Showing 33001 words to 36000 words out of 48809 words

Chapter 12 - BA JININA BA CE Part 2 End by MAMAN ISLAM.pdf

15 Apr 2025

2956

cikin sa ya kwanta a rigin
rigine tare da kamo kanta ya manna mata kiss a goshi da tattausan leben d'in ta.



A haka shima baccin yai gaba daahi, bacci ne wanda ya jima baiyi irin sa ba bacci ne rabon da
mai dad'in sa da nauyin sa ya d'auke shi shekara guda kenan kamar dai ita hakanan ya wani
kankame ta a jikinsa tamkar wani zai k'wace masa ita.

"Ka kwantar da hankalin ka Baffa insha Allah komai zai daidaita yanzun ma b'acin rai ne yasa
take abinda takeyin, koda tasan da cewa ba yin kamka bane dole hakan zai mata zafi ace
wannan ya fito daga gareka ne ya kake tunanin zata d'auki abin wane kalar tunani zuciyar ta
zaiyi akan hakan?"


Ga mamaki na kawai Baffa ya rushe da kuka "ya zanyi ya zanyi Deedah ina zan tsoma raina
naji sanyi ace ni da kaina ne na wulak'anta 'yata wulak'anci mafi muni a duniya agaban jama'a
na rik'a tozarta ta wannan wane irin bala'i ne aina zan tsoma raina da wannan babban abin
kunyar da na d'aukar wa kaina da wane ido zan dubi wannan yarinyar mafi soyuwa a cikin
yarana?"



"Baffa, Deedah ta kira sunan sa tare da dafe ka fad'unsa, ka daina damuwa wallahi Allah na
rantse da Allah babu wanda ya zarge ka akan hakan idan har akwai wanda zai zarge ka akan
hakan to wawa ne mara tunani domin ko makaho ya shafa yasan Maryam JININ KACE"



Wata irin ajiyar zuciya Baffa ya sauke yace "yanzu ya zanyi Deedah?"

"Ka kwantar da hankalin ka Baffa mu bata lokaci nasan Muhammad zai RARRASHE ta insha
Allah sai dai bamu san lokacin da zata sauko ba.





Kiran sallar la'asar ne kawai ya tada shi ya k'ure fuskar ta da ido har lokacin bacci take sannan
ga zafin jikinta da ya kuma karuwa hakan yasa cikin sauri ya mik'e ya shiga ban d'aki yay wanka
ya sauya kayan sa ya tafi masallaci daga nan yaje wata shopping mafi kusa da su ya siyo mata
dogayen riguna da riga da sket 'yan kanti da riga da wandunan tree quarter.



Ya fito ya shiga d'aya wajen ya sai mata su chaculete da bscuit yasan mayyar suce
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing

45




Lokacin da ya dawo ta farka a baccin har ta yi alwala itama tayi sallar sai dai tana idar da sallar
ta d'ora kukan ta daga inda ta tsaya, kukane wanda yake tahowa tun daga karkashin zuciyar ta
wanda ta kasa tsaida shi.



Lokacin da ya turo d'akin yaga irin zaman da tayi tana gurshe k'en kuka sai da gabansa ya
yanke ya fad'i amma hakan bai hana shi k'araso wa wajen taba, ya durk'usa agaban ta yasa
hannunsa ya d'ago kanta ya k'ura mata ido sai da gabanshi yai mugun fad'uwa saboda ganin
yadda idanunta sukai wani irin jawur, cikin raunin murya yace.


"Haba happiness dan Allah dan Annabi ki taimake ni ki tsaida kukan nan naki haka in kuma
baso kike wani ciwon ya kama min ke na shiga uku ba"



Hararan da ta watsa masa baisan sanda ya zaune a gaban ta ba k'wace rik'on da yai mata tayi
da k'arfi tace "ina ruwanka dani ina ruwanka da kuka ne in shekara inayi mana meye matsalar
ka da hakan?"


"Ni kuwa nake da matsala da hakan tunda ke d'in rayuwata ce gaba d'aya domin kece farin ciki
na walwala na da jin dad'i na damuwar ki yana nufin nima tawa damuwar"



"A haba dan Allah ashe haka ne to bari na kashe kaina da kukan naga kaima zaka bini tunda ni
rayuwar Kane"


Tayi maganar tanayi masa wani kallon sama da k'asa kafin ya ankare ta saki wani uban ihun da

ta rusa baisan sanda yai saurin janyo ta ba ya had'e bakinsu waje guda jikinsa na wani irin
rawa.




Sosai ya shiga kissing d'in ta yana shafar sassan jikinta, wani irin romantic d'in ta yake mai
matuk'ar kashe gabban jikin mutum take kuwa tayi lakwas tsabar shok din da ta shiga kukan ma
tsayawa yayi chak sai idanunta da ta lumshe tana karb'ar sak'onnin sa.





Da kyar Deedah ta samu ta lallab'a Baffa har yasamu yay wanka yaci abinci suka fita shi da
Nassar.




Sai da ya tabbatar ya kashe bakin rigimar kafin ya zaunar da ita a gaban sa tare da tsura mata
ido ya kamo tattausan hannunta ya rik'e cikin nasa yana cigaba da binta da kallo wanda sam ta
kasa had'a idonu dashi.



"Dan Allah ki bani dama muyi magana" ta tsinci sassanyar muryan shi yana fad'a duk da cewa
bata tanka masa ba yasan cewa zata saurare shi kenan tunda bata k'wace daga rik'on da yayi
mata ba "duk da cewa nasan kina jin haushin mu akan abinda ya faru amma bai kamata ace kin
d'ora mana laifi ba Maryam"

A zabure ta d'ago jajayen idanunta ta kafe shi da su, wannan shine karo na farko da MD ya
tab'a ambatar ainihin sunan ta domin koda ace yana kira bai tab'a kira a gaban ta ba.



Nan MD ya cigaba da bawa Maryam labarin abinda yay ta faruwa bayan tabar gida da irin
yadda Sailuba ta maida Baffa d'an aikin ta komai shi yake mata hatta moopin da girka abincin ta
kuma yanayi tana masa tsawa jiki na rawa da kuma yadda tasa Baffa ya kyautar da Nassar ga
anty Shamsiyya tare da koran da tasa yayiwa Inna da kuma shi akan yak'i sakin auren da akayi
musu wanda ita Sailuba tace dole Baffa yasa MD ya saketa.

Sosai ta rik'a kukan bak'in ciki da takaicin kasancewar rik'on ta a hannun jakar mace irin Sailuba
kafin ta dubeshi tace "Ammey na kumafa?"



Dam dam dam yaji zuciyar sa ya wani irin tsinkewa ido ta k'ure shi dashi haka nan taji gabanta
yai wani irin mummunan fad'uwa tace "bross magana fa nake ina Ammeyna?"



"Innalillahi wainnailahi raji'un MD ina Ammeyna?" ta fad'a jikin ta yana rawa gaba d'aya ta rik'o
hannayen sa tana jijjiga wa, chak ta tsaya tana kallon yadda hawayen sa suke digowa saman
fararen hannunta take jikinta ya kama wani irin tsuma tace


"Me kana nufin Ammey na ta mutu?"
Maganar ta ya k'ara tsinkar masa da zuciya ya fashe da kukan da bai shirya masa ba yayin da
numfashin ta ya d'auke daf sakamakon amsar da zuciyar ta ya bata cewar babu Ammeyn ta a
wannan duniyar.



Shima kukan naahi ne ya tsaya cikin wani irin tashin hankali ya fara jijjiga ta yana kiran sunan ta
da k'arfi kafin ya kwala kiran sunan Baffa da wani irin k'arfi yana jijjiga ta.



Kiran da yaiwa Baffa yayi dai dai dawowar su da Nassar daga fitar da sukayi a guje suka hau
rige rigen shiga d'akin dan ganin abinda yake faruwa
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing


43


A mugun sanyaye Baffa ya bi bayansa yayin da zuciyar sa ke wani irin bugawa hankalin sa a
k'ololuwar tasha lallai Maryam ba d'an kad'an ba tayi fushi da shi.



Da ido Saira ta bisu cikin wani irin farin ciki da kuma jimamin rabuwa da Maryam dan ba d'an

kad'an ba take jinta a jikin ta kamar JININ TA, wasu irin hawaye ne suka zubo mata lokacin da
ta tuna nata iyayen wanda tasan sunyi mata nisan da bazata cimma su ba sai dai a darussalam
idan da rabon ganawar su, ga shi 'yan uwan iyayen nata babu wanda ya rik'e amanar ta saboda
son duniya suka kasa rik'e amanar ta suka wofintar da ita suka nemi kashe ta saboda abin
duniya wanda babu wanda zaiyi guzirin sa zuwa lahira dole dai inda ka same shi anan zaka
barshi, hawayen ta tashare tare da addu'a aranta Allah ya kawo mata d'auki.




Lokacin da sukaje masaukin su tuni Deedah ta jima da farkawa ta afka tunanin inda suka shiga,
turo k'ofar ne yasa Deedah maida hankali wajen k'ofar, wani irin zaro ido tayi ta mik'e tsaye
sakamakon ganin yadda MD ya d'auko Maryam tana ta bige bige da ihun su sauke ta, saida
suka shigo Baffa ya maida k'ofar ya datse ya zare key sannan MD ya direta a tsakar d'akin yana
kallon yadda ta fashe da wani irin kuka tace.



"Wallahi duk abinda zakuyi sai dai kuyi amma babu inda zan biku dan bansan ku ba kuma bani
da had'i da ku bansan kuba kuma bana fatan in sanku"


Deedah ce ta k'araso kusa da ita ta rik'o hannayen ta, sai dai kafin takai ga cewa komai Maryam
ta doke hannunta ta daga jikinta tare da sakar mata wata muguwar harara, bata dai ce mata
komai ba sai uban tsakin da ta saki.



"Maryam matar Baffa ce fa" MD ya fad'a yana kallon ta da mamakin yadda take ta abubuwa
haka ba d'an kad'an ba taji dukan furucin MD wai matar Baffa ce wannan d'iyar matsafan
shikenan Ammey ta Kuma shiga wata masifar bayan ta Sailuba "sai me? tayi k'arfin halin fad'i
zuciyar ta na wani irin bugawa saboda tsabar bak'in cikin jin wai Baffa ya kuma wani auren dan
son kuma k'untatawa Ammeyn ta babu shakka wannan shirin Sailuba ne yar gaban goshin
Baffa, kada ka K'ara sakani a cikin abinda ya shafe ku ni bai dame niba"
Bata san Baffa ya k'araso kusa da itaba yace "mary""""""""""""dan Allah dan Allah dan Allah ku
k'yale ni nayi tafiya ta dan Allah rayuwa ta haka yana min dad'i dan Allah" ta k'arasa cikin kalar
tausayi tare da rushewa da wani fitinannen kuka zuciyar ta na wani irin zafi.



"Zamuje d'aki na da ita Baffa" MD ya fad'a a sanyaye kasa magana Baffa yayi sai jinjina masa
kai da yayi, yayin da Deedah ta k'araso ta kama Baffan dan ganin kamar jikin shi na d'an rawa,
Nassar kuwa fita yayi ya bar d'akin.

MD kuwa ganin Maryam na nuna masa taurin kai ya kuma sab'ar ta kamar d'azun yay waje da
ita tana wani irin kuka, koda suka shiga d'akin kasa rarrashin ta yayi sai zama da yayi a gefen
gado ya rungumeta k'am k'am a jikin shi zuciyar sa na wani irin mugun zafi



Manage plss
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing



46



A gigice yake jijjiga ta cikin tsantsar taahin hankali tare da nadamar sanar da ita wannan
mummunan labarin, sai dai kuma ya riga da ya zama dole ta sani sannan kuma babu wanda ya
cancanta ya fad'a mata sama dashi.




A tare Baffa Nassar da Deedah wacce bata jima itama da tashi daga nata baccin ba, a
matuk'ar firgice sukayi kanta gaba d'aya a rud'e Baffa yake tambayar abinda ya same ta, cikin
tashin hankali MD yace.


"Baffa na fad'a mata babu Ammey ne munyi rashin Ammey a wannan duniyar babu ita tayi
mana nisa nisan da bazata tab'a dawowa ba har abada"


MD yakewa Baffa wannan bayanin yana kuka tamkar wani k'aramin yaro kukan da baiyi shi da
ba shine yake yinsa yanzu kukane mai tsananin k'una da bak'in cikin rashin wanda akayi
babban rashin sa.



Baffa Nassar Deedah duk kukan suka fashe da shi bama kamar Baffa da bak'in cikin shi ya
ninka na MD Baffa shine wanda ya cancanci kuka shine wanda ya dace yayi kuka ba wai MD
dake tare da farin cikin shi ba bare kuma da Nassar da ko matakin farko bai hau ba na

RAYUWA sai kuwa Deedah da ta sadaukar da farin cikin ta saboda laifin da ba ita ta aikata ba.


Deedah ce tayi k'arfin halin samo ruwa aka shafa mata ta dawo hayyacin ta cikin wani irin
yanayi mai wuyar fassara cikin tsantsar damuwa da tashin hankali abune wanda ya zo mata a
wani irin bahagon yanayin da bata tab'a kawowa ranta ba rasa Ammeyn ta a wannan duniyar
tamkar rugujewar duk wani tsarin rayuwar tane to duka duka ma yaushe tasan cewa Ammey ita
ne mahaifiyar ta duka duka yaushe tasan matsayin Ammey a gare ta batafa farama jin dad'in
taba Nassar shi ya more tunda shi yasan dad'in adalar uwa irin Ammey ita kuwa wannan
tsinanniyar matar tayi mata katangar k'arfe da mahaifiyar ta wannan shine katan katana
mutuwar almuru.



"Bazan yafe mata ba, bazan yafe mata ba, bazan tab'a yafe mataba har duniya ta nad'e, ta
cutar da da rayuwa ta, ta rabani da farin ciki na Allah ya isa na bazan tab'a yafewa ba"


Ta k'arasa tare da fashewa da wani kafirin kuka mai azabar k'arfi, da sauri MD yajata jikinsa ya
rungume kamkam yana shafar bayanta a hankali shima nashi hawayen ya kasa tsayawa.


Baffa kuwa da Nassar ganin kamar yana K'ara rikita yanayin ta saboda kukan da suke wanda
Baffa da biyu yake nashi kukan yasa Deedah ta jasu suka koma d'akin su.





Shi kanshi saida ya arowa kansa jarumta sannan ya iya d'ago ta yana kallon cikin idonta wanda
suka sauya kala tsabar damuwa cikin wani irin sassanyar murya yace



"Kiyi hak'uri dan Allah ki daina kukan haka kada ya illata ki kinga tunda abin nan ya faru kike ta
faman kuka har zuwa yanzun da ba kuka ya kamata kiyi ba"



Kamar waya doluwa take kallon sa kafin cikin wani irin rauni da rawan murya tace "to me kake
so nayi idan banyi kuka ba?
Ko ba kai kacemin na rasa Ammeyna ba?
Rasata fa nayi kuma rashi na har abada bamu wani shak'u ba kuma tazo ta gudu tabar ni me

kakeso nayi to?"



Kararasa cikin fashewa da kuka tana jijjiga shi.
"Addu'ar ki take buk'ata Maryam ba kuka ba wannan shine gatan da zakiyi mata a halin yanzu
kuma shine sahihiyar k'aunar da zaki nuna mata a halin yanzu sannan itama zatayi farin ciki da
hakan wanda kema sai kin sami nutsuwa a bisa hakan"




"Kofa darajar samun ganin gawar ta banyi ba bare muyi bankwana ban samu damar ganin
gawar mahaifiyata ba taya kake tunanin zan sami nutsuwa?"




"Kiyi hak'uri dan Allah Maryam ya fad'a yana d'ora ta saman cinyar sa yana rarrashin ta da
sanyayan kalamai da k'yar ya iya shawo kanta ta daina wannan kukan amma fa saida ya had'a
da tofa mata addu'o'i dan ya lura kamar bata cikin hayyacin ta.
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing


47


Assalamualaikum masoyana barkanmu da sallah da fatan duk munyi sallah lafiya naga
sak'wannin ku kala kala na gode sosai da irin k'aunar da kuka numin nasami lafiya Allah ya bar
zumunci.




A hankali ya rik'a shafa bayanta yana d'an bugawa kad'an kad'an har yaji numfashin ta ya fara
sauyawa alamun bacci ya kwashe ta, kafeta yayi da rinannun idanunsa wani irin tausayin ta na
huda shi, musamman ganin irin fitinannen raman da tayi jiyai wani irin abu nabin jikin shi take ya
d'ago ta ya wani irin rungumeta tsam tsam a jikinsa yana sauke wani irin zazzafan numfashi
kafin ya ya soma magana.

"Kaddara ne kaddara ne tasa banyi tunanin komai ba na tafi na barki da rabon zaki sha wannan
gwagwarmayar bansan cewa rayuwar ki zata kasance a haka ba da ban tafi na barki ba
Maryam mai tallah fa?
Mai talla akan titi wayyo ni Allah na wannan wane irin bala'i ne matata wacce igiyar aurena yake
kanta ne ta kasance a wannan halin ki yafe min, ki yafemin happyness ki yafemin sarauniya ta
tun wancen lokacin zuciya da ruhina basu hutaba wajen nemanki sai yau Allah ya dubeni ya
kawomin k'arshen wahala na.

Daga haka wasu irin zafafan hawaye suka kama zubo masa babu k'ak'k'autawa idan ya tuna
wai Maryam ce ya ganta a bakim titi tana siyar da lemo da ruwa sai yaji wani irin abu ya tokare
masa a wuya.




Jin ana kiran sallar magriba yasa ya d'an zameta yaje ya dauro alwala ya fito suka had'u da su
Baffa suka wuce masallacin cikin hotel d'in, sai bayan sallar isha suka fito a masallacin Nassar
ya wuce yayin da Baffa da MD suka tsaya dan tattaunawa akan abinda ya shafe su.



Duban MD Baffa yayi cikin k'unan rai yace "Muhammadu ada banyi niyyar rabuwa da Sailuba
ba amma a yau abisa faruwan wannan abubuwan ka zama shaida ni Ahmad Abubakar Baffa na
yanke duk wata alak'a dake TSAKANINMU dan haka na sake ta saki uku".


Ya fad'a yana zubar da hawayen bak'in ciki domin Sailuba ta cutar da shi ba d'an kad'an ba.



Wani irin sanyi ne MD yaji aransa ko ba komai Baffa ya wanke masa zuciya tas yaji dad'in
hukuncin da ya yanke akan wannan tsinanniyar Sailubar.



Lokacin da ya shiga d'akin akan sallaya ya tadda ita, ta idar da salla sai gursheken kuka take
"ya salam ya furta can k'asan makoshi kafin ya k'arasa kusa da ita cikin rauni yace "wayyo Allah
na"


A firgice ta d'ago tana kallon shi ganin yadda ya dafe k'irjin shi yasa tayi saurin d'ora hannunta
saman nashi sai dai ta kasa cewa komai sai hawayen dake cigaba da zubo Mata

Eid Mubarak
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing



48



A hankali taga yanayin baya kamar zai fad'i da sauri tasaka dukan k'arfinta ta finciko shi sai
gashi sun zube a k'asa tayi flat yayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login