Showing 3001 words to 6000 words out of 43727 words
Chapter 2 - ABULLE TA MAI UNGUWA 1to End Book Writing By Momy Yusra.txt
"To, a dawo lafiya."
Ummyn yusrah
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HWA*
_Ummyn Yusrah_
_7_
Duk suka nufi gida rai bai so haka ba, don basu samu sun raba raini da Abulle ba. A cewarsu tsoro ta ji tunda har ta k'i zuwa dandalin.
Itama ta nufi gida rai b'ace na rashin samun biyar buk'atar ta, don ta gama tsara yadda za ta luguɗen tsuntsayen kan Karime, tunda ta gaggaya mata magana. Don tasan halin Karime da son gulma da neman shiga, duk yanda aka yi ta je ta sanar ma Indo abun da ya faru. Kuma tabbas tasan tare za su zo, gashi iya zaman da suka yi a hanyar zuwa dandali ba wak'iyarsu.
Haka ta nufi gidan rai b'ace, tana shiga ba tare da sallama ba ta yanki hanyar bukkar d'akinta.
"Ke Abulle zo nan." Juyowa ta yi tana tura baki, ta dawo ta durƙusa kusa da Inno ba tare da ta ce komai ba.
"Me ya haɗaki da Indo 'yar gidan mai unguwa?"
"Ba komai."
"K'arya ki ke yi, za ki gayamin ko sai na sassab'a miki."
Sake turo baki gaba ta yi tana mai matsawa baya, don tasan abu mai sauk'ine Inno ta sauk'e mata wannan busheshshen hannun nata.
"Da gaske ba komai fa Inno."
"Amma ai an ce kun je fad'a ne."
"Lahhhh! In ji wani munafukin?"
"In ji ni."
"A a!" Tana mai gyad'a kai.
"Ahir d'inki wallahi na kuma jin, ko a ce mun kin je gidan mai unguwa wallahi sai na tara miki gajiya. Ɓacemun da gani shashasha kawai."
Wuf! Ta mik'e kamar tana jira, ta nufi d'aki zuciyarta fal tunanin me Inno take nufi da har zata hanata zuwa gidan mai unguwa? Kenan sun yi ban kwana da 'yar sati kenan ko kuwa? Taɓ! Da sake wai an ma mai zani ɗaya sata.
Washegari Mai Unguwa da sarkin fada.
Bayan 'yan zaman fadan sun watse ne mai unguwa ya ke tambayar Sarkin fadan.
"Kai! Wai yaya ne zancenmu?"
"Ai yallaɓai wannan fa inaga so yake ya hanamu. Bai wani bani k'wararren amsa ba, cewa ya yi in je zai zo har fadan idan sun zanta da shak'ik'anshi."
Shafe fuskarshi ya yi, tare da tsefe gashin gemunshi da ya gama zamewa fari.
"Ba komai, mu bishi a hankali, kasan 'yar shi ce. Mu da muke nema muke da hak'uri da k'ask'antar da kai. Yanzu dai abun da za a yi ita 'yarinyar zaka yi k'ok'arin shawo mana kanta."
"Yallaɓoi shi da ke k'ark'ashinmu ai shi zai bimu ba mu za mu bishi ba."
"Kai! Wa ya fad'a maka? Ai inda aka san darajar goro, nan ake nema masa ganye. Mu jira dai muji me Baba Ilun zai ce."
Cike da mamaki sarkin fada ya d'ago kanshi, ya kafe 'yan k'ananan idanuwanshi ya sauk'esu kan mai unguwar ya ce, "Am fad'o daga dabino, an fad'a rijiya. Yallaɓoi Ilune fa!"
"Eh, shi dai." "Ikon Allah! Wai na kwance ya fad'i."
Cike da mamaki Mai Unguwa ya bishi da kallo yana fad'in, "Wanda ya cika, ai ya mallakeka kai da iyalanka. Tunda naga d'iyar shi ina so ai dole in girmamashi."
Yana karkad'a kai ya ce "Um! Haka ne."
Nan suka ci gaba da zantawa.
Tafe take hannunta rik'e da ganyen rama, ta sayo a kasuwa za ta gida, sai ga Sarkin fada.
Wangale baki ya yi yana fad'in, "A a! Kaga manyan mata, kalan manyan mutane. Ina aka fito kuma?"
Cikin jin kunya ta durk'usa k'asa tana sunkuyar da kai, ta ce "Baba sarki ina wuni?" "Lafiya lau Abulle. Abulle ta mai unguwa."
Kunya ce ta sake kamata jin ya k'irata da Abulle ta Mai Unguwa, tasan tsokanar ta yake kan yadda aka ritsasu a fadar Mai Unguwa.
Mik'ewa ta yi za ta tafi, ya ce "Za a je gida ne?" "Eh." "To, a gaida Malam Ilu kuma ki fad'a mishi ina tuni da sak'onnan." "To." Kawai ta ce ta yi gaba.
_Ummyn Yusrah_
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HWA*
_Ummyn Yusrah_
_Ina mai baku hak'urin rashin jina da ku ka yi na 'yan kwanaki, jiki da jini._
_6_
"Kai Muntari, wai Ina Abulle ta yi ne tun ɗazu bata ɗau tallan Gyaɗar nan ta tafi dandali ba."
"Inno, wata Abuwar? Sai dai ki tura mata da shi can. Don tun da aka ida sallar magariba suka fice ita da Saratun gidan Shawai wai za su dandali faɗa."
"La ilaha illallahu! Faɗa dai? Ita da wa."
"Da Indon gidan Mai Unguwa."
"Na shiga magana! Yi maza ka je ka yo k'iranta tun kafin ta jawo mana magana a gari."
A guje ya fice, ya d'au hanyar dandali.
Abulle ne da Saratu ke tsaye a kan hanyar zuwa dandali, jiran isowar Indo kawai suke yi, sai dai shiru har yanzun ba alamar zuwansu da tawagarta.
"Sarai! Anya ko Indo zata zo yau kuwa?"
"Yo, nima shi nake tunani, har yanzu banga ɓullowarsu ba."
"To, ya za a yi?"
"Binta zamu yi har gida, mu yi kamar mun biyo mata zuwa dandali, idan ta fito mu tari mu tara mata gajiya, mu fitar mata da jini da majina, daga baka har hanci."
"Ke! Kina hauka ko? To Yasin ba dani zaki je ba. Kin san wannan me sharb'eb'iyar dorinar idan ya rik'emu sai d'an burinmu."
"Haka fa! To kawai mu yi jiranta."
"Ke nifa ba Indon ce damuwata a yanzu ba."
"Hamusu ko?"
"Hamusu? Hamuso. Ni baya gabana ma yanzu, don naga idonshi rawa ya ke yi, baya tsayuwa waje guda. Yaje can su k'arata da Indon."
"Kuma don iskanci shine kika tsaidamu kan hanya kamar wasu ram-santi na cikin garin Jinjin."
Dariya Abuwa ta tuntsire da shi, har da durk'usawa k'asa tana fad'in.
"Sarai meye kuma wani rafsanti?"
Tsaki ta ja tana hararar Abuwar, "Matsalata da ke k'auyanci. Ram-santi ake cewa dallah. Lokacin zuwanmu cikin garin Jinjin bikin 'yar gidan Baffana Tallene muka wuce wasu da kayan sarki tsaye a kan kwalta suna bincike, dana tambayi su kuma su waye? nagansu da kaya daban ba irin na holis d'in da suke zuwa kama mai laifi bane a garin Mai ludaya ba. Shine aka ce mun wai Ram-santi sunansu."
Cike da mamaki Abuwa ta ce,
"Yo shi cikin Jinjin ai komai gani ake, Allah dai ya kai ni nima inga yarda take."
"Amin dai, inda kuna da dangi a can."
Kallon sama da k'asa gami da yatsina fusa ta bita da shi, "Mu a suwa da zamu yi dangi a birni? Ku da ke da dangi ai shiyasa naga kullum k'afarku na can, dad'in abun dai k'auye dai tushen birni ne, idan aka bi diddigi su Baffa a cikin k'auyen mai ludaya za a bankad'osu." Ta k'arashe maganar tana mai d'auke kanta daga kan Saratun.
"Ikon Allah! Daga magana kuma sai cibi ya zama k'ari? To, Allah ya baki hak'uri. Kinga tafiyata." Ta k'arashe maganar tana kunce mayafinta da ta d'aure a k'ugunta shirin fad'a.
"Sauk'a lafiya, agaida na gaba."
Sak'e-sak'e tashiga ya azuciyarta, na takoma gida ne? Ko tawuce dandali? Idan kuma ta je dandalin ba wani burgewa abun za ta gani ba.
Har ta juya zata yi gida, sai kuma ta sake juyowa ta nufi hanyar dandalin.
Tana gab da isa ne ta ji an k'wala mata k'ira, ko bata juyo ba ta shaida muryar mai k'iran nata.
Juyowa ta yi don ganin dalilin k'iran nata.
Hasken farin watan da ya haskaka duniya ne, ya hasko mata fuskar Muntari da yake ta zuba haki dalilin gudun da ya ci.
Tsaki ta ja kafin ta ce, "Lafiya ka ke k'wala min uwar k'ira a daren nan?"
"Inno ce ta ce in zo in k'iraki, na manta na tsaya yin Langa dasu Sabitu. Sai da naga wucewar Saratu na tuna Aradu."
"Jeka da Allah ina zuwa."
Ta juya zata tafi.
"Alk'ur an ta ce ki zo yanzu-yanzu."
Juyowa ta yi ta zabga mishi harara sannan ta d'au hanyar gida.
Indo da Karime da k'awayensu guda biyu da suka iso Dandalin tun da magribar fari suna jiran zuwan Abulle shiru ba labarinta, yasa suka fara taraddadin zuwan nata.
"Karime anya ko Abulle zata zo?"
"Tsaf zata zo in dai Abulle ce, kinsanta bata fashin zuwa dandali sai da dalili mai k'arfi, balle kuma yau a cike take, mu jira muga zuwanta."
"Ke nifa tunda kika zo gida ki ka gayan zancen nan nake tsuma, Allah-Allah nake ta iso. Aradu in sunkuya na kwashi k'afarta ku bita da duka."
"Ke, ni kayan tallana nake tunani a gidanku."
"Yanzu kika tuno da tallan naki?" Inji d'aya k'awar tasu.
"Lantana ai ina nan hankalina na can ne, tun fa rana dana fita ban koma gida ba."
"Ni fa kunga tafiyata ma zan yi."
"Ke Sahura ai dama ruwan ciki ne da ke."
"Hu umm! Ku ji Indon nan? Kuma dare ya yi sai in yi ta zaman jiran gawon shanu ko? To, ba da ni ba. Sai kun zo." Ta juya ta yi tafiyar ta.
Karime ta ce
"Kai, mu tafinku muna, gobe za ta fito ne, sai mun kwashi 'yan kallo."
Duk suka amsa da, "Mu je."
_Ummyn Yusrah_
[9/11, 9:31 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*© UMMYN YUSRAH*
*8*
Da dare, Abulle suna zaune a kan tabarmar da suka shimfiɗa a ƙarƙashin barandar ɗakin Inno, suna cikin tuwon dare.
Wani kafcecen loma Abullen ta yanko, ta iza shi cikin bakinta, ji ka ke ya ba da sautin "Muƙutt!" Sanadiyar haɗiyar da ta yi masa ba tare da ta tsaya taunawa ba.
Haka ta yi ta wurga lomomin nan, tana haɗiɗɗiyar su, ba tare da ta tsaya ɓata lokaci wajen taune su ba.
Ga zufar da ta gama wanke mata fuska, wanda har ɗiga ya ke a ƙasa.
Inno da ke can gefe kan kujerar tsuguno, ta ɗago fitilar ƙwan da ke gefen ta ta haska fuskar Abullen, a daidai lokacin da ta yanko wani tiƙeken loma ta zazzaro idanuwanta waje masu kama da ƙwan zabbi, tana shirin wurgashi baka, ganin hasken fitilar yasa ta tsagaitawa tana mai kallon Innon da ta saki baki tana binta da idanuwanta kafin ta ce.
"Ikon Allah! Wai ke a rayuwarki ba ki iya cin abinci cikin nutsuwa ba ne? Ki duba dai ki gani, ke ɗaya ke ci amma Allah-Allah ki ke ya ƙare, kamar wata mai warwaso kina tsoron kada a ƙwashe a barki hannu rabbana."
Turo baki ta yi gaba ta yi tana faɗin,
"Inno! Nifa a hankali na ke cikin abincina."
"Hoɗijam! A hakan?" Ta tambayeta.
"Eh." Ta bata amsa a taƙaice gami da wurga lomar da ta ke ta juya shi a hannunta.
"Ummmhh! Lallai da aiki. Da alama gidan Sarkin noma za a wurgaki, domin wannan irin ci naki ba dai gidan rago ba."
Ta faɗa a lokacin da ta ke ajiye fitilar da ke hannunta a ƙasa.
"Shiyasa kullum ki ke ta hawa kamar farashi ai, daidai da sakan guda ba ki fatan bakin ki ya zauna shiru, ko da yaushe yana cikin motsi hayayam-hayayam. Ki sama ma kan ki lafiya tun wuri ina gaya miki, ba ko wani namiji ne zai iya da wannan cin naki ba ina gaya miki."
Ta ƙarashe maganar tana mai ci gaba da saƙar hular da ta ke yi da ƙwarashi.
"Inno! Shima fa cin nan lafiya ne aradu, idan mutum ba ya lafiya ina ya ga wani bakin cikin abinci, Allah duk randa aka kai ni gidan da ba abinci kullum gida zan riƙa turo da ƙwarya ta ana yi mun zubi, gara ma tun da wuri kada ku cire ƙwaryata ku barni a layi." Tana maganar ne tana lashe hannunta da ta gama damalmale shi da miya, tana gamawa ta kuma rarumo kwanon tuwon ta hau suɗewa.
Inno ta ce, "Wannan ai an yi, ba a yi ba kenan. An sai da akuya, ta dawo kuma tana ci mana danga."
Ba ta kula ta ba sai ma ci gaba da ta yi da suɗe kwanon, wanda baya buƙatar wani ruwa da omo wajen wanke shi, domin yawun Abullen ya wanke shi tas.
"Ko da yake shi gwanin naki ma Hamusu rago ne, tunda tun zamanin ƙuruciya da aka bashi gwaji a kan kaza ya gaza riƙe ta, duk da yake ita ɗin dabba ce, ina kuma ga an bashi ɗan mutum?"
"Taɓ! To ni me ruwana da wani Hamusu kuma? Can, su ƙarata da Indo ƴar gidan mai unguwa ni na wuce ajinsa"
"Iyee! Zamani. Kukam dai yaran yau sai dai abarku, kina gabana ko kunya ba ki ji."
"Yo, to Inno naga dai zancen nan ke ki ka fara yowa ita, ni ko na ɗora."
"Uhmmm! Haka ne."
"Inno shi kiwon kazar kuma ta me cece ne da na ji kin ce an ba shi Hamusun ya kasa riƙon ta?"
Kallon ta ta yi, kafin ta ce, "Ita wannan kazar da ki ka ga ana ba duk wani ɗa namiji da ke wannan ƙauyen kiwo, ana bashi ne don gwajin yadda zai iya riƙe iyali. Idan aka ga yana kula da ita wannan kazar sosai, to a hankali za a bashi tunkiya, kinsan ita tunkiya uwar tamɓele ce, idan nan ma aka ga ba laifi, sai a yi mishi canji zuwa rago, da haka dai har zuwa kan saniya, idan aka ga ya iya kiwo to anan ne za a bashi mata. Idan kuma shiririta ya sa a gaba to sai dai a wurgashi gona kuma ya yi ta fama."
Baki ta saki tana jin jawabin Inno har ta dire, ita ma ta jefo mata tambaya da faɗin, " Kuma Inno shi wannan gwagwarmayar duk mutum ɗin na ƙarami ne zai yi shi? Kuma dama ba su noma ne sai sun gaza riƙon dabba?"
Ummyn yusrah
[9/13, 4:57 PM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
*9*
"Suna yi mana, idan yaro ya kai munzali kuma sai a yi mishi auren ladan noma." Cewar Inno.
Keɓe baki Abullen ta yi ta ce,
"Hu'umm! Sun ji daɗinsu."
Shigowa gidan ya yi, ba ko sallama sai ma bambamin faɗa da ya ke ta yi har ya iso inda suke zaune, ya ja ya tsaya.
Bayan shi ya yi ma masauƙi da garun ginin jar ƙasar da ke bayan shi, yana huci da huro iska daga cikin bakin shi, ya harɗe hannayeshi bisa ƙirjinshi yayin da ya ɗago ƙafarshi ɗaya ya dogare ta jikin garun, ɗayar kuma tana ajiye a ƙasa.
"Barka da shigowa Malam! Yanzu na ke neman Muntari ya kai muku abincinku waje, baya nan, ina ga ya fita dandali wasa ne."
Tsaki ya ja, ya ce, "Wa ke batun abinci kuma."
"To, mai kuma ya faru? Na ji ka shigo kana ta bambamin faɗa."
"Sarkin fada ne ya bi duk ya matsamin da zancen auren nan wallahi, ba dama ya ganni, duk ya bi ya hanani sukuni."
Jin an ambaci Sarkin fada yasa Abulle ta zaburo tana faɗin, "Walle ɗazu ma ya aikoni, wai ko yana maka tuni ko me na dai manta."
Inno ta galla mata harara, "Ina kuka haɗu da shi? Ko binshi fadar ki ka yi?"
Zaro ido ta yi alamar tsoro, "Walle Inno a hanya muka haɗu, da na je sayo rama a kasuwa ina dawowa."
"To, dama da kin ganshi kafin ya hangoki, ki maza ki sake hanya, kin ji na faɗa miki."
"Inno!"
"Innon gidanku." Ta yi mata daƙuwa da yatsunta biyar.
"To, Malam yanzu meye abun yi?"
Ƙarasowa ya yi, ya zauna a gefen tabarmar da Abullen ke zaune.
Da sauri ta tashi ta koma ƙasa ta zauna.
"Ni kaina na rasa ta cewa, da ina tunanin in ce mata cikin manemanta ta fidda gwani kawai, idan na je sai in sanar musu tana da gwaninta dama a hannu."
Cewar Ilun mahaifin Abulle.
"Hakan ma ya yi, ke cikin maneman naki waye gwaninki?" Ta jefa ma Abulle tambayar.
"Ni... Ni... Ba kowa."
"Ba kowa ki kace?"
"Ba kowa Inno."
"Umm! To kaji Malam. Da alama rabon mai unguwar ne."
"Ke Inno! Hauka nake zan ɗau Abulle in ba sa ar kakana?"
"To Malam, idan rabon shi ce fa?"
"Bama rabon shi ba ne."
"U um fa Malam! Kasan fa rabo ajali ne, ba mu san me Allah ke nufi kan hakan ba. Idan dai ita Abullen tana so ai shikennan."
Jinjina kai ya yi, kafin ya ce, "Kuma fa kin kashen jiki, kince Allah a lamarin dole in saduda tunda ita ɗin ma bata da wani tsayayye."
"Ke Abulle! Mai Unguwa ne ya turo Sarkin fada cewar yana son aurenki, me kika ce?"
Sai yanzu ta gane kan wa suke zancen su, domin da duk a baibai take fuskantar zancen nasu.
'Wai yau ni Mai Unguwa ke son aure? Lallai ina da sa a.'
Zancen zuciyarta kenan, kafin ta sake dulmuya wata duniyar tunanin.
Hangota ta yi a gidan Mai Unguwa, an dire mata wani ƙaton kwanon kaya shaƙe da dafaffiyar shinkafa 'yar gwamnati mai santsi da miyar ja, ga kuma ƙatuwar kaza a kai, gefe kuma ga babban kwanon sha cike da sassanyar ruwan ranar ƙasa.
Sake kallon ƙeta ta yi ma hinkahwar a karo na ba adadi, tana kuma tuna irin cin walaƙancin da za ta yi mishi.
Sake ware ɗaurin zaninta ta yi don yayi sako-sako gudun kada cikin nata ya yi saurin cika, ta kalmashe ƙafafunta waje guda, ta zura hannunta ciki ta gauraya gefe guda, ta ciko hannunta ta kai shi zuwa bakinta.
"Kingani ko Inno! Na gaya miki yarinyar nan ba son auren nan za ta yi ba, gashi ko amsa bata bamu ba."
Maganar da mahaifinta ya yi, shi ya hanata jin ɗanɗanon hinkahwar da ta shaƙe hannunta da shi, maganar ce kuma ta yi silar dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.
Ta ji takaicin rashin ɗanɗana girkin, sai dai duk ranar da Allah ya kai damo ga harawa ba ƙaramin ɓarna za ta tafka ba, cin huce haushi za ta yi mishi.
Murmushi ta yi, wanda sautinshi ya fito, "Kin gani ko Inno? Kuka fa ta ke yi, gara a janye maganar nan idan yaso a jira har ta samu gwani."
Cewar Malam Ilu.
Salallami Inno ta sanya tare da tafa hannayenta, ta iza ɗaya a haɓarta ɗayan kuma ta ɗago fitilar dake ajiye ta haska fuskar Abullen da shi.
Kallo suka bita da shi, fuskokinsu fal mamaki.
Madadin suga hawaye ya wanke fuskarta, murmushi ne ke ta bayyana a fuskarta, idanunta kuma a rufe.
"Ke Abulle! Lafiyar ki kuwa?"
Inno ta tambayeta.
Da sauri ta buɗe idon ta sunkuyar da kai