Showing 1 words to 3000 words out of 48809 words

Chapter 1 - BA JININA BA CE Part 2 End by MAMAN ISLAM.pdf

15 Apr 2025

2946

[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing



40



Da k'yar Saira ta iya had'iye nata kukan saboda itama saida taji nata damuwar ya dawo tamkar
yanzu yake faruwa da ita hakan yasa ta kuka mai yawan gaske kafin ta samu tayi shiru ta soma
da fad'in.



"Ba komai Maryam kiyi hak'uri ki barwa Allah komai yana sane da ke shi zai kawo k'arahen
komai dan haka ki daina kukan shima karin wani damuwar ne kuma zai iya zama ciwo a gareki
dan Allah ki daina wannan kukan na rok'eki"


Ta fad'a tana ci gaba da share nata hawayen "naga rayuwa na koma tamkar mai tab'in hankali
saboda tsabar dattin da kazantar da ya taru a jikina sai da kalan zanen kayana ya b'ace saboda
rashin abin wanka bare na wanki, wanda take na cikin tama taya zatayi wani tunanin wanka da
wanki Saira"?

Ta fad'a tana kallon Saira wacce ta kuma rushewa da wani irin kuka yayin da Maryam taci gaba
da cewa "harfaon abinci na rik'a yi Saira wani ya bani wani ya nemi lalata dani wannan wane
irin bala'i ne Saira?
Ina yake me yake akan wane dalilin zai barni cikin wannan k'ask'antaciyar rayuwa kenan tayi
galaba akan mu?
Akaf abinda ta fad'a guda d'aya ne banyi ba Saira shine ZINA amma nayi bara nayi yawo akan
bola na kwana a gefen hanya naci abincin da bashi da kyau saboda tsananin azabar yunwa
sannan nayi yawo tamkar mahauciya mara gata mara galihu mara 'yanci, yayin da shi yake can
cikin farin ciki da daula babu ruwan shi da rayuwar da nake yi bai damu da halin da nake ciki ba
dan haka idan har akwai igiyar auren sa akaina dole ya rabata dan na tsane shi?"



Ta fad'a tare da zubowar wasu zafafan hawaye masu uban yawan da ya firgita Saira, abinda
kawai ta iya cewa shine"inane garin ku?"

Sunan garin da Maryam ta fad'awa Saira saida ta mik'e tsaye tana kallon ta kafin tace "Maryam
wallahi wannan garin kawo ki akayi ta hanyar asiri kinji kuma na rantse koma waye aka rabaki

dashi ta hanyar asirin ne dan haka ina rok'on ki da dan Allah kada ki yanke hukuncin abinda
baki da tabbacin sa"




Ita Maryam bata k'ara tankawa Saira ba sai mik'ewa datayi taci gaba da tafiya dan bata buk'atar
ko wane irin RARRASHI a halin yanzu zuciyar ta ci yake da wuta.



Koda sukaje masaukin su babu yadda Saira batayi ba akan Maryam taci abincin da suka taho
da shi ta kasa ci duk kuwa da irin fitinannen yunwar dake damun ta har hawaye sai da Saira tayi
amma Maryam ta kasa ci sai ma kukan da take ta sharb'a shima tun Saira na RARRASHI har ta
gaji ta sa mata idanu cikin fushi.


Sallah ne kad'ai ya tada Saira daga inda take a gaban Maryam da ta kafe da ido cikin tsantsar
tausayi.


Ganin yanayin da Maryam ta kwana yasa washegari tunda wuri Saira ta fice taje ta fara amso
ruwa da lemon da Maryam take karb'a ta siyar ta wuce takai wanda suke zama tare ta bawa
ajiya sannan taje ta amso doyar ta, ataikace dai ranan sai Saira ce ta saidawa Maryam lemon
da ruwan ta kwashe mata riban ta ta kaiwa masu kayan kud'in su.

Sai da Maryam tayi kwana uku kullum tana karkashin gadar nan da suke kwana kafin ta daure
ta fito dan ta fahimci kuka da damuwa babu abinda zai sa mata sai ciwo da wahala haka ta
watsar da komai taci gaba da fita neman na abinci ga tsantsar d'acin rai da ta kuma d'orawa
ranta bata dariya bata magana sai ya zama dole hakan ya matuk'ar damun Saira



"Yau kwanan mu goma a wannan garin babu inda bamuje ba amma bamu ganta ba kowa zaice
da yana ganin ta amma yamzu ya daina ganin ta, mu koma gida kawai mici gaba da addu'a"



Wani irin kallo MD yayiwa Baffa na k'asan ido ko Baffan bai kula da kallon ba amma Deedah ta
gani har dariya yaso kwace mata tasan kuma sarai mai yake tunani ido suka had'a da MD ya

galla mata harara take ta had'iye murmushin dake neman subce mata a can k'asan makoshi
yace "zaku iya tafiya Baffa amma ni sai dai na mutu anan dan ina ji a jiki na princess tana
wannan yankin
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: *مسب الله نمحرلا ميحرلا *

*☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION ☀️*

FCWA

*Home of qualities and trusted writers of the nation*



https://free.facebook.com/111719967001810/photos/a.111720050335135/116072649899875/?ty
pe=3&source=45&refid=17

______________________________________
*BA JININA BACE*
*2021*

BOOK 2


NA


*HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI*

*MAMAN ISLAM*

ASSALAMUALAIKUM MASOYANA KAMAR YADDA KUKA JI NA FAD'A BA JININA BACE
KASHI NA BIYU NA K'UDI NE GA MAI BUK'ATA K'OFA A BUD'E YAKE DAN BIYA DAN ALLAH
DAN ALLAH DAN ALLAH 'YAR UWATA IDAN KINSAN ZAKI SIYA DAN KI FITAR MIN DASHI
TO KI HAKURA NIMA NA YAFE DA CINIKIN KI INA ALFAHARI DA MASOYA NA A DUK INDA
SUKE A FAD'IN DUNIYA MA'ASSALAM DAGA TAKU MAMAN ISLAM
GA MAI BUK'ATA ZAI IYA TURA D'ARI BIYUNSA TA WANNAN ACCOUNT D'IN KAMAR HAKA
1401305206 SADIYA AUWAL ABDULLAHI ACCESS BANK KO KUMA KATIN MTN TA
WANNAN NOMBER 09030311095

PAGE 2



Duk irin yadda wanda abin ya faru agaban idon su, sukaso tsaida ita sam kasa fahimtar su tayi
ta fashe da kuka tana rok'on su Allah da Annabi akan su k'yale ta ta nisan ta kanta da wannan
gidan da take jinta kamar a cikin wuta.




Inna na ganin Maryam ta fice ta fashe da kuka, ta dubi mutanen da suke tare tace "dan Allah ku
taimaka min kada ta shiga duniya kunga ta fita, kai Amadu kana ina zo ka kamomin jika ta
wallahi Amadu ka bar rayuwar Maryam ya wulak'anta bazan tab'a yafe maka ba"



Inna ta dire zancen da fashewa da wani irin kuka tanayi tana shid'ewa tare da fyace majina.




Duk abinda ake MD baisan abin yayi zafi haka ba domin shine ya daukarma su kawu Ammey
kuma shine yaja motar hankali a tsananin tashe, sam bai san abinda yake faruwa a gidan ba
bai sawa ransa Baffa zai iya koran Maryam a gaban Inna ba.




Haj. Sailuba kuwa bayan taci bala'in duka wajen Maryam hakan baisa bakinta ya mutu ba fad'i
take "wallahi Maryam koda aure ko babu sai kin zama karuwa sai kin aje tarihi Maryam sai kin
kawowa Amadu d'an shege amatsayin jika"........dal inna ta d'alle bakin Sailuba tace "fitinanniyar
banza insha Allahu bazan ga wannan tashin hankalin ba, bazan tab'a ganin bara gurbi a
zuriyata ba, Sailuba ina tausaya miki, zaki dana nasani, ina jiye miki ranan NADAMA"



"Ai duk kece silar faruwar komai Inna" haj. Sailuba ta fad'a tana shafa kumburarren bakin ta da
ya isheta da azaba, cak Inna ta tsaya tana kallonta kafin tace "kamar ya ban gane laufina ba?".

"Eh Inna kece kika ja komai da kika dage sai Baffa ya k'ara aure akan ban haihu ba, inbanda
fitina irin naki ina ruwan ki da rayuwar mu? ke naki zamanin waya takura miki? wa yasaka miki
Ido? sai mune kika bi kika takura mana, to bari kiji abinda baki tab'a sani ba kafin zuwan
Maryam duniya duk b'are b'arin da Amina take yi nice, hakama haifar yara guda uku datayi suna
komawa duk nice nan nake shak'e musu wuya abisa shirin malamina, ina so kisan cewa Inna
tunda nake arayuwa ban tab'a jin ina k'aunar Maryam ba dai dai da na second d'aya, idan akwai
abinda nayi mafi wahalarwa a duniya shine rainon Maryam da nayi, duk da cewa akan hanyar
banza nake d'ora ta sai dai kash shegiyar yarinyar taurin kaine da ita domin tak'i yarda tabi
maza kamar yadda nake buk'ata, amma yanzun nasan ya zamar mata dole kodan yunwar
cikinta dan nasan cewa ko nawa ta fita dashi zai K'are, barema babu abinda ya tafi dashi,
akarshe kema Inna ina son ki d'auke hankalin ki akan ni da mijina idan ba haka ba kawar dake
ba komai bane a wajena"




Sosai Inna ta kafe Sailuba da ido ta kasa cewa komai sai hawayen da ke ta faman shatata a
idanunta wai 'yar da ta rik'a tun tana 'yar kwanaki a duniya, taci kashin ta, taci fitsarin ta, tasha
bak'ar wahala akanta, yau itace ta mayar mata da d'a salamamme? Kai innalillahi wainnailahi
raji'un wannan wacce irin masifa ce?.




Ana haka MD ya shigo hankali a tashe domin jikin na Ammey babu dad'i nan ya samu abinda
ke faruwa, wai Baffa ya kori Maryam a gidan, abinda MD bai tab'a yiba a rayuwar sa duk
tsananin azabtuwar da suke a filin daga shine fashewa da kuka yau sai gashi ya fashe da
mugun kuka, zuciyar sa tayi wani irin rauni, "me yasa da ya koreki baki jira na dawoba? Me yasa zaki min haka?
Ina kika tafi?
Baki san cewa kece rayuwata ba kece farin ciki na?
Dan Allah ki dawo farin ciki na" ya fad'a yana kuka wurjanjan.



"Sai dai kuwa ka mutu dan ina mai tabbatar maka wannan yarinyar tayi nisan da ita da gida har
abada ta riga tayi NISA DA GIDA HHHHHHHHHH" ta saki wata muguwar dariya.

Sam MD bai kula da ita ba saida tayi wannan maganar, sannan yasan tana wajen, ai kuwa wani
irin kukan kura yayi, yayi kanta kamar mayunwacin zakin da ya shekara babu abinci, tana ganin
haka ta mik'e da wani irin sauri dan tseratar da kanta.




Saidai ina, bafa dukan wasa Maryam tayi mata ba dan har ta tardad'a mata k'afa, hakan yasa
MD yacin mata ya rufeta da wani irin matsiyacin duka.


'yan wajen fad'i suke kashe tsinanniya ai wannan shine hukuncin mai raba d'a da mahaifi,
matsiyaciya, ke ba mutuwa ba amma kina neman raba yarinya da asalin ta Allah yayi
wadaranki.



Duk abinnan Inna tana kallo amma ta kasa hanawa saboda tsabar tashin hankalin datake ciki.

Sai Baffa ne yasauko da gudu sakamakon jin kukanta da neman taimako, ganin irin fitinannen
dukan da MD yakewa haj. Sailuba, yasa baisan sanda yayi kansa ba yasa dukan k'arfin sa dan
ture sahi daga kusa da ita, amma ko gezau MD baiyi ba hakan tasa Baffa ya d'auke shi da wani
mugun mari wanda babu tantama saida yajiwa hannunsa ciwo, sakamakon k'arar da yayi, danji
yayi kamar ya mari dutse.




Cak MD ya tsaya daga k'wallo da yake da haj. Sailuba sakamakon marin da Baffa yai masa,
abin bai d'aga masa hankali ba saida Baffa ya bashi ta karda da biro yace "na tambayi malam
Babba ya tabbatar min da cewa an riga da an d'aura aurenku da Maryam dan haka sake ta dan
d'ana bazai zauna da shegiya mar........


"BAFFA"" MD ya katse shi da wani irin rud'ad'd'en yanayi.

Kafe Baffa yayi da ido yace "ko dukana zakayi, nace dukana zakayi kake min wannan banzan
kallon?"


"Eh dukan ka zaiyi Amadu" inna a bashi amsa masa cikin muryar kuka"wallahi Amadu kayi
asara tunda har kake wasa da addu'a da har wannan makirar matar tayi galaba akanka, wallahi

ka bani kunya"




Ta fad'a tana gurshek'en kuka, sosai kukanta yake tab'a ransa yanajin wani iri acan kasan
zuciyar sa, sai dai kuma yadda yake ji a ransa da ran Sailuba ya b'aci gwanda na Inna ya b'aci
ya bita ya rarrashe ta.




Hakan yasa ya maida hankalin sa kan MD yana fad'in "ungo nan wallahi saika saketa"



"Wallahi ya saketa saika saki Sailuba, ko na tsine maka albarka" Inna ta fad'a tana huci sannan
taci gaba da fad'in maza jeka nemo matar ka Muhammadu, kayi nisa da ita, nisan da zai nisan
ta wannan uban banzan da ita, ina so kayi nisan da ko a lahira sai tsananin rabone zai sa ya
ganta, tunda shi ya wulakantar, ya wofintar, akwai masu so"


Jin ance matuk'ar MD ya saki Maryam itama sai an saketa ba k'aramin d'aga mata hankali yayi
ba, tabbas hakan zai iya faruwa tunda a yarjejeniyar da sukayi da boka babu musu wa
mahaifiyar sa, taya ma akay ta manta wannan?



"Bazai saketa ba kamar yadda kika gindaya sharad'i Inna amma hakan bazai tab'a hanawa ta
zama gawurtacciyar karuw..... d'as d'as d'as MD ya d'auke ta da wani irin fitinannen maruka har
guda uku kafin yayi mata wani irin hauri agefen ciki ya fita a guje ya yana hawaye.





Duk inda yake tunanin ganin Maryam yaje amma babu ita babu labarin ta k'awayen ta kuwa
agabansu komai ya faru bare ya bincike su, haka MD ya rik'a yawo kamar mahaukaci gaba
d'aya ya fita hayyacin sa ko gidan bai waiwaya ba a anan cikin motar sa ya kwana a gefen titi.

Haka ma Inna yadda taga rana haka taga dare kuka kuwa tayishi babu adadi tashin hankali iya
tashin hankali, tunda take bata tab'a tsintar kanta a mugun yanayi irin wannan ba.





Ammey kuwa sanda aka isa asbiti da ita ta jima da suma bata san wayake kanta ba, tuni likitoci
suka rufu akanta dan ceto rayuwar ta,sai dai yanayin da sukaga bugun zuciyar ta ba k'aramin
d'aga musu hankali yayi ba, sai kawai sukayi wanda zasu iya suka barwa Allah sauran hukuncin
sa



Tana fitowa daga gida, ganin wasu daga cikin danginta sun biyo ta yasa ta taka da mugun gudu,
hakan yasa wasu suka rufa mata baya saidai tana shan kwana ta b'ace musu b'at, sun jima
suna dubata har kusan awa guda kafin su hak'ura su koma gida subi sahun masu la antar haj.
Sailuba.




Ita kuwa tana ganin sun bar wajen ta fito daga inda ta b'uya achab'a ta tare tace ya kaita tasha
mafi nisa da wannan garin hakan yasa da ya tashi sai yabar garin gaba d'aya da ita ya kaita
wani d'an k'auye.





Hakan ne yasa koda MD ya rik'a bin tashoshin babu wanda yasamu yace ya ganta.



Muje zuwa
[8/22, 7:25 PM] MAMAN ISLAM: Typing
N 4

Suna sauka kowa ya kama gabansa, anan ne idonta ya raina fata, ga uban gajiya, ga yunwar
da ya addabeta, ga k'ishi ga tarin baccin da bata samu tayi ba.

Haka taci gaba da bin wajen da kallo tana tunanin inda ya kamata ace ta nufa, tunda take bata
tab'a yin tafiyar da yakai tsayin haka ba, asalima ita daga makaranta sai gida, sai kuma idan ta
kaiwa k'awayenta biyu ziyara, wato Maryam da Halima.


Ganin cewa zaman bazai kai mata ba yasa ta tashi ta kama hanyar fita daga tashan cikin
tsantsar damuwa ga idanunta sunyi wani irin luhu luhu na tsabar gajiya da yunwa.


Tafiya take tana tunanin inda ya kamata ta dosa, bata da kowa, batasan kowa ba, bata san inda
zata nufa ta tsira ba, hakanan ta kama magana ita kad'ai.


"Koda ace abinda mama ta fad'a akanki gaskiya ne hakan yafimin kwanciyar hankali akan ace
wannan fajirar ce uwarta, tasani kaddara ce ta samar da ita mummunan kaddaran da bata da
ikon dakileta.



Hakanan taji zuciyar ta yayi tsinkewar da baiyi tun faruwar abin ba, take ta fashe da wani irin
kuka, wanda yake tahowa daga can k'asan zuciyar ta "Allah gani gareka ,Allah ka dubani badan
halina ba, Allah ka yafemin Allah ka yafemin na cutar dake Ammeyna, ban miki biyayya ba ki
yafe min dan Allah Ammey naaaaaaaa" taja kalman ta na k'arshe tare da fashewa da wani irin
fitinannen kuka mai cin rai, dan dole ta durkushe a wajan tana rasgar kukanta mai rai da lafiya.


Ta jima sosai a wajen kafin ta mik'e taci gaba da tafiya tana kuka, ganin yunwa na neman yi
mata illah yasa ta nemi wajen mai shayi tace, yasa mata ruwan Lipton a leda tare da kwai guda
biyu, gudar dubu day'a ta bashi ya d'auki kudinsa ya bata canjin.




Tsabar yunwar da take ji haka ta rik'a shan Lipton d'in yana k'ona mata baki ta shanye ta cinye
kwan, a take taji wata 'yar nutsuwa ta kamata haka taci gaba da tafiya tana kuka tana magana
kamar wata tab'ab'b'iya.

"MUHAMMAD dan Allah kar kabar Maryam ta shiga duniya, dan Allah ka Nemo ta duk inda
shiga a duniya ka tabbatar mata da cewa ita d'in cikakkiyar 'yar halak ce mai cikakken gata ita
d'in d'iya ce ga BAFFA Abubakar dan haka tasa a ranta wata k'addararren al'amari ne ya gifta
mata wanda bamu da ikon dakileta dan Allah kace ta kasance maiyi min addu'a bayan raina
abune mai wahala in tashi Muhammad najifa abinda likita yace ba yace zuciya na ya tsage ba?"



Sosai MD ya razana dajin abinda tace dama ta farfad'o taji abinda yake fad'a Kennan? Kai
innalillahi wainnailaihi raji'un fashewa yayi da wani irin fitinannen kuka ya kasa magana.


Murmushi Ammey tayi ta kamo hannun MD tace "haba Muhammad yanzun dan Allah idan kayi
kuka Kuma Nassar yayi Yaya kana so Maryam tayi ta kuka dan Allah kazama jarumi haba soja
na?"

Ta fad'a da wani irin salon da yasa MD yana hawaye yana wani irin murmushi, itama murmushin
k'arfin hali tayi tace "ko kaifa Muhammad dina dan Allah karka bari suyi kuka nasan basu da
wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login