Showing 3001 words to 6000 words out of 40828 words

Chapter 2 - IKLAS BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Maman Noorul- Hudah--.txt

28 Dec 2024

2531

da sai ta nimi in sake ta da kanta wallahi


Islam ne ta shigo d'aki tace"yaya baza ka je FM bane yau?"


Tashi yayi yace"bari inje it will cheer me up iam in worry,


Ciro wanan abun yayi na baki ya saka


Islam tace"yaya wallahi muryar ka yafi dadi in baka saka wanan abun bakin ba,why not kayi ta using natural voice d'in ka sai kafi samun fans"


Zaro ido yayi yace"ke kin manta da halin Abba ne?in ya gane nike program d'in daddalin masoya hmmm sai na gane shayi ruwane"


Tace"yaya ka hakura mana tunda abba baya so"


Yace"wallahi sister ba zan iya ba abin da ya rage mun nike tuna nuratu kenan dan in ina yi sai naji kamar ina tare da ita ne"


"Bangaren IKLAS kuwa zazzabi ya mata mugun kamu yanzu ma da k'yar tayi tsalla isha'i ta jawo radio ta tafara sauraren daddalin masoya yau ma kamar kullum batayi magana ba har ya gaji ya yanke call d'in haka ta cigaba da ji FM har barci yayi gaba da ita


Washe gari ta shirya ta sauko sai dai bata da walwala


A makaranta ta had'u da minal tana ganin ta,ta rungume ta ta fashe da kuka


Minal tace"IKLAS me aka miki kike kuka haka?"


IKLAS tace"minal zan auri wani ba R M D ba,minal daddy yayi mun miji ji nake kamar zan mutu"


Tsaki minal tayi tace"ai yayi mun dai-dai dan ko yace ki fito da R M D ba sanin shi kikayi ba balle ya aure ki,ni naji kamar ance yana da mata dan ance shekaru biyar da suka wuce mace ne ke program d'in kuma mutane ke zargi Matan shi ne"


Kuka IKLAS ta sake tace"may be ba zai soni ba tunda yana da mata"


Minal tace"IKLAS ki dage da addu'a ki daure kiyi wa iyayen ki addu'a inshaallahu zaki ga dai-dai"


Bayan sati uku IKLAS ta gama jarabawan ta kuma biki ya rage sati biyu amma har yanzu basu had'u da ango ba ko waya be taba kiran ta ba"


Abba ne zaune a palour yace"Islam kira mun RAYHAN"


Bayan tafiyar ta sai gashi sun dawo tare


Zama yayi Abba yace"ya kamata Kaje gidan su yariyar nan Ku fahimci juna"


Gaban shine ya fadi dan shi gaskiya baya tunani zai iya zuwa gidan ko wace mace ba da sunan zance"


Abba ne ya dawo dashi daga duniyar tunani da ya fad'a


Yace"da kai nike magana"


Yace"inshaallah gobe zani"


Abba yace"toh"


Nawal tace"dad nima zani wajen new mummy d'ina"


Hararar ta yayi yace je ki shirya muje kasuwa siyar teddy"


Tsalle tayi tace"toh daddy"


Ummi tace"Ku siyo mun irin wanan atampa kelle ta basu"


Minal ne zaune a falo mamy tana cewa"IKLAS yi sauri muje mu fito da anko dibi biki saura sati biyu amma a ce ba anko friends sai kira na suke"


Mamy tace"kema dai kye fad'i"


Minal tace"suma angon ina nan ina jiran su sai na ci musu tara for coming late"


Hijabi IKLAS ta saka tace"muje" ba dan ta so ba


Wani babban shago zanuwa suka shiga


Minal sai tsurutu take tana duba kaya


Itako IKLAS zama tayi a kujera tana fuskanta kofan shago


RAYHAN ne a wani shago yana tambayar su ko suna da zanin da ummi tace su siyo mata
A ka ce babu tsaki yayi yace"ummi ma sai tayi ta ma mutum aiken mata"


Kallon d'aya daga bodyguard din shi yayi dan sometimes kan yi yawo da su amma not always ya bashi kellen zani


Yace"je shagon can ka tambayo ko za a samu"yayi mishi nuni da shagon da su IKLAS ke ciki


Yana tsaye sai ga wani me yiwa Abba aiki a shagon su na cikin kasuwa tsayawa sukayi suna fira


Be lura da nawal bata kusa dasu ba sai fira su suke hankali kwance


IKLAS ne ta hango wata karamar yariya machine na son ya kwashe ta da gudu ta fito ta tureta suka fad'i tare kasancewar shagon na gab da titi


Yariyar ta gurje a hanun jini na fita


Mai machine ko sai mita ya kayi yana cewa"sai Ku kawo yara kasuwa baza Ku kula da su ba salon Ku jawowa mutane magana"dan shi a zaton shi yariyar tare suke da IKLAS




Tashi tayi ta d'auke ta,ta rungume tana cewa"ina maman ki?da wa kuke ne"




Nawal ko rungume ta tayi ko magana ba tayi dan ta tsorata sosai


IKLAS tace"muje in siya miki big teddy"tayi haka ne dan yariyar ta sake da ita sanan daga baya ta tambaye ta Inda zata sami maman ta


Barin gaban shago suka yi zuwa wani shagon teddy




Juyowa RAYHAN yayi ya kalli d'ayan bodyguard d'in yace"ina nawal"


Zare ido yayi yace"d'azu fa tana nan"


RAYHAN yace"what? kaji sakarai wallahi in wani abu ya sami nawal bazan yafe ma ba"


Niman nawal suka fara yi abu kamar wasa sai da suka kai awa biyu suna niman ta


dan bayan sun shiga shagon teddy nawal ta hango wani shago da ake sayar da kayar wasan yara


Tace sai IKLAS ta siya mata babu musu suka shiga sai jido mata takeyi amma da ta fara tambayar ta gidan su ko maman ta sai ta fashe da kuma


RAYHAN ko gajiya yayi da nimar ta ya sanar da yan sanda cikin kasuwa










Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ9⃣&1⃣0⃣


IKLAS ko gajiya tayi da ita, ta zaunar da ita shagon wata mai abinci,abinci ta siye mata ta fara feeding nata


Minal ma gajiya tayi da nimar IKLAS gashi in ta kira ta bata d'agawa tace"wai ina ta shiga ne"


Sai daga baya yaron shagon ke bata labari abun da ya faru


Tace"toh bari in tafi yanzu hakama ta kai ta gida ko station"


Kamar ance RAYHAN kalli can ya hango su zaune sai surutu nawal ke zuba mata har da cewa ita baza ta koma gidansu ba sai dai su tafi tare


IKLAS ko ta fara gajiya da surutun ta gashi ta bar waya a motar minal


Tana zaune kawai ta ji saukan mari da yayi sanadiyan d'aukewan wuta ta na wasu mintoci


Fisge abincin hanun nawal yayi yace"how dare you give my daughter street food"


Magana take son yi ta kara jin wani saukan mari da yayi sanadiya fad'iwarta kasa


Rike kumatu tayi tana kallon shi


Nawal ko ta fara kuka tana mummy ta zo ta rungume ta


Janta yayi da karfi sanda ta saki kara kallon hanun ta yayi ya ga ciwo


Cikin b'acin rai yace"su tafi da ita tana son tayi kidnapping d'in dota shi


Kuka IKLAS ta fara yi ganin police na kokarin saka ta a mota


Tace"please ka saurare wallahi ni ba kidnapper bane taimakon ta nayi"


Amma ko kallonta beyi ba ya ja nawal wanda ke ta kuka ta kiran mummy


Police station aka kai ta aka saka ta a canter


Kuka take ga ba waya a hanun ta balle tayi waya gida


Yana shiga gida ya ga jama'a cike a cikin gidan ana shirin kai lafe gaishe su yayi


Bayan sun gaisa ya mikawa ummi sakon ta ya shige ciki rike da hanun ta


Nawal ta fashe da kuka yace"wai me na kuka ne?"


Tace"zani wajen mummy yace"ai ba mummy ki bane"


Fashewa tayi da kuka tana birgima a kasa


Yace"wai ina ma kuka had'u ne har kike ce mata mummy?"


Nan ta kwashe komai ta sanar da shi a zuciyar shi yace"tayi brain washing d'inta amma bari in kira ayi reasing d'inta nasan yanzu tayi realizing mistake d'inta"


Waya ya d'auka ya kira police station yace"a yi releasing d'inta"


Tana fito hawaye ya sauko mata a kumatu tace"daga taimako"ji take sanar shi na ratsa ta


Bayan wasu kwanaki Wanda a yanzu bikin su saura kwana uku


Kuma har yanzu basu san junan su ba dan be zo ba sai dai ya aiko Abdul abokin shi


Yau daddy ya tilasta shi ya je ya gaida iyayen ta amma yana zuwa bayan sun gaisa


Mamy tace"yanzu suka je saloon da kawayenta"


A zuciyar shi yace"who cares?"


Amma a fili


Murmushi yayi yace"ba damuwa mamy zamu yi waya da ita"


Cikin jin dadi mamy tace"Allah ya sanya albarka"


Yace"amin"Abdul yace"toh mu zamu wuce"


Sallama sukayi kowa suka bar gidan


Washe gari ya kama kamu Abdul yace"dun Allah RAHYAN ka saki jikin ka a wajen kamu nan kar ka bari a fahimci wani abu tsakani Ku pls


Murmushi yayi yace"hmmmm abokina har na fara tunanin rashin mutunci da zan mata Wanda da kanta zata bar gidan"


Abdul yace"ka dai bi a hankali kar wata rana ka fad'i a rami da ka gina da kanka"


Karfe 4:30 Ravi aka shirya amarya cikin kaya na alfama tayi kyau sosai


Tana zaune tayi zurfi cikin tunani minal ta shigo tace"kizo mata ya zo"


Fita tayi minal ta kaita motar da RAYHAN ke ciki


Shiga tayi ta zauna juyawar da za tayi suka yi 4eyes


Gabanta ne ya fad'i ganin shi a mota tunani tafara a zuciyar ta tace"kar dai shine ango?"


Matse mata hanun da yayi ne ya dawo da ita daga duniyar da ta fad'a


Take mata kafa yayi yace"dama dan niman suna shine kika ce wa nawal tayi ta kiran ki mama?toh bari in fad'a miki ba zaki taba replacing nuratu ba


Kuma ki d'auka wanan auren an d'auke ki yar aiki ne dan wallahi ba zaki taba samun position din mata a wajena ba domin ko house help dina sai fiki gata"


Hawaye take yi dan har yanzu ba saki hanun ba


Suna kaiwa hall d'in driver yayi parking kallonta yayi yace"kuma in kika kuskura kika bari mutane suka fahimci halin da ake ciki toh wallahy sai kiyi regretting zuwar ki duniya"


Goge fuskanta tayi ta fito shima zagayowa yayi ya rike mata hanun ya matse da karfi zafi take ji amma sai murmushi take tayi


Da yaga tana murmushi ya kara matse hanun da karfi kallon shi tayi ya harare ta


Masu hoto ko sai hotuna suke d'aukan su ga yan jarida na d'aukan rohoto




Haka akayi dinner aka ga suka shiga mota dan komawa gida a hanya ma sanda ya ja mata suma


Yace"wawiya araha wanda aka gaji da ita a gidansu"


Kara matse kanta yayi sanda ta saki kara


Driver yace"ayi mata hafuwa ihu ya daka me yace"kana hauka ne waya ce kasa baki?


Washe gari jumm'a aka d'aura auren RAYHAN Mohammed d'ahiru da IKLAS umar faruq a sadaki naira dubu d'ari


IKLAS na ji an d'aura aure ta saki wani irin kuka main rai


Misallin karfe 7:45 aka shirya amarya dan kai ta d'akin mijin ta


Rakota akayi wajen dady nasiha yayi mata mai ratsa jiki har da d'an kwalla shi yace"Allah yayi miki albarka,ya
baki zuri'a nagari"


Yan rakiya suka amsa da amin


Daga nan wajen mamy aka kaita itama adu'a tayi mata da albarka sanan tayi mata nasiha










Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEOUS WRITERS FURUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the
best among the rest.




1⃣1⃣&1⃣2⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


Bayan mamy ta gama yi mata nasiha


Suka fito tashiga mota da ita da minal sai sauran mutane da zasu rakata


Minal tace"IKLAS ya kama kiyi wa kan ki sauki da wanan kuka ni ban ga abin kuka Allah ya baki miji na kece raini wallahi jiya baki gan inda kukayi matching bane a wajen dinner ba"


Cikin kuka IKLAS tace"minal baza ki gane bane"


Gidan ummi aka kaisu d'aki baki aka sauke su bayan su samu tarba mai kyau


Ummi ko baki yaki rufuwa saboda murna bama kamar nawal da ta like wa IKLAS mutane sai ya ba kyaun ta suke ana cewa"gaskiya RAYHAN yayi sa'a mata"


Misalin karfe 8:pm bayan an idar da sallah isha'i aka shirya amarya cikin wedding gown dan zuwa reception


Dr Abida ne zaune a palour ta tana kallon firm remote ta dauka ta canja channel kawai sai ta gan an hasko fuskar RAYHAN da wata a event of the week a na nuna kamu da akayi jiya


tashi tayi tace what!!!wallahy baki isa ba nice kad'ai mata RAYHAN duk macen da ta aure shi zan kaw da ita a doron kasa


'Bagaren Mahmud ma haka ne yana rike da news paper ya gan pics dinsu bushewa yayi da dariya yace"aiki banza ai IKLAS nawa ne amma zan bari ka latsa kwana biyu kafin in yi executing plan d'ina"


Suna isa hall d'in reception RAYHAN yayi saurin fitowa ya bude mata kofa sai murmushi yake yi masu hoto da yan jaridu na aikin su


Minal da Abdul suka mara musu bays


RAYHAN ba karamin kyau yayi ba cikin blue suit


hanun ta ya saka cikin nata ya matse dan mugunta da sauri ta kalleshi ya sakar mata murmushi


Suna shiga hall suka zauna a mazaunin su RAYHAN ya take wa IKLAS kafa tana jin zafi kukan zuci take yi amma ta share shi


Ganin alama bata ji zafi ba yasa ya kuma take wa da karfi


Batare da b'ata lokaci ba mc ya fara jawabi inda daga karshe aka bukaci amarya da ango su fito su taka rawa


Tashi sukayi zuwa filin rawa rugumeta ya yi yana juya ta


Kallonshi tayi ya harare ta ya kawo bakin shi dai-dai kunne ta


Yace"shegiya ballagaza nasan kina jin dadin rugume ki dana yi sha-shasha


Hawaye ne ya ya cika a idon ta yace"in kika bari ya sauko zaki sha mamaki"




Mutane ko sai tafi sukeyi Abdul yace"RAYHAN d'an duniya ya iya basaja"


Minal da ke zaune kusa dashi tace"me ka ce?"


Hararrantaa yayi dan haushi take bashi tun ranan da ya fara zuwa gidan su IKLAS kan maganan biki tayi me tas wai yazo latti


Bayan sun gama rawa mc yace su yanka cake


Cake suka yanka tayi feeding nashi ta bashi juice a baki


Shiko da ya yanko San da ya saka a bakishi ya kawo dai-dai nata ya saka mata


Juice ko yana tana bude baki ya sake glass cup sai kafan ta ya tarwase ga jikin ta ya lalace da juice karami yatsanta sai jinin yake yi"


Yace"sorry"


Mc yace ya kuma bata wani bata yayi daga nan aka kulle taro da addua


Suna fitowa har za su shiga mota su jiyo ana cewa RAYHAN Dr Abida ne duk tasha atarce ga nails dan bata rabo da artificial nails


Tace"haba RAYHAN yanzu a ce zakayi aure amma ko gayyata babu sai dai in ji a gari"


Rike hanun IKLAS yayi yace"sorry wallahi abubuwa ne suka yi mun yawa"


Kallon IKLAS yayi yace"sweet heart ga friend dina"


Itako Dr Abida a ran ta tace"a gaba na ma yake soyewa lallai ya kamata nayi gaggawan yin wani abu dan da dukan alamu yana son ta"


Mika mata hanun tayi tace"iam Dr Abida Nasir"


IKLAS tace"IKLAS umar faroq"


Abdul ne yazo yace"RAYHAN ga wani old friend na gaishe ka"


RAYHAN yace"muje toh"


Yana Baron wurin Abida tace"ina fatan kin d'aura d'an mara yaki because the battle line has just been drawn"


IKLAS tace"ban fahimce ki ba"


A fusace abida tace"RAYHAN is my and I will go to any extent to get him,I dt want to share him with anyoneone including you"ta nuna ta da yatsa


Cikin mamaki IKLAS tace"are you threatening me"


Tace"is just an assurance"


Murmushi IKLAS tayi tace"childish"ta shige mota ta bar abida tsaya


Direct gidan RAYHAN aka kaita nan kowa ya watse


Sai misalin karfe 11:20 RAYHAN ya shigo gidan direct bedroom d'inta ya je ya hango ta kwance a gado tana barci hankali kwance


Yace"lallai ma kin samu wuri toh wa yace miki kina da lokacin barci a nan gidan?"


Karasawa yayi ya ciro ruwa a fridge ya bude goran ruwa d'agawa yayi sama ruwan ya fara sauka akan ta


A firgice ta tashi yace"same ni a parlour"


Tana fitowa ta same shi zaune a parlour


Tace "gani"


Kallonta yayi yace".........








Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:42] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah


🌟GORGEUOUS WRITERS FORUM🌟


🌟G.W.F.🌟


Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


Dedicated to Smasher and Hubbey group


πŸ…Ώ1⃣3⃣&1⃣4⃣


Yace"kina hauka ne? Zaki tsaya a tsaye ina magana da ke,common be on your kneels"


Jiki na rawa tayi knell down


Yace"good ina so ki bude kunne ki da kyau ki ji abun da zan fad'a miki,ina so ki sani ba barci ya kawo ki nan gidan ba and baki da wani matsayi a waje na you are just a maid to me nothing more,inaso by 5:am na safe kin tashi kin gyra gidan nan ki share compound da bawa flower ruwa,and by 6:40 kin gama breakfast wallahi kika Bari har kika wuce lukatan nan baki gama ba sai kin gane baki da wayau


Kallonshi tayi tana hawaye


Yace"bari kallona da mayu idanuwan ki kamar bob


Bayan haka shiru ne ya biyo baya na wasu mintina


Jin shiru yasa ta mike zata wuce dan barci take ji


Amma tana mikewa yace"ubanwa yace ki tafi?"


Sungunawa tayi tace"yi hakuri na d'au ka gama ne"


Yace"zonan"zuwa tayi kusa da shi


Yace"zauna"zama tayi


Kafafun shi ya kwashe ya aza a kafad'a ta ya kunna tv yana kallo hakalin shi kwance


Kuka take yi,ihu da daka mata ne yasa ta yin shiru gyangedi take amma ko a jikin shi


Haka ta ci gaba da zama har tsawon awa biyu


Sanan ya kalleta yace"you can go"


Da gudu ta tashi shiga bedroom ta kwanta ta saki kuka mai suma zuciya har barci yayi awon gaba da ita


Washe Bari around 6:30am tana barci taji saukan ruwan sanyi a jiki


A firgice ta tashi yace"me na fad'a miki jiya?"


Tace"yi hakuri pls na gaji kuma ban kwanta da wuri ba"


Yace"my friend will you shut your dirty mouth and go and do your how chores"


Da sauri ta tashi ta shiga kitchen ta fara had'a breakfast


Tana gamawa ta jera a dining ta je d'akin shi


Tace"breakfast is ready"


Ta dawo ta zauna a dining ta fara cin abinci dan yuwa take ji rabon ta da abin tun kan a kaita gidan ummi


Yana saukowa ya gan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login