Showing 75001 words to 78000 words out of 78127 words
taqi, wai tafi son can,"
"Allah sarki Iya, ai shikenan Allah dai ya qara lafiya, Kuma har yau Sahabee be zo neman ta ba ko?"
"Be zo ba, ba Wanda ya zo neman ta, uhmmm ya wajen su Hajiyan taku,"
Cikin ladabi Anwar ya amsa da,
"Suna lafiya, yanzu ma seda mu ka biya ta can suna gaida ku sosai,"
" Muna amsawa Kuma muna godiya,"
" Abu Fadheemah muje mu ga Iya kan ka tafi ko? Anjima sai ka zo ka d'auke ni,"
Tashi suka yi tsaye Eamaan ta Maida mayafin ta,suka fita dan zagayawa ta kitchen su je wajen Iya, su na shiga kitchen d'in ya ga ba kowa sai ya kama qugun ta, da sauri ta jujjuya ta na kallon kowanne gefe kar Wani ya gan su a haka, buge hannun shi ta yi har da Wani d'an cije lebe
"In wani ya gan mu fa,"
"Sai in ce ke ki ka ce na d'auke ki kin gaji da tafiya...baby ba maganar wasa ba tin a gida nake kula da ke gaba d'aya kin sauya kamar baki da lafiya ko kin gaji, ina jin zan zo da wuri na maida ki gida dan ki samu ki ware kan gobe tafiya, ko kina ganin mu jinkirta tafiyar sai kin huta? Abubuwa sun maki yawa ko da yaushe cikin aikace-aikace ki ke?"
Girgiza masa kai ta yi, alamar a'a, tana matuqar jin dad'in yanda yake kulawa da ita, yake son sata farin ciki a Koda yaushe.
"Kar ka damu I am ok, mu je ko?"
Suna isa qofar dakin Iya ya duqa ya cire takalmin shi, ita kuma ta shiga ciki, sanan shima ya bi bayan ta,Iya zaune take akan abin sallah, ta yi 'yar qiba abinta a cikin wata d'aya,da yake dama can ita me jikin qiba ce, to komai take so shi take ci dole kuwa ƙiba ta samu muhalli,uwa uba kuma ga kwanciyar hankali ya same ta, banda tinanin halin da Sahabee yake ciki ba abinda ke damun ta a yanzu,su Hajiya Iya se tasbihi ake yi, juyowa ta yi tare da fad'ad'a murmushin ta tana kallon Anwar da Eamaan,addu'a ta yi ta shafa, sannan suka shiga gaisawa, cikin fara'a Iya tace,
"Wannan ne sirikin nawa? Tabarakalla Masha Allahu gashi nan kamar Wanda aka haifa larabawa na Kiran ta'ali ta'ali"
Sosa kai Anwar yayi ya na dariya qasa-qasa Eamaan ma na dariya ta ji ana tab'a ta, shi kuma amfani yayi da d'ayan hannun shi ya zura shi ta bayan Eamaan dake zaune kusa da shi, ya shafa bayan ta, lumshe ido ta yi a hankali ta bud'e su akan shi, girkiza masa kai ta yi alamun ya dena, murmushi ya yi ya kauda kan shi kamar be gan ta ba, ya ci gaba da shafa bayan ta, kyale shi ta yi da halin shi dan ta San ba denawa ze yi ba, ta kalli Iya da ke nad'e abun sallar ta ta na saka wa a saman hannun kujerar da ta tashi kusan ta ta ce,
" Iya me yasa wai baki son komawa cikin gida ne inda kowa yake ki ka zab'i zama a nan wajen ke ɗaya? Ai bai kamata ba hakan a gani na tinda waje ne da aka yi shi Dan masu aiki"
Murmushi kawai Iya ta yi sannan tace,
" Eamaan kenan baiwar Allah, Eamaan Mai saka alkhairi ko da an mata Sharri,Eamaan 'yar aljannah da yardar Allah,kar ki damu Kan ki Eamaan nan shine ya dace dani, dan ba zan koma cikin gida ba gaskiya nan ma ya Isa Kuma na ga nan din ma ai ba laifi, kalli fa gado da kujerun da ke d'akin, tsohuwa da ni har da fridge,ai ba abinda zan ce maku sai dai Allah ya saka da alkairi,"
Ta qarashe maganar ta tare da matse ragowar guntun hawayen da bai sauka ba.
"To Iya yanzu abinda ki ke so dai shi za ayi maki, amma dik sanda kk ji ki na son komawa ciki ki yi magana, akwai d'aki da Zaki yi zaman ki a ciki"
Iya da Anwar har sun Saba saboda hira da suka zage suka sha abun su kamar ba ranar suka fara ganin juna ba, sai labarin yaran ta take bashi, anan ne ya fuskanci irin zaman da Eamaan ta d'an yi da su, dik da ma ta na kauda wasu zantukan na Iya kar ya ji, abinka da tsohon mutum in ya so labari se ya labarta abinda ke cikin shi zai ji dad'i, Anwar ya ji son Eamaan da ganin qimar ta da mutuncin ta sun qaru a idon shi,fatan shi Allah ya bashi zuri'a Mai albarka da ita su zama masu BIYAYYAH kamar ta ko fiye da ita ma.
Se da aka kira la'asar sannan yace zai tafi se ya dawo an jima zai sake leqa Iya yayi mata sallama, rako shi Eamaan ta yi har jikin motar su, bud'e masa mazaunin driver ta yi bayan ya buɗe motar tin Kan su Isa, godiya ya mata ya zauna, can Kuma ya fito kamar Wanda ya yi mantuwa ya manna mata kiss a lips d'in ta,ya na dariya ya koma ya zauna ya rufe qofar shi, zaro idanu waje ta yi daga baya ta qanqance su ta had'e haqoran ta tare da kiran sunan shi, gwalo ya yi mata ya d'aga mata hannu, ya fara tafiya a hankali
"Sai na dawo da anyi magrib zan zo ki shirya, Love you"
"I love you too"
Shiga gida ta yi fuskar ta d'auke da annuri da farin ciki, Mama ce ta kalle ta ta miqa mata hannu d'aya, isa ta yi wajen Maman ta zauna gefen ta sannan ta gyara ta kwantar da kan ta a cinyar Maman
"Nikam Eamaan dama kin gama al'ada ne akai auren ki ko kuma zaki fara ne aka yi?"
Tinani Eamaa ta yi sosai, nan ta gano kamata ya yi ace kwana uku da auren su ta fara amma gashi har yanzu shiru, sanar da Mama ta yi, sai taga Mama na murmushi,
"Ko da na ji, yanayin ki se yake tinamin wasu 'yan shekaru kamar uku da suka wuce" cike da tsokana Maman ta yi maganar ta.
"Maaa mene ne Dan Allah?"
Eamaan ta fada a shagwabe, shafa kan ta Maman ta yi sannan tace,
" Eamaan i think zaki sake zama Mummy ne nan da wasu watanni masu zuwa,ko har kin manta yanda cikin Fateema ya yi miki ne? Ko da yake kowanne ciki yana zuwa da nashi salo,amma shi mijin naki da yake likita be gane komai ba?"
Eamaan tashi ta yi ta zauna da kyau, a hankali komai ke dawo mata a kwakwalwar ta, Wani yawan kwad'ayi, saurin hasala, yawan kasala da sauran su, ga uwa uba an yi tsallaken al'ada, kunya ce ta kama ta ta duqunqune a jikin Mama, tana ta dariya,
"Me ye haka zaki balla min Yaya? Me ake tattaunawa ba da ni ba," Ammaah ce ta qaraso dauke da fara'a itama ta yi wa Kan ta mazauni a gefen su.
" I thing we ar going to become grannies again,"
Ammaah tayi murna a qasan zuciyar ta sosai ,sai ta dinga yi wa Allah godiya, a zahiri Kuma sai tace,
" Lallai wannan angon naki ko amaryar taki da gaske suke, tinda ke kadai ki ka gane samuwar su tin Kan likita ya gano su,ko mijin naki ne ya gwada ki? (Kad'a Kai Eamaan ta yi ta tabbatar mata da ko asibiti ma Basu je ba) amma dai Ina me baku shawara ya kamata ku je asibiti a tabbatar,ko Kuma shi ya duba ki a gida, ba aikin shi bane dama?"
Tashi ta yi ta d'akko musu dambun naman kaza da ta yi da Kan ta a daren jiya da lemon kankana da ta sa Masa ginger da lemo,a hankali Eamaan ta d'iba ta sa a baki, dad'in shi da ya ratsa ta se gata zaune ta tankwashe qafa ta na dumbuza ta na kaiwa baki, se da akai magariba Daddy ya dawo, ya yi matuqar murnar ganin ta itan ma ta yi murnar ganin shi sosai, sannan ta Sanar da shi yanda tayi kewar shi sosai a kwanakin nan, nan fa suka dinga hira da Daddyn ta, har da labarin da ba su yi da Ammaah da Mama ba ta kwashe ta na ba Daddyn ta, Ammaah da Maman ne suka kalli juna suka miqe a tare mama tace,
"Toooo lallai ne, uba ya fi uwa se an jiman ku ku sha hira lafiya,"
Tattara wa Eamaan duk wasu kayayyaki masu amfani da suka San za ta buqata in ta je Bauchin ita da Hafsat suka shiga yi, su Daddawa ne da aka daka da kayan qamshi, su dakakken zogale ne, kayan qamshi ne, su magarya da bagaruwar mata ne, su kuka kub'ewa busasshiya da markad'add'iyar gyad'a ne, abubuwa dai birjik kamar 'yar makarantar boarding haka suka had'a musu ita da 'yar uwar ta Hafsat.
( kar ku manta, matan da ba su da isasshen kud'in siyan turaruka, ko Kuma masu warin zufa da sun yi aiki kad'an za su iya saka Alim a hammatar su bayan sun fito wanka sai su goga shi alim d'in a hammatar, saboda ya dauke wari, in ka saka tirare ba zai warin zufa ba ko wanne irin aiki za kai, sai dai qamshin tiraren ne zalla zai na tashi,mu kiyaye ba a tsarki da alim, yana da illa Daga baya, ganyen zogale Kuma da aka Maida shi gari zata na sha da madara da zuma ne Dan qarin ni'ima,sai ganyen magarya za a na tafasa shi a kama ruwa da shi in ya huce, a wanke HQ da shi, dan dauke wari da qarni da datti, ko ta dafa shi da lalle tai wanka, yana gyara jiki, kayan qamshi kuma musamman mai had'in minannas a ciki na fada maku yana gyara jikin mace, ya bata dumin jiki, da ni'ima, kar muna wasa da aje kayan qamshi, maganin wannan mugun ciwon ne na infection)
Kan a kira isha'i sun kammala had'a mata kayan,Mama ta markada cucumber, da kankana, ta matse ta zuba kayan qamshi a ciki,ta matsa lemon zaqi a ciki, sai ta debo zuma ta saka cokali biyu, asalin mai kyau din ba narkakken sugar ba,(shi din ma ba laifi in ba zumar) sannan ta saka mata madarar shanu, ta juya sosai ta bata ta shanye, komai akan idon ta aka yi, Mama na yi ta na fad'a mata wasu had'e had'en da ke qara saukar da ni'ima da gyara wa mace skin.
Daddy ya tafi masjid Dan gabatar da sallahr isha'i ana idar wa ya dawo gida,saboda Anwar na nan tafe ya na so su gaisa, kafin Anwar ya zo suna zaune Daddy na ta mata nasiha se ya bata kudi masu yawa yace ta ajiye ko zata buqace su, sannan ya bata shawarar ta fara sana'a in ta ga yanayin gurin zai kyau da hakan, zama ba sana'a lalura ne sosai, bani bani bai da dad'i, ya nuna mata yanda su Mama ke business din kayan kitchen da abayoyi ta online, Kuma suke da shaguna a kasuwa, godiya tayi sosai suka zauna zaman jiran Anwar ko minti biyar ba a yi ba kuwa suka Jiyo qarar bud'e gate da dirin mota, Eamaan ta gane cewa Anwar d'in ne amma ta yi shiru se da ya yi sallama ya shiga.
Kafin su gama gaisawa da tab'a hira Eamaan ta shiga d'akin Mama ta sheqa wanka da irin kayan wankan Mama masu dad'in qamshi da gyara fata, Yayah ke siyo musu Daga qasashen waje in ta je kowa da nashi ita da Ammaah, wata doguwar riga Mai bin jiki Mama ta bawa Eamaan ta Sanya, d'aya daga irin kayan da suke siyarwa kenan a shagunan su ita da Ammaah.
Kwalliya Mai sanyi da sanyaya rai Mama ta sa Eamaan yi, Ammaah na ta yi musu dariya, ta na cewa su bar d'an mutane haka Dan Allah ai ya kamu, mama kuwa ta ce inaaa namiji ba a Dena kama shi, yanzu ma suka fara
"To Allah ya baku sa'a kenan zan ce ko? "
"Ameen" Mama ta amsa da shi, Eamaan kuwa sinne Kai ta yi jikin Mama, turaruka masu sanyin qamshi ta fesa sannan ta Sanya mayafi Mai bayyana komai a jikin ta a saman rigar tinda dare ne, Kuma a motar su suke, sallama suka yi wa mutanen gidan, suka raka su har mota, Anwar ne ya tina da Iya ya ce wa Eamaan su je su yi mata sallama, ai kuwa da suka je Iya kukan farin ciki ta dinga yi, ta na musu addu'a da Sanya albarka, se suka qara burge ta, musamman yanda ta ga Eamaan na cike da annashuwa da annuri Wanda ya dace da ita.
Tin a hanya Anwar ke Sanar da ita yanda ya yi missing din ta gaba d'aya ranar,
"Kaiiii Abu Fadheemah yaushe yaushe muka rabu ma? Ko Dake Nima fa na yi missing din ka, Anya za mu Iya kwana bama tare da juna kuwa?"
Ina Jin maganganun su na gane yau gidan su Eamaan fa za a soye za a qurmushe za a raqashe Kuma gidan ba na shigata bane ba, na lallaba nai baya na koma d'akin Iya mu Kwan tare.
Da asuba bayan sun yi wanka sun gabatar da sallahr nafila da farillah suka hau shiri a gurguje, a so samun Anwar su Isa bauchi da qarfe tara ko goma, Dan haka french toast kawai ta musu, da tea suka karya da shi, sannan ta debo dambun naman da ta masu tin kan su fita da su meatpie, da duk dai dan abubuwan da zasu tafi da shi, shi Kuma ya yi ta kaiwa mota, ya na dawowa d'iban wasu kayan, hijab din ta ta saka suka ja qofar suka yi addu'ar fita daga gida suka qara da ta shiga abin hawa, makullan gidan ya damqa a hannun Mai gadin gidan suka masa bankwana suka fita a motar su sai Bauchin Yakubu.
A gidan su da bashi da nisa da na su Hafsat suka sauka, sun tarar Hafsat ta gyara ko Ina ta musu girki sun sha kwalliya gaba d'ayan su ita da Fateema da kamal gwanin sha'awa, sun yi murna sosai da ganin juna, Fatee tafi kowa murna da ganin Daddyn ta Wanda suke waya kullum ba adadi , sanda Hafsat da Kamal suka zo tafiya qin bin su ta yi,dik nacin da Kamal ya yi sai hakura suka yi suka barta, Anwar ya ce kar su damu ta hutar da shi Jin kunyar tambayar a bar masa ita ne, Kamal ya ce gobe za su kawo kayan ta, Eamaan tai masu godiya sosai, suka raka su bakin gate.
*BAYAN SHEKARU TAKWAS*
Fatee na gani da wasu yara guda biyu, ta ruqo masu hannu bayan sun fito daga mota, na mijin na ta tsalle-tsalle sun dawo daga school, da gudu namijin ya je ya rungume Mummyn su sannan ya ce,
" Mummyyyy"
Dariya d'aya yarinyar ta yi ta ce,
"Shiyasa 'yan ajin ku suke ce maka Mama's boy, ji yanda kake abu kamar yaro, kowa ya San kai twin d'ina ne amma kana wani sawa ana raina ni,"
Gashin kanta mai kananan kalba da ya zuba a gaban fuskar ta ta mayar baya ta kada idon ta tana wani yanga, in a matured way ta ce,
" Assalamu alaikum Mummy,"
" Wa'alaikumussalam habibty, ya school ɗin uwar manyance?"
" Alhamdu lilLAAH Mummy, kaifal yaum Mummy?"
" Alhamdu lilLAAH Subai'a"
Fateema ce ta sunkuya ta sumbaci kuncin Eamaan itama ta yi mata sallama, kallo suka nad'e hannaye suna bin qaramin su mai suna Abdullah takwaran Alhaji wanda suke kiran shi da Ameer, cike da tab'ara ya ce musu
" Whattt?"
" Amir say ur salam to Mummy" in ji Fateema, cikin tura baki shima ya yi sannan suka wuce ciki dan cire uniforms din su da Kuma watsa ruwa.
Kafin su fito Eamaan ta haɗa masu abinci, Anwar ne ya shiga kitchen d'in ya same ta ya riqe ta ta baya ya dora wuyan shi a kafadar ta, ya ce
" Allah ya miki albarka mata ta, in dai namiji ke d'aga qafa mace ta shiga aljanna ni kam bana fatan na sake tafiya a qasa, Eamaan na gode, kin ban happy and beautiful family, Wanda suke da tarbiyya da BIYAYYAH kamar ki, Eamaan ke ta daban ce, banda qiriniyar ki wanda itan ma Ina so, har yau ban ga abinda zan kushe ki akai ba, Eamaan ki na da kirki ga ki da tsafta, iya kwalliya, girki, tafiya, magana, bani shawara akan komai, kina son iyayena kamar naki, ga uwa uba tsoron Allah, Eamaan ke mai cikakken imani ce, Allah ya qara son shi da tsoron shi a ran ki, Eamaan kin ci sunan naki dama bahaushe ya ce suna linzami ne, me shi yaka wa Zane to tabbas sunan ki ya bi ki Eamaan Ina son ki Eamaaniii na"
Ba qaramin dad'i ta ji ba da wannan yabon da mijin ta yayi mata, dan haka kawai sai ta juya ta rungume shi ta na sauke ajiyar zuciyar kwanciyar hankali,takun yaran suka ji suka saki juna su na murmushi, kawai se ya fara taya ta diban kayan abincin zuwa dinning, yaran sai suka koma suka zauna suka nutsu suna jiran a kawo abinci, zuzzuba abincin Fateema ta miqe ta fara yi, dan Eamaan ta koya mata yanda zata dinga taimaka mata da aikace aikace a gidan, shi yasa ko Mai aiki Bata da shi, ko rashin lafiya ce ta kama ta Fateema ke mata ayyuka, bismillah suka yi suka fara cin abincin shiru wajen ya yi kamar ba kowa, se Abdullah da ke 'yan maganganun shi in ya ga dama.
Hafsat ta haifi 'yar ta mace mai suna, Amal, ta d'an girmi Subai'a kad'an, amma iyayin Subai'a sai ya sa mutum ya zaci ita ce babba,Yayah itama Allah ya bata yara biyu maza, Sudais da Farouq.
Malam Sahabee kuwa an jima da sakin shi daga gidan yari,ya so matuƙa wajen aikin shi su yafe masa ya ci gaba da aiki da su,amma sai suka qi sam,se fafutukar neman aiki yake abun ya gagara banda kwakwa ba abinda yake ci a rayuwa, in ya je duba Iya ne ma a gidan su Eamaan yake samu ya ci ya qoshi, har ya tafi da Wani,Iya ta qi bashi fuska Sam balle ma ya ce zai kwaso