Showing 12001 words to 15000 words out of 16110 words

Chapter 5 - AUREN WATA BAKWAI FREE Book BY XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH.txt

maimakon Bread din da take fada ya ce, "Aa fa wannan ba Bread bane Gaaji wani abunne daban."


"To mene ne in ba burodi ba? Aradun Allah burodine ai ko lokacin ma da Baffana yana siyomin in ya shigo birni nidai ka siyamun." Ta fada tana taɓe fuska.


Adnan ya karba kawai yasa cikin besket din ba tare da ya ce komai ba.
Kara dauko wasu guda biyu tayi ta ce, "Yo ai Aradu wa inshen sunmun kadan akara wa innan su zama uku yau inta shin abuna in ji dadi."


Shi kam dai bai ce mata komai ba tasa a ciki.
Kaya ya zaɓa mata daidai wa inda zasu mata dogayan riguna da wasu mini hijab, chocolate ,sweet da su biscuit ma kamar wa inda zasu bude provisions ban da washe baki ba abun da take tana jin dadi.


Saida suka gama tas kafin suka koma mota, Prince na ciki yana danna waya, sai da Adnan ya budewa Gaaji ta shiga sannan shima ya shiga, tana shiga tayi tsaki da kwafa, ganin Adeel bai ma san tana yi ba ta dunga dage tana harararsa da murguda masa baki.
Kamar ance ya kalli morrown gaban motan suka hada ta takarkare tana murguda masa karamin bakinta ta ko ina a fuskarta ba inda baya motsi.


Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba don ya fara fahimtar Indai ya biyewa wannan yarinyar sai ta maidasa karamin mahaukaci.
Kan su isa Fada an fara kiran sallan magriba, haka yasa Adnan ya na aje mota ya bude mata cikin sauri ya ce tazo ya maida ta ciki gun Uwar Soro tun kafin wani ya gansu.
Ita kuwa Gaaji tsayawa tayi lallai fa sai ta ci gaba da murgudawa Adeel baki kan ya fito a motar taje tana kokarin tura kanta daidai da lokacin da yake kokarin turo kofar ya fito bai na ganta ba.
Da sauri Adnan yaja hannunta yana, "kina so muyi fada ko? Baki ga lokacin sallah ya yi bane? Oya muje ki shiga ciki muma zamu shiga Masallaci."




Shigewa tayi da tarin ledar kayanta guda biyu tana juyowa tana daga masa hannu a dole byeebyee.


Aiko tana shiga ciki ta baza kayan nan kaf a kasa tana murna take ta cire kayan fulaninta tasa wata Abaya ta mata kyau Sosai, Uwar Soro kuwa binta da kallo take kawai na mamaki ganin yau da kanta ta cire kayan Gadonta tasa wani ah lallai Gaaji an fara canjawa.


Ita kadai tana ta sambatu, "Ai aradu ba a tabani a zauna lafiya She na gyarawa mutum hankali tunda shi an ishka ne kuma mugu, Shi kam Abokina ba ruwansa Dan albarka she siyamun kaya yake."
Pad dinnan ta ciro ta jera gabanta tana, "Yawwa wannan Burodin zanci yau Baba ba zan ci abinshinki ba abokina ne ya sayo mun mai dadi."


Uwar Soro ta ce, "Mu ga Burodin naki Gaaji."


Tashi tayi tana yage ledar ta ce, "Kadan fa zan sammaki ba duka ba ,zan shi abina duka ni kadai."


Uwar Soro na karba ta ce, "Wannan ai Audugace ba burodi ba."


Gaaji ta karbe abunta tana, "Audugar me? Burodi ne fa aboki ya siyamun."


Dariya Uwar Soro ta yi ta ce, "na san dai kin fara al'ada to Da kika fara jini na fito miki da me kike amfani lokacin kina Ruga?"


Gaaji ta ce, "Ni tsumma nake sawa in tare sai ranar da naga jinin ya dauke sai in Jefar a shara."


Da sauri Uwar Soro ta riketa ta ce, "Subhanallahi to wannan abun ake sawa ba tsumma ba,kin san tsumma kuwa cuta yake sawa? Zai saki ki yi tsutsa,yana fito miki kuma kina wari a karshe ma ki mutu."
Nan take Gaaji ta gwalalo ido tsoro ya gama cikata.
Uwar Soro ta ci gaba da cewa, "Kin ga shi wannan kullum ma in kina yi a kalla sau biyu ko sau uku ake so kina canja wani,da zaran ya baci ko ya dan dau lokaci ake cirewa saboda gujewa shigar wata cuta kinji ko?"


Jikinta ya yi sanyi ta ce, "ni kam ba zan kara sa tsumma ba kar inyi tsutsa Ysn ba ruwana na daina, tun yanzu ma zansa wannan din ya fara taremun kafin ya zo."


Uwar Soro ta yi Murmushi tana, "Aa ai sai yazo ake sawa yanzu zan boye miki kinji baza ki yi tsutsa ba In Sha Allah."


Saida Adnan ya dawo ya mata tatsuniya kafin tayi barci kuma ya tafi.


★★
Khalesa ban da zabga kira a waya ba abun da take yiwa Adeel ya ki dauka da ta gaji kawai sai ta nufi bangarensa tana zuwa ta tatarar da shi tsaye da Nasmah suna magana.


Wani irin kallon raini ta bi Nasmah da shi, ita ma ta maida mata da kallon tara saura kwata.
Karasa tayi daf da Adeel ta ce, "Prince na zo gunka ne fa kuma na ga wata."


Adeel ya ce, "Nasmah ce ai dukan ku ɗayane."


Cikin bacin rai Khalesa ta ce, "Aa wallahi ni da ita ba ɗaya bane kama daina haɗamu ko a shekaru na fita bare kuma batun kasancewa gareka muna da tazarana matsayina daban nata daban, so ta bani waje ina so inyi magana da kai."


Nasmah tayi murmushi kawai tana kallonta.


Prince Adeel ya yi shiru shima ba tare da ya ce komai ba sun maidata fanko kawai.


A har zuke ta kara fadin, "Magana fa nake, ke Nasmah wai ba kyajine? matar sa na son yin magana da shi?"


"Matata?" Yareema ya fada cike da mamaki fal a fuskarsa.


"Eheen ko ka manta ne?"
Khalesa ta fada cikin isa.


Ya ce, "ke da ita duk dayane duk abun da zaki fada ki fada gabanta zai fi miki."


Wani irin fusata Khalesa tayi tana sakin tsaki ta kara bin Nasmah da wani kallo tare da yin kwafa,ita kuwa Nasmah gwalo ta mata da wata irin dariyar mugunta.


Nasmah na ganin Khalesa ta tafi murya a raunane ta ce, "Na dameka ko Prince? Sorry Gudnyt ka je ka kwanta ka huta gobe kawai mayi maganar ko Lokacin da kake free ka kula da kanka."


"Alright thanks." Ya fada kawai ya shige.


Sai da taga shigewarsa sannan ta tafi tana sakin murmishin da ita kadai ta san Dalilin sa.


★★★Misalin karfe Tara na safe Gaaji ta sha wanka ta karasa kaya da ɗaya cikin wanda Adnan ya siya mata sau juyi ake, ranar ba fada ta tsaya aka mata wanka tayi brush da kanta, wanke dambun gashin ta ne dai har yanzu taki Yarda Uwar Soro ta taba bare a wanke mata shi.


Daukan hanya tayi bijigun-bijigun zata fita, Uwar Soro ta ce, "Ina zuwa?"
Tunani ta tsaya yi ta tana sakawa a zuciyar ta indai ta fadawa Uwar Soro asalin abun da zata yi bazata barta ba , can sai ta washe baki ta ce, "Zan ni in nunawa abokina Adona ne ns irin kayan yan birnin da ya shiyamun inshe mishi na gode."


Uwar Soro ta ce, "to kardai kiyi wani gun kina fita ki shiga can in ba haka ba ana kamaki yanki ki za ayi na fada miki."


Gaaji ta ce to sannan ta fice.
Bin bayanta Uwar Soro tayi saida ta tabbatar ta shiga bangaren Yareema kafin ta dawo nata bangaren.




A hankali ta tura kofar ta shige.
Tana shiga kuwa taga Yareema na barci hankalinsa kwance daga shi sai gajeran wando.


Ta ce, "Ji an ishka barcinma ba kaya yake yi aiki yau zaka shi gidanku aradu."
Ta karasa gabansa a hankali tana zuwa ta sake masa mari a kumatu tauuu ta kara sake wani tauuu.
Yareema ji ya yi kamar a maraki ana zabga masa wasu irin zafafan maruka.
Ya yi saurin bude idonsa ya ganta tsaye kansa amman ya kasa gasgata hakan.
Rike hannu tayi a kugu tana fadin, "Kalle ni da kyau mai idon mage nishe nan Zainabu Gaajin Baffa ramawa na zo yi na rama marin da kamun ehee kai ma Kaji inda Dadi ai da wani wandon ka kamar nafkin."


Sai a lokacin ya tabbatar da a zahiri yake kokarin tashi ya fara a fusace.
Ai Gaaji da taja dogayen kafafunta masu kama da sandar sunuka sai waje.


Tashi ya yi ya.........








*TO FA FREE PAGES NA DAF DA KAREWA SAURA PAGES BIYU IN SHA ALLAH, ZAKU IYA FARA PAYMENT YANZU ₦300 KACAL VIA 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank Evidence of payment to 08103080717*


Luvs U Oll😘🫶💃😻
[8/9, 8:47 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *AUREN WATA BAKWAI*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*


© *Xayyeesherthul-humaerath*


Page-17&18




Cikin Fushi zai fita har sai da yaje bakin kofa ya tuna da gajeran wando ne a jikinsa, tsaki ya yi ya koma,yana zura jallabiya ya fita zuwa bangaren Uwar Soro.


Gaaji na ganin shigarsa da gudu ta koma bayan Uwar Soro tana kankameta, "Baba Wallahi shin zalina zai kara yi don kawai na rama marin da ya mun."


Bude baki Uwar Soro tayi da mamaki tana kallon Gaaji ,Don ita a iya saninta babu wani mahalukin da ya taba dagawa Yareema hannu,bare kuma batun mari, ah lallai Yar nan kin taro ruwa.
Ta fada aranta.


Yanayin yadda yake huci ita kanta Uwar Soro ta razana ta yadda ta kasa ce masa uffan.
Gaaji kuwa kara kankameta take tana, "Aradu mugune karki bari ya taɓani zai kashe ni."
Ji tayi kawai ya dauketa cak.
Ya fice da ita,ba direta a ko ina ba sai kofar wani kurkukun daki, karami, mai bala'in duhu mutum baya iya ganin ko hannunsa a ciki, jefata ciki ya yi ya rufe kofar sannan ya koma dakinsa.


Nan take Gaaji ta birkice, Wani irin kuka take tamkar ba mutum ba, ta gama ficewa a hayyacinta, kayanta duk ta yayyaga su da fisga,gashin kanta ma sunyi carko-carko, tana ta fisga cikin lokaci kalilan ta dawo mahaukaciya.




Uwar Soro kuwa Tana ganin Prince Adeel ya shigar da Gaaji dakin nan hankalinta ya matukar tashi,tasan Manya ma aka shigar da su ya suka kare bare kuma mutum? Dakin da babu ko windo bare wani sakon da haske zai shiga, nunfashi ma mutum na ciki in ya dau lokaci dakyar yake iya yi, wasu ma kan a cirosu sun mutu.


Ganin bata da wata mafita yasata saurin kiran Adnan ta sanar da shi halin da ake ciki, Wayar Adnan sam bata shiga domin ya tafi India gun aikin Baban Gaaji Ya duba yadda lamuran ke gudana, kuma daga nan zai koma America domin yin wani bincike da yake.


Tun tana gwada kiran har ta gaji ta hakura, domin babu alamar shiga.


Adnan ya sanar da shamaki cewa bai yarda wani yaje Gaaji take ba sai shi,kuma shi ma din ruwa kadai zaina bata kada a kuskura a bata abinci.


Gaaji tun tana ihu har ta gaji ta daina ban da ajiyar zuciya babu abun da take,kamar wasa har dare ya yi,ya tabbata dai sai da ta kwana adakin, duk da cewa ita batasan dare ko rana ba saidai wani lokacin kawai ta ji barci ya dauketa, inko ta farka ma duk daya tunda duk abu ɗaya idonta ke gani wato duhu,barcinma tana farawa wasu irin samudawan sauro zasu isheta da kuka a kunne, a jiki suna cizo, ya zamana bata da aikin yin da ya zarce kuka.


Uwar Soro ce ta roki shamaki da ya taimaka yana bata abinci ko da kadan ne ba tare da sanin Yareema ba, tunda ita ma ya ce ba ruwanta kada ta bari a hannunta ya shiga ciki,hakan kuwa ya kasance a boye kullum yake bata abinci da ruwa.
Gaaji na cin abinci tana kuka,laluba take domin ko bakinta ma takan iya rasawa wani abincin ma kan ya shiga bakinta ta zubar a lalube lalube,kusan rabin abincin a kasa yake,kafin rabi ya shiga cikinta.


Ranar da ta kwana uku a dakin Adnan ya dawo,yana zuwa MASARAUTAR bangaren Uwar Soro ya fara nufa domin ya yiwa Gaaji tsaraba sosai kasancewar yasan zai sha daru zata ce yaki zuwa gunta inko yace yayi tafiyane ma zata ce me yasa bai tafi da ita ba.


Da fara'arsa ya shiga yana fadin, "Wai ina Gaaji Beautyn ne? Tana ina? Bata ji Yayanta ya zo bane? Ko dai fushi tayi ne? In fara tsallen kwado daga nesa ko? To na fara."
Ya ƙarasa maganar yana shiga cikin Parlourn Uwar soro, tsayawa ya yi turus ganin Uwar Soro ce ita kadai babu Gaaji bare alamar ta.


Ya ce, "Kardai fushin yasa ta buya bata son ganina?"


Cikin yanayi na rashin jin dadi Uwar Soro ta ce, "Ina fa, Gaaji na dakin Duhu."


Zaro ido Adnan ya yi cikin fargaba ya ce, "Subhanallahi! Me ya faru? Waya kaita?"


Nan da nan Uwar Soro ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da Adnan.


Ko magana bai kara ba cikin fushi ya nufi gun Adeel.
Yana shiga Yaga Adeel hankali kwance yana zaune a daining yana cin abinci.
Ko sallama gagararsa ta yi yana shiga kawai a harzuke ya ce, "Akan me zaka Rufe Gaaji a wancen dakin duhun? Nikam wai ina imaninka ne Prince? Me yasa zaka kulleta kullewan ma bana lokaci kadan ba yau har kwana uku? Wannan Yarinyar Amana ce fa agunka Wallahi in har ka cutar da ita wani abu ya sameta Ubangiji ba zai taba barinka,me yasa zaka aikata haka?"


A gajarce Adeel ya ce, "saboda na isa na yi mata hukunci a matsayina na mijinta."


Kallonsa Adnan ya tsaya yi da mamaki,wai har Adeel ne ke dangata kansa da Gaaji matsayin miji,abun da bai taba furtawa ba koda da wasa?
Ya ce, "To naji ni kuma a matsayina wanda nake yaya awajenta ka fitomun da kanwata."


Adeel ya tashi ya nufi 2sita ya zauna kafin ya ce, "Baka isa ba,in kuma kace zaka shiga sabgar da ba taka ba zan nuna maka asalin wane ne Prince Adeel Muhammad Rohaan."




Ran Adnan ya matukar kara ɓaci zuciyarsa na bugawa cikin zafin rai ya ce, "Au haka za ayi? Ya karasa maganar ya bugawa Adeel hannu a kirji.


Adeel ma a fusace ya buga masa kirji yana fadin , "Kwarai."
Kokarin fara kokuwa suka yi kowannensu na wuce zuciyar maza na bugu rai ya baci.
Uwar Soro ce ta katse su da fadin, "Subhanallahi! Me zan gani? Me yake shirin faruwa anan kuma,da girmanku?"


Adnan na wuce ya ce, "Na rantse da girman Allah indai yau bai fito da Yarinyar nan ba babu shakka sai na je Fada na sanar da Mai Martaba da kowa ma , in tabbatar da cewa gata nan matarsa ce."




Cikin fushi ADEEL ya wurga masa keyn dakin yana huci ya shige cikin bed room.
Adnan ya fice Uwar Soro ma ta bi bayansa suna zuwa cikin sauri jikinsa na rawa ya bude Gaaji.
Hasken da tagani ya kashe mata ido rufe idon tayi a tsorace ,haske har ya fara zame mata sabon abu.


Uwar Soro ce ta shige ta riko hannunta da sauri ta fito da ita.
Gabadaya yanayinta ya canja mata da maraba da mahaukaciya har ta fi fasali lokacin da ta fara zuwa fadan akan yanzu.
Jikinta duk wasu irin cuhuka da kuraje.
Idonta arufe ban da hawaye babu abun da take.
Adnan ya tsaya yana kallonta bai san lokacin da hawaye suka fara zuba daga idanunsa ba jikinsa kuwa ya kasa daina rawa.


Cikin Muryar kuka ta ce, "Ina za akaini? Don Allah kar amaidani irin wancen dakin zan mutu."


Uwar Soro ta ce, "ba za amaidaki ba, Gimbiyata nice nan kinji daga yau ma baza ki kara shiga cikin dakin ba In Sha Allah,ki bude idon ki a hankali kinji mu tafi."


Tana bude ido tana ganin haske sai ta kara rufewa a karshe sai haka suka tafi kawai.
Adnan kumq tsabar tausayinta ya kasa furta komai ma sai binsu da kallo kawai.


Suna shigewa cikin daki shima ya fice a Masarautar rai bace ba tare da ya koma bangaren Prince ba.




Dakyar ta iya bude ido , uwar Soro ta mata wanka ,ana wankanma tana kuka domin ko ina aka taba ciwo yake mata,dakyar aka wanke mata jikin sama-sama ta sha magani, duk son abincin Gaaji kasa ci tayi dakyar tasha tea dan kadan ta kwanta barci.


Tana barcinma ban da razana ,ihu da surutai babu abun da take tana birgita, sai da Uwar Soro ta mata addu'a to tofa mata sannan ta samu barcin nata ya danyi nisa.


Gabadaya duk ta kumbura,har yanayin kamanninta ya canja.




Tun daga Ranar Adnan ko ya shiga fada baya neman Adeel sai dai ya duba Gaaji suyi hira ya tafi, ko da sun hadu da Yareema sai dai kowa ya yi harkar gabansa ba mai kula Wani.


Ita kuwa Gaaji na zaune sai dai aji tayi kwafa, in Adeel ko Uwar Soro suka ce mene ne? Saidai kawai ta washe baki ta ce ba komai.




Daukan Gaaji Adnan ya yi zasu fita kenan sai ga Adeel ma ya fito suka ci karo da juna Gaaji ta.....








*Second to the last free page, ka da a manta gobe za a gaba free pages in sha Allah , duk mai son ci gaba da karantawa zata biya ₦300 kacal via 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank, masu Opay kuma 8103080717, Evidence of payment to 08103080717, can't' luv you less oll😘😘😘😘*




Urs Xayyeesherthuo
[8/11, 8:42 PM] Xayyeesherthul-humaerath🥀: *AUREN WATA BAKWAI*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*


© *Xayyeesherthul-humaerath*


Page-19&20


*Last Free Page*


Kallon juna suka yi na tsayin daƙiƙo, Everyone has the thoughts that are in his heart, A hankali cike da nutsuwa Prince ya yake kallon hannunsu da yake sarƙafe dana juna, gently kuma ya zame idanunsa without knowing yadda ya fahimci abun, ya nemi waje can saman ladduma mai taushi da wani kumbo a gefe ya zauna, ya gyara zama farar Alkyabbar dake jininsa, yau ya tuna da cewa shi ɗin jinin sarauta ne.


"Hold on.." ya furta shortly yana ɗauke kai tare da mai da ganinsa kan wayar da yake dannawa, Adnan ya tsaya sai kuma ya juya yana cewa "Is there any problem?" Prince ya yatsuna fuska ya ce "No!" Ya sauke numfashi, sai kuma ya ɗago kai bakiɗaya yana zubawa Adnan idanu sai kuma ya mayar kan Fulani gul ɗin calmly ya ce "Baka jin kunyar fita da wannan datti gal ɗin? Why you're always making problem? Baka jin kunyar jama'ar masarauta?"


"Masarauta? The royal kingdom, or kuyangi, ko barori, hadimai? Jakadan fada ko hakimai? Dagatai ko masu unguwarmu? Ko mutanen da kake mulki, wanne kake so na ji kunya danna fita da Zainab?" Ya yi murmushi yana neman wajan zama looking at yarima's direction ya ce "Tell me something Prince Adeel, do you love her?" Cikin sanyin murya Adeel ya ce


"Goodness, love? Me da wancan? Ka ke imagine ko a reflection kaga haka? Har gaban abada babu wannan" Ya faɗa so Clam Adnan ya ce "Ohk, am so happy for that, idan haka ne mu yi deal mana"
"For?" Prince asked. Adnan ya ce "Baka san Zainab Gaaji,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login