Showing 3001 words to 6000 words out of 13946 words

Chapter 2 - KANKANA (Uwar Ruwa) Book 1 Complete By Oum Aphnan .pdf

Ido qauyanci fal cikinta wannan wani irin motane
? aiko yaci sunan sa Lamban gini . Shikam Adam tunda ta gaishesa yace lafiya bai qara kallon
inda direction dinta ma yake ba ,bare ya tantance kamanninta ,abu daya ya lura da shi wankar

tarwaÉ—a ne mai matsakaciyar tsawo da matsakaicin qiba ,sannan ya lura azaqwaqwaine akwai
zaqin murya bayan nan bai kalli koda fuskarta ba,har suka qarasa Tangamemen mansion house
din ,saida suka wuce gates uku sannan suka shigo wawagegen haraban gidan mai É—auke da
rukunin gine ginen kuma a kowanne qarqashin gini an yi rumfar adana motoci ,mai daukan
motoci guda 4 ,kazalika kamar anyi anko haka aka zuba motoci guda hur-huÉ—u a qarqashin
kowani haraba.
1.Ferarri fara tas kamar spot car dai
2. GLE 53 baqa wulum
3. CLE 200 year 2024 suma baqaqe
4. Sai Audi RS3 2018
Dukkan motocin nan kowacce mata an zuba mata irinsu a qarqashin haraban building
dinta.,ukun motocin Hawanta ne ,sai AUDI 2018 na masu aikinta in zata aike su saqo ko wani
laluran cikin gida dai.

Ai tuni Idanuwan Hassenat sun fara raina fata ,duk daburcewa tayi ga motoci sabbi fil sai
kashema rana ido suke da gani yau din nan aka shigo dasu guda 16 duk hur-huÉ—u iri daya ,ga
lafcecen gida da ya gaji da tsaruwa kamar wata qasaitaccen masarautan India.

Tunda Adam ya faka mota a rumfar adana motocinsa ,ya kashe motar yayi shiru ya kasa mata
magana ,shi ba gwanin mata bane so bai iya wani hira da mace ba

Hassena a daburce ta kallesa "Har mun kawo?😒"
Jinjina mata kai yayi "Uhm "

"In sauka?😟" Ta fada da dan tsoro tsoro a ranta

"Yes gidanki ne ai" ya bata amsa a taqaice.
Wani yanka ihu tayi wanda saida ya firgita "Gidana !!? Gidana fa kace ? Wayyo Allah daÉ—iiiiii"
tana magana ta kama hannun kofar motan tana girgizawa saidai ta kasa budewa abunka da er
qauye.....lolz.

Da kansa ya bude mata aiko tana ganin kofan motar ya buÉ—u ta dirko da gudu tayi tsalle zuwa
tsakar gidan tana shaqan wani irin qamshin furanni da ya hade da wani irin niimtaccen iska
tamkar ba a duniyar nan take ba.

"Wayyo Allah ,Ji motoci ji gida ??" Waigawa tayi ta kalli Sir Adam da yake tsaye a nutse abunsa
ya mata qur da ido yana kallon yanda take faman tsalle tsalle kamar qaramar yarinya dukda a
shekaru takai 23years.

Watso mashi matsakaitan idanuwarta tayi da alamar tambaya "Oga duk motocin nan naka ne?"

Girgiza mata kai yayi ban faye hawa mota ba sai jirgi nawa biyu ne rak gasu nan da wannan
G-waggon din sai wannan da muka taho a ciki sauran duk nakune kowaccenku guda 3 nata

daya na masu kula da ita,so ki zaga kiga gidan yayi maki ko akwai abunda kike so a saka?"
fasa ihun murna tayi

"Kai lahaula.....Arziki ga inda ake gwanjonka ......" Qurrrr wayarta rakani toilet ya fara daukan
kwaratsin ihu ma'ana dai ana kiranta a waya.

"Hello Zainabu ,Zainabu kinga gidaaaa, Ya Allahu ,kinga motoci zuqa zuqa wai nawa ,kinga
fulawoyi kinga benaye ,benaye benaye wayyo Allah "

Tana waya tana ihun santi tana kewaye gidan ,ta wajen shaqatawarsu tabi taga tafkeken
Swimming pool ruwan shi garai garai sun hade da kalar sararin samaniya ,ga wajen table tennis
ga lilo . Da gudu ta isa wajen ta tsuguna tana wasa da ruwan Swimming pool din

"Zainab harda wajen wankan turawa da muke gani a film.....laaa da tebur din qwallo ,irin
qananun qwallon nan ...yauwa da lilo .wayyo Zainabu ko ina tayil da ciyawa masu laushi (Grass
Carpet)hummm ni'ima kinji sanyi kinga bishiyoyi humm zainabuuu ,Zainabu sai na dawo da
akwai labari".
Adam da ya gaji da tsayuwar jiranta haure en takalmarsa yayi zai shige cikin sashen da ya
kasance mallakinta

Ai da gudu tabi bayansa ,saidai tana fara taka matakalen da zai sadaka da kofan shiga nata
part din ,ta fara daddagewa saboda yanda tsantsin tiles yake kokawan nanata da qasa ,da taga
zata ba kanta wuya ,sai ta tsuguna ta zare takalman qafafuwarta ta gurfana ta cigaba da binsa
da rarrafe.
Waigowa adam yayi yaga abinda takeyi ,baisan sanda ya bushe da dariya ba a ransa yana
cewa "Wannan is not only a cook but comedian For me😂"(wannan ba wai kawai mai girki
momy ta samo mun ba ,aah harda mai bani dariya).













___________

_Guys ga Janan ga Haseenat_

_Wannan ta iya koyar da Girki🍟🍔🥛 wannan Kuma ta iya koyar da cin Duri da bura🍑🍌Ba
ruwana �wai abinda ta koya kenan a makaranta_

_Wacece Jarumarku?�_

_Ga ZAKIYYA ga JANAN ga HASEENAT muna shirin zuwan ta hudun zamu gani daga wani
duniyar zata zo ne?_

_A biyoni a page 5&6_

_Comments É—inku yana bani qwarin gwuiwa saidai yayi mun kadan shiyasa yau na baku guntun
page_😄



***
Littafin Kudine
Regular ₦500
Vip 1k
Special 2k

Kisa ta Opay
9065990265
Mohammed Hassana

Ko
Fcmb
7782217014
Mohammed Hassana

Shaidar biya ki turo ta whatsapp ma wannan Numbern
09065990265




Oum Aphnan �

*_KANKANA..._*
_(Uwar ruwa)_

Na
Oum Aphnan
2025®
_____________
P5&6
4pm
Cikin Tashin hankali ya kinkimota daga back seat din Motarsa ,ya runtuma a guje da ita zuwa
cikin gidansa ,direct sashensa ya wuce da ita ya mata masauki akan makeken gadonsa ,still
idonta a rufe yake tabbas bata farfaÉ—o ba.
Sir Adam samun gefen gadon yayi ya zauna gamida rafka uban tagumi ,a hankali ya ke magna
cike da tarin nadama.

"Me ya aikeni tuqa mota bayan nasan tuqi wahala yake mun?.....tuni wata sashe na zuciyarshi
ta bashi amsa da ...Kaidin macen kenan,duk zakiyyace ke neman birkita rayuwarka a abunda
baikai awanni 48 ba ......da qarfi ya girgiza kai idanuwansa sunyi wani irin ja......Shikenan
gayinan naje na kaÉ—e er mutane ,yanzu kila ma jini ya hade mata da kwanya ta qare ta haukace
in shiga uku!"

Ai yana kaiwa nan a tunaninsa ya qwalla qara da sauri ,oh No!!! inshaAllah bazata haukace ba
Subhanallh na shiga uku!"

Qarfin qaran da runtuma shi yasa Yusrah sakin wani qaqqarfan ajiyar zuciya ta zabura zata
mike ta falla da gudu da Iyakan qarfinta.

Da sauri Sir Adam ya kamota ya maida ta kan gadon ya zaunar da ita cikin saukin murya yace
"Relaxxxxxx!!! Ok?"
Jinjina masa kai tayi idonta fal qwalla lokaci daya kuma wasu Mayun hawaye da ta rike su a
kwarmin idonta suka samu nasaran silalowa a idonta .

Gabadaya qarasa birkicewa yayi , she's very gentle daga ganin ta bata da hayaniya .

"Kiyi hakuri kinji ba abinda ya sameki da ikon Allah"
Sai sannan ta bude baki da qyar ta fara masa magana da sassanyar muryarta mai rauni da
sakawa zuciyar mai sauraronta son ya tausaya mata (Innocent voice)
"Wanene kai ? Ina ne nan? Kuma ya akayi nazo nan?"

"Kiyi hakuri kinji.Ni sunana Adam ,Ni babban Industrialist ne kuma É—an kwangila and also
Ambassador na manyan teams na qwallon qafa. Nan da muke ciki gida nan ne ,Nazo wucewa
ne a hanya bansan ya akayi ba kawai naga kin gifto mun shine na kusa takaki infact dai na
hankadeki da mota ,ina fitowa da motan sai naga kin sume...."
Kafin ya qarasa maganarsa ta katsesa a hankali "Kuma me yasa baka kaini asibiti ba sai

gidanka?"

"Matana tana cikin gidan nan so bazan cutar dake ba"

"Baka bani amsar tambayar da nayi maka ba"

"Me kenan?".

"Nace why Hospital?".

"I had Pobia to hospital "( Ina da laluran tsoron asibiti)

Yamutse fuska tayi "Kana nufin Nosopobia?"

Duddulo ido yayi "Ya akayi kika sanshi in a medical term?ke likita ce?"

"Hummm Ni dalibar jinya ce ina shekarar qarshe na karatuna na Degree a halin yanzu ,sai
dai...sai dai...."
Kawai ta kece da kuka

Tuni Sir Adam ya rude gabadaya
"Sorry calm down everything will be alright ,Can I know more about You? I mean can You share
your stuff with me?"

Jan ajiyar numfashi tayi a hankali kana ta lumshe idanuwarta suna kallon qasa.

"Sunana Yusrah mu en biyu ne a wajen mahaifan mu ina da sister sunanta Yumnah ,saidai tun
da aka haife mu iyayenmu suka sauya mana suna ,na taso da mafarkin burin karatun likita
dukda iyayenmu ba masu qarfi bane ba a yayin da Hussaina ta ta kasance Er kwalliya karatun
ma bai dameta ba ,wannan yasa halin kowa yasaba a lokacin damuk gama secondary samari
suka kabbaro mana kasantuwar mu na Fulani and ba laifi munada kyawun mu daidai mu . Ni
bana sauraron samari saboda babbar burina inyi karatu mi zurfi in zama likita....
Saidai kash burina bai cikaba saboda halin Hussaina ta na tara samari daga qarshe dai taja
sanadiyya aka muna aure Ni aka bani wani yaron babanmu malamin makarantar primary ne
,itakuma ta auri wani Mahmud da suke son junansu ,Mahmud din da rufin asirinsa saboda
lokacin bikin mu ma yana final year dinsa na karatun engineering kuma yana kasiwanci.....Na
fuskanci qalubalai masu yawa a gidan aurena cikin yunwa da azaban rayuwa na haifo masa
yara biyu daga nan ya gudu ya barni cikin qunci,an neme shi yazo ya zauna in laifi ma nayi
masa a mana sulhu saidai fafur yaqi zuwa yana ganin ya gama dani shi ba ajina bane ba
....Nayi tawakkali na dangana na koma gidanmu da naga zaman ba amfani haka sai na dauki
firinji na na saida na sayi Form din jami'a na fara karautun Degree na na likitanci ,bawan Allah
nan bai taba neman mu ba For over 6 years now balle yayi tunanin wani hali muke ciki Ni da
yaransa ,sai a wannan satin yaji labarin ina shekarar qarshe a jami'a kuma zan zama babbar

likita zan fishi tunda shi malamin makaranta ne,shine ya dawo wai sai in koma ma aurensa ,bai
taba tunanin zai ganni na dawo da kyau na da aji na ba fiyen fiyen da na da.....nikuma na bushe
ido na nace bana komawa gidansa ,a take yamun barazana har yana mun mugun fatan wai in
har ina masa gadara ne don ina taqama nayi boko to na kama igiyar wala don bazan taba
gamawa ba .......nace ta Allah ba taka ba ai kai ba ubana bane ba ,Anyi abun da kwana biyu za
biya kudin final exams din mu dubu dari da saba'in wanda naci baqar wuya kafin in iya ta rasu
harda kudin adashi duk aka bani na farko na harhada zan biya saidai abun tsautsayi hackers
masu kwashe kudin banki suka samamaye account din banki na suka kwashe,saidai suka
barmin Naira tara da kobbai.....zuciyata ta tsinke nayi kuka na tausaya ma rayuwata gashi
banda mataimaki sai Allah . A wannan yanayin ya sake dawowa wai sai in bashi ya É—ebe yaran
da nike ganinsu inji sanyi ,ya tafi dasu tunda yaransa ne ,nikuma naga baida mata in na bashi
yarana harda diya mace wani hali zata fada? A take na yanke shawarar sace su in kaisu gidan
marayu ,Allah barshi idan komai yayi mun daidai a rayuwa na dauko su😿Wannan dalilin ne ya
fiddo Ni daga gida da nufin tafiya gidan marayu in magana da masu gidan in sun amince in
kawo su ,to a hanyar ne na shigan ma motarka saboda azaban tunani kai kuma ka ture Ni baka
sani ba ....amma sam baka da laifi a accident din da na samu face damuwa ce ta dameni"


Tuni kan Adam ya kulle wani mugun tausayinsa ya sake kamashi kallonta yayi yaga yarinya ce
er qararrama da qyar ya iya magana bayan dogon shirun da yayi yana sauraron ta

"Shekaranki nawa da kika dauki duk wannan bala'un a kanki , na ganki er qararrama"
Murmushine ya Qwace ma Yusrah

"Shekara ta Ashirin da biyar fa ai Ni ba yarinya bace ba "

"Yes still You Are young.....karki damu ki dauke Ni kamar yaya a wajenki and nayi alkawarin za
tsaya maki iyakan qarfina ,Bara in kawo maki abinci ok? Kici ki qoshi kafin in maidake gida
.....kudin jarabawa ba matsala zan biya maki ,yaranki ba matsala zan tsaya masu....."

Wani dadi ne ya rufe Yusrah ta mike da sauri a daga kan gadon zata fada masa

"Are You serious? 😄fada mun da gaske kake zaka kula mun da yarana zaka biyamin kudin
makaranta na?"

Jinjina masa kai yai cikin jin dadi ,shi ya taimake ta ,amma faraar da ya gani a fuskar ta da
annurin fuskarta ,yafi ta jin Dadi

You na weldone my people 🥰A karkade zani mun kusa wajen Ehyanehhh🍌🍑😄🙈Saura
kiris muna kan shimfidan Labarin ne🤌🏽😘






_Dont move far ,yanzu muka fara .Kowa tazo ta bani fatawan wannan aure da Adamu ya
jajibo😂_

_Kuna ganin anyiwa Zakiyya Adalci kuwa??_

_Shin zai iya samun kalar matan nan da ya lissafa??_

_Waima Yaya haka ? Jarumin littafin babu kayan jarumta🍌😂🤔_

_Qaqa hakan ta farune ? Ko dai haka Allah ya yisa? Shin zai iya satisfying matan da ya auro 3
rinkis???_








***
Littafin Kudine
Regular ₦500
Vip 1k
Special 2k

Kisa ta Opay
9065990265
Mohammed Hassana

Ko
Fcmb
7782217014
Mohammed Hassana

Shaidar biya ki turo ta whatsapp ma wannan Numbern
09065990265




Oum Aphnan �
*_KANKANA..._*
_(Uwar ruwa)_


Na
Oum Aphnan
2025®
_____________
P7&8
POV Surayya

Qarfe 2.15pm ta fito falon bayan yasa an kawo mata abinci which dan kadan ta ci taji duk ya
gundureta ,murna ne fal ranta dama akwai mutane irin Adamu a duniya ? Kai Alhamdullh God
answered my prayer .
A nutse take takawa tana dan wawwaigawa saboda bata san hanya ba ,can ta hango shi kan
wani wargajejen royal 3seater gabanshi madaidaicin Centre table ne da laptop akai sai
wayoyinsa guda biyu sai dan mug na coffee da yake sipping lokaci bayan lokaci
Cike da ladabi da biyayya ta isa gabansa tadan russuna kadan ,kana ta ce "Ina yini"
Lumshe Ido yayi a hankali wow when last matata ta gaishe Ni?
Bai ankara ba yaji ta sake maimaita gaishe shi ,da sauri bakinsa har yana dan rawa yace
"Ayyyy sorry lafiya qalau"
"Tom inaso ne zan wuce makaranta ,Nagode sosai da abinci da kuma taimako na da kayi ,Allah
ya saka da Alkhair"
Murmushi ya dan yi kasantuwarsa ba maabocin magana ba ,sai kawai ya cigaba da daddana
wayan hannunsa .jin shiru ba alamar za'a tankata yasa Yusrah juyawa zata tafi gwuiwarta a dan
sanyaye.

"Uhm wait plz amshi nan"
A nutse ta waigo ganin ya mika mata wayarsa yasa ta kalleshi da alamar tambaya "Account
number Please kamar yanda nayi alkawarin"
Ba musu tasa hannu ta amsa ta saka mata numbobin Opay dinta sannan ta mika masa wayan.
Dan murmushi yayi bayan ya loda password din bankin nasa
"Ok done!"
Murmushi tayi Tom Nagode ,sai anjima a gaida Madam,har zan tafi bamu hadu ba"
"Ok zatajine"
Har takai qofa ta juyo saidai bansan hanya ba ina ne nan?"

"Ko inzo in kaiki?"
"Ni na isa babban mutum kamar ka ya kaini wani waje?"
Murmushi yayi yana sosa qeya,saboda shi a karan kansa ma tsoron tuqi yakeyi but wajibinsa
ne ya gyara abunda yaso batawa.

"Muje ko?" Ya fada yana gaba tana binsa a baya,mamakin tsaruwar gidan kawai takeyi ,Ko'ina
remoting system daidai da kofar gidan smart door ne ,mai amfani da numfashin mutum ya bude
kansa gashi tafkeken qofa ga tsawo ga girma bullet proof bayajin bindiga .

A hankali yake tuqa motar kamar mai tausayin kan kwaltan karatun Kur'ani ne yake tashi a
motan qasa qasa. Wayarsa ne ya fara vibrating alamun ana kiransa
"Hello mom Barka da rana" shiru yayi na dan lokaci
"Mom yanzu ya za ayi bikin nan fa so nike yi a yi shi ranar Asabar din nan ,please mom indai da
yanda za'ayi a samo mun matan nan Ni ko nawa ne mom kinsan zan biya auren ne kawai nike
so mom"
Jim yayi na en seconds "Ok Nagode Allah ya qara girma hajiyata"

Lokaci daya Yusrah taji jikinta yayi sanyi meye dalili ita dai bata sani ba? Idanuwarta taji ya
mata nauyi lokaci guda suka dan qanqance a take taji salon maganarta ya sauya da qyar ta
fizgo kalmomin bakinta zuwa kan halshenta
"Waye zai aure ? Ba dai kai ba?" Jinjina mata kai yayi lokaci daya kuma yaji wani ya tsirga
masa take ya kafe qwarar idonta da kallo yana son karantan wani abu a cikinsu .Rausayar
dakai tayi gwanin ban tausayi "Kuma kace Asabar din nan? Amma baka da wanda zaka aura
din?"
"Eh its urgent ne ,ban damu ko wacece ba ,ko zaki aure Ni?"

Dammm! Taji gabanta ya fadi lokaci daya ta lumshe ido saidai ta kasa magana

Dafe kai yayi da sauri "Oh sorry na manta kina da aure ki gafarce Ni kinji .i'm desperate ne"

Bakinta yana dan rawa tace "Ai an raba auren 6months back"

Lokaci daya ya saki murmushi mara dalili "Wow zaki aure Ni? Feel free with me banda matsala
,kawai ina neman macen da zata ta yani rainon zuciyata ne...In kuma ban maki ba shikenan "

A sanyaye tace "Ai ba wata mace a duniyar nan da zatace bakayi mata ba ,and beside Ni a
wace Ni? Taimako na fa zakayi a single mother ga yara biyu gani bazawara"
Murmushi yayi "Ina sonki da duk abunda kika fada din indai zaki iya aure na "
















*.........Wannan shine mafarin*
Don Haka mu dawo farkon Labarin🥰Tom lokacin Cin abubuwa ya fara🍌🍑🙈

Before

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login