Showing 6001 words to 6282 words out of 6282 words

Chapter 3 - MATAR HARIJI Part 1 Free PAGE 1-10.txt

NIl   

07 Apr 2025

2460

haye samansa ya cire kayansa ya faɗa bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi duk da sanyin damunar da yake garin badon komai ba saidon ya samu sauqin abinda yake masa tuƙuƙi a ƙalbinsa amma ina kamar turi ma haka yaji.









Fitowa yayi ya zauna a saman resting chair din ya dafe kansa yana furzar da iska me zafi cikin ƙunar zuciya, zabura yayi ya miƙe ya fara safa da marwa yana tunanin mataki na gaba maganganun Arɗo Jibo suna dawo masa inda yake cewa "kai kaɗo dubeni nan ni ba ɗan iska bane mu ba asararru bane ba rakiya mukayowa bayin Allah duniya ba idanma kana tunanin haɗa zuri'a dani to ka daina aradun Allah dana baka auren ɗiyata Jiddoh ƙwamma ni tsireta na cinye namanta"

wannan Kalami sun daki zuciyar Lameer fiye da dukan dorina sosai suke zaga masa a kwanyarsa kuma suka sashi cikin tunani da son sanin meye dalilin da yasa Arɗo Jibo yayi wannan furucin tare da ƙara ɗaura ɗambar neman auren Jiddoh.

"Kuma munyiwa Jiddoh miji dama mun daɗe da samun lbrn kaine kake hure mata kunne har kanayi mata juyen nono kana janta ku shiga duhun dawa kasata ta fito innininta ta baka kasha..." "meye innini ya tambayi kansa tare da miƙewa ya buɗe ƙofar ya shiga kitchen ɗin dake saman ya dafa tea ya dawo parlourn nasa ya zauna ya tusa kofin a gaba ya kasa shan ko kurɓa daya saboda Hauwah kawai yake gani a idonsa dukan kansa yayi tare da tambayar kansa wai yaushe ya shiga wannan cakwakiyar rayuwar ne wacce ƙaddara ta kaishi Alƙalawa har ya ƙarasa Rugar Sambajo ya haɗu da Jiddoh ya fara yimata wannan son na mutuwa da rayuwa................

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login