Showing 6001 words to 9000 words out of 13980 words

Chapter 3 - ZUCIYA DA KWANJI 4 Complete Writing by MAIMUNA IDRIS SANI BELI .pdf

sai ko ta kula,ta ci gaba da

magana
cikin sarkewa harshe. "Abdul me ya sa ba ka
yi
shawara danu ba kafin ka kai maganar nan
kunnen malam? Idan matsalar ita ce
damuwa da
na yi sai na bar gidan nan me ya sa ba ka
bani
zabi ba ni ji ko zan iya zabar in zauna?
Shekara
daya da na zauna daure ni ka yi ne
abdul....? Ya
fahimci ba cikin hayyacinmta take ba,ya kai
hannu ya rufe bakinta sannan ya sake ta ya
mike. "Ki yi hakuri ba bisa son raina hakan
ta
faru ba,kamawa ta yi bisa dole,ko baki da
labarin
kamun da aka yi min na Alh ne?"
2 · Like · React · Report · May 21, 2015
Zulaikha Haroun
Tnks
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4

8)Ta dafe kai da sauri tana ambaton
innalillahi
wa'ina ilaihir raji'un! Ta dago cikin hawaye
ta
dube shi. "Na rantse maka da Allah, abdul
babu
hannuna a ciki". Ya yi gaba dan baya son su
ci
gana da shanya malam,yana cewa. "Na sani
kar
ki damu,ki skirya malam din ya shigo. Ta
tashi
da sauri ta biyo shi. "Amma dai sai ka tsaya
ka
fada min da fuskar da zan karbe shi,na
yarda
bani da zabi sai abin da ka zaba min abdul"
Ya yi
dum yana kallon ta, ya tattara dukkan
hankalinsa
gare ta, kai tsaye ya amsa mata. "Ki sami
nutsuwa ai ba tuhumarki zai yi ba, bana
tsammanin zai yi hakan,kawai dai ki bude
kunnena basira ki saurare shi,duk abin da
kika ji

daga gare shi ki hada shi da hankali ki yanke
hukunci,shawarar da zan iya baki ke
nan....." Bai
jira cewarta ba ya fice,babu jimawa suka
dawo da
malam,har shigowar su ba ta yanke
tsayayyen
hukunci ba. Ta dai ganta a tsaye lokacin da
malam ya shigo,kanta a kasa har sai lokacin
da
malam ya zauna sannan ta. Zube ta gaishe
shi
har wannan lokacin kanta na duban kasa.
Malam
na ta faman sanya mata albarka,ita kuma
tana
jin ina ma ta girgiza ta zama ba ita ba,
saboda
tsabar kunya da muzanta. A nutse abdullahi
ya
juya ya fice. Malam ya yi gyaran murya ya
ce.
"Fatima zauna sosai mana" Ta dan muskta
a
takure saboda zaman da ta yi ita kanta ta

kasa
numfashiwa sosai. Malam bai gajiya ba ya
kuma
cewa. "Wai bani na ce ki zauna ba ne, ki
koma
kujera ki zauna,lalura ai ta kori komai"
Cikin
tsannanin kunya da kasa iya dagao ido ta
koma
kujerar. Malam ya gyara zama ya ce. "Ina
fatan
ranki ba zai baci baci game da shishshigin da
na
sa kaina yi a cikin al'amuranki ba". Ta yi
saurin
girgiza kai amma ba ta tanka ba. Shima bai
jira
ta ba ya dora. "Zan yi hakan ne dan ina ji
a raina
na isa da ke kamar yadda na isa da mijinki
da
nake ganin ba ki da bambanci da shi, sannan
a
waje daya da yunkurin kyautata amanar da
iyayenki suka bamu,da kuma kwatanta rama

karamcin da suka yi mana. Fadima ke ba
yarinya
ba ce kin yiwa shekarun da idan kin yi abu
za a
hada kallon sa da kuruciyarki,ga shi kuma
kin
rayu cikin ilimi babu jahilci a
kwanyarki,sannan
kin sami tarbiya bare in kin yi abu a ce an
san za
ki rina saboda iyayenki sun kasa sauke
nauyin
tarbiyarki. Abin mamaki iyayenki sun san ya
kamata matuka,kuma ba sa salwantar da
tarbiyar
addininsu haka.kawai. Fadima me ya sa
kuke son
jaza musu ayi musu irin kallon nan da ake
wa
mutumin da ake ganin an fitar da matacce
daga
rayayye? Ga shi kuma Allah ya halicceki
mace
mai rauni wadda karkonta ke samuwa ta
silar

biyayyarta ga Allah tare da saukake wa kai
rayuwa. Ba dan jinsin mace ba shi da daraja
ba,sai dan rauninsu da ya zagaye rayuwarsu
da
daraja. Bare musanmman a zamanin nan da
mutum ke wa kansa fada ya rasa mai masa,
saboda haka masu mafada suka zama wasu
shalele wanda kuma ya rasa mafadin ya
kuma
kasa yiwa kansa fada sai a kira shi dan iska
kowa na gani. To a 'yan uwance, 'yan
uwantaka
ta musulunci zan miki nasiha wadda babu
doka
cikinta illa na cika da fatan ki fadaka dan
ki sami
babban rabo,nasihar da na tabbatar ba
sabuwa
ba ce a kunnenki illa dai tunatarwa kawai.
Kamar
yadda kika sani,an kama mijinki Abdullahi
tsawon
wata uku kan hudu,da farko ba mu san
dalilin
kamun da aka yi masa ba da wanda ya yi

kamun,
daga baya da muka tsannanta bincike sai
muka
gano tsohon mijinki sulaiman ya sa aka kama
shi. Sai dai har zuwa jiya da Allah ya kubuto
da
shi babu labarin laifin da ake tuhumar sa da
shi,sai a jiya da na matsa masa sannan ya
labarta min yadda kuka yi. Bayan wannan
ya yi
min magangun. Masu yawa,kuma masu nauyi
akanki. Bai kamata na dawo miki dasu baya
ba
ne dan kar ki zaci goyob bayansa nake,dan a
nan
ba zan taba cewa Abdullahi ya kyauta ba,
saboda
yaudara ba ta da kyau. Rashin kyauta kuma
na
muni musamman a cikin sha'anin aure
wanda
ubangiji ya sharadan ta soyayya da tausayi
a
tsakanin miji da mata wanda sune tushen
samar

da zaman lafoya a tsakanin iyali masu hadin
kai
da kaunar juna. To abdullahi bai nemi
yardarki ba
bare soyayarki,ya kawo ki karkashinsa dan ki
yi
rayuwa ta har abada. Tabbas bai miki adalci
ba,kuma Allah zai bi hakkin ki matukar ba ki
yafe
masa ba,domin babu wanda ya
Hafsat
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
9)Aike shi auren ki kwanji dan ya hana ki
sabawa
Allah na halatta abin da ya haramta,in Allah
bai
miki dolen sai kin bi shi ba ya baki zabin wuta
da
aljanna babu dalilin da Abdullahi zai rike ya
ce
sai kin bi Allah. Amma fa ki sani wannan ba
zai
zame miki lasisin da za ki ki biyayyar auren

da
aka auro ki da basaja na,kuma ba zai zama
dalilan da za a karkade littafin hisabinki ya
tafi
hutu daga kurankuran da kike tafkawa ido
bude
ba. Sai dai ba za rufe ban kara nanata miki
abin
da kika dade da sani ba, wannan kullin da
kuka
taru ku uku kuka kulla ubangiji ya haramta
shi,
manzon Allah (S A W) ya tsinewa wanda ya
auri
mace dan ya. Halattawa wani ita,da kuma
wanda
aka hallatawa din. Ban san wanne tanadi
kuke wa
kanku ba a cikin damararku ta dorewa da
rayuwarku cikin sabon Allah,tsakanin ke da
Alh
babu babba babu yaro bare a gane wanda ya
fi
marisa cikin wannan guguwar zamanin. To ba
zan cika ki da dogon surutu ba fadima,na zo

ne
dan in shawarce ki sannan in baki zabi,
zamanki
a gidan nan bisa zabin kanki naki. Tunda
wanda
ya halicce ki bai matsa miki sai kin bishi ba
bare
ni da Abdullahi,sai dai zan yi farin ciki idan
kika
zabi biyayya ga ubangijiki. Kika watsar da
shaidan wanda ke kada miki gangansa
alhalin kin
sa makiyin ne gare ki,kin fahimci ni? Ta yi
shiru
kanta na kasa,illa hawaye da yake diga a
sannu.
Har malam ya gaji da jiran cewar ta yi nisa
ya
ce. "Ko kina ganin in baki lokaci ki yi
nazari? Ba
matsa miki nake son yi ba,ina dai son a yiwa
tufkar hanci ne. Game da yadda rayuwa
abdullahi
ke cikin halin kila wakala ta bangaren Alh.
Kuma

da muryaki zan yanke duk hukunci da zan
yanke,in kin karbi abdullahi in na sami Alh
zan
dorar masa dan ya saurara hak,in kuma kin
zabi
rabuwarku kin ga babu bukatar ma na ga
Alh. Sai
lokacin ta fara goge hawayen da ke zuba
idonta
iyakar son ransa,ta girgiza kai cikin
rarraunar
murya ta ce. "Na sadaukar maka da
biyayyata ka
yi duk abin da ka zaba a cikin aurena da
abdullahi,ka bar auren idan za ka iya juriya
da
runyse ido a cikin zamana cikin a
halinka,idan ma
ba ka zabi hakan ba ai na cancanta Abdul
ya bar
aure na,ni kuma na yi alkwarin ba zan
komawa
Alh ba". Cike da farin ciki malam ya ce. "Me
ne
sai na runtse ido cikin za$mowar ki ahalina?

Na
rantse miki duk cikin surukaina ban so wata
kamar ki ba, saboda karamci da mutumcin
iyayenki,kema kuma kina kwatantawa. Ku yi
irin
wannan zaman tsawon shekara amma babu
wanda ya taba jin kanku ba kya sa ran da
wata
riba amma haka kike tattalin 'yan
uwansa.ina
yawan jin suna yabonki. Saboda haka ni har
yau
ba ki canja a idon ba sai ma wata karin
kima da
kima karawa kanki a gurina na dauka na
uba,tare
da nuna na isa a cikin lamuranki. Na gode
miki
Allah ya yi miki albarka. To ina rokonko
zama da
abdullahi,ki yi bautar aure yadda ubangiji
ya tsaro
miki,ki yawaita istigafari,ki kuma nemi
gafarar
mijinki,sannan ki yawaita addu'ar ubangiji

ya
sanya miki soyayyar mijinki. Ku zauna
lafiya,dan
Allah ku bawa mara da kunya,ku kafawa
zuri'ar
tushe mai kyau mai karko da sha'awa,hadin
kanku shine farko abin da zai hada kanku a
tarbiyar 'ya'yanku. Allah ya yi muku
albarka,Allah
ya sauke ki lafiya fadima,ya baku 'ya 'ya
na
gari". Har yanzu kuka kawai take. Malam ya
rufe
batunsa da cewa "Abu na karshe da nake
nema
gare ki shi ne,ki rubuto takardar amincewar
zaman da abdullahi da radin akanki ki san
hannu,ku hada da duk wani abu da kuka
karba
daga. Alh game da auren,ni zan ganshi mu yi
sulhu in mayar masa da kudadensa,in ya
yarda da
sulhu zamu yi,in kuma ya ki amincewa zan
biyo
masa ta hanyar da yake biyo mana". Ta

kada kai
kawai malam ya mike yana ta sheka mata
kwandunnan albarka,sannan ya yi mata
sallama
ya fita. Abdullahi na jin motsin fitowarsa ya
yi
saurin mikewa ya fito tsakar gida,kai tsaye
malam ya doshi waje yana cewa. "Ka sanar
da su
na tafi". Abdullahi na amsawa a ladabce
cikin
sanyin jiki,ya take wa malam baya har sai
da
motarsa ta daga yana godiya. Sannan ya
juyo
gida jiki a sanyaye cike da fargaba ko dokin
sanin
abin da ya shiga tsakanin fadima da
malam,ga
shi babu halin da zai nufi dakinta yanzu
alhalin
ga su hindatu da sadiya zagaye da shi suna
ta
faman tattalinsa. ***************
***************

*********** Tun bayan fitar malam fadima
ta
zauna wa kuka,ta rasa ta inda za ta
kamfato
wannan rayuwar bare yadda za ta yi ta, duk
kuwa
da dama ba tun yau take jin tilashin zama
da
abdullahi ya kama ta ba,amma yau da
malam ya
kaddamar da shi sai ta ji duk abubuwan sun
yi
mata nauyi. Shaidan ya dinga yi mata
hudubobi
iri iri yana nuna mata gidan abdullahi
kurkuku
ne,babu iko ko kankani na yin abin da mutun
ke
so,ga dima diman mata biyu a matsayin
kishiyoyinta,cikinsu har da wadda ta dauki
kisa
ba a bakin komai ba,wannan babban kalibale
ne a
cikin zamanta a gida. Amma data damu da
kanta

da neman fin karfin zuciyarta,sai ta so ta yi
wannan nasarar ta hanyar halarto ajin
wanda za
ta zauna a karkashinsa wato abdullahi. Ta
fara
tuno shine tun daga ranar da suka fara
haduwa,ganin farko ta raina masa wayo
matuka,kallon da ta yi masa na jin kai ya sa
ta ji
ta tsane. Amma da yake jarumi ne da
wannan jin
kan nasa ya fanshe rainin da ta yi masa ta
hanyar kin sarayar da dukkan hakin da ba
nata ba
yake gudun kasawa,sannan yake kin a raina
shi.
Cikin hikima yana kai wa wannan matakin sai
ya
fito mata da kyawawan halayen masu wahala
a
maza mai sassaukar mu'amala,mai sanyaya
soyayyarta kullum da kari. Ya zama bawanta
na
bayar da labari,ya hana ta hawaye,ya nuna
wa

kowa yana sonta ciki har da abokan
burminta. A
wani bangaren kuma ya nuna tsayuwa da
kafafu
cikin tarbiyarta. A dunkule abdullahi ya
amsa
sunan namiji wanda ya amsa shugabancin da
aka
ba shi a kan mace, wadda ya fita karfin
zuciya da
na kwanji,sannan ya mallaki soyayyarta da
tausayi,kuma ya zama mai yawan
kyautatawa
gare ta. Wannan karfin gwiwa ne a cikin
zama da
abdullahi,musamman da yake wadancan
matsaloli ne wadanda ba za su gagara gyara
ba.
Har karfe goma da rabi na dare tana cikin
wannan damuwar ta tufka da warwara. Duk
dauriyarta dole rayuwar gidan nan ta yi
wuya,ba
za ta iya tana katsina mijinta na daura a
muhali
guda ba. In akwai abin da zai dinga ci mata

tuwo
a kwarya bayan wannan zai bi,amma dai
kafin ta
ma fito da kwaryar tata za ta zama mai
kwarjini.
Ta daga kai ta dubi agogo wanda ya nuna
sha
daya saura. Ba wai kasala da yawan 'yan
jaje ya
hana abdullahi neman fatima ba,sai dan
yadda
sadiya ta dage da tattalinsa,duk motsin da
ya yi
sai ta yi sai ta yi masa sannu,ko ina ya yi
idonta
na kai. Abin ci da sha daga wannan sai
wancan,
wannan ne ya kauwame shi watsa mata kasa
a
ido ya tafi neman fatima kamar yadda ya
kwana
da sanin ita ba za ta Zo wajensa ba ko
fuskarta
ya kalla ya ji sanyi. Amma duk yadda yake
daurewa sadiya,karfe goma da rabi sai ta

fara
kular da shi. Hindatu ta yi musu bankwana ta
tafi,kawai sai sadiya ta mike ta garkame
kofar
daki, ke nan ta kulle masa maganar ya ce
zai je
ganin fatima. Wannan ya sa ya dauke mata
wuta
dif! Ya dinga faman kunci,yana
numfarfashi.ta yi
masa maganar wanka ya yi wankan ya
fito,ta
miko masa kayan bacci amma sai ya karba
kawai
ya ajiye ya sanya jallabiya ya fito falo ta
biyo
shi. Fuskarsa babu walwala ya ce. "Ba ni
tea".
Jikinta na baru ta tafi ta kawo masa
maimakon
ya sha sai kawai ya bige da juya shi cikin
dogon
tunani. Dai dai wannan lokacin fatima ta
kawo
gabar da take son motsa nata kwanjin,ta

zabi
amsa kaddarowa tarayya a kan namiji
guda. Dole
ta koyi hadda domin ta samu wanke allonta.
Ta
yi wanka a gaggauce ta saka kayan
bacci,sannan
ta saka zundumemen hijabi ta tunkari fadar
oga.
A razane abdullahi ya daga kai ya dubi kofa
lokacin da fatima ta kwankwasa,duk da ya
san
yaudarar kai ne zargi cewa fatina ce, amma
sai
kawai ya ji ya kamata a ce ita din ce
Like · React · Report · May 21, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 4
10)Sadiya ta san ita ce,kumallonta kuma ya
yunkuro
nan take kuka ta fashe shi. "Waye! Mts!!
Mene
ne?" Da sauri abdullahi ya yi mata wani irin
kallo
rai bace ya ce. "Sadiya wanne irin rashin

hankali
ne wannan?" Ta yi saroro cikin mamaki ta ce
"Rashin hankali kuma abu turab?" Ya yi fusk
ya
kawar da kai, tsaurin idon da ta yi masa
kwanaki
na dawo masa a rai. Ya ji kaico ya cika
ransa,dole ne su zauna ta janye wadancan
kalmomin in ba haka ba zai ci gaba da ganin
bakinsu har abda. Yanzu dai sai ya daure ya
ce.
"Ki je ki bude kofar" Ta yi karamar kwabar
da ta
sa shi bin ta da kallo tana ba shi haushi har
ta
dawo ta zauna. Idonsa a kan kofa fatima ta
murza ta shigo,sanye cikin hijabi mai hannu
har
kasa,sai fara fuskarta tas wadda ta kara
haske a
kyan lantarki,sai dai idanuwanta ba su boye
sun
sha kuka ba. Ta yi sallama cikin kasala
sadiya ta
bi ta da satar harara,shi kuwa sai da ya

sauke
kofin tea dinsa ma sannan ya amsa mata
fuska
cike da mamaki. Kai tsaye kuma ta tarar da
shi
inda yake zaune, saboda haka ya dauki
barin jikin
janyo fillallukan kujera ya zube yana gyara
mata
yana hadu mata da sannu. Ta zauna
hankalinta
na kansa kuncinta da murmushinta mai kyau
ta
ce. "Sannu abdul". Ya kasa amsawa saboda
rikita,sai kawai ya yi murmushi ya bige da
karbar
shayi. Ta dan bi dakin da kallo ciki har da
sadiya
mai harara a duhu,sannan ta sauke idonta a
kan
abdullahi.ta ce. "Abdul zuciya da gangar
jikina
sun yi rashi mai ciwo,sun yi kuka har sun gaji
sai
kawai suka koma fatan ya zama

kaffara....." Ya
jima dakin na juyawa da shi, ya san ba dan
akwai
sadiya ba sai ya kusa somewa da dadin
wadannan kalaman daga bakin fatima.
Amma da
yake ido mashi ne ,ya iya hadiye kaso
casa'in da
tara da digo tara na murnarsa da martanin
da zai
mayar,muryarsa na rawa ya ce. "Duk girman
kunne ai ba ya fin kai fatima,me ji ninkin
abin da
kike ji, nima ina fatan ya zama karshen ke
nan.
Da sauri ta lumshe ido tana gyada kai ta ce.
"Insha'Allah". Ta mika hannu ta dauki tea
din da
yake sha ta dan kurba ta ajiye tana cewa.
"Ai ya
yi sanyi abdul". Muryarsa na rawa ya ce.
"Haka
ne, amma akwai gudunmowarki". Ta mike
tana
dariya. "Ko? To kwantar da hankalimka.

Zan
wanke kaina,mu kwana lafiya. Ya yi galala
yana
binta da kallo. Har ta kai tsakiyar falon
sannan a
tausashe ya ce. "Ki yi min alfarma cire
damuwar
da na gani a idunawanki fatima,ki yi bacci
mai
kyau don Allah. Ta tsaya cak ba tare da ta
juyo
ba,sannan ta kada kai ta yi gaba tana cewa.
"Ok!
Ina jiranka ko a mafarki nel Ya yi saurin
amsawa.
"Zan zo in Allah ya so". Ya hakura ya sauke
ido
lokacin da ta gama ficewa,yana ji a ransa
kamar
wata duniyar suka canja,shi ya sa ya shanye
tea
din sa ba tare da ya ankara ba. Duk yadda
sadiya
ta so ta hadiye masifarta sai abin ya
fuskara,

cikin zafin rai ta ce. "Abu turab bana son
cin
fuska". Ya tattaro dukkan hankalinsa gare
ta
fuska babu walwala. "Sadiya idan kina son
kaucewa cin fuska kuma kina son in dore da
yi
miki adalci,to lallai ne ki janye kalmomin ki
da
suka zubo min dafin ganin bakin ki a
zuciya". Nan
da nan ta dawo cikin hankalinta fuskarta a
raunane ta ce. "Na janye,Allah kuma ya
baka
hakuri,ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login