta sake ƙular
da hafsa


Daga ƙofar part ɗin su zuwa wajen parcking lot ɗin seda tayi mugun ɓata musu lokaci kafin ta
ƙarasa,

Da ka gani kasan da gangan take, tsabar neman magana ne


Abunda bata sani ba shine, tunda ta fito ta fara tafiyar ta ya faruÆ™ ke kallon ta da mamaki a
fuskar shi, sarai zaka ga zallar neman fitina da neman saka su suyi latti a fuskar ta


Kasa cewa komi yayi yana jiran ganin gudun ruwan mumtaz ɗin har ta ƙarasa wajen motar inda
suke jiranta


Daga can ya hango yarda take murguɗa ƙaramin bakin ta, da dukkan alamu rashin kunya take
ma hafsa dan tana gaba da ita a shekaru


Seda ta gama murguÉ—e-murguÉ—en ta tukun ta buÉ—e baya kusa da najwa ta zauna, tukun bala
driver yaja suka tafi.


Seda ya faruÆ™ yaga fitar su tukun ya maida idon shi kan systerm É—in shi dake ajiye akan stool
É—in gaban shi yana shigar da wasu bayanai.



Suna shiga aji mumtaz ta kalli najwa dake ƙoƙarin zama a gaba tace


"hour É—aya kafin a tashi ki tashe ni dan Allah"


Balla mata harara najwa tayi kafin tace

"wai da gaske baccin zaki yi yau ma?"

Seda mumtaz ta rama hararar da najwa tayi mata, kanta tsaye tace

"kina da damuwa ne a ciki?"


Banza najwa tayi da ita, dan ta san ba ƙaramin aikin mumtaz bane tasa su raba hali


Ganin najwa ta juya yasa mumtaz sake maimaita mata tafa tashe ta kafin a tashi, tukun ta juya
ta koma can baya ta zauana.


Tun kafin a fara tafsir bacci me nauyi yayi awon gaba da ita, ba itace ta farka ba har seda aka
tashi sannan najwa ta tashe ta suka fito


Tunda suka fito mumtaz ke mata ƙorafin taƙi tashin ta


Da dai najwa ta gaji da ƙorafin mumtaz tace


"inda na tashe ki ina zaki je to?"


Tsaki mumtaz taja, tukun tayi gaba inda anan bala driver ke É—aukan su ta barta a nan


Sosai mumtaz ta haÉ—e rai har suka kai gida, bata ce ma kowa uffan ba ta wuce part É—in su duk
ba haka ranta yaso ba.



Bilkisu da hafsa na ganin wucewar mumtaz har wani rige rigen tambayar najwa suke da "me
akayi ma warcan mara kunyar ne?"


Murmushi kawai najwa tayi, bata basu amasa ba, itama ta É—auki jakar ta tayi nasu part É—in.

Sosai rana ta take, kusan kowa na side ɗin shi yana bacci, dan azumin yau yana ƙwala jama'a


Tunda mumtaz ta shiga part ɗin su ta tabbatar da kowa bacci yake bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi
maza ta cire hijabin uniform É—in ta tasauya wani,

Jakar makarantar ta buÉ—e ta É—auki wannan agogunan da ta É—akko a É—akin ya faruÆ™ ta saka a
hand bag ɗin ta, se ƙaramar wayar ta nokia data saka a ciki, sam bata lura ba ko sisi a ciki ba,
haka ta fice sauri-sauri tayi waje, ko ta kan mama dake bacci bata bi ba tayi waje tana waiwaye
kamar warce za'a ce ma tak ta kwasa da gudu.


Dai dai ya faruÆ™ ze tashi daga wajen da yake zaune yaga fitowar Mumtaz da sauri, tana yi tana
waige, rashin gaskiya ƙuru-ƙuru a tattare da ita


Shiru yayi yana kallon ta har ta fice ta ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan,
Cikin É—aga murya malam ado yace

"Sauka lafiya zankaÉ—aziya"

Haka ya ke kiran Mumtaz tun tana ƙarama


Cuno baki mumtaz tayi ta ƙarashe ficewa da sauri, dan kar tsautsayi yasa wani a gidan ya
ganta.



Ya faruÆ™ har ya juya ciki, amma zuciyar shi sam ta kasa nutsuwa, a rayuwar shi be cika shiga
abinda ba ruwan shi ba, amma sam ya kasa nutsuwa da yarda yaga fitar mumtaz.


Haka ya danne ya buɗe ƙofar ɗakin shi ya shige,
Amma me?, kwata kwata ya kasa samun nutsuwar rai


ganin ya kasa nutsuwa yasa ya juya ya fice da sauri yayi hanyar fita shima


Wayam layin, ba alamun mutum ko É—aya a layin, yanayin layin dama bana jama'a bane, da
wahala kaga mutum tafe a ƙafa

Haka ya gama wurwurga manyan idanun shi da suka zama na gado ya haƙura ya juya cikin
gidan da niyar shima ya É—an kishin giÉ—a zuwa yamma, lokacin ranar ta É—an yi sanyi.


Seda ya watsa ruwa tukun ya kwanta, amma sam ya kasa baccin da yayi niyar yi, al'amarin
mumtaz na daÉ—a É—aure mishi kai, shi ya san kaf yaran gidan nan babu warce ta kai nutsuwar
ta, amma wannan dawowar da yayi yaga saɓanin haka daga gare ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login