Showing 30001 words to 33000 words out of 121577 words

Chapter 11 - TURKEN GIDA COMPLETE by Janafty.txt

24 Sep 2025

3426

sai da film ɗin ya ƙare, sannan muka kashe komai muka koma ɗaki. Yusuf ya yi wanka sannan muka kwanta muna rumgume da juna, dukkanmu mun yi shuru muna jin bugun zuciyan juna.

"Yallaɓai na"

"Uhmm"

  Sai na gyara kwanciya a saman ƙirjinsa ina faɗin" Ka yi hakuri, na gaza ba ka dukkan farinciki ta bangaren ƴa'ƴa. Na san kana son yara domin tun kafin mu yi aure in ka zancen wajena sai ka yi ta faɗin Sadiya ko ƴaya goma kika haifa min ba za su isheni ba, na daɗe da sanin kai mai so ka ga gidanka cike da yara ne, bayan haka kuma ƴan'uwanka ma son ka haihu da yawa Nene ma haka, uwa uba ƙannenka da suka yi aure bayanmu duk sun fika yawan ƴaƴa na san ko yaya ne kana jin ba daɗi a ƙasan ranka, ka yi hakuri ba ni da wata mafitar ne."

  Na faɗa muryata na yin ƙasa,. Kamar ba zai yi magana ba na ma ɗauka yana barci ne. Sai da na ɗago ta cikin duhun ɗakin akwai ɗan hasken dake shigowa ta window, na ganshi idanuwansa a lumshe, na fahimci ba barci ya ke yi ba da ya ƙara rumgumeni ƙam a samam kirjinsa. Ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Ni ba ki taɓa gazamin ba,kin ba ni dukkan wani farincikin da ko wani namiji ya ke bukata. Kin zame min matar rufin asiri, da me kika rage ni? Ba ki rageni da komai ba mganar ƴaƴa na faɗa miki in biyun Allah ya bar mana mun gode in ya ƙara mana mun gode, mganar ƴan uwana kuma wannan na su ra'ayin ne, ba wanda ba ya son ya tara kyakyawan zuru'a Sadiya. Ita kuma Nene ki daina maganarta jikokinta nawa? Me ya sa sai nawa ne za ta damu domin ban haifa da yawa ba?

  Idanuwana suka kawo kwallah kafin na ce"Saboda kai ne Tafida. Kowa ya shaida kai ɗan gatan Nene, ne ta sha yi maka addu'an ka gaji mahaifinka wajen tara  zuru'a mai yawa. Sannan ka manta burin ka na sake haihuwata domin na yi ma Alhajinku takwara?

  Numfashi ya saki ya fesar kafin ya ce"Ban manta ba. In kin sake haihuwan zan yi ma Allah godiya in ma ba ki sake ba duka godiyar zan yi masa, ai bar ni haka ba ya bani biyu, ina waɗanda suke nema har yau ko ɗaya ba su samu ba? Ko ban yi ma Alhajinmu takwara ba, ƴaƴan sa nawa ne suka yi masa? Masu sunan Alhaji ai ba su da adadi  ballatana in sha Allahu za ki sake haihuwa bayan Alhajinn Gwammaja har Alhajinmu za mu yi ma takwara in sha Allahu."

  Kansa na ɗago na sumbata kafin na ce" Allah ya amsa" ya amsa min da Amin, ƙara shiga jikin juna muka yi, ya na so ya yi barci ni kuma ba na jin barci.

  "Sadiya ta"

  "Yallaɓai na."

  "Barci na ke ji,"

  Haka ya faɗa mini a saitin kunnena, sai na yi mirmishi kafin na ce"Saura magana ɗaya ta rage, in muka gama sai mu yi barcin ko?

"Umh"

Kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba, ni kuma sai na yi shuru saboda ina ƙoƙarin iya faɗin abun da ke cikin raina.

"Yallaɓai."

"Ina jin ki"

  Haka ya faɗa ya na tusa hannunsa a cikin rigata, wani sanyi na ji a cikin raina nima sai na kai hannuna saman kirjinsa ina shafawa kafin na ce.

  "Yallaɓai na, kana son ka ƙara aure ko?

Ya ji ni, amman bai yi mgana ba ina wasa da gashin ƙirjinsa cikin wani salo, mirginawa ya yi kaina ya kama bakina ya na kissing, nima sai na tallafi kanshi, daga nan mu ɗan birkita juna da salon wassani kafin mu koma muna maida nunfashi, tunda mai jan mota ya yi bakare a ƙofar boda ba halin shiga kuma ba halin fita.

  "Ƙarin aure hukunci ne na ubangiji. In Allah ya kaddaromin zan iya ƙarawa, amman ni a yanzu ba ni da ra'ayi domin duk abinda namijin kwarai ke nema a wajen mace ina samu a wajen ki, me zan nema kuma a wajen wata macen?
Raɗa na yi masa a kunne sai ya zille ya na dariya kafin ya mirgina ni na dawo saman shi ya ɗaga ni na zauna a saman cikinsa yana kallona ya ce" Ina samun natsuwa a tare da ke, har ina jin ba Namijin da ya kai ni morewa ma aure. Ko wata na aura an ya za ta kai ki a wajena?
Ina dariya na ce"Oho. Amman dai ni nasan halin maza ne, kun ce ba kwa ta cin shinkafa ba sirki ba, gwara ku sirka da taliya ko macaroni"

  Dariya ya fashe dashi ina taya shi.
"To ni ke ce komai na, Taliyar macaronin tuwon duka kowani nau'in"
Kafaɗa na noƙe ina faɗin"Ba na son yaudara da daɗin baki"

"Sadiya ni zan yaudare ki? Yusuf ɗin ki ne fa?

  Sukuwa na yi a kansa ina faɗin"Daɗin bakin maza ba, shi ne yaudaran"
Nishi ya yi kafin ya ce"Ba dadin baki fa a tsakanin Yusuf da Sadiyarsa. Allah da gaske na ke yi  ke ce duka kayan daɗi na."

  Ya faɗa ya na saka duka hannuwansa cikin rigata ta ƙasa, ya fara matsa min ciki da karfi, ina bige hannunsa ina cewa ya bari yaƙi, sai da na mirgina ya bina ya hau kaina yana ta matse mini ciki ina ta dariya har da hawaye sai da ya ga zan shiɗe sannan ya ɗagani yana faɗin"Ba daɗin baki Yusuf ke yi ba ko?
Ina dariya na ce"Yallaɓaina ba ya daɗin baki."

  Sai ya koma gefe ya na faɗin"Good. Girl."
Kafa na saka na shure sa ina faɗin" Sai na rama"
Yana dariyan keta ya ce"To taho mana, zo ki rama."

  Ya faɗa yana ƙokarin kamoni na matsa baya ina dariya na san halinshi, yanzu sai ya yi min mugunta, bi na ya yi yana faɗin taho ki rama mana Allah ba komai,

  Na haura ƙarshen gado ina faɗin" Ina ga na yafe maka." Dariya saka irin ta nishaɗin nan, sai da na tabbatar da ya ce ba zai min komai ba sannan na dawo jikinsa muka kwanta muna maida numfashi.

"Ka matse min ciki, in ka kashemin ƙwayayon haihuwata fa?

Ya na ƙokarin mikewa ya ce" Mu ga ni?  Ni fa na san in da na matse."

  Hannunsa na bige ina faɗin" Wato su ƙarishe mutuwa ka samu hujjar ƙara aure ko? Na faɗa ina yar dariya shi kuma ya daina dariyan ya koma ya kwanta kawai na fahimci baya son maganar yasa na koma na lafe saman kirjinsa ina faɗin.

"Ka sa ni ko aure ka ƙara ba zan taɓa juya maka baya ba. Saboda duk abin da ka kake so nima ina so, sannan ina son ka tara zuru'a kaima, amman abu ɗaya na ke so, don Allah kar ka yi hakuri ka ji a ranka saboda ban cike maka wani gurbi ba, mun kusa cika adadin shekaru sha biyar da auran mu, har ga Allah ban sa a raina zamu dauwama mu kaɗai ba, amman ina fatan lokacin da za ka yi auran ka wadatamu ka wadata kanka kada ka ɗauko aure ba tare da ka shirya ma hakan ba ka ji ko Yallabai na?

"Na ji."

  Haka kawai ya ce, na san halin kayana sai na fara shafa fuskarsa zuwa gemunsa ina faɗin" Ka yi fushi da ni ne?
Hannuna ya riƙe kafin ya ce"Ko ɗaya. Na ji maganarki amman ina so ki sani ko mata nawa zan aura a bayanki ne, kin zama Turken gidana ke ce tsanin duk matakin da na taka arayuwata. Ki bar ni da maganar auren nan."

  "Mu kwanta mu yi barci"

  Haka ya faɗa ganin ina shirin yin magana, dare ya yi domin ɗaya ma ta gota. Lafewa na yi saman kirjinsa shima haka tun muna jin bugun zuciyar juna, har barci ya kwashe mu gabaɗaya.

  Sanin halin da na ke ciki ya sa Yusuf bai ma tashe ni ba, ko da na tashi har su Jidda sun tafi makaranta. Yusuf ya yi musu abin karyawa da na lunch box, sannan muma ya dafa mana Tea ya soya mana ƙwai, ina ta shi ya ta sani tiolet ya ce na yi wanka ko da na fito ya zubomin tea a mug ya ce na sha sannan shima ya shiga wanka,  ban yi mamakin Yusuf ba sanin halin shi, ba shi da ƙiyuwar aiki, ya kuma iya komai yanzu ne ma aiki ya yi masa yawa amman zamanin farko farkon auran mu ai na mori Yusuf sosai. Shi ya yi zaman Bording School, shi ya sa aiki ba ya gagaran shi na tuna haihuwan Jidda na farko a gida na haihu kafin Gwaggo ta zo har ya gama wanke duka kayan jinin nan, haka zan tafi makaranta ban gyara gida ba sai dai na dawo na ga ya gyara gidan ya yi mana abinci, lokacin nan har makaranta ya ke rakani ya ɗaukar min Jidda,  kafin ya samu aikin nan na shi ya kankama mun gina wata rayuwa ne mai wuyar mantawa.

  Har ya bar gidan nan bai barni na ɗauki ko kofi ba. Sai da na raka shi ya tafi sannan na je na wanke kayana na jiya  da na ɓata na fita haraba na shanya, na ɗaga waya na kira wayar Saude na ce yau ta zo da wuri, kasala na ke ji na kasa komai gashi har lokacin jinin bai tsaya ba amman dai ba ya zuba sosai.

Da wuri Saude ta zo ta yi mini aikace aikace ta yi girki, sai wajen ukun rana na ba ta kuɗin mota ta koma gida, sukuku sukuku dai na yini Hauwa ma ta kira ni wai jiya ba ta san tafiya na ba, na ce ban jin daɗi ne, ta yi min sannu har ta na cewa ko zan leƙo can gidan Haliman? Na ce gaskiya a'a saboda ba na jin ƙarfin jikina ta yi min sannu sannan muka yi sallama.
Ni fa ko lafiyata ƙalau ba zan koma ba ko Rahila da ta haihu sau ɗaya na je sai ana gobe suna da ranar suna na koma.

  Saboda yanayina tun ranar ban ƙara fita ba ina gida ina shirin tafiya Zariya. Na gama haɗa duka takardun gwaje gwajen da aka yi min a asibitocin kano da tests da sauransu waje ɗaya saboda kar na manta. Na ma kira Anty Khaleesat na faɗa mata ina nan zuwa, Yaya Hamzan dai na kira shi ban samu ba.
Ranar asabar da yamma muka je gidanmu tare da Yara na sanar da Gwaggo tafiyata Zariya ta ce Allah ya sa a dace. Na jira har Alhajinmu ya dawo shima na faɗa masa.

"Allah ya sa ki je a sa'a. Allah ya sa a samu abin da ake nema."

  Na amsa masa da Amin Amin, mun daɗe a gidan sai wajen goman dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu, shima baya samun zama a Rano ya ke yini, saboda ya samu kwangilan gina wannan gidan biredin, gabaɗaya ya kwashe kuɗin hannunsa ya zura a ciki.
Sai da muka dawo gida mun yi shirin kwanciya na ji suna waya da Uncle Abba, na ji kuma ya na faɗin bashi da kuɗi.

  Sai da suka gama waya, ina gaban madubi ina saka Humra, yau ni amarya ce domin jinin ya ɗauke min yau da safe,shi kuma ya na zaune gefen gado daga shi sai ƙaramin wando.

"Wai an ya za ka samu rakani asibitin nan kuwa?

  Na faɗa ina kallon bayansa ta cikin madubi, bai juyo ba na ji ya ce"Ina tunanin haka nima, saboda aikin nan kuma kin ga ana buƙata ta a wajen"
 
  Sai da na gama fesa turaren na gyara gashina da na kasa kitso har yau, kuma na kasa wanke shi a gida na kuma kasa zuwa a sake wanke mini.

  Gabansa na zagayo ina faɗin"In ba ka da lokaci ka bari gobe kawai na tafi, in na ga likitan zuwa jibi sai na dawo in sha Allahu."

  Kallona ya yi kafin ya ijiye wayarsa a gefe, ya saka hannu ya jawo ni na zauna a saman cinyarsa ya zagaye hannayensa a kuguna muna kallon juna.

"Kin tabbatar da ba matsala in kika tafi ke kaɗai?

  Ina yar dariya na ce"Haba! Kamar wata yarinya? Ba matsala Allah tunda aiki ne ya hana ka rakani."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce"Ga lambar Dr Fadil Abba ya turamin ya ce sun yi mgana in kika je asibitin shi za ki fara nema."

  Sai na gyaɗa masa kaina gudun mantuwa sai ya ce na ɗauko wayata na kwashe lambar, tashi na yi na ɗauko ya faɗamin na saka na yi saving ina so na yi masa maganar kuɗi amman kuma sai na fasa na san Yusuf game da lafiyata in dai yana da shi ba abin da ba zai yi min ba, ni ina da kudi a hannuna 40k, na so na siya ma Halima turmi atamfa da rigan yaro amman sai na ga Yusuf ba shi da kuɗi ya saka a wannan aikin sai na dakata, in har bai ba ni da yawa ba sai na ɗauka na ƙara dashi.

  A daran mun raba dare muna farantama juna rai.
Muna ƙamƙame juna, cikin shauƙi da kauna.

"I miss you Sadiya ta."

Mirmishi na yi ban yi magana ba. Shi ya ta shi ya fara yin wanka sannan ya tasheni nima na yi wankan Sannan muka dawo muka sake kwanciya sai asuba muka tashi, Saboda ina da tafiya a gaba na da wuri na tashi.

  Lahadi ne yara suna gida, shima Yusuf din ya ce mini sai azahar zai tafi Rano. Ni na yi mana Breakfast muka karya gabaɗaya sannan na yi wanka na shirya Yallaɓai ya ce na tafi da wuri baya son na yi yammah a hanya..
Kaya kala biyu na haɗa a karamar akwatina Baby na ganin na haɗa kaya ta fara rigiman sai ta je, Babanta ne ya zauna ya na lallashinta.

  Na kira wayar Saude ban samu ba sai na kira na Balaraba mamanta, na faɗa mata zan yi tafiya Saude ta zo da wuri ta gyara gida ta yi ma yara abinci sannan in ba damuwa ta kwana da su kafin na dawo duk da nasan Yallabai zai kula da su ga jidda amman gwara dai na barsu tare da Sauden tun da shi sai dare yake dawowa Balaraba ta yi min fatan dawowa lafiya tace Saude ta je islamiya in ta dawo za ta zo in sha Allahu.

  Yallaɓai ya saka mini duka Report ɗina na asibitin da na ta zuwa a baya a cikin ƙaramar jakata ya turamin 30k a acct ɗina lokacin muna hanya shi da yara za su kaini  tasha misalin sha ɗaya na safe.

"Na ga 30k Yallaɓaina. Ina godiya."

  Duk na san kuɗin sun yi kaɗan amman ban iya masa ƙorafi ba, ba halina ba ne.

  Ya na tuki su Jidda na bayan mota ya waiwaya yana kallona ina sanye da hijabi, na saka abaya da mayafi ya ce na cire na saka hijabi sai na sauya kaya zuwa atamfa doguwar riga.

"Ki yi hakuri Sadiya ba kuɗi a hannuna in akwai kuɗi a hannunki ki cika duk abin da kika kashe ki rubuta, in an biya mu zan biya ki duka kudaɗenki in sha Allahu."

"To."

  Kawai na ce masa, domin na saba jin in aka biyamu zan biyaki duka kuɗinki kuma an sha biyan shi ɗin amman sai ya manta da ni in na yi mgana sai ya ce kuɗin sun ƙare na yi hakuri a gaba zai biyani.

Ba su bar tasha ba sai da motar mu ta tashi, sit ɗin mutum biyu Yallaɓai ya biya min kada na takura, sannan ya biya kuɗin mota muka rumgume juna ni da shi, yaran ma haka suna ɗaga min hannu ina ɗaga musu motar mu ta bar tashan, sai bayam mun tashi ina ga shima ya tuka motar zuwa gida.

  Muna hanya ma na sake kiran Anty Khaleesat, tunda da safe ta kirani ta ce yaushe zan ta so,  na ce mata zuwa sha ɗaya na rana lokacin da na ce mata mun taso Yaya Hamza na gida har ya karɓi wayar ya na faɗin" Na ɗauka Yallaɓan na ki ne zai kawo ki?

  Ina dariya na ce"Haka ya so, amman ya fara wani aiki kuma ka san ana bukatarsa sai na ce kawai ya yi zamansa ni na je na dawo"

  Sai ya ce ai shikenan Allah ya kawo mu lafiiya. Na amsa musu da Amin sannan muka yi sallama.
 
  Kafin mu sauka Zariya ban san sau nawa Yallaɓai ya kirani ba, na sauka ma a kwangila Zariya ya sake kirana na ce yanzu zan samu Adaidaita zuwa anguwan da Gidan Yaya Hamza ya ke. Gra kusa da bankin Gt Bank in da yake aiki.

****

  Ina zaune a falon gidan Yaya Hamza rashe rashe ina cin abinci shinkafa da miyar Naman rago da Anty Khalesat ta yi min, ita ta na zaune a saman kujera ta ba ma Amna nono muna hira sai ga kiran wayata da ke saman kujera a cikin jakata tun da na iso na watsar da su saman kujera ban bi ta kai ba.

Na iske Yaya Hamza a gida amman ban daɗe da zuwa ba ya fita ya ce wani abokin aikinsa mahaifinshi ya rasu za su je Ta'aziyya.

Khaleesat ta fi kusa da jakar ita ta matsa ta ɗauko jakar ta, bude ta ɗauko wayar.

"Waye?

" Wata wai Sameena Tafida Rano."

Mirmishi na saki kafin na ce Allah Sarki  da hannuna na hagu na miƙa hannu na karɓi wayar.

"Wace ce? Ƙanwar Yallaɓai ce?

Sai na girgiza mata kai, kafin na ce"E, a'a. Ɗiyar marigayi Tafidan Rano ce."

  Ɗaga kiran na yi da fara'arta kamar yadda muka saba mace ƙwara ɗaya da muke mutumci sosai daga gidan Marigayi Alhaji Yusuf Tafidan rano, duk cikin su da ita kaɗai na saba kuma na ke zumunci ko Gimbiya  da muke da lambar juna ba ma waya iyaka ta dai in mun haɗu a gidan Nene ko Rano gaisuwan fatar baki ce.

"Matar Baba."

Haka ta faɗa daga bangarenta ina dariya na amsa mata mu ka gaisa da tambayan yara. Da ta ce min ta zo sunan Halima na gobe ba ta ganni ba an ce ina Zaria. Daman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login