Showing 24001 words to 27000 words out of 48809 words
nufi asbitin dashi hankalin Inna da Baffa a tashe yayin da Nassar kuwa banda
kuka babu abinda yake.
Tashin farko likita ya gano mugun hawan da jinin sa yayi ga ciwon k'irjin da yake son
kamashi,taimakon gaggawa aka bashi sannan aka d'aura masa ruwa.
Gefen gadon Baffa yajawa Inna kujera ta zauna yayin da Baffa yake gefen ta a tsaye Nassar
kuwa gefen gadon yaje ya zauna ya kafe yayan nasu da ido, yayin da gefen zuciyar sa yake
tambayar sa ina addar sa?
Ina ta tafi ne ga mijin ta babu lafiya amma bata sani ba?
"Baffa ina addata?"
Nassar yaiwa Baffa tambaya yana kafe shi da ido hakan kuwa yayi daidai da bud'e idon MD
yayin da Baffa ya ji wani irin abu mai k'arfin gaske ya daki kansa, take ya yanke jiki ya fad'i a
wajen.
Cikin tashin hankali suka yi kan Baffa da ya hau wani irin girgiza yayin da MD yayi k'arfin halin
mik'ewa ya kama Baffan yayin da Nassar ya ruga ya kira Dr da k'yar suka samu suka sha kan
matsalar.
Maryam kuwa
Tunda taga tayi inda tasan D boy ba zai ganta ba ta nutsu taci gaba da tafiyar ta ga jikak'ak'k'un
kayan ta a leda haka ta kwana ta yini tana yawo bata raina kanta ba sai da taji wata irin
fitinannen yunwa ya damk'e ta, ta duba jakar ta babu A T M da 'yan chanjin ta take ta fashe da
wani irin kuka [8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
30
Yana gama karanta sak'on yai wani irin zama a nan k'asa yana mamakin yadda yarinyar ta
shammace shi, domin ko a fuskar ta bai gane cewa bata buk'atar binsa da bazai tab'a nuna
mata cewa zai tafi da itaba.
Da k'yar Maryam ta iya takawa sukaje gidan mutumin nan dake daga inda ya ganta da d'an
tazara tsakanin su da gidan nasa.
Matar sa Gwaggo Laure gama kwasar tuwon dawar ta kenan miyar d'anyen kub'ewa suka
shiga, da k'yar Maryam ta iya gaida Gwaggo Laure tsabar juwar da yake kwasar ta.
"Laure ga bak'uwa bata abinci taci" babu musu ta zubowa Maryam tuwon nan ta kawo mata,
yadda ta rik'a cin tuwon nan sai da Gwaggo ta zubar mata da hawaye yayin da malam Umar ya
rik'a girgiza kansa cikin tausaya mata.
Cikin abinda bai gaza minti bakwai ba Maryam ta gama da tuwon nan mai uban yawa.
"K'ara mata Laure" cewar malam Umar yana kallon Maryam cikin tausaya wa.
"A a Alhamdulillah na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya ciyar daku a gidan ALJANNAH
kamar yadda kuka ciyar dani kuka tamake ni kuka bani abinda yafi k'arfi na"
"Kar ki damu yarinya ai shi d'a na kowa ne amma me ya kaiki wancan layin mai hatsari layin da
darana ma farautan 'yan mata ake dan a wulakan ta rayuwar su bare kuma yanzu da duhu ya
rufa?"
Shiru tayi na d'an lokaci kafin tasamu kanta da gilla masa k'aryar daga wani gari suke sunzo cin
kasuwa b'arayi suka tare su suka kwace musu kud'ad'en su da kayayyakin su".
Sosai suka tausaya musu tare da Allah wadai da b'arayin anan malam Umar yace "ki kwana
zuwa wayewar gari sai na baki kud'in mota ki koma gida"
Sosai Maryam ta godewa wannan bawan Allahn ranta fari kwal zata samu wasu 'yan chanjika a
hannunta ta.
Yau aka d'aura auren Baffa da Deedah D'AURIN AUREN da ya tara manyan mutane sosai
Baffa yake wani irin farin ciki da auren kamar wannan ne auren sa na farko.
Inna ma duk da kasancewar suna cikin alhinin yadda zata kasance idan an d'aura auren sai da
ta d'an tara mutanen da ta dan sani.
Tsabar abin kunya harda haj. Zakiyya a rako Deedah abisa umarnin boka sha anin da ya hana
haj. Sailuba sakat ta haukace musu ta rik'a zage zage a cikin mutane
Dan Allah kuyi hak'uri da wannan kad'an ne
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
33
"Shikenan, kun halaka ni kun kawo k'arshen rayuwa na, yanzu me nayi miki Zakiyya saboda
Allah da kike son dole sai kinga k'arshe na?"
Ta fad'a idanunta akan tukunyar dake fitar da wani irin azzalumin hayak'i wanda gaba d'aya ya
hanasu jan numfashin kirki.
Idanunta k'yam akan tukunyar ko kibyawa batayi yayin da zuciyar ta yake wani irin fitinannen
bugu,
"Wannan tukunyar ban tab'a bawa kowa ita ba domin makale take da sirrika na masu yawan
gaske kuma na baku ne domin yarda da aminci kada ku sake ku bawa wani ko ku bari wani ya
ganta domin hakan yana nifin lalacewar komai harda ni kaina bazan tsira ba.
Tunanin abinda boka yace take ta kuma fashewa da wani marayan kuka a fili take fad'in "ai
shikenan ba ni kad'ai abin ya shafa ba harda ke da kuma boka dan haka ba ni kad'ai hakan zai
ruguza ba" tai maganar a fili idanunta akan tukunyar dake ci balbal yayin da Baffa yai ka sake
yana kallon yadda wutar take ci.
"Akwai wani abu akasan kafet d'in falon nan MD a ciro shi sannan mushiga d'akin Maryam da
Ammey suma an binne sai d'akin Inna wanda shine zai warware komai kuma hakan ne yasa ta
muku wulak'anci ta kore ku dan tasamu damar ajiya a d'akin Inna".
Da sauri MD ya mik'e dan ya kagu akawo k'arshen komai Baffa yasa hannu a neman Maryam
dan yasan muddun Baffa ya shiga maganar za'a ganta tunda yana da alfarma a garuruwa,
ganin ta kawai yayi tasha gabansa ta kasa magana sai girgiza masa kai kawai take yayin da
idanunta suke zubar da wasu irin hawaye masu yawan gaske, cikin wani irin fushi yasa hannu
ya wulla ta gefe ta daki bango take hannunta yayi k'ara wani irin gigitacciyar k'ara ta saki, ko ta
kanta bai bi ba ya wuce dan aiwatar da abinda ya akace.
Gaba d'aya ta bar tashar taci gaba da tafiya zuwa wajen tashar da yake tashar da nisa sosai da
unguwar su malam Umar sai bata wani d'aga hankalin ta ba haka taci gaba da tafiya, wannan
karon bata damu da yawa ba saboda akwai kud'in da zata sai abinci duk kuwa da irin tsadar
abincin.
Wata irin k'ask'antaciyar rayuwa take yi mara gata da galihu karkashin wata gada ta samu suke
kwana ita da wasu almajirai mata dake tana da 'yan kud'in ta bata binsu bara sai dai tayi zaman
ta anan, sai dai kullum takan bisu tashar da suke bara tayi wanka a gidan wankan da suke
biyan kud'i suyi uzurorin su.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya har tsayin wata guda zuwa lokacin Maryam sun saba da wata
Saira 'yar yaren Igbo wacce ita kuma sanadin maraici ya kawo ta tashar sakamakon had'ama
da son zuciya irin na dangin mahaifan ta da suka handame komai ita kuma suke farautan
rayuwar ta hakan yasa ta dawo nan ta fake tsayin shekara guda da rabi kenan idan sun san ma
tanan basu damu ba tunda babu wanda ya tab'a nemanta ko ya nuna ya damu da ita.
Sab'anin Maryam da bazata iya cewa ga takamiman abinda ya rabota da gida ba a lokacin
domin abu kad'an take tunawa koranta da Baffa yayi yace ita ba 'yarsa bace sai kuma MD da
auren sa ta kasa manta wannan saboda fargaban shin tana da aure ya kasa neman ta ko kuwa
suna can suna nemanta? Take taji ranta yayi wani irin mugun d'aci tace a fili Ammey kiyi hak'uri mahaifiya ta bazan iya
k'ara zama inda kike ba bare nasa kaki a matsala, domin nasan kema bayin kanki bane
yaudarar ki akayi aka same ni saboda kowa ya ganki yaga kamilar mace.
Ta fashe da wani irin kuka mai cin rai, haka Saira ta rik'a rarrashin ta da k'yar ta samu tayi shiru
kafin ta wuce wajen tallar ta dake ita Saira ba bara take ba doya take d'auka irin gasashen nan,
idan ta siyar ta d'auki nata ta kaiwa mai doyan kud'in ta da haka take samu taci abincin har ta
tara wani abu.
Bayan wata guda.
Abubuwa da yawa sun faru ciki har da k'arewar yan kud'ad'en da ake taci ya kasance yanzun
Saira ke ci da ita har ta bata na wanka, abin yai matuk'ar damun ta hakan yasa ta nemi da Saira
itama ta nemo mata sana'ar yi dake wajen da suke babu mai ruwa da kemo hakan yasa ta bata
shawaran ta rik'a ajewa a inda take sai da doyar ta can bakin babban titi dake wajen kamar
kasu yake kunsan dai yadda bakin babban hanya yake.
Cikin kankanin lokaci Maryam ta fara karb'an ruwa da lemo a wajen wani mai shago da masu
talla suke karb'a ta fara bin Saira.
Bani da bakin baku hak'uri sai dai naja baki nayi shiru nasan bana kyautawa
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
31
Gadan gadan ta tun karo haj. Zakiyya tana auna mata wani mummunan zagi, tana tana fad'in
"koni ko ke azzaluma maciciya maha'inciya macijiya mai harbi a k'ahon zuci".
Kafeta haj. Zakiyya tayi tana wani irin murmushin gefen baki ranta fal mugunta tace.
"Haba k'awata ta ya kike haka a bainan nasi so kike ki barwa kanki abin fad'a? ni har kinsa na
fara shakkar barin yarinya ta a gidan nan, saboda nansan cewa gidan mahaukaciyar kishiya na
kawota ba saida naga zahiri"
"Uwar ki da uban ki da duka dangin ku sune mahaukata muguwar'yar ta'adda azzaluma wallahi
sai kinyi nadamar cin amana ta bak'ar makira""""karasawa tayi kusa da ita tayi mata rad'a kunne
bansan me tace mata ba kawai naga haj. Sailuba ta zube a gaban ta tana fad'in.
"Na rasa me na aikata miki da zafi haka da kike yimin irin wannan tozarci, shin k'aunar da na
gwada miki ne laifi, ko kuma jan ki da nayi a jiki nane na maida ke wani abu arayuwa laifi na?"
Ta fad'a tana kafe haj. Zakiyya da ido wasu irin zafafan hawaye na zubo mata wanda yake
tafiya da matsanan cin bugun da zuciyar ta yakeyi.
Kuma matsawa tayi kusa da Sailuba tana K'are mata kallo ranta fari kwal itama zata fito a cikin
sahun manyan, domin duk matar da tayi dacen zama surukar Baffa Abubakar kakar ta ta yanke
sak'a.
Yadda taga yanayin Sailuba ba k'aramin tausaya mata tayi ba sannan ita da kanta ta gane bata
kyautata mata ba akan abinda ta aikata mata sai dai kuma son kanta bazai tab'a bari tayi mata
adalci ba.
"Yanzun kin san abinda nake so dake?"
Ta fad'a tana kallon Sailuba ba, a mugun kasale ta girgiza kanta tana kafe zakiyyan da ido har
lokacin zuciyar ta yana wani irin bugu, idanunta na zubar da ruwan hawaye mai uban yawa.
"Yanzu abinda nake so dake shine ki daina kukan kada ki jamin zagi wajen k'awayen mu
sannan kije ki wanka kizo ayi komai dake kuma ki tabbatar wa da k'awayen mu da amincewar ki
akayi wannan abun hasali ma kece kika dage ayin".
Wani abin mamakin babu musu da wannan shure shuren ta mik'e a sab'ule, yayin da tabita da
kallo tana sakin murmushin mugun ta.
Duk abinda ta umarce ta saida ta aiwatar sannan duk irin yadda k'awayen nasu suka so janta
da zance bata basu dama ba ga kuma abin yana masifar sukan zuciyar ta, haka taro ya watse
Zakiyya na kuma tsarawa Deedah abubuwan da zata yi tare da bata wasu abubuwan da take
so kafin mijin ya kwanta da ita ta aiwatar, wani irin mugun kallo ta rik'a bin maman mata da
kallo, aranta kuwa tana fad'in sai dai ki mutu Mama amma wallahi babu wand zaki cuta da
hannu na.
MARYAM kuwa a gidan malam Umar ta kwana washegari da safe tayi wanka ta maida dogon
rigar da D boy ya bata sannan ta ninke kayan da ta shanya wanda ta wanke su sa'an nan ta
zauna taci d'umamen da Gwaggo Laure ta sa mata, inda Maryam tacewa malam Umar garin su
akalla kud'in mota zaikai dubu goma sha d'aya kuma ba k'arya tayi ba makotan garin da take ta
fad'a masa Allah sarki bawan Allahn duk wani tanadin sa ya kwashe ya bawa Maryam, wadda
tsabar farin ciki kawai ta kama zubar da hawaye tana godiya yace mata babu komai d'a na
kowa ne, har tasha ya kaita wanda yana zuwa yasata a mota tare da yi mata fatan alkhairi,
sosai ta rik'a yi masa godiya sannan ya tafi, tana ganin tafiyar sa tayi saurin fita a motar ta
chanja wani.
A can kuwa bayan kowa ya watse aka bar amarya da ango tare da hud'ubar uwar ta.
Idan baku manta ba nace Deedah tace zata aure Baffa ne dan ta fito zatayi ne dan kawai ta
taimaki Baffa ya dawo hankalin sa amma da k'awayen ta da mahaifin ta suka yi mata nasiha sai
ta share ta tsarkake zuciyar ta.
A ranan kuwa taci amarcin ta da Baffa wanda taga tsagwaran soyayyar da batayi tunanin zata
samu ba domin ganin babban mutum takewa Baffa a wannan dare dai Baffa ya d'auke hankali
da tunanin Deedah.
Washe gari da safe Baffa ya tashi da wani irin fad'uwar gaba kafin kuma ya tafi wajen Inna yasa
ta agaba sai kuka yace "Inna wai me ya faru da Amina?"
Shiru Inna tayi tana kallon sa da tausaya wa yayin da ranta take jin wani irin farin ciki amma
bata da halin bashi amsar tambayar sa, aranta kuwa sai tsarkake ubangiji take tana yi masa
tasbihi tare da sanyawa Deedah albarka.
Ita kuwa Deedah da wannan damar tayi amfani duk da cewa a jigace take domin ba k'aramin
wuya taci a hannun Baffa ba haka ta daure ta rik'a cire cire a d'akin ai kuwa taga abin mamakin
da bata san dashi ba, wani abin ma idan ta taba har zafi hannunta yake haka ta hargitse d'akin
duk wani abu da take tunanin gani saida ta nemo sannan ta kira MD tace su had'u a d'akin Inna
ya taho da wannan kayayyakin da ta bashi
Wash na gaji
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
35
"Kai meye haka bana son shashanci fa" Inna ta fad'a tana hararan MD da ya cakumi wuyan D
boy "sakeshi ko ranka ya b'aci yanzun nan" ta fad'a tana hararan MD da idanunta ta da sukayi
jawur tsabar kuka, shi kuwa Baffa ko ganin D boy baisa ya daina kukan ba sai da yaji d boy
yace sak'o ne daga Maryam ba Baffa ba hatta MD kasa nutsuwa yayi ya cakume D boy yana
fad'in "dan Allah tana ina zamuje nemanta ne dan Allah taimaka ka kaimu ko ka kwatanta mana
inda ka ganta.
Wani irin tausayin sune ya kama D boy har baisan sanda idanunsa yayi jawur ba ganin yadda
yadda duk suka yanyameshi cikin tashin hankali kasa magana yayi sai abubuwan ta da ya
mik'awa MD.
Kayan MD ya rik'a bi da kallo kafin ya maida hankalin sa kan D boy dayake fad'in "Ina kyautata
zaton wannan kud'ad'en da A T M d'in mantawa tayi ta had'o dashi dan wallahi yanayin dana
ganta babu nutsuwa a tare da ita"
Kafe shi MD yay da idanunsa wasu irin hawaye na zubo masa fafin ya maida idanunsa kan
sark'an da yasawa Maryam da hannun sa ranan D'AURIN AUREN SU "shine kika zauna cikin
wahala princess bayan ga kayan kud'ad'e masu nauyi a tare dake?
Haba happiness me yasa zakimin haka?
Ya fad'a a sarari cikin wani irin rauni.
Baffa kam abu d'aya ya iya tambaya shine inda D boy ya had'u da Maryam, nan D boy ya fad'a
masa tare da bashi labarin abinda ya faru, basu san sanda suka muk'e tsaye ba dukansu kafin
Baffa ya rushe da kuka yace "shikenan na lalata rayuwar 'yata da kaina na ruguje zaman kafiyar
zuciya ta da hannu na"
Ya fad'a yana kuka wurjanjan.
Suko su MD shiru kawai sukayi yayin da jiki da zuciyar MD duka rawa suke ya bud'e sak'on
ransa na zafi tare da mamakin yadda akayi Maryam ta iya wannan tafiyar wanda ya tabbatar da
a motama sai ta kwashe kwana hud'u a jirgine kawai zata isa a ranan kuma cikin karamin lokaci
ga abinda sak'on yace [8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
32
Sai da ta had'o duk abinda haj. Zakiyya ta fad'a mata har da wanda bata fad'a mata ba, tasha
mamakin yadda ta riga ganin gawar tsuntsaye a jikin wani abun wanima zuciyar wani tsuntsun
ne, sai da ta zubar da hawaye dan tsabar tausayin maman tata da k'awar ta, dan sune abin
tausayi ba wanda suke cutarwa ba.
Lokacin da ta shiga d'akin Inna Baffa ne agaban ta kamar k'aramin yaro yana ta magiya akan ta
fad'a masa abinda ya aikatawa Amina me tayi masa da har ya yanke mata hukuncin da zuciyar
ta ya buga.
Ba tare da wani tunani ba MD yana hango Deedah ya fasa shiga d'akin Inna, ya dubi Deedah
da murmushi mai ciwo kwance a fuskar shi sai kuma ya saki tunkyar, innalillahi wainnailahi
raji'un, wani irin bindiga da tukunyar tayi basu san ta ina