Showing 126001 words to 127256 words out of 127256 words

Chapter 43 - Jiddatul Khair Complete Writing by Khalisat Haidar .txt

23 Nov 2024

7828

shi yasa take samun daman yin duk abinda take yi, Sannan ina gaya maki abinda Aliyu yake Allah ba banxa ba" Ummi tace "Bari kiji, jira yake dama ki gama surutanki ki bar wajen ya tashi ya bi bayanta, kice wai bai san abinda yake ba, wllh tsabagen rainin wayo da walakanci ke damunsa, ba dai Hafsah ba gashi ga ta, sae ynxu abun nasu ke wuce misali, kinsan har kudi ya bata wai ta siya masa fili biyu for two months now, amma sae last week muna wata maganar ta gaya min, ni dai bance komai ba" Umma dai ta saki baki tana kallonta, can tace "Allah mai iko ni Ramlah" Umma tayi wani murmushi tace "Mu je dai xuwa kawai" Abuturrab na dakin Aunty tace "Toh kai baka da bakin budewa kace masu gidan ubanka kake son xama har Allah ya yaye maka ka koma bakin aikin ka?" Ya shafa kansa yace "Aunty ae xuwa gobe i will be very okay in sha Allah, da safe xan dawo gida" Aunty ta ja tsaki tace "Aikin banxa kawai wani ke tashi fadi a kanka banda ni, ita ta wani xo har gida nemana da fada, sai kace idan wani abun ya sameka ta ta6a tsayawa a kanka idan ba kinibibi da ya kawota ynxu ba" Yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri Aunty" tsaki ta kuma ja tace "Dai dai nake da ita wllh wllh, kuma xan nuna mata na fi ta iko da kai tunda auren ubanka nake kuma matsayin uwa nake a gareka" Ya shafa kansa ganin ba shiru xata yi ba, yace "Sai na dawo da safen Aunty" tace "Toh transfer din da kace xaka yi fa, gwara fa ayi ayi a hada abun nan, nan da nan xaka ga har lkcn yayi" Yace "Nawa kika ce?" Tace "Ko akwati ynxu ai yayi kusan dubu dari hudu da wani abu Aliyu" Abuturrab dake ta kallonta yace "Akwatin guda nawa?" Tace "Aa seti biyu xa ayi ai" Yace "Dubu dari hudu da wani abu?" Tace "Atoh don bance maka dubu dari biyar ba, ni na ma san sai na cika wllh, ai ba wai akwatin yaku bayi xa mu siya a xuba masu kaya a ciki ba" A hankali yace "Toh shkkn, idan na isa can gidan xan saka maki kudin ai ina da account dinki" Aunty tace "Toh shkkn, amma gobe dai kamar yanda ka fada ka dawo da safe" Yace "In sha Allah" daga haka yayi mata sai da safe ya fita... Parlor ya tadda su Umma da Ummi har sannan suna magana, Umma ta mike ganin ya fito tace "Yaya bari inje kar Hajja ta shigo yanxu tace ba haka ake a Masar ba" Ummi tayi dariya tace "Lallai kam, toh sai da safe" Umma tace "Allah ya tashe mu lfya" daga haka ta nufi kofa, Abuturrab ya karaso gun Ummi yace "Sai da safe Ummi" Tace "Allah ya kai mu" Kofa ya nufa ya fita parlon. Hajja da Jiddah suka shiga motar Ummi da Umma ke driving suka bar gidan, sun riga su Ahmad isa gida, Jiddah na kawo ma Hajja abinci Abuturrab ya shiga parlon, Ko kallon Hajja Abuturrab bai yi ba ya wuce dakin Ahmad, Hajja ta bi sa da kallo sannan ta ta6e baki tana kallon Umma tace "Idan kin lura komai nasa yanxu irin na Kishiyar uwar yake, wllh abun na damuna amma ni nasan me xanyi..." Umma dai bata ce komai ba, su Maimoon da Safiyya suka shigo parlon sannan Ahmad. Karfe sha daya saura Umma ta shiga dakin Ahmad, Ahmad na xaune yana danna laptop dinsa Abuturrab kuma yayi bacci, Umma tace "Toh drip din fa? Naga baka maida masa ba" Ahmad yace "Yace he is feeling much better, xan jira in ga har xuwa gobe" Umma tace "Toh Allah ya basa lafiya" Ya amsa da Ameen, sannan Umma ta fita dakin. Washegari da safe su Ramlah da Safiyya suka shirya suka tafi makaranta, Ahmad kuma ya tafi can gidansu Abuturrab duba Ramlah, Umma da Hajja na can daki, Jiddah na taya Huraira goge goge kafin malamarta ta karaso don karfe tara bai yi ba, Kamar ance ta daga kai taga Abuturrab ya fito parlon, Dauke kai tayi bayan sun hada ido tana ci gaba da goge gogenta tace "Ina kwana" Ya bi parlon da kallo bai ce komai ba, bata damu da hakan ba tace "Ya jiki?" Yace "Ki kawo min shayi yanxu" Yana fadin haka ya juya ya koma dakin Ahmad, ta bi sa da kallo sannan ta wuce kitchen, ta dauraye hannunta ta dau mug ta xuba ruwan flask a ciki ta yi making masa shayin, ta dauka ta fita kitchen din, ta fi minti daya tsaye kofar dakin Ahmad rike da cup din shayin, tana juyawa taga Ahmad yana tahowa, ya karaso kusa da ita yana murmushi yace "Shayi xaki kai masa..." Ta mika masa tace "Aa ce min yyi in kawo masa" Amsa Ahmad yyi yace "Malamarki ta xo tana balcony" Tace "Toh" sannan ta juya ta bar bakin kofar ta wuce dakinsu ta dau Hijab dinta ta saka ta dau takardunta ta fita, tunda Ahmad ya shigo Abuturrab ke kallonsa da cup din shayin, Ahmad ya ajiye masa shayin yace "Ya jikin?" Abuturrab yace "Shayin waye wannan ka kawo?" Ahmad yace "Jiddah ta bada a kawo maka" Abuturrab yace "Toh ni na riga na sha sai dai ka shanye" Tun da gari ya waye Aunty ke ta kiran Abuturrab, ta kirasa ya fi sau biyar daga karshe kawai ya dau account number dinta ya mata transfer din kudin da tace, ba a dau lkci ba ta turo masa message tace "Yauwa sun shigo, xan fita kasuwan yanxu" Ya dinga kallon message din kafin ya ajiye wayar, wajen karfe goma ya fita ya hado wani shayin da kansa sannan ya dawo ya sha, ya sha magungunan sa ya koma bacci.... Jiddah ta shigo parlor karfe biyu saura rike da takardunta, babu kowa a parlon, ta karasa dakin da Hajja take ta bude a hankali taga bacci take, dakin Umma ta wuce ita ma taga baccin take, sannan ta kai takardunta daki ta ajiye ta fito ta shiga kitchen, plates da taga anyi amfani da ta fara wankewa, ta gama kenan aka bude kofar kitchen din....


*I really appreciate the birthday wishes everyone, Allah ya bar xumunci, ku ma free Readers naga wishes dinku and i appreciate wholly but i am shock, don haka domin sauke maku bashi a kai xan maku bonanzan Jiddatul Khair yau, daga yau xuwa gobe da safe Jiddatul Khair will be 300 naira only* ☺️ To gashi dai na maku sauki sosai sosai sbda kauna🥰




3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you











Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems


Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada


Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login