Showing 6001 words to 9000 words out of 48129 words

Chapter 3 - NAMIJI BAYA KADAN 1 to End By Aisha Garkuwa.txt

Allah ne kuma insha Allah gobe zanje muyi mgn da Abban naku
Sannan ka dena damuwa da batun masu zuwa gareta in dai rebonka ce ba makawa zaka samu".


Shi kuwa kai ya sunkuyar cikin jin dad'i da k'arfin guiwa yace
"Baba Amman da yau za,ayiwa Abba mgn dan fa su iyayen Nazir d'in sunce goben zasuzo ai kuma gwara mu rigasu".


murmushi yayi tare da kallon yaron yana tunani shiko wanne irin hallitta Allah ya mishi
Cikin dan fara,a yace
" toh yau zanzo da dare"
Toh yace cikin jin dad'i tare da mik'ewa zai fita
Adam da yanzu ya shigo kuma yaji mgnar tasu kad'an cikin mmk yabi Mahmoud d'in da ido shiko hannu ya mik'a mai suka gaisa sannan ya juya gun
Goggo Zahra ya kalleta a dan sokane
ya karya wuya cikin sanyi yace
"Ayyah Goggo Zahra baki yi Allah sanya Alkhairi cikin Auren ba "
dariya sukayi baki d'aya Adam yace
"Tab har anyi Auren kenan har kuna Neman sanya Alkhairi mijin bazawara manya"


Juyawa yayi gun Adam d'in cikin shafa kanshi yace
"Sunnah ce babba Annabinmu ma da bazawara ya fara".


Mlm ne da Goggo Zahra sukace
" wannan haka yake
Allah baka ladan raya sunnar"


Amin yace tare da yi musu slm ya tafi.




A wunin ranar Mahmoud ya wuni cikin farin ciki sai dai kuma yakanji far gaba bai San ya iyayenshi zasu d'auki zancen ba sannan uwa uba Khadijan,


Cikin wunin ya kuma gano yadda zai boye zancen gareta in yaso sai taji abin daga baya,




Da dare bayan anyi sallan inshah
Malam Abubakar ya fito cikin kamala bai zame ko ina ba sai
gidan Alhj Ibrahim.

cikin mutun ta juna suka isa parlon shi


Bayan sun gaggaisa malam ya gyara zama tare da gyaran murya cikin nitsuwa yace.


"Ibrahim wata mgn ce mai mahinmanci ke tafe dani fatan zamu samu fahimtar juna"
Shima zaman ya gyara tare da juyowa gareshi cikin kula yace.


"Insha Allah zamu fahimci juna".


Kai ya jinjina sannan cikin hikima ya koro mai jawabin da Mahmoud din yaje ya fad'a mai,


Shiru Abban yayi tare da jinjina kai sannan ya kalli
Mlma Abubakar tare da sauk'e ajiyar zuciya yace.


" Abubakar yanzu kai me ka fahimta a zancen Yaron nan,?
Yanzu ina Mahmoud ina Aure?
yanzu anyama Mahmoud yasan me ake cewa Aure?
Abubakar Yanzu nefa Mahmoud d'in ya jona University anya yaro nan yasan me ake cewa Aure ai ko yayunshi mata ban tab'a Aurar dasuba har sai sun gama secondary sun fara zuwa F,C,E kafin suke Aure"


Tunda ya fara mgnar Malam Abubakar ke binshi da ido har saida yazo k'arshe sannan yace.


"Amman nayi mmkin jin zantu kan nan daga bakinka shin
A sheri,a ace akece sai yaro yayi digiri zaiyi Aure?
Shin Wanne matsayin da sharad'u musulunci ya gindayar in NAMIJI ko mace sun kai za,a basu damar suyi Auren?
Shin a cikin su wanne Mahmoud ya gaza bai kaiba?
Ibrahim ase baza ka marawa Mahmoudu baya ba ko dan a kauda shi daga sharrin zina, shin baka tsoro yaron fa ya fito fili yace Aure yake so in mun hanashi zai iya aikata komai
shin kana tunanin bazai san ya zai zauna da maceba?
Ko ka manta Mahmoudu yaro ne mai ilimin Addini duk abin da kake tunani bai saniba K'ur,ani da hadisai sun sanar dashi,
Haba Ibrahim ase kaima kana da tuaninnan Na tauye rayuwar yaro ko yarinya Wai da sunan sai Sunyi karatu mai zurfi kuma kana sane da illan da hakan ke jazawa yaran mu shin kasan irin halittar da Allah ya masane? kana da yakinin zai iya danne buk'a tarsa har yayi shekarun da kake tunani? Kuma kana da dukiyar da damar da zaka warewa rayuwarsa da matarsa komai cikin wadata haba Ibrahim kayi tunani mu a shekara nawa iyayenmu suka Aura mana mata"?


Tun da ya fara jero mai tabb'ayoyi sai shiru yayi mgnganusa Na ratsashi cikin sanyi ya rink'a gyad'a kai,
alamar a,a a,a.


Shi kuwa mlm cikin sanyi yace.

"Toh matuk'ar dai ba so kake muyi sanadin yaduwar barna da fasadiba to ayi mishi abinda yake buk'atar dan wlh illace baba iyaye su kafe kan yayansu bazasu yi Aureba har sai sunkai wani mataki a karatu boko hakan Na jawo yawan barna da fasadi ".


Kai ya kinji yace.
"Tohhh"
ganin kamar har yanzu bai nitsuba da abin gaba yasa
Mlm Abubakar ciro woyarsa
Mahmoud d'in ya kira yana d'agawa yace.


"Kazo gani a Parlon Abban ka".


Toh ya amsa tare da tasowa cikin happy ya iso parlon,


Yana shiga gaban su ya zauna a kasa kan carpet cinkin girmamawa yace.


" Baba gani"


Abba kam ido ya tsura mai cikin mmk
Shiko kai ya sad'a k'asa.


A hankali Baba yace.


"Yana da kyau Abban ka yaji buk'a tarka daga bakinka"


Kai ya kuma shafawa sannan a hankali yace.


"Abba dama eh ni dama Abba ni Aure nake sonyi kuma Khadija ce nake so sannan mun gama mgn da ita ni nafi son ayi Auren nan kusa".


Abba kam tunda ya fara mgnar ya bud'e baki da mmk yana binshi da ido shi har tsoro Yaron ya bashi (wai Aure nake so)


Mlm Abubakar ne yace.
"Toh Ibrahim kaji ko"?
Ehh yace cikin sanyi sannan ya kalleshi cikin kura mai ido yace.


" Mahmoud Aure kake so ko"?
Kai ya gyad'a tare da cewa "ehh"


Abin yanzu dariya ya bawa Abba shiyasa cikin sanyi yace.


"Wato kun gama shirya zancenku kai da Khadijan. ita Khadijan ta yarda da Auren"?


_Kai Mahmoud ya isa dan duniyar domain ta kar karewa yayi ya rink'a tsara zance yadda abin zai tafin mai dai-dai_


Gyara zama yayi cikin sanyi yace.
"Yauwa Abba daman mun gama mgnar da ita ita tace duk abinda za,ayi kar a kirata Dan kunya yakeji ta kuma amince dani shiyasa ma tak'i komawa gidan Sulaiman"


Ido Abban ya tsura mai cikin son gane gskyar zance sai kuma yace "Khadijan ko ta amince"?


Ehh yace cikin k'arfin hali
Baba ne ya kalleshi cikin sanyi yace.
" toh tashi ka tafi"
toh yace tare da mik'ewa ya fice abin shi.


Mlm Abubakar ya juyo gunshi cikin mgn irin ta manya yace.


"Toh ka ga da idon ka dai tunda sun dai-daita Kansu to kar a shiga hak'insu
Mgnar. Khadija kuwa ni inaga kunya takeji ace ita bazawara zata Auri saurayi kuma k'aninta dan haka kar a tuntub'eta da zancen
In inna samu zama zama nanda kwana 4 zanje gun Alhj Sani muyi mgnar zanzo mu tafi da kai din
Kuma ko iyayensu mata a bari sai mun gama komai a gaya musu kasan zasu iya yin k'ananan mgn ganu a kai.


A haka suka Ajiye shawara shiko Mahmoud duk abinda ake ciki mlm kan kirashi ya gaya mai.


sannan sunje sun samu Baba Sani
Shi ba Abin da yace sai sanya Alkhairi.


Sannan sun tsaida zance za,a daura Auren randa za,ayi na Amira.


Shi kuwa Mahmoud yana sane da komai Amman baiyi gigin gayawa Khadijan da itako bata san komai ba akan zancen.


Sai dai yana yawan shige mata shak'uwa kuma mai k'arfi ta k'ara shiga tsaka ninsu.




Yau ta kama jumma,a kuma gone asabar ne ta kama Daurin Auren Amira da Amir d'inta sai kuma Mahmoud da Amarya Khadija da bata san da zancen ba.


Ran jumman kuma akayi walima mai k'aya tarwa.


Da daddere bayan sallan insha,a
Khadija ne cikin sauri ta nufi d'akin su Mahmoud d'in cikin d'an had'e fuska ta lek'a parlon hank'oshi tayi yana kwance kan 3 str daga shi sai 3 qtr a jikinshi.
ganin shi hakan sai taji wani irin nauyi ya rufeta da sauri ta juya tana.


Dan Allah ka fito kazo ka kaini
Target zan karbo dinku nanmu gun Yaxid yace yana jirana".


Cikin kasala ya mik'e tare da rataye rigarsa a kafad'a ya fito ya tsaya a gabanta da sauri ta kuma juyawa dan wlh bata son ganin shi hakan
Shi kuwa rigar yasa cikin kasala yace.


"Muje ko".


Ita kam tuni tayi gaba cikin mota ko cikin sanyi ya dan rink'a mata hira har sukaje suka karbo dinkunan suka juyo suna dawowa.
tuk'in yake cikin sanyi da k'orewa tafiya yake a hankali sun mik'e kan titin da zai maidasu cikin Yola a hankali kamar maiyin rad'a cikin kasala da wani yanayi ya juyo yana mata wani irin kallo yace.


Khady gobe fa...






By Garkuwan Fulani
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 6⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Pure moment of life writer's
P.m.l.w


_Dedicated 2 my lovely Namecy Aysha Aliyu tsamiya😍😘😍😘😍_




Juyowa ya kuma yi gareta tare da tsura mata ido,
Itama idon ta zuba mai tare da cewa


"aha inajin ka"


A hankali ya k'ara rege tafiyar tare da maida hankali shi gareta cikin tsareta da ido yace.


"Khadija gobe fa zanyi Aure".


Da sauri ta cilla mai harara tare da tab'e baki ta kuma juyo cikin yanayin kai yaro ne tace.


" Auren ai ba wasan yara bane kuma ba iya zance bane bare kace ka iya kai yanzu ko nauyin kalmar bakaji ba"?.


Tun da ta fara mgn ya tsura mata ido bakinta kawai yake kallo sai da tai shiru sannan yace.


"Na tab'a miki irin zancen nanne"?.


Kai ta girgiza sannan ya k'ara juyowa yana fuskantan ta yace.


" Toh wlh ki yarda gobe zanyi Aure insha Allah tare dana Amira za,a daura".


Itama kara juyowa tayi cikin tab'e fuska tace.


"Ya za,ayi na yarda tunda ban tab'a sanin kana neman Aure ba sannan banji zancen daga bak'in manya ba hakazali ka ai da sauran ka ina kai ina Aure shin kama san mene Auren"?.


Fuska ya had'e nan da can ya kafeta da ido cikin had'e murya yace.
" ki shiga taitayinki fa da gaya min duk mgnar da tazo bakinki wlh zaki k'ona kanki ina gaya miki ki kama bakinki da cemin yaro tam".


"Toh fa Sannu yayana ai kam dole nace yaro kai ba yaron bane"?.


sai ta kuma sa dariya ta nunashi da yatsa sai ta kuma dariya tana
fad'in.


" kalle ka fa yaro ko rink'a baka faraba bare ka gama wai shine harda wani zakayi Aure Amman dai sai in Yar k'auye zaka Aura ko? yar 12 years kai wlh kai kam ma ba wanda zai baka yarsa".


Dariya take sosai tana fad'i mai abinda bai sonji.


Cikin tunzura ya damk'o hannu ta ya matse da k'arfi har saida taji hannun ya bada sauti das sannan zafi ya ratsata har saida ta zaro ido woje tare da cewa.


"Wayyo hannuna kai Mahmoud karyani zakayi ka sake min hannu kaji mugunta dan na fad'i gsky".


Shi kuwa ido ya tsura mata sannan ya k'ara matsota yana mai piki-piki da ido tuni fuskarsa ta juya k'ara matsota yayi har kamar zai danneta jikin marfin motar murya na rawa yace.


" Wlh kina jawa kanki fitinar da bazaki iyaba kici gaba da cemin yaro wata ran zakiyi nadama".


Ita dai hannu daya tasa tana kai da Allah sakar min hannu dan ni ba Sa,ar kabace sai ka jira y'ar shilan da zaka sauran ita zaka zarewa ido bani ba ehe"?


dariya mugunta yayi sannan ya fizgota saida ta fad'a jikinshi ya matseta cikin k'irjinshi lkci d'aya ya fara sake kan mota suna k'ok'arin afkawa cikin ramin.
Ita kuwa cikin jin zafin yadda ya matan da takaici wannan wanne irin rainine ko iskanci hannu tasa ta hankad'eshi amman ta kasa k'watar kanta cikin takaicin tace.


"Me haka Mahmoud ban son iskanci ni Sa,arkace ko rashin kunya zaka nuna min aikin banza yaro dan kaga ana wasa da kai sai kuma raini ya shiga".


Kicini ya take ta k'wace kanta amman ta kasa sai shi da kanshi ya saketa tare da juyawa ya kalli titi.


Habawa ita kam Khadija fad'a take kamar ta mareshi dan ya cikata tab.


Shi kuwa shiru yayi yana tuk'i sai zufan da ya keto mai duk da sanyin AC hannu yenshi kab rawa suke. So yake yayi mgn Amman kuma ya kasa bazai iyaba ko yace zai maganar zatake fita da i ina shiyasa sai kawai ya kame lips inshi na k'asa yai ta tsotsa yana jinta tana ta bala,i harda cewa.
" ai kai dole amaka Auren tun baka jamana abin kunya ba aikin banza aikin wofi"


Shi kam bai kulaba har suka dawa ana bud'e musu gate yana shiga ko parking bai k'arisa yiba ta kama k'ok'arin bud'e mota zata fita shiko komawa yayi ya jingina jikin sit sai numfashi yake fiddawa cikin sanyi.


Cikin fad'a tace.
"Ka bud'e min in fita dan ina da abinyi"


Cikin wani irin murya yace .


"In in nak'ifa, ina gaya miki kibini a hankali"


sun kuyowa tayi zata dannan pin d'in dan ta bud'e.
Cikin isa yace.
"Allah in kika yadda kika tab'ani wlh zakisha matsa, ba abinda kika iya sai baki ai tida kince ban fara rink'a bama bare Na gama, ako bai kamata ki kasa k'wace kanki a hannuna ba"


Komawa tayi ta zauna danji zai kuma matseta cikin had'e fuska tace.
"Wlh ka bud'e min banson mgn da kai"


Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya bud'e mata tana fita.
ta juyo ta watsamai harara tare da Jan tsaki ta juya ta tafi ko kayan bata dauka ba,


Shima fita yayi tare da binta yana.


" ba laifinki bane Amman time na zuwa zaki bari"


A bakin shiga cikin gidan suka had'u dasu Abba da malam Abubakar Na fitowa


tare suka dan kauce suka basu hanya tare da gaishesu mlm Abubakar ya fara amsawa cikin girma yace
"Allah ya muku albarka yasa haske a rayuwarku".


Tare suka amsa shi oga yasan wacce Addu,ar akayi musu itako ta dauka a matsayin su na yaransune suka musu Addu,arga,


Suna wucewa Abba yace "kai Mahmoud zonan"


Ita kuwa cikin gida ta shige abita.


Tana shiga parlon Anty ta shiga inda ta samu su Anty da Su Goggo Zahra gasu Aysha dasu Rayhana da Fatima dama duk sunzo Anty Rayhana tana yar fawa Amarya Amira kitso suna ta hira da nishad'i tana shiga suka bige da hira suna ta raha, har dare yayi sanyi sannan suka farashirin bacci Fatima ce ta kalli Khadija cikin kula tace.


"Ni kam Khadija ina dinkin namu kin dawo shiru kinsan harda nasu Mami da Anty sannan harda na Amarya"


Tsaki ta dan ja tare da kwanciya tana dan k'ulle igiyar rigar baccin ta
tace
"Kayan suna cikin motar Mahmoud sai goben zai kawosu "
Ajiyar zuciya Anty tayi tare da cewa "har naji tsoro kar bai d'inka ba"


Dariya sukayi tare da kwanciya.




*Kashe gari*
da safe misalin karfe 11 k'ofar gidan Alhj Ibrahim cike yake mak'il da Al,ummar Annabi manyan mutanen masu fad'a aji da malamai manya da matasa da yara tako ina a cike ake.


Haka kuwa cikin gida
ma makil yake yan uwa da abokan arziki.
Su Khadija an tasa Amira a gaba dasu Fatima suna ta mata tsiya ita ko tuni ta nemi idannunta.


Cikin juyawar iska sautin d'aura Auren _Mahmoud Ibrahim Mahmoud_ da *Khadija Sani Mahmoud* ya ratsa kunnuwan illahirin mutanen dake cikin gidan cikin mmk da Al,ajabi aka rink'a kallo kallon juna.


Cikin sanyi Goggo Zahra dake gefe tace.


"Alhamdulillah Allah ya sanya Alkhairi Mahmoudu Allah ya tayaka rik'o"


Rayhana ce cikin kad'uwa tace.


"Goggo Wai wanne Mahmoud d'inne yayi Aure kuma da wacce Khadijan"?


Lkci d'aya kuma Aysha ma tace .


"Nima an d'aure min kai Wai da gske Mahmoud ne yayi Auren"?.


Mami ce ta fito cikin bak'in ciki da had'e fuska da takaici taje gaban Goggo Zahra cikin fushi kamar zatayi kuma tace.


" fisabilillahi Zahra yayanki yayi mana adalci ace ina Mahmoud ina Aure kuma ko Aure zaiyi ai sai a nema mai dai-dai dashi ina Khadija ina Mahmoud"?.


Khadija dake gefe cikin mmk da kad'uwa ta zazzaro ido woje tare da dafe k'irjinta
Murya na rawa tace.


"Wai me kuke fad'a ne ban gane kan mgnar ba Wai wacce Khadija kuma wanne Mahmoud d'in"?.


Cikin fushi Mami tace
"waye kuma in banda ke akwai wata Khadijan ne bayan ke kin juya k'ok'olwan yaro"


Anty ma dake gefe cikin mmk tace
"Mami Khadija nanne aka aurawa Mahmoud"?.
Goggo Zahra ne cikin had'e fuska tace
" toh haramun ne ko yayuna basu kai suyi ikonsu kan yaran su bane"?
Kamo hannu Khadija tayi cikin kula tace


"ki nitsu ki rik'e mijinki Allah yasa shine mijinki na har abada rabbi yasa sai mutuwa ce zata rabaku".


Lkci d'aya Hawaye ya ballo mata kamar da bak'in kwarya cikin zubda k'ollah tace.
" Na shiga uku Goggo Zahra me kuke nufi. Mahmoud k'anina shine kike kirada sunan mijina"

Sai kuma kuka mai k'arfi ya kofce mata fad'a wa jikin Goggo Zahra tayi cikin kuka mai tsuma rai da kaji kasan zuciyar mai yinshi cike yake da takaici.
Cikin kukan ta rik'e hannun Goggo Zahra ta kalleta fuska duk hawaye tace.
"Goggo Zahra ase yanzu Dan Allah ya jarabceni da mutuwar Aure sai a maidani tamkar y'ar kaza Goggo Zahra a rasa Wanda za,a cusamin sai Mahmoud yaro k'arami Goggo yanzu su Abba ne suka min haka me Na aikata musu da zasu hukuntani da haka".


Cikin bacin rai Anty da ke gefenta ta yarfa mata mari baki na rawa tace.


" iyayen naki kike gayawa haka ase basu isa dakeba kenan Khadija ase bazaki iya musu biyeyya ba"?.


Ita kam Khadija zuwa yanzu duhu ya rufe mata ido lkci d'aya ta fara jin jiri.


Kalaman, Mami yasata ta k'ara rud'ewa
Cewa take
"Ji muna furci ai da saninki bake kikace kar a gayawa kowa ba Dan gulma yanzu kice baki saniba"?.

Cikin kuka tace.
" Wlh Mami ban saniba wlh bada yardana akayi ba ".
Sai Kuma ta zame tayi k'asa cikin.......


By Garkuwan Fulani
Maman Jabeer da ikram da Ibrahim😍😘
πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*NAMIJI BAYA KAD'AN* pg 7⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


Pure moment of life writer's
P.m.l.w


www.aishaaligarkuwa.blogspot.com


*Bani da lkcin ku bare nace naji zafin zantu kanku a kaina zaginku kanku zai koma abinda na sani baku da damar dakatar dani akan harkar nan na rubuce-rubuce baku isaba dan baku kuka saniba kuma bansa ko wacce karantawa a doleba kuma bazan FASA abin danayi niya ba fans Na muje zuwa ga Mahmoud on top*






Zamewa kan gado tayi tare da kife kanta cikin pillows ta saki kuka mai tsuma rai tana kukanne har numfashinta na fizga,
Goggo Zahra yace ta matso kanta cikin sanyi tace.


"Haba Khadija Aure fa akayi muku ba zaman banza ba Mahmoud fa d'an uwanki ne shin akwai abinda baki sani bane a yanzu ba abinda ya rage face kiyi biyeyya ga Allah da manzonsa sai kuma kiyiwa iyayenkin d'a,a kiyiwa mijinki biyeyyah".


Mgnar Goggo Zahra k'ara sata kuka tayi dan ji take kamar wuta take watsa mata in tace Wai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login