Showing 9001 words to 12000 words out of 43727 words
Chapter 4 - ABULLE TA MAI UNGUWA 1to End Book Writing By Momy Yusra.txt
ar kirki babu ta miƙe ta nufi falon, don dama bata so aka dagata kan kallon ba.
Ba kowa a falon, sai ƙaton tibin da ke ta faman aiki. Zama ta yi, ta kuma baza idanunta, kan kwalbar. Tashar turawa take kallo, wani tsamurarren bature sai zabga surutu yake, ita dai ba ji take ba nata ido.
A hankali-a hankali taga yana ta tahowa yana kuma nuni da hannunshi tamkar mai nunata.
Ganin yana shirin faso kwalbar ya fito ne yasa Abulle fasa wani uban ƙara. A kiɗime ta zabura, duk ta gigice ta rasa ina ta dosa? Ta ma rasa inda za ta gudu ta tsira kafin aljanin tibin ya gama fitowa ya risketa.
Shiko gadan-gadan yake ƙara matsowa, a waige-waigen da take na neman yanyar tsira ne ta hango hanyar da zai sadata da ɗakunan gida.
A guje ta ɗiba, yayin da mutanen gidan suma suka fito a guje don ganin ihun me take yi?
Karo suka yi da Hajiya, take ta sake sake ihu ta hau roƙo da magiya gami da bada haƙuri.
"Ke wai lafiyarki ne?"
Hajiyar ta tambayeta, karkarwa ta shiga yi tana magiyar kada ya cutar da ita tasan shi namiji ne ya koma muryar mata, ta tuba ya mata rai, yau ma zata bar gidan ta fasa yin kwana biyun.
Cike da mamaki Hajiya ta ce,
"Abin Allah! Budurwa da ciki; Gwauro da yaye. Inno 'yar taki na tare da ƙwanƙwamai ne?"
Ihu ta sake kurmawa tana faɗin,
"Don Allah kada ku cutar da Inno! Tare za mu tattara duk mu tafi. Mun tuba ku yi mana rai, har abada ba zamu kuma Jinjin ba."
Duk suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah.
"Ina fa wani ƙwanƙwamai! Rashin kunya ne kawai, mace ta auri mace."
"Na shiga uku! Muryar Innon ma ɗaukewa ku ka yi." Ta sake zabura.
Janyota Inno ta yi tana faɗin,
"Wai wani iya shege ne haka ƙauri da kare? Mu ne zaki mayar aljannu? Zaki buɗe idanuwan ko sai na kwakwkwaɗa miki mari?"
Da sauri ta ware idanunta, taga jama an gidan duk tsaye suna kallon ikon Allah.
Juyawa ta yi ta kuma kallon tibin, sai taga wasu masu jajayen kunnuwane ke ta tiƙar rawa.
'Ikon Allah! Wai na kwance ya faɗi. Ko ina ma mutumin ya nufa ne ohho.'
Ta tamabiyi zuciyarta.
"Tambayar ki ake, me ya faru kike kurma mana ihu a cikin gida?"
In ji Inno.
"Wani mutumi na gani yana ta ƙoƙarin fitowa a cikin kwalbar can, yana ta zuwa inda nake."
Duk suka sa dariyar ƙauyancin Abulle.
"Kedai akwai shashanci, tayaya mutum zai fito daga cikin tibi har yakamaki? Sai kace wani almara? Allah ya shiryeki. Inno muje ku ci abinci kada ki rasa moto tunda kinƙi kwana, kuma kince ba za ki jira Alhajin ba."
"Gaskiya kam!"
Duk suka nufi wajen da aka tanadar musu abincin.
'Ikon Allah! Shima wajen cin abincin har da wajenshi? To ko dai nan ne aljannar duniyar?'
Tana daɗi a zuciyarta tana ƙare ma wajen kallo.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
*(HWA)*
_Ummyn Yusrah_
_Ku yi haƙuri, idona ke ciwo._
_14_
Tunda Abulle ta yi ido biyu da shinkafar da ke cikin kulan da ake ta zuzzubashi kan faranti take haɗiyar yawu, inda tare yawun nan ake a ƙiyasi zai iya kaiwa durom biyu.
Iya zaƙuwa ta yi shi, sai dai sam Lubna bata lura da hakan ba, sai wani yanga take wajen zuba abincin, wani abun mamakin ma sai ɗigashi take tamkar za a ba yaron goye. Domin duka-duka baya wuce rabin farantin.
Ganin abun nata ba na ƙare ba ne, yasa Abulle hangame baki alamar hamma.
"To mai cikin zani! Idan kika haƙura yanzu za ki ci."
Kallon Innon ta yi, ta kuma maida hankalinta kan ƙwaryar shinkafar, tana kuma jin kamar ta wafce kular ta afka miya ta hau loda ma cikin ta.
"Ka ji Inno! Ai ta ma yi ƙoƙari, tun karin safe gashi har wajen daya da rabi ace bata buƙaci abinci ba? A kinsan da kamar wuya, idan ke kin iya daurewa ai ita da yaranta ba za ta iya ba."
Kallon Lubna ta yi ta ce,
"Ke ki yi ki ba mutane abinci da Allah. Kina abu kamar mai karyayyen hannu."
Ta gama zubawa ta zuba miya da ya sha namar kaji, ga kuma ruwan lemo a kofuna da kuma ruwan gora duk a wajen.
"Ina kos lo ɗin kuma? Ko gaya za mu ci abincin?
Hajiya ta watso mata tambaya.
Da sauri ta miƙe ta nufi hanyar kicin.
'Gosulo? Gaya? To duk wannan miya da ya rufe hinkahwar ta mene ne da za a ƙirashi da gaya? Mene ne kuma gosulon Ohho!'
Abulle ta gama tunanin zuci, lokacin da ta kai hannunta cikin farantin abincin tana shirin gauraya.
"A a, Zainab! Ba ga cokali a cikin abincin ba?"
Hajiya ta tambayeta.
"Hajiya da hannun yafi ɗebuwa ne, tattara ɗaya za ka yi ya cike hannu, cokali kuwa sai ka yi ta fafutukar tattarowa. Idan ma akai rashin sa a wajen juyewa a baki, duk sai ya zube, kinga ai gara in sa hannuna da Allah ya min ba hannun bature ba."
Ta faɗa tana afa shinkafar a bakinta.
"To, ki jira a kawo kos lo ɗin mana, ai ya fi daɗin ci da shi."
'Uhmm! Ke kika ma san wani gosulo. Ni burina in gama a ƙaramin.'
Ta faɗa a zuciyarta.
A fili kuma ta yi yaƙe, ta tsame hannu a farantin tana zaman jiran zuwan gosulo.
Takaici ne ya rufe Abulle lokacin da gosuln ya iso.
'Shegen sanabe! A ƙira abu da kwaɗon kabeji an wani lauyance masa suna wai gosulo. Koda yake ma naga an yi haɗe-haɗe, barin ji shi kuma ya yake, don in shiga gidan Mai Unguwa da sabon salo da sabon tsari. Na shigo Jinjin na waye.'
Wani murmushi ta yi, da ta tuno da gidan Sahibi Mai Unguwa.
"Nikam in ce ko dai Abulle ta ƙoshi ne? Kin bar abinci kin tafi karanto wasiƙar jaki."
Kallon Inno ta yi ba tare da ta amsa ta ba, ta hau laftar shinkafa da gosulo.
Sosai ta ci, don abun ya kai mata karo. Ya mata daɗi sosai, sai da kowa ya tashi ya bar Abulle a wajen tana ta lodar abinci kamar jaka.
Salamar da Inno suke yi da Hajiya Sabuwa ce ta ankarar da ita, ashe har tafiyar Innon ya tashi.
Ba shiri ta baro wajen cin abincin ta taho gun su Innon.
"Hajiya don Allah kada ku bar Abulle ta wuce sati biyu don akwai gidajen da za ta je sallama idan ta dawo."
"In Sha Allahu ba za ta wuce kwanakin ba. Lado direba zai kawota har gida."
"Allah ya kai mu lokacin."
"To, Allah ya tsare hanya ya kaiku lafiya, sai mun zo kenan."
Inno ta amsa da amin.
Sai da suka iso bakin get, Ɗayyabu ya ɗauki kayan da Hajiyar ta sallameta da shi suka nufi bakin hanya neman abun hawar da zai kai ta tashe.
Tana ta addu ar samun abun hawa don biyu ma ta wuce har da minti ishirin.
Allah kiyaye ya yi mata, tare da alƙawarin zuwa ɗaurin Abulle idan lokacin ya zo. A lokacin da ta shige cikin adaidaita bayan ta mishi bayanin inda zai kai ta.
****
Sai daf! Magriba Inno suka isa Mai Ludaya.
Mai mashin na sauƙeta a ƙofar gida, yara na ganinta rugo da gudu, suna ihu da murnar dawowar Inno kamar wacce ta shekara da tafiya.
2019
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
(*HWA*)
_Ummyn Yusrah_
_Ina miƙo saƙon godiya a gareku masoyana na tayani murna lashe gasar gajerun labarai da muka yi, wanda labarina mai suna Rashin Kula ya zo na ɗaya. Na gode sosai Allah ya bar zumunci._
_Haɗin Allah da Hazaƙa banda kalmar da zan iya faɗi a gareku, sai dai fatan alkairi da ƙaruwar so da ƙaunar juna da kuma ƙarin haɗin kai da zaman lafiya. Na gode sosai._
_15_
Tura ƙofar gidan ta yi, yaran suka ɗebi kayan da ta zo da shi suka shigar ciki.
"Inno! Inno!! Inno!!!"
Da sauri ta ɗago daga sunkuyon da ta yi da niyyar cire ɗan kwaɗon da aka maƙala a jikin ƙofar.
"Wannan wani irin ƙirane Muntari? Na hanaka irin hakan amma ba ka ji ko?"
Ƙarasowa ya yi yana haki ya ce,
"Inno kin san meye?"
Bai jira amssrta ba ya ci gaba da faɗin,
"Wai Hamusu ne ya ɓata, yau kwana uku kenan ba a ganshi ba."
"Ya ɓata!"
Ta faɗa cikin mamaki.
"Ya ɓata fa ka ce?"
"Eh, an nemeshi ba a sameshi ba."
"Yo allura ne shi da za ai ɓata a rasashi? Wataƙila dai ya yi tafiya ne ba a sani ba dai ko?"
"Wallahi ɓata ya yi Inno, Baba Marka ma fa yau sau biyu tana zuwa gidan nan bata samun kowa, ta ce idan kika dawo za ta zo."
Cikin yanayi na jimami da zancen Muntari ta buɗe ƙofar ta shiga ɗakin, zuciyarta na ta tufka da warwara.
Kaya kawai ta ajiye, ta fito ta nufi ɗakin girki don haɗa musu abincin dare, duk da kasancewar dare ya yi.
Tana tsaka da haɗa wuta a murhu ta ji ƙarar buɗe ƙofar gidan tare da sallama.
Fitowa ta yi, tare da amsawa.
"Inna Talle ke ce tafe?"
Inno ta tambaye tana mai isa gurin da tabarma ke jingine ta shimfida musu.
Wacce aka ƙira da Inna Tallen ta amsa da,
"Gani tafe, na taki sa a. Zuwana sau uku yau bakyanan wai kin je Jinjin."
Ta faɗa tana ƙara dogara sandar da ke riƙe a hannunta na dama, na hagun kuma riƙe da kafaɗar yaron da ya rakota.
"Bismillah Inna! ku zauna. Na je raka yarinyar nan ne gidan Baffanta, kinsan abun ya matso."
Hawayen da ya gangaro a idanunta da ke rufe ta sanya hannunta na hagu ta goge.
"Iro je ka yi wasa wajen yara, idan na gama zan yi ƙiranka mu koma."
Ta faɗa ma ɗan jagoran tana, lokacin da ta zauna akan tabarmar.
A guje ya ɗiba kamar dama jira yake yi.
Zama Inno ta yi daga can gefe ta gaida Inna Tallen.
Shiru ne ya ratsa wajen na ɗan lokaci kafin ta ce,
"Sai kuma kika ji ɓatan Hamusu?"
"I, ɗazu ina dawowa Muntari yake faɗamin. Na ɗauka ma shirmene kawai irin na yara."
Sake share hawayen tayi,
"Na rasa Hamusu! Na rasa shi, shine mun ɗa daya tilo da ke ɗawainiya da ni. Tunda aka ba Mai Unguwa yarinyar nan hankalinshi ya tashi, ya kasa sukuni."
Ta tsagaita tana mai jan zuciya, da alamar jin ciwon lamarin.
"Hamusu ya kasa samun nutsuwa, kullum cikin kuka yake. Babbar ma abum da ya dameshi ya ce sam Abulle ta ƙi ta tsaya ta saurareshi ya yi mata cikakken bayanin dalilil zuwanshi gurin 'yar gidan Mai Unguwa."
Sake dakatawa ta yi, tana sheshsheƙar kuka.
"Tun lokacin da ya zo min da zancen samun saɓaninsu da ita, da kuma ƙin saurareshi na ce ya bari in zo in yi muku bayani, amma ya hanani. Ya ce, yasan halin Abulle, fushi kawai ta ke yi, nan ba da jimawa ba za ta sauƙo."
Shiru ta yi, da alama hutawa take yi, gami da jimamin lamarin.
"Ikon Allah! Amma kuma Inna duk an bincika yanda ya kamata kuwa?"
Bata bata amsar tambayar ta ba, sai ma ci gaba da ta yi da zancen ta.
"Haka muka haƙura zuwa hucewar tata. Duk da haka yana ci-gaba da bibiyarta da bata haƙuri a duk inda suka haɗu. Ba mu kwatsam sai muka ji labarin cewar anba Mai Unguwa Abulle."
Tunowa da ta yi na halin da ɗan nata ya shiga ne ya sanya ta kuma tsagaitawa.
***
Tunda aka yi mata bayanin cewar ba wani mutumin da zai fito ta cikin akwatin talabijin ɗin ta saduda, don har hannunta aka iza bisa ƙwalbar don ta tabbatar.
Idanunta da duk wani imani nata ta tattara ta bar ma kwalbar, masu jajayen kunnuwane ke ta kaiwa da komowa daga mazan har matan.
Ita dai mamaki take yi, ganin kowa tsaf-tsaf! Tambayar kanta ma take anya ko suna yin dotti kuwa? Daga jikinsu har cikin garin nasu ba wani dauɗa kamar na garinsu.
Zabura ta yi kamar an tsikareta, yayin da cikinta ya sake murɗawa a karo na ba adadi.
Zuwa yanzu kam, ta kai magaryar tiƙewa domin kuwa ba abinda take buƙata baya ga kai ma banɗaki ziyara.
A guje ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saƙesu da Inno ɗazu, ta shige banɗaki.
Yadda Allah ya taimaketa ma, ɗazu kafin tafiyar Inno ta gwada mata randar kashi, ba don haka ba, da sai dai ta sauƙeshi a ƙasa.
Tana shiga ko kamar an buɗe bakin famfo, ga azabar murɗewar ciki.
A iya tunaninta dai tasan ba ta ci komai ba.
A wahale ta fito, hannunta na dama riƙe da ciki, na hagun kuma riƙe da ƙwanƙwasonta.
Zuwa yanzu duk ta gama laushi, don ta zaga ba adadi. Tun tana tafiya da ƙafafunta har ta dawo yi a durƙushe, ta sake dawowa da rarrafe. Ƙarshe ma mazauni kawai ta nema a cikin banɗakin domin abun ya ci tura.
2019
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
*NA*
*Ummyn Yusrah*
_Alhamdulillah! Ido da sauƙi, ras nake kallonku_
_16_
Jin shirun ya yi yawa ne yasa Hajiya Sabuwa ta tura Lubna ta dubota.
Tun daga ƙofar ɗakin ta ji iska ya canza, tana kutsa kai ta ji hanjin cikinta ya fara hautsinewa, take zuciyarta ta tashi da gudu ta fice tana yunƙirin amai.
Fallon ta dawo tana faɗin,
"Mami! Kin ji ɗakin baƙin can kuwa? Wallahi wari kamar mushen jaki."
Kallonta ta yi tana faɗin,
"Me ya mutu a ciki to? Ina ita Zainab ɗin take."
"Nikam ban ganta a ciki ba, ina sa kai na fito don wallahi mutum ya ɗauki tsawon lokaci a ciki zai iya tsintar kanshi a gadon asibiti."
"Ungo nan."
Ta ware yatsun hannunta alamar zagi.
"Kuma shine ba za ki shiga ki duba ko lafiya ba, kin ji yanayin wajen amma ki ka barta anan?"
Tsaki ta ja, ta miƙe.
"Baki da hankali."
Ɗakin ta nufa, tana kunna kai itama ta ci karo da baƙon al'amari.
Ba shiri ta ware ɗankwalin da ke kanta ta toshe hancinta hannu bibbiyu.
Ba Abulle babi dalilinta.
'Ina ta shiga? Warin meye haka a ɗakin nan?'
Ta tambayi kanta.
Har ta juya za ta fita sai kuma ta nufi banɗaki ko za ta ji motsinta.
Jin shiru ba alamar motsin mutum yasa Hajiya kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar. Shiru ta ji ba magana, ta sake ƙwanƙwasa shiru, kawai sai ta tura.
Abulle ta hango zaune kan randar ta, duk jiki ba ƙwari.
Yafutota ta yi da hannu, da yake idanunta na jikin ƙofar, duk bugawar nan da take tana jin ta, kawai kuzari ne bata da shi, duk gwuiwoyinta sun mutu.
Da ƙyar ta samu ta iya miƙewa, da taimakon bango ta samu isowa kusa da Hajiyar.
Riƙeta ta yi suka fito daga ɗakin gaba ɗaya, don tanason ta yi mata magana tana tsoron buɗe bakinta ta shaƙo wari, yanzun ma ba don ƙamshin turaren da ke jikin ɗankwalin ba da abun ba dama ne.
Tana jin warin, amma ba can ba.
Suna barin wajen ta buɗe hancin, ta ja wani dogon numfashi ta shaƙi iska mai ni'ima.
"Sannu Zainab! Me ya sameki haka, lokaci ɗaya duk kin fita hayyacinki?"
Suna tafiya tana tambayarta.
Ba bakin magana Abulle, gayu yau ansha wuya, an yi ma gosulo ɗiban karen mahaukaciya shi kuma ya yi mata lalata.
Kan kujerar falon ta yi mata masauƙi, tana yi mata sannu.
"Hajiya wannan yarinyar anya ba asibiti za a kai ta ba kuwa? Dubi yadda idanunta ya dawo kamar na kifin nan Kafi zuru lokaci ɗaya."
Cewar Afreen.
"Ai banma san me ke damunta ba, daga zuwa yau kuma sai ciwo? Me ke damunki Zainab? Ki yi magana idan na zuwa asibiti ne sai a tafi."
Hajiya ta tambayeta.
"Mami! Anya ba Salad ɗin da ta ci bane da yawa wa ɓata mata ciki?"
Kallo Abulle ta bi Lubna da shi mai haɗe da harara, da ƙyar take faɗin,
"Ni...kuma? Yaushe na ci wani salati? Wancan wancan kwaɗon da kuka cikashi da wasu shirgin ya waren ciki. "
Dariya suka sa dukansu.
Iya wuya ta kai don haushi, wato ma ba tsusaya mata za su yi ba, dariya za su yi mata don rashin tausayi.
Juya kai ta yi ta a basu baya.
" Wai salati?"
Ta sa dariya.
"Salad fa aka ce miki, ba salati ba."
'Koma dai mene ne ku kusa sani.'
"Ke Lubna ya isheki! Yanzu me ke damunki Zainab?"
"Ba komai."
Ta faɗa ba tare da ta juyo ba.
"Riƙeta Lubna ku je ɗakinki, ta yi wanka, Afreen ya kaiku Jinjin sifeshiyal hosfitan ko ruwa ne sai su ɗaura mata su bata magani ko zata ɗan ji ƙarfin jikinta."
"Mami! Ɗakina kuma? Kada ta je ta..."
"Zan ɗaura miki mari. Riƙeta ku je. Kai ƙaramin Asabe ta je ta tsaftace can ɗakin."
Haka ta kamata tana yatsina fuska suka tafi.
***
Inna Talle ta cigaba da magana.
"Ya shiga tashin hankali mara iyaka, haka na yi ta bashi baki ina bashi haƙuri kan cewar idan Allah ya nufa Abulle matarshi ce sai ƙaddara ta bashi ita, idan kuma ba matarshi bace ya yi haƙuri tun can haka Allah ya nufa, ya yi addu'ar zaɓi na gari. Ganin yadda nima na shiga damuwa a 'yan tsakanin nan ne yasa ya daina tunƙarata da zancen, ganin haka yasa nima na kwantar da hankali na."
Shiru ya sake ratsa tsakani.
Inno kan na tsugunne kan ƙafafunta da suka gama yi mata tsami, ta kasa magana sai sauraro kawai.
"Lokacin da Abulle ta fara zaga gidajen sallamar tafiya gidan aure lokacin ne muka tabbatar da ta fita rabonmu. Ranar ya zo ya ce mun sun haɗu da Abulle ta faɗa mishi maganganu marasa daɗi, ya kuma samu labarin tafiyarta Rangwangwan a ranar tunda ya fita ban ƙara jin motsin shi ba har yau, duk wanda na tambaya sai ya ce ya ganshi da kaya a leda ya ce za shi garin Dagal aike wajen kawunshi. Ashe tafiyar kenan..."
Kuka ya ci ƙarfinta.
"Shi ɗaya ke gareni, shike tallafamin saboda lalurata ta rashin ido, yau anwayi gari na rasashi, kukuma taku ɗiyar tana tare da ku..."
Ta sake rushewa da kuka.
Hamusu ya yi hijira a soyayya.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_Gwiwoyina a ƙasa, hannayena bisa kunnuwana ina neman afwa._
_17_
"Inna Talle ki yi haƙuri! Bansan komai game da wannan lamari ba, kwanaki dai Muntari ya faɗamin Abulle sun tafi faɗa a dandali ita da Indo, tun a lokacin na sa aka ƙirata na haneta da hakan. Ta kuma yi min bayanin dalilin faɗan cewar shi Hamusun yana zuwa gurinta, tun