Showing 9001 words to 12000 words out of 22399 words

Chapter 4 - GIDAN DADI ( Duniya) Book Complete Oum Aphnan.txt

na gama secondary school ɗin a saidai naci waec na faɗi jamb ,nan kuwa na dawo gida na rashe na cigaba da tsula rashin m . Ban iya girka komai ba sai indomie




Lokacin da na zana jamb ɗina a shekaran Anty Nusaiba ta dawo 9ja da shaidar kammala degree ɗin ta a medicine ta fara inten ɗin ta anan Abuja
Sosai taga rashin jina yayi gaba don haka ta fara jana a jiki saidai Nikam ina nayi nesa


Anty Nusaiba tunda ta gama degree dinta ta fara tunanin yin aure saidai kowani saurayinta yazo nice nan mai kora mata su da baƙin halina ,abun yina damun Antyna amma ya zatayi dani.....?
Ni Nadiya ƙazamace Ni kaina na sani don akan wanka kullum sai munyi faɗa da Anty Nusaiba ,akan ɗakin kwana kullum sai munyi dambe don takance mai warin maza bazata kwana a ɗaki da itaba sai nayi wanka ,in tsiyan ya ishi Iyayenmu sai su roƙeni inje in wanka to sananne zanyi ,Abu ɗaya Anty Nusaiba ta mora girki, subhanallh duk cin abinci saita take table da abinci munci naci a fitar da ragowa, wannan yasa na liƙe mata tanayi inaci tun a wuta ,hakan yasa nasan yanda ake sarrafa abinci amma yiɗinne dai banayi kuma ko an sakani haka zanta kuka wai ai ga Anty Nusaiba nan


Don't think Ni yarinyace shekaruna Sha bakwai a duniya ,amma childhood characters suna wulwuli da rayuwata


Akwai wataranan Asabar ba aiki kowa yina gida tun safe yaya Nusaiba ta gama mana abinci ta shiga wanka ,ta fito tana ta en gayunta a gaban dressing mirror ,juyi nayi na wuce dinning na lafto chips da farfesun kaza ba brush nahau cusawa saida naci na ƙoshi nayi gyatsa sannan na haɗa tea mai kauri cikin cup ɗin who send you ,tamkar dai gejin cin abincin wani gardin shima haka na ɗaura da bread da butter ,warwas nayi akan kafet ɗin bedroom ɗin mu sanyin fanka na hurani saboda yanda zufa ke tsatsafo mun a duk gaɓɓan jikina to Ni abu ba kaɗanba ƙatuwa.


Anty Nusaiba raɓeni tazoyi gamida liƙe hanci ta ɗauko riga da wandon fakistan milk da maroon ta saka ɗauko mayafin kayan ta taho gaban mirror tana rolling ,pillow nayi da hannuna ina kallonta har ta gama shiryawa kana nace "To sai ina isashiyar kanta ,fita zakiyi da sassafen nan iyayenki na barci? To kina saka ƙafa kika fita a kunnen dady dama kin riƙa kin zama riƙaƙƙiyar kuɓewa anje an kaiki Sudan kin iskance " ɗaga hannu tayi ta make bakina


"Ke nice kike zagi nifa yanki ne" wani ihu na ƙwalla da ya tsorata Iyayenmu aiko sai gasu a guje "Lafiya ?"
"Mum...dady Anty Nusaiba Bata sona nace zan bita inda zata wai bazata daniba wai Ni ƙazamace bla...bla"


Juyowa mamana tayi ta kalli Nusaiba "wai ke me yasa bakida hali keda yar uwan taki ma ?" Shiru kawai ya Nusaiba tayi ta girgiza kai batace komai ba inaji anata mata faɗa haka kuma duk sai naji ta bani tausayi ,ƙarshe akace in shirya in bita sai sannan tace "Dady plz kace tayi wanka da brush to ,don wallahi a haka zatace zata bini kuma wari takeyi "


Harara na banka mata "Kin haɗiya reza a gicciye nice zanyi wanka a sanyin nan ? Bazata saɓuba"


"To mumy kinjiko ,nikuma in har da ƙazanta zata bini ina likita gwara in haƙura na fasa siyan cosmetics ɗin"


Yafitoni Dadyna yayi ,nakuwa shagwargwaɓe naje na haye cinyarsa ,shafa kalbar kitsona da tsagon suka haɗe saboda daɗewa ba kitso yayi yina mun magana cikin rarrashi


"Mamana ai kinajin yawo ko?" Ɗaga masa kai nayi da sauri
"To maza nadyn dady aje ayi wanka kar Anty ta fasa fitan"
"Kambu to sai kuma dady ka ƙyaleta ? Ai dole taje ko?" Murmushi yayi "ƙwarai kuwa tunda kema wankan zakiyi "
"Eh nadaiji " hakana dai na tafi naje na rage datti wankan 2mns badon na fita ba ,ina fitowa naga iyayen namu sun fita sai ita dake zaune akan stool ta ɗaura jakarta dazata fita dashi akan cinya tana chart da wayarta ,tsaki naja naje na ɗauko Vaseline ɗina na shashafa fuskana caɗai kamar ɗanwake ,itadai sai bina da ido take ,saida naje na hangame kwabana ina lalubo wasu cukurkuɗaɗɗun kaya marasa guga kafin ta maza tace "Ga kayan na ciro maki my love"


Kallon banza na wulla mata "Anty banason saka wandon jeans ƙaiƙayi yikemun baki ganina ƙatuwace ?"


"Amma inkinsa yina maki kyau don kina fina kyau Ni bakiga kayan larabawa na sakaba,Ni basamun kyau" caɓe baki nayi "Kumafa haka ne kece ya Nusaiba akwai rama ga muni,to zuciya ba hali,Ni ban insa " itadai murmushi tayi wai itace nadiya take kiranta da mummuna yarinyar da a Sudan sajewa takeyi da en ƙasan har kalan skin ɗinsu ɗaya wai itace mummuna? Wayo tai mun ta lallaɓani nasan marasa squeezing tamun rolling nan kuwa cikina yayi tuiii a waje ga manyan ass ,inda zaka gane ba wata babba bace shine Banda cikan ƙirji kuma fuskata kwaɓa² yike irin na shafwaɓaɓɓun yara ,ipad ɗina na ɗauka mara sim don Banda mai kirana na saka cambas irin na zuwa ball na fito na wuce car na tsaya ina jiranta


Ɗakin mumy ta shiga amsar makullin mota,suna liƙe suna hira kamar wasu Romeo ba masu manyan en mata ba,A sannan ne take bata haƙuri tana ƙara nuna mata niɗin dai eruwarta ne tana haƙuri dani


"Shikenan mumy amma dai in kun sama lokaci a kaita Psychiatric hospital taga likitan ƙwalwa ke likitane kinsan alamomin hauka ,kuma Nady ta ɗebi kaso da dama " babanmu dake gefene ya kwashe da dariya "Lallai Nusaiba kin tsorata da lamarin er uwarki "


*****
A mota ƙira'ar sudais tasa har suka isa Suhash shopping mall ,nan tayi parking suka fito ,tana tafe tana mata nasiha kar tayi tsiya da kowa ,aiko bata rufe bakiba wata mata tazo wucewa da ɗan ta riƙe da ice cream yaron bai wuce 7 years ba ,cikin rashin kula irin na yaro ya bangaji cikinta ya kuwa sheƙa mata ice cream a takalmi ,wayyo Ji kake ɗauuuuuuuu ta yanka ma yaron mari mai tsananin zafi a take yaron ya gigice ,ya fasa ihu ,aiko uwarsa ta juyo da sauri ta rungume ɗan ta tana kallon nadiya dake hura hanci tana masifa ya ɓata mata takalmi


"Haba en mata bakisan yaro ba"


"Yaci kazan ubansa shi yaron ,nima ai yarinyar ce ,kece dai baki bawa ɗanki tarbiyya ba"


"Shikenan keda iyayenki suka baki tarbiyya cigaba da faɗa da ƙaramin yaro ..." Da sauri ta katse ta


"Ahhhh karki zageni wallahi Ni pepper ne yanzu zan kwaɓe muyi dambe in kinfi ƙarfina shikenan sai in kuka ina share hawaye"


Nusaiba takai ta dawo ta rasa yanda zatayi haƙuri take ba matar in matar nikuma tana mun faɗa,kawai sai na fashe mata da kuka wai tafison bare a kaina .


Wani Chubby guy ne ya tako a hankali cikin ƙwalisarsa ya matso inda muke so yike ya janyeni ta baya amma ina na aza anty Nusaiba ce ba zato ba sakan masa one blow a baki da sauri ya riƙe bakinsa yina nanata "Ah....ah....ah" ruɗewa Nusaiba ta ƙarayi ,dasauri takai gwuiwonta ƙasa "Man Plz sorry she's young " zare hannunsa yayi a saman bakinsa


Ya sa hannu ya ɗago ta ,maye gurbin mamakinsa yayi da wani irin lafiyayyen murmushi mai tsadan gaske "Karki damu ƙuruciya ke damunta jiba da ta nausheni ma ta gudu" waigawa tayi nankuwa taga na ɓace ,can ta hangoni wajen kayan chocolate na maƙale Ina leƙe


Girgiza kai tayi cikin takaici ,shikuwa sai dariya yike yi "kayi haƙuri kaji "


"Ƙanwatace ain't vex? Muje ki zaɓi abinda zaki siya joooor "


Ɗan murmushine ya ƙwace ma Nusaiba ,lallai guy ɗin is so friendly tasata yayi suka wuce wajen turaruka


Nikuwa taune yatsa nayi "shegiya Anty Nusaiba anga kyakyawar namiji sai rawar kai akeyi ,to baidaice yina sonta ba kuma bari inje masu"


09065990265
Wxp only plz🙏🏻
[6/20, 11:26] 😘😘😘: *GIDAN DAƊI*
_(Duniya)_


Oum Aphnan✍️


Free page
007




Tun daga parking lot nake ƙwalla mata kira har cikin gida ,da ƙarfi na hankaɗa ƙofar na shiga tana kwance ta ƙanƙame pillow tana shan love ,a tsorace ta miƙe zaune tana maida gashin kanta daya wargaje saboda kwanciya
"Nadiya why are you banging the door like that,are you mad "
Dafe kaina nayi na koma na jingina a jikin ƙofa ina lalubo video ɗin da na ma ya Hisham "Come and see ,come nowww?!" Ƙur ta mun da ido bata da niyyar miƙewa
"Come on ! Kizo ki gani mana"
"Hello!" Ta ɗan kira attention ɗina ɗagowa nayi na kalleta "Who is your senior sister,who age who?" Turo baki nayi ,da har nayi zuciya zan tafi ganin interest ɗina ne yasa na dawo nabita kan gadon na miƙa mata "watch your naked evil" a tsorace ta karɓa Saidai wani ƙara ta fashe dashi da sauri na rufe mata baki da hannuna "Malamansu momy is around ,she may definitely need to dig the true ,to shawara ya rage naki me kike gani zaki fasa auransa ne ko zaki auri mayaudari ɗan iska mai rungume mata a titi"


Kwantawa tayi akan pillow wasu kyawawan hawaye suna layi a kuncinta "Dole zan fasa auren Hisham ,Nagode ƙanwata"
Rungumeta nayi "Da kyau" na bata amsa na wuce bathroom Ina bouncing kamar wacce tayi abun arziƙi


****
32hours Later


Muna zaune a ɗakinmu Ni ina game a laptop ɗina Anty Nusaiba tana chating a wayarta fuskarta a murtuke ,Hisham ya kira wayarta yafi sau ba Adadi taƙi ɗagawa,a hankali momy ta Turo ƙofar ɗakin ,da sallamata saidai ba wanda ya amsa ta
Kewayowa gefen bed ɗin tayi daidai an sake kiran wayarta ,direct Anty Nusaiba ta nufa ta miƙa ma wayar "Amshi Hisham yace yina kiran wayarki bako ɗagawa"
Da muryarta adashe kamar wacce tayi kuka tace "ok mom kije zan kira shi da wayana"
"Oh no pick up" a hankali ta ɗauki wayar ,batayi magana ba na ɗan lokaci Saida yace salamu Alaikum ,kafin tace "hello"
Ta bangaren Hisham ya zarce da cewa "Sweetheart how are you I've been wondering what happen to my blossom..." Da sauri ta katsesa da
"Oh sorry I will call you later" kafin yayi wani magana ta datse kiran ta mika ma momyn wayan


Karɓa tayi tana jujjuyawa tana saka abubuwa a ranta "me ke damunki?" A takaice ta amsa da ba komai
"Ok me ya hanaki magana da Hisham"
"Haba momy ki ƙyaleta mana may be she is not in the mood tayi magana ne" na karɓe maganar da sauri ina wani tattare gira


"Yi mun shiru dake nake magana ehen,ko kece mouthpiece ɗin ta"
Danna wayar nayi na nuna mata wayana "to kalli nan" wani shock tayi amma da sauri tayi maintaining kanta
"Oh really? Nusaiba zo muje" ta faɗa tana kamo hannunta
"Momy go where now,kuyi maganar anan mana "
Kallona tayi ta bankaɗa mun harara "kece big informant banso kiji,na gaji da rabata da masoyanta da kikeyi wannan bazaki yi nasara ba..." Shiru tayi saboda Dady da ya Turo ƙofar
"Ohoo haɗe mun kai zakuyi? So kuke ku nuna mun nine kaɗai namiji a gidan ,zan ƙaro wata ,gaskiya zan ƙaro mai tayani hira"
Dukda momy tasan wasa yike bai hanata tankawa ba "Come on,daga naxo ganin lafiyarsu ...kawai ma dai muje" ta tasa ƙeyarsa suka fice ,Ni kam dariya na saki abuna rai fes ,itakuwa Anty Nusaiba taɓe fuska tayi ta juya ta kwanta ,ta rarumo wayarta ,a hankali na miƙe tsaye ,ina nanata mata "karki yarda ki ɗauki wayarsa kinji ,You guys should break up!"


*****
Muna zaune a dinning muna lunch mu ukune ,still Kiran wayar Anty Nusaiba ya damemu ,duk dauriyar momy saida ta magantu
"Haba pick nah" na saka fork Ina ƙaƙarin gutsuran kaza kenan nayi saurin cewa "momy its ya Hisham fa,Anty karki ɗauka"
Muzurai momy ta mun kana ta sanyaya muryarta "Nusaiba ɗauki wayar mana" a zafafe na cusa naman a bakina na soma magana yagau yagau "Yawwa ɗauka ki ci masa You locked the relationship with him ,ya aiko a amsan masa kayan baikonsa...."
Harara momy ta kwasa mun
"Nadiya Inaso inga young man ɗin da zai zo auranki" caɓe baki nayi na magantu ciki ² "Aiko ba rana bare wata"
"Me kika ce?" Da ƙarfi nai magana ina ɗan bubbuga kai "Ahhh bance komai ba " kallon banza tayi mun "ohooo bakomai ?" Gyada mata kai nayi "gwara ya zama bakoman "ta faɗa ranta a ɗan ɓace ,saboda taji zafin mugun alkaba'in da nikewa kaina "momy sorry it joke"
"Gwara ya zama ba'an Nadiya "
Daidai nan ya sake Kiran wayar
"Oya ɗauka in ga gari"
Dakan dinning table ɗin nayi a zafafe nace "yawwa ɗauka ki faɗa masa bazaki iya ba kuma, wedding is cancelled ,baki yi kawai period"
"Kinajina bazan ce maki lallae ki auresa dole ba ,kawai abunda nikeso shine ki ɗauki wayarsa ki faɗa masa me ya faru let him confess,in kinason sa then you move,in baki sonsa daga nan mu manya sai mu shigo maganar"
"Momy idan har yina sonta bazai je yina rungumar wata akan titi ba ,harda cewa wai bashida masoyiya"
"Aushhh,Nadiya jeki ɗauko mun wayata a bedroom" zaro Ido nayi "momyyyyy" na ja sunanta kamar zan kuka "Nadiya you heard me, so , go",ta fada cikin tsawa²
tashi nayi na tura kujeran baya na fara stepping zuwa ɗakinta da sauri saboda in dawo kafin ya kira
"Ok my love me kika yanke a ranki uhum"
"Momy zan ɗauka wayarsa kamar yanda kikace saidai abunda nikeso ki gane shine ,bazan faɗa masa maganar nan ba ,saboda koda na gaya masa dole kare kansa zaiyi ya kuma cemun sorry ,to idan hakan ne why not in yafe masan kafin ya zama jacks da musayan yamu tunda dole za'a dawo one circle ne?"


"Kenan You truely forgive him,or...?"
"Gaskiya momy banda option din da ya wuce hakan ne shiyasa "
"Ina sonki da hakurin ki ,unlike your sister ..." A hankali ta ɗauki wayar ta mika ma Nusaiban "ok talk to him kamar ko yaushe don't let evil to break this good..."
"Momy banga wayanki ba" na fadi da karfi tun kafin in ƙaraso ,dasauri na dawo na zauna
"Ok go and check my car"
Kwaɓa² nayi kamar zanyi kuka
"Ah ah momy taya zaki bar wayarki a cikin mota"
"Nadiya wuce na ce" diddirke ƙafa na shigayi haka dole na fita ,har na kulle ƙofa na buɗe na leƙo da kaina
"Kar ki ɗauki wayar nan fa Anty" tsaki sukaja suka cigaba da shirya maganarsu irin na masu hankali
Yina kira ina shigowa ,a hankali Nusaiba ta dauki wayar zata shafa screen ɗin na ƙwalla ihu ,wanda ya tsorata su duka
"Anty no zakiyi kuskure ,uhm uhm I'm warning You"
Dafe kai momy tayi "Nadiya what again? Ina wayar nawa yake "
"Momy mukullin motan nazo amsa" ɗauka tayi ta miƙa mun
Kawai saiga ƙwalla a kuncina "mumuuu na gaji ƙafana zafi,wallahi aikena kuke kuna mun wayo kuma na gane"
"Oh haka ne? To tunda har tunaninki ya baki haka ai MashaAllah ko banza mun samu cigaba ,wuce ki bani waje " ,sannan ta juyo ta kalli Nusaiba a karo na barkatai "Nusaiba bari in baki wani hint da baki sani ba ,99.9% na maza Are cheat ,let's say budurwansa ne ,so what is your business tunda ke ya zaɓa out of those girls ya zaɓeki a matsayin abokiyar rayuwarsa dukda kyawunsa,dukiyarsa and his prestige ,let's this be enough to you durling ,kiyi haƙuri plz Ni mamanki na baki hakuri don Allah"
"No mah I will...ki bar bani haƙuri I will" da sauri ta ɗauki wayar "hello"
"Babe what's wrong ?"
"Sorry wayata na jefa lungu sai yanzu naga Ni" sassanyar ajiyar numfashi yayi
"Oh har kin tayar mun da hankali kwana da wuni,naji ba daɗi gani ,ina jirgi on my way to China da kin ganni a gidanku saidai i don wanna miss the flight babe ,anya kin damu dani kuwa,anya kina kewana"
"I'm missing you love ,kawai dai ina tare da mama yanzu will talk later?" Shikennan nima za mu tashi zamuyi chat ok?"
"Yes safe trip durling"
"Ok thanks" ya kashe wayar a hankali ya kwanta a bayan seat din jirgin ,yina manne da wayar a ƙirjinsa a hankali wani sanyi ke shigarsa ,nan danan yaji wasai an ɗauke masa damuwarsa ,sanarwar kowa ya saka belt ɗin jirgin a shirya jirgi zata tashi shi ya dawo dashi tunaninsa ,da sauri ya miƙe a inda yike saboda yina wajen en regular passengers ne ,shikuma late yazo airport ɗin bai booking ba don haka na en vips ya biya wanda yafi tsada ,yafi secure kuma .
A nutse ya ɗauki jakar bayansa ya goya ya shige can ,tsayawa yayi yina kallon nature d'in wajen,Govenor ne da mukararrabansa ,sai wani calm guy cikin track suit da tuntumemen cambas ,ji yayi yafi masa sauki ya zauna kusada saurayi kamarshi,ba cikin wanda zasu damesa da hayaniyar siyasa ba


"Hey Assalamu alaikum" fuskarsa a hade ya miƙa masa hannu sukayi shaking
"I'm Hisham entrepreneur ne ni ,and you?" Haushi yaji ya bashi baison maza masu saurin sabo "I'm Adams" ya faɗa a taƙaice ya gyara zaman Bluetooth nasa yina bada umurni kamar wani boss"


***
Daga wannan ranar momy suka ƙulle da Anty Nusaiba suka wareni Ni Nusaiba ,bansan wani munafurcin suka kitsa ba ,shine aka zuge Babana ya samar mun Nursing aka wurgoni wannan baƙar Hostel ɗin mai mutane iri dabam dabam masu mabanbantan tarbiyya ,nayi kuka nayi takaici saboda Ni Babana yayi mun Alƙawari inna gama secondary zai fita dani ƙasar waje karatu kamar dai Anty Nusaiba wai gashi an kawo Ni Nursing a 9ja bayan kurin da na gama yiwa kawayena Ni zan je ina karanta architecture ne a uk......






Back to the frame work of the story








Click here for your payment info.
09065990265
[6/20, 11:26] 😘😘😘: *GIDAN DAƊI*
_(Duniya🌏)_




Oum Aphnan✍️




Free page
006


_O&A organic care products_
Ina kuke ƴan mata en ƙwalisa masu son kece raini da sallah babba ,ina Amaran bayan Sallah ,ina uwar gida mai son dawo da martabar kanta kina haske kina glowing, mai gida yina kallon kansa a fuskarki tamkar tangaran ,kiyi masa dariya yina ƴan matan waje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login