Showing 3001 words to 6000 words out of 98009 words

Chapter 2 - GIDAN LIKITOCI Part 1 Free Complete Book By Ameera Adam .pdf

15 Apr 2025

29868


"Inno wai ni za ku yi wa dirama? Ke da Laraba wa ya ba ku ikon tashi daga wurin nan. Wallahi

ba don ina duba darajar marigayi Baffa babba ba, da ke da jikarki tuni na kore ku daga garin
nan."
Mai gari yana rufe baki, suka hango Laraba ta tunkaro wurinsu a guje, hannuwanta É—auke da
wasu tafka-tafkan reshen bishiya. Ba ta yi wata-wata ba ta shiga tafka musu kan mai uwa da
wabi a haukace tana wani irin ƙaraji. Lokaci ɗaya wurin ya hautsine, Mai gari saboda tashin
hankali da rarrafe ya dinga tafiya, domin da farko da ya saka gudu sai da ya yi adungure sau
uku babbar rigarsa tana taÉ—e shi.


07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA BIYU

Kamar wata fusatacciyar zakanya, haka Laraba ta cigaba da yin kan mutane tana fatka
musu itacen da yake hannunta. Ban da wani irin gurnani babu abin da take yi, Inno da ke raɓe a
can gefe jikinta ya shiga karkarwa saboda tsoro da tashin hankali. Don tun da take da Laraba
ba ta taɓa ganin ta yi irin haka ba, Sanƙira ta hango maƙale a gefen bishiya. Ta yi wani irin zullo
haɗe da ƙaraji ta tunkari wurinsa, kamar sabon marayan da ba shi da mafita. Haka Sanƙiran ya
saki wani marayan kuka zai fita da gudu, Laraba ta tuna yadda Sanƙira ya dinga zuge ganyen
bishiyar yana wurga mata harara sai kawai ya ɗaga hannu ta tafka masa itace a baya. Sanƙira

ya gantsare cikin azaba ya ce, "Wayyo Mai gari bayana wash! Wallahi wannan ba dukan
bil'adama ba ne."

Mai gari da babbar riga ta sarkafe shi yana rarrafe yana dungurawa ya ce, "Wallahi na ajiya
sarautar na damƙa maka yanzu kai ne mai garin."
Laraba ta saki murmushin ƙeta ta riƙo babbar rigar Sanƙira ta baya, suna gudu tana tafka
masa ice a baya. Ganin Larabar tana neman kai shi ƙasa, ya sa Sanƙira ya yi wani ƙaraji ya
dara gaban rigarsa gida biyu, da yake dama rigar ta kwana biyu nan take ta rabe biyu. Sanƙira
ya zuba a guje ya bar Laraba da babbar riga a hannu, filin wurin ya sake cakamewa da ƙurar
ƙasar da take tashi. Mai gari ya hango Laraba tana tunkaro shi, cikin tashin hankali ya zuba
kabbara kamar wanda yake filin jihadi. A wannan karon Allah Ya ba shi sa'a ya samu da ya
miƙe bai sake faɗuwa ba, gudun kada babbar za ta sake ba shi matsala ya sa ya tuɓe ta ya
wurgar. Ya taƙarƙare ya fita da gudu, takalmansa da hularsa sai tsalle suke yi suna tashi sama.
Laraba ta so ƙyale shi amma da ta tuna irin marin da ya zazzabga mata sai ita ma ta rufa masa
baya da gudu.

A lokacin da Mai gari ya ƙarasa gida, Salame matarsa ta rako Inna mahaifiyarta da ta zo duba
ta sakamakon rashin lafiyar da ta yi. Suna nan a soro ya shiga a guje, cikin neman maɓoya ya
fisgi hijabin jikin Inna ya yi gaba da ita. Cikin tashin hankali Inna ta fara ihu tana kiciniyar ƙwace
kanta, don Mai gari janta yake da gudu ga kanta ya cukwikwiye mata a cikin hijabi. Ragowar mutanen gidan suna jin ihu daga waje, da suka ga a yadda mai gidansu ya shiga
yara da manya sai kowa ya nemi maɓoya. Laraba ce ta yi tsaye tana wani gurnani, ta ga tsakar
gidan kowa ya fashe sai wani ɗan ƙaramin yaro da bai fi shekara biyu da rabi zaune a kan fo.
Irin kallon da Laraba take yi masa tana gwalo ido, ga zungureren itacen da ya gani ya sa yaron
ya miƙe a zabure yana ihu ya shige ɗakin mahaifiyarta.

Tun da Mai gari ya fisgi hijabin Inna, ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a uwar É—akin Salame a
can ƙarƙashim gadon ƙarfenta. Ya shiga sauke numfashi da ƙyar yana muzurai, hannunsa ya
kai wurin wandonsa ya ji ya yi sharkaf. Jiki yana karkarwa ya zura kansa cikin hijabin Inna ya
ce.
"Salame ina jin fa gudawa na yi, wallahi har yanzu ji nake abu yana tsiyaya a jikina kamar an
kunna fanfo."

Inna da kunya, haushi da baƙincikin Mai gari suka cika ta murya a dakushe ta ce.
"Ai kana da hannu ko?Sai ka yi ƙoƙari ka kashe fanfon."
A razane Mai gari ya É—ago, sai a lokacin idanunsa suka sauka a kan fuskar sirikarsa. Ya fito
daga ƙarƙashin gadon a guje, yana zuro kai ya ga Laraba ta ƙwalla wata irin ƙara ta yanke jiki ta
faɗi. Daga Mai gari har ragowar mutanen garin da suke leƙowa tsaye suka yi suna kallonta, aka
rasa wanda zai tunkare ta ballantana ya yi yunƙurin tashinta. Laraba ta ɗan jima a haka sai
kuma ta fara buÉ—e idonta a hankali tana salati, tashi ta yi zaune tana kalle-kalle kamar mai
neman wani abu ta ce, "Kai, waye ya kawo ni nan?"
Shiru gabaÉ—aya suka yi mata, ta tunkari wurin mai gari a É—an razane ta ce.

"Mai gari me nake yi a nan?"
Baki yana rawa Mai gari ya ce, "Ni ma tambayar da nake son yi miki kenan, amma yanzu ki
fara zuwa gida tukunna."
Laraba ta saki murmushi a fakaici ganin yadda duk ya birkice, sannan ta fito ta nufi hanyar
gida. Kamar sun ga sabuwar hallita haka mutane suka dinga bin Laraba da kallo, ita kuwa ta
maze tana tafe tana hura hanci tana buÉ—a kafaÉ—a har ta je gida.

Baba Inu yana shiga gida kai tsaye ɓangarensa ya nufa, tun daga bakin ƙofa ya tsaya ya yi
gyaran murya yana haÉ—e fuska, lokaci É—aya yaran suka fara shiga taitayinsu. Iyayensu kuma
suka shiga tsawatarwa 'yan ƙananun da ba su yi wayo ba.
Larai ce da girki ranar, a tsakiyar gida ta ajiye tukunyar abincin rana sai ƙanana da manyan
kwanuka birjik a gabanta. Waɗansu ƙananan yara ne kusan su huɗu waɗanda ba su wuce
shekara ɗaya zuwa da rabi ba, biyunsu riƙe suke da kwanuka suna kukan yunwa suna kama
zanin Larai.
"Gaskiya Indo ba kwa kyauta mini, da wanne zan ji? Da aikin abinci ko da waÉ—annan yaran. Ke
Kulu zo ki janye mini su don ubanki!" Ta ƙarasa maganar a fusace ta fisge kwanukan hannun
yaran.
Baba Inu ne ya ƙarewa tukunyar kallo, ya matsa gabanta a kausashe ya ce.
"Ke Larai satar mini abinci kika yi? Kika ƙara a kan wanda na ɗebar muku, da na ga kin rafka
wannan rafkekiyar tukunyar?"
Jiki yana rawa Larai ta buÉ—e tukunyar ta ce.
"Mai gida tukunyar girkin ce ta ɓule shi ya sa na ɗora wannan." Leƙa tukunyar ya yi ya hango
abinci a can ƙasan tukunyar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya wuce ɗakinsa.
Mukulli ya saka ya buɗe, ya ɗauko wata 'yar madaidaiciyar tukunya ya miƙa mata yana daga
tsaye ya ce.

"Maza ɗumama mini miyar nan." Da sauri Larai ta karɓa ta ɗora a kan murhun, Baba Inu ya
koma kan benci ya kasa ya tsare yana ganin yadda take rabon abinci. Kowanne kwano idan ta
É—auko bai fi ta yafita ludayi É—aya da rabi ba, saboda idan da sabo sun saba a kullum abincin ba
isarsu yake yi ba.
"Mai gida a zuba maka kana marmarinsa?"
Larai ta tambaya tana gyara goyon Fure da ke bayanta.
"A'a ku ci kawai!"
Baba Inu ya furta a daƙile. Larai ta ɗebi ragowar wanda ta rage masa cikin murna ta shiga ƙara
wa kwanonta.

"Ke Larai wallahi son zuciyarki yawa gare shi, ba za ta saɓu ba wallahi sai kin ƙara wa kowa."
Hansatu ta yi caraf ta yi maganar ganin abin da Larai take yi. Babu yadda ta iya ganin Baba Inu
yana wurin ya sa ta shiga ƙarawa kowanne kwano bai fi cokali ɗaiɗai ba. Bayan ta gama ta ce
kowa ya É—auka, a guje yara da 'yan matasan cikinsu suka É—auka da sauri, wasu tun a tsaye

suka fara zuba loma duk da abincin yana ƙona su.

Ƙamshin ɗumamen miyar ne ya fara dukan hancinsu, Larai ta sauke har za ta kai masa ɗaki
Baba Inu ya ce ta kawo gaban bencinsa ta ajiye. Abu da ke da tsohon ciki wani irin ƙwaɗayi ya
taso mata. Kwanon abincinta ta ɗauka ya ƙarasa wurinsa cikin marairaicewa ta ce.

"Don Allah mai gida ko man miyar ne, ka taimaka ka yafa mini na ci ko na samu sauƙin abin da
nake ji. Wallahi ƙwaɗayi ne ya addabe ni."
Wani banzan kallo Baba Inu ya yi mata ya ce. "Cewa aka yi idan ba ci ba za ki mutu?"
Abu ta yi saurin girgiza masa kai, Baba Inu ya sake haÉ—e fuska ya ce.

"To yanzu baƙincikin wanda zan ci kike yi? Idan kuma ba na cin mai maiƙon, ta ya ya zan iya
samun ƙwarin jikin nemo muku abincin da kuke ci." Abu ta haɗiyi yawu tana kallon farantin da
Baba Inu ya zuba miyar da ƙirjin kaza, sai da ya rufe tukunyar ya miƙa wa Larai ta mayar masa
É—aki sannan ya ce, "Wallahi ba don cikin jikinki ba, da idan ba ki matsa daga kaina ba sai na
sheme ki. Dubi yadda kike É—ebo mini fuska kamar an matse lemon tsami."
Abu babu yadda ta iya, haka ta ja jiki a sanyaye ta koma ƙofar ɗakinta ta zauna.
Ƙaton biredi ya ɗauko ya gutsira sannan ya mayar ya saka kwaɗo ya rufe ɗakin nasa. Kan
bencin ya koma ya fara yagar biredin yana dangwalar miyar da ita, daga yaran da suke wurin
har iyayensu ban da haɗiyar yawu babu abin da suke yi. Wani ɗan ƙaramin kwanon sha ya
buɗe kusan cike yake da nono, ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ƙullin maganin ƙarin kuzari
da ya saya a daren ranar. Ragowar ƙullin ya kunce ya zuba ya jujjuya ya ajiye shi a gefe, ya ci
gaba da yagar kazar yana dangwalar biredi da miya.

Baba Saleh sai da ya gama loda duka magungunansa a cikin mota sannan ya koma gida,
domin ya yi wa ÆŠan Bishir sallamar tafiya yawon tallar magani.
Yana shiga sashensa, ya samu ɗan bishir yana tsanyara ihu kamar wanda ake ƙwaƙwalewa
idanu. Wani irin bugu ƙirjinsa ya yi, kamar wanda ya yi tozali da gawar mahaifiyarsa. A hargitse
ya janyo ÆŠan Bishir ya rungume yana jin zuciyarsa tana zafi ya ce.
"Ɗan bishiririna, waye ya taɓa ka? Me aka yi maka?"

Ɗan Bishir ya sake narkewa yana wani tale baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran da aka sangarta
ya ce.
"Innaaaaaa! Inna ce ta dungure mini kai. Wayyo Allah kaina."

Jikin Baba Saleh har karkarwa yake, saboda a duk duniya idan da abin da yake É—aga masa
hankali ganin kukan ÆŠan Bishir. Ya nuna Uwale idanu cike da masifa ya ce.

"Sau nawa zan ce ki daina zalintar yaron nan Uwale? Ke wacce irin uwa ce kamar ba ke kika
haife shi ba tsabar rashin imani, wallahi ba don kin ci darajar ke kika haife shi ba yau sai ranki
ya yi mummunan ɓaci."
Ran Uwale ya gama ɓaci ta nuna masa randar ruwan da suke sha ta ce.
"Wallahi Mai gida wannan abin da kake yi ba soyayya ba ce, ɓata tarbiyyarsa kake yi. Dubi fa

randar ruwan shan mu ya É—auki omo da mai ya zuba mini, don na dungure masa kai kake yi
mini wannan tijarar? To wallahi na gaji, na gaji da wannan abin da kake yi mini. Kai kuma don
ubanka ko yau ka sake yi mini irin wannan ɓarnar sai na dungure ka." Uwale ta ƙarasa maganar
tana sakarwa Ɗan Bishir ƙozo a ka. Wata irin gantsarewa ya yi yana canyara ihu tamkar wanda
aka caka wa wuƙa, a fusace Baba Saleh ya kai wa randar duka ta bada tus! Ruwanta ya
mamale a tsakar ɗakin, cikin ƙaraji ya ce.
"Ba dai a kan randa za ki illata mini ÆŠan Bishir ba? To wallahi idan ba ki da gaske ba, yadda
na ragargaje randar nan kema sai na ragargaza ki."
Baba Saleh ya yi furcin yana sunkutar ÆŠan Bishir da zai yi shekara shida a tsaye, ya É—auke
shi yana shafa bayansa zuwa kansa yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki. Ya rungume
shi a ƙirji cike da so, ya waiga yana wurga wa Uwale mugun kallo. Har lokacin Ɗan Bishiri bai
daina tale baki yana kuka a shagwaɓe ba, Baba Saleh ya kalle shi har lokacin zuciyarsa zafi
take ya ce.

"Me kake so ka ci ÆŠan Bishirina."

ÆŠan Bishir ya wale baki yana duban mahaifiyarsa tana mata harara sannan ya ce.
"Namaaaa!"
Baba Saleh ya sauke shi ya ce, "Don nama banza ÆŠan Bishir, bari na je na yanko maka na zabi
ko kaji."
"Na zabiiiiiiiiii."
ÆŠan Bishir ya faÉ—a a sangarce.
Harara ya wurga wa Uwale sannan ya fice daga sashensu, yana zuwa ƙofar gida ya yi turus
ganin abokinsa Sani yana ba wa yaro sakon a kira shi.

"Ga ni na zo a daidai ya aka yi?"

Sani ya ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa, sannan ya sauke idonsa a kan jakar
wanzaman da ke rataye a kafaÉ—ar Baba Saleh.
"Karenka ya kai tsaiko ko Sale? Wai har ni za a kira na cire beli na yi wa jaririya aski, amma
sai na ji labarin ka yi mini shigar ɓurtu alhalin ka sani ni ɗan gado ne a harkar wanzanci ba ɗan
ka-ta-haye kamar kai ba?"
Baba Sale ya saki tsaki cikin halin ko-in-kula ya ce.
"To mene ne marabar dambe da faÉ—a? Don kana É—an gado ka koya mini harkar wanzanci, na
zo ni kuma Allah Ya saka mini nasibi duka costomers É—inka sun dawo wurina wani avu ne? Wai
ma da kake wannan abin, kai da kake jin ka É—an gado da ni ta-ka-haye ba duka wanzamai za a
ce mana ba? Kai matsa ka ba ni wuri ÆŠan Bishiri ya aike ni, don aikensa ya fi mini wannan
sokiburutsun banzan da kake yi mini."

Baba Sale ya gegara ya wuce shi, ya nufi wurin Sadau mai nama.
Bayan fitar Baba Saleh cikin takaici Uwale ta É—auko zani ta shiga tsane ruwan tana
matsewa. Mugun kallon da take jifan ÆŠan Bishir da shi ya sa ya yi saurin ficewa daga É—akin. Kai
tsaye sashen Baba Inu ya nufa don tun da ya ji shiru ya san abinci suke ci. ÆŠan Bishir irin

kwaÉ—ayayyun yaran nan ne da duk abin da suka ga ni, za su ce suna ci koda a hannun babba
ne. Sangartar da Baba Sale ya yi masa ce ta sa ya koyi wannan mummunar É—abi'ar. A lokacin
da ya shiga sashen Baba Inu da bencinsa ya fara cin karo, ya hangi Baba Inu a can ƙofar
ɗakinsa yana rabawa yaransa waɗansu ƙananun alewa. ragowar naman kazar da ya gani ya saka hannu ya ɗauka, ya kai ba ki ya fara zuge tsokarta
yana lumshe ido. Sai da ya gama cinyewa tas, sannan ya É—auki kindirmon nonon da Baba Inu
ya zuba magani ya ɗaga kansa ya ɗaɗɗaka, a shagwaɓe ya wurgar da kwanon ƙasa bayan ya
shanye ya ɗauki ƙashin kazar ya fara tauna. Ƙarar jefar da kwanon ce ta ja hankalin Baba Inu, da yara da suke gabansa. Ganin abin da
Ɗan Bishir ya yi ya sa Baba Sale ya ƙarasa wurinsa rai a ɓace ya kai masa duka a baya.
Ɗan Bishir ya tale baki a shagwaɓe ya saka kuka yana yi wa Baba Inu daƙuwa haɗe da faɗin.
"Uwakaaaa!"

Zuciyar Baba Inu ce ta fara tafasa, ya saka hannu zai dake shi da sauri ÆŠan Bishir ya fita da
gudu yana faÉ—in.
"Allah Ya isa."
Zucya tana tafasa Baba Inu ya rufa masa baya, suna zuwa mararrabar hanyar da take haÉ—a
kowa da ke cikin gidan ya samu nasarar cafko shi, bai yi wata-wata ba ya tsinke shi da mari. A
daidai lokacin Baba Sale ya ƙarasa wurin, ganin abin da aka yi wa Ɗan bishir ya sa shi wata irin
zabura a haukace ya yi kukan kura ya tunkari wurin da suke tsaye.

Share pls

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login