Showing 1 words to 3000 words out of 98009 words
Chapter 1 - GIDAN LIKITOCI Part 1 Free Complete Book By Ameera Adam .pdf
[02/02, 15:02] Ameerah Adamí ¼í¼š: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA ÆŠAYA
Jar mota ƙirar golf ce take tafiya a hankali, saboda tsufa da lodin magunguna tare
É—ima-É—iman manyan sifikun da suka yi mata nauyi. Ta baya boot É—in motar a buÉ—e yake
waɗansu matasan samari ne a zaune, hannuwansu riƙe da jarkokin magunguna suna ɗagawa.
Tayoyi da gefen motar duk sun yi butu-butu, saboda ƙura da jar ƙasa. Mai maganin gargajiyar
yana daga cikin motar, ya sake ƙara volum ɗin recording ɗin tallan magungun da yake yi.
"Alhaji ko Hajiya idan har matsalarku sanyi ne ku zo ga babansa. Ni fa ba na rantsuwa a kan
magungunana saboda sadidan ne, amma idan har kuka sha maganina bai yi muku aiki ba ku
dawo na ba ku kuɗinku. Ina mai fama da sanyin ƙashi, sanyin mara da ciwon baya ku zo ga
waraka ta zo muku har gida. Alhaji kai ne ake ganinka kullum cikin babbar riga, ana yi maka
kallon cikakken namiji amma a baÉ—ini kana jin kunya to ka zo mu saka labule don Allah." Mai
maganin ya rage volum ɗin recording ɗin, sai ya zuro kansa ta window ganin ya ƙaraso wurin da
jama'a suke zirga-zirga ya ce.
"Al'ummar Annabi ina magidancin da yake son huce takaicin sanyin nan da muke ciki? Amma
É—an kanoma ya yi masa mugun kamu. Don Allah kada ya ji kunya, ya zo ya samu mai warakar
sanyi matsalarsa ta kau da ikon Allah. Cutar rana, kumburin ciki, zafin bayan gida, basir da
cutar sanyi duk ni ne likitan da ke magance su."
Baba Inu da ke kishingiɗe a kan benci ya tashi zaune, ya ɗan ƙanƙance ido yana ƙarewa
motar da mai motar kallo, saboda masu magungunan ba baƙinsa ba ne, don yana iya tantance
duka masu magungunan gargajiyar da suke shigowa garinsu. Musamman yadda suke
haba-haba da shi, duba da yadda ya zame musu babban costomer.
"Kai mai magani, zo nan."
Baba Inu ya kira shi yana yafito shi da hannu. Da sauri mai maganin ya gyara paking É—in
motar yana kaikaitata a daidai ƙofar gidan.
"Babana da Innata ga É—an baiwar masu magani ya sauka, mai warkar da matsalar sanyi ya zo
kada a yi wasa."
Mai maganin ya sake furtawa a loudspeakersa. Ƙuri Baba Inu ya yi masa ya ce. "Abokina
amma dai kai baƙo ne a garin nan ko?"
Mai maganin ya gyaÉ—a kai ya ce, "Yanzu ma wucewa na zo yi, duk mai matsalar sanyi ya zo
muna bayar da taimako don Allah. Idan ya sake na tafi ba zan sake dawowa ba sai baÉ—i."
"Miƙo mini wancan maganin na jarka, nawa ne kuɗinsa?"
Baba Inu ya tambaya, yana nuna wata zungureriyar jarka da ke cike da jiƙaƙƙun itatuwa a ciki.
Jarka biyu mai maganin ya miƙa masa yana faɗin.
"Wannan da kake gani darr kenan, Mai gida ba kowa nake sayarwa ba sai mai sa'a. Ko kana
shan kunya a wurin iyalinka, don Allah ka É—aga roba ka sha rabi ka shiga wurin uwargida ka
dawo ka ba ni bayani."
Baba Inu bai jira cewarsa ba ya ɓalle murfin robar, ya ɗaga ta sama sai da ya ga maganin ya
ƙare sannan ya wurgar da jarkar. Mai maganin ya zaro ido waje ya ce, "Master amma ka kwana
a wannan layin ko?"
Horn É—in da Baba Ibrahim ya yi ne ya katse Baba Inu da yake shirin bayar da amsa.
"Abokina ja motarka gefe ga masu iko da gidan sun ƙaraso."
Mai maganin ya ja motarsa gaba, a daidai lokacin Baba Ibrahim ya ƙarasa da ta shi motar ya
yi parking sannan ya fito daga ciki. Tun lokacin da mai maganin ya ƙarasa gaban Baba Inu ya
shawo kwanar layinsu, a kan idonsa Baba Inu ya ɗaga ya shanye. Da sallama ya ƙarasa
wurinsa haÉ—e da faÉ—in.
"Yaya barka da hutawa."
Baba Inu ya ɗan kalle shi a sheƙe ya ce. "Bokan turai yau kuma lafiya na ga ka dawo da wuri?"
Baba Ibrahim ya ce, "Lafiya ƙalau Yaya."
Ganin Baba Ibrahim ya tsaya ba tare da ya yi magana ba ya sa Baba Inu ya ce, "Iro ya aka yi?
Ka saka ni a gaba ko kai ma a miƙo maka maganin ne?"
Da sauri Baba Ibrahim ya ce, "Allah ya kiyashe ni, ni kam."
Baba Inu ya dube shi a gwasale ya ce, "Yo dama ina abin yake maye ya ci jariri, mai mace
ɗaya har ya bugi ƙirji ya saka kansa a sahun mazaje. Ai maza kam suna inda suke."
Baba Ibrahim ya girgiza kai ya ce.
"Yanzu Yaya hanyar da ka ɗauko wa kanka mai ɓillewa ce? Saboda Allah a ce kai kullum cikin
shaye-shaye da jiƙe-jiƙen magunguna kake kala-kala. Kullum masu magani sai dai su dinga layi
a ƙofar gidan nan, mutanen garin har sun fara gane ka? Magungunan fa yawanci waɗanda
kake sha babu wata ƙa'ida kai tsaye kake hankaɗa wa cikinka, kuma mafi yawa masu haɗa
magungunan nan da ka suke yi ba su da ilimin abin. Ko mu da muke likitocin asibiti, babu yadda
za a yi mu É—auki magani mu ba ka ba tare da mun duba ka ba."
Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya cigaba da cewa.
"Yaya da ace kuÉ—aÉ—en nan da kake kashewa a sayen magungunan tara su kake, da ko nauyin
karatun yara ka rage da su. Amma ka bar yara haka, hatta makarantar allo ba duka ne suke
zuwa ba. Kuma saboda Allah ga shi nan, kullum wasu ƙananan ƙwayayan ake sake
ƙyanƙyashe maka." Baba Inu ya ɗago fuska a haɗe ya ce, "Ka gama ubana? Idan ba ka gama ba na yi shiru ka
cigaba."
Baba Ibrahim ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Na gama."
"To shige ciki ka ba ni wuri, ashe shi ya sa ka kwaso fuska kamar akwatin zaɓe ka zo ka tsaya
mini a ka. Wallahi Iro ka fara ba ni tsoro, da ace kana da iko na tabbata da sai ka yi duk yadda
za ka yi domin ka turmushe mini ƙwaiƙwayen haihuwa. Amma ka don kanka, na lura baƙinciki
da hassadar ne fal ranka. Allah bai hore maka irin ƙwaiƙwayen haihuwa masu yawa da albarka
kamar ni ba."
Bab Ibrahim a fusace ya ce, "Wallahi gaskiya ka faÉ—a, yadda kake sakin jiki kai da matan da
kake aura kana saki da ina da iko sai na farke ka na ƙone maka su kowa ya huta. Tun da
haihuwar kawai ka sani ba ka san jidalinsu ba."
A ɗan tsorace Baba Inu ya dafe ƙirji, yana bin Baba Ibrahim da wani irin kallo ya ce.
"Kai dai Iro an yi mai mugun hali, mugun bakinka ya faÉ—a kanka. Sai ja je ka yi ta fama da
'ya'ya huɗu, ni kam haihuwa yanzu na fara tun da ban san mai jin ƙaina ba."
Ganin Baba Inu bai É—auki zugar Baba Ibrahim ba ya sa Mai maganin ya zuro kai ya ce.
"Ai mai gida shi ya sa a kullum idan za mu fito, muke addu'ar neman tsari miyagu irinsu masu
hana a yiwa bayin Allah ciniki." Takaici ya sa Baba Ibrahim ya shige cikin gida ba tare da ya
tanka musu ba. Saboda halin yayan nasa ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba.
Baba Iro yana shirin yin magana daga soron gidan ya ji, gijif! Kwacakwar! Alamar ana jan kaya
a buhu. Baba Saleh ne ya fito da ƙaton buhun magungunansa, ganin motar mai magani a ƙofar
gidan ya sa ya murtuke fuska yana harare-harare cikin habaici ya fara waƙa.
Komai baƙin cikin tsololon ƙato.
Wallahi sai dai ya yi ƙototo.
Na zama kainuwa a wannan loto.
Ƙaryar mai baƙinciki ya ga bayana, har masu ƙin sayan maganina.
Yana gama faɗar haka ya fizgo ƙaton buhunsa da yake ja da ƙyar, sai ga shi bisa tsautsayi ya
fiszo da ƙafar bencin da Baba Inu yake kai. Bencin ya yi gaba shi kuma Baba Inu ya hantsila ta
baya ji kake darr ya yi zaman 'yan bori a ƙasa.
Kamar bai san da shi a wurin ba Baba Saleh ya saki buhun hannunsa yana rafka salati sannan
ya ce.
"Wai Yaya dama kana nan ƙofar gida? Ikon Allah sannu!"
Ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin riƙo hannun Baba Inu, da sauri ya bige hannunsa rai a ɓace
ya ce.
"Wallahi duk baƙincikin mutum bai isa ya ga bayana ni Inusa don uban mutum! Haka zan daɗe
na yi ƙarko shekaru irin na dabino, sai na ga bayan maƙiyana. Kai mai magani, ungo dubu biyar
ka yi mini haÉ—in komai da ruwanka."
Baba Inu bai yi niyyar sayen maganin dubu biyar ba, amma don ya ɓa ta wa Baba Saleh rai ya
yi haka. Baba Saleh ya buga tsaki yana wurgawa mai maganin harara, ya nufi wata tsohuwar
motarsa da yake tallan magungunansa, ya buÉ—e ya tura buhun maganin da ke cike da jarkokin
magani sannan ya rufe.
Inna ce ta fito daga gida a fusace hannunta riƙe da Laraba, ta dubi Baba Inu bayan sun yi
sallama da mai maganin ta ce.
"Inu na gaji da cin kashin da ake yi mini a cikin garin nan."
Da mamaki Baba Inu ya dube ta ya ce, "Me aka yi miki Inno?"
"Ba ni aka yi ba Laraba aka yi wa, kuma duk wanda ya yi wa Laraba ni ya yi wa. Mai gari ne
yake son ganina da ita, wai Laraba ta tare ÆŠahe É—an gidan Sa'a mai ragadada ta cinye masa.
Saboda Allah ina Laraba za ta kai ragadada cikin É—an bokiti ban da son zuciya?"
Jin haka ya sa Laraba ta juya gefe a fakaice ta sake suÉ—e hannunta da ya yi shanana da
miyar ragadada.
Baba Inu ya zuba mata ido ya ce, "Wallahi duk abin da aka ce mini wannan hatsabibiyar
yarinyar ta yi ba zan musa ba, shi ya sa tun da satin nan ya kama nake jiran shigowar Uwar
marayi garin nan. Wallahi babu abin da zai hana Laraba zuwa birni, ta je can ta yi aikatau ko na
huta da takaicinta. Ni duk cikin 'ya'yana babu sai siffar 'ya'yan aljanu irinta." Wani irin haushin Baba Inu ya kama Inno, sai kawai ta ja hannunta suka wuce wurin mai gari.
Tun daga nesa da aka hango Inno tafe da Laraba ƙananan maganganu suka fara tashi a fadar
mai gari. Sanƙira ne ya yi magana sannan kowa ya yi shiru. Da sallama Inno ta zauna a kan
tabarmar fuska a haÉ—e ta ce.
"Allah Ya taimake ka, na ji wai kana nemanmu ni da Laraba!"
Mai gari da tun da Laraba ta zauna yake bin ta da mugun kallo ya ce, "Wai ne ma Inno?"
Ya mayar da kallonsa wurin Laraba ya ce.
"Ke Laraba waye wannan?"
Laraba ta yi kicin-kicin da fuska tana duban ÆŠahe kamar ba ta gane shi ba ta ce, "Ban san shi
ba, amma na ga yana yi mini kama da 'ya'yan Baraka mai hancin salansa."
Haushi ya sake cika Mai gari ganin irin rainin hankalin da Laraba ta yi masa. Ya sake nuna
Huwaila wacce ta kai ƙarar Laraba, a kan ta jefa mata bokiti da guga a cikin rijiya. Laraba ta
sake ƙanƙance ido ta ce.
"Wannan kam Lado ƙeya ne!"
Sai kuma Laraba ta washe baki ta ce, "Lado ƙeya dama ka dawo daga Legas?"
Haushi ne ya lulluɓe mai gari, mutanen wurin wasu suka fara dariya yayin da wasu kuma
haushin Laraba ya cika su, don kusan duka mutanen garin babu wanda ba shi da tabon ɓacin
ranta.
Tsam mai gari ya taso ya zo gaban Laraba, a tunaninta tambayarta zai yi sai ji ta yi ya zabga
mata gigitaccan mari, har sai da ta ga waÉ—ansu taurari sun gilma mata. A razane Laraba ta dafe
kunci saboda marin ba ƙaramin zafi ya yi mata, amma sai ta basar don ba ta san ta kunyata
kanta a gaban mutanen garin. Ta sake basarwa ta sake ba shi irin amsar da ta ba shi da farko.
A wannan karon ma haushi ya sa Mai gari ya sake É—auke fuskarta da mari, abinka da farar fata
lokaci ɗaya fuskarta ta yi jajir. Ganin haka ya sa ran Inno ya ɓaci ta dube shi a fusace ta ce.
"Wallahi Sama'ila ka kiyaye ni, jikata fa ba jaka ba ce..."
"Ai dama duk wani iskanci da yarinyar nan take yi ke ce kike É—aure mata, wallahi mai gari sisina
ba zai yi ciwon kai ba sai an biya ni ragadadata. Har kayan miya da mahaÉ—i kusan dubu biyar
na kashe."
Sa'a mai ragadada ta faɗa a ƙufule.
Cikin tsoratarwa da burgagi Mai magari ya miƙe tsaye yana buɗa kafaɗu ya ce, "Inno tun da
haka kika ce, bari na aika ku birni wurin hukuma ta yanke mata hukunci. Kin ga idan aiƙali ya ji
irin tuhume-tuhumen da ake yi mata ƙila ma ya aikata gidan yari."
Jin haka ya kaÉ—a hantar cikin Inno, hankali a tashe ta zungoro Laraba ta ce.
"Ke Laraba ki yi magana."
Laraba ta yi wa Mai gari ƙuri tana yi masa kallon ba ka daki banza ba, har sai da cikinsa ya
kaÉ—a amma sai ya basar ya ce.
"Laraba kin tare Ɗahe kin cinye masa ragadada kin tula masa ƙasa a ciki, ita kuma Huwaila kin
jefa mata guga da bokita a rijiya yanzu da kin jefa ta ciki me za ki ce?"
Laraba ta wurga wa Huwaila harara ta ce, "Kai Lado ƙeya tun da ka dawo garin nan yaushe
muka haÉ—u da kai!"
Huwaila ta fashe da kuka cike da takaici ta ce, "Mai gari kana ji tana mayar da ni Lado, yanzu
Laraba ta rasa da wa za ta haɗa ni sai Lado ƙeya?"
Mai gari ya kalli Sanƙira yace ya tsinko masa itacen dalbejiya ya zuge masa ganyenta. Jikin
Sanƙira har rawa yake ya haye bishiyar da ke gefensu, ya fisgo manyan reshe ya zuge ya miƙa
wa mai gari. Kafiya da taurin kan Laraba ya sa ko gezau ba ta yi ba, duk da gabanta sai faÉ—uwa
yake yi.
Rai a ɓace Mai gari ya shiga rafta mata ta ko ina, mutanen wurin suka marmatsa don kar a
same su. Tun Laraba tana daurewa har dauriyarta ta ƙare ta fashe da kuka tana mutsu-mutsu.
Inno ban da kuka da kururwar neman taimako babu abin da take yi.
Yaran da suke zagaye da su ne suka fara tafi suna tsalle da waƙa, saboda tun da suke ba su
taɓa ganin abin da ya saka Laraba kuka ba.
Laraba mai kuka ye ye.
Ga majina da yawu ahayye.
Gobe ma ta ƙara ye ye.
Ku zo mu yi mata ɓarɓaɗan tusa a tsakar ka.
Idan suka kai baitin waƙar sai su ƙarasa su dunguro kan Laraba da ke shasshekar kuka.
Mai gari sai da ya gaji don kansa sannan ya koma kujerarsa cike da son nuna birgewa ya ce.
"Duk wanda ya sake aikata makamancin abin da Laraba ta yi, hukuncin da za mu yi masa
kenan. Ina Inno take?"
Cike da jin haushi a daƙile Inno ta ce, "Ga ni."
"Za ki biya Huwaila da Sa'a kuɗin ɓarnar da Laraba ta yi musu." Inno ta yi tsagal ta ce.
"Ai kuwa ba za ta saɓu ba, ya za a yi a daki yarinya sannan kuma na biya."
Mai gari zai yi magana suka ga Laraba ta miƙe zumbur! Kamar wacce aka yi wa allurar doki.
Don irin zaburar da ta yi ba ƙaramin tsoro ta ba shi ba, ba shi kaɗai ba, hatta ragowar mutanen
wurin sai da suka ja da baya.
Idanunta sun yi jawur saboda kuka, ta dube su É—aya bayan É—aya abinka da mai manyan idanu
sai suka sake fito. Ta fara takawa a hankali wurin saitin fuskokinsu, ta cigaba da kallonsu É—aya
bayan É—aya kamar wacce take haddace kamanni da sunayensu. Da ta je kan mai gari sai ta
matsa dab da shi ta gwalalo masa ido waje har sai da ta ja baya, sannan ta cigaba da kallon
mutanen gefensa Tana zuwa ƙarshe, sai kawai suka ga ta ɗiba a guje ta fice daga cikin fili ta
nausa daji, hankali a tashe Inno ta rufa mata baya tana faÉ—in.
"Laraba! Ke Laraba ina za ki je?"
Tun ba a je ko ina ba Laraba ta yi wa Inno nisa, ganin Inno za ta tafi ya sa Mai gari ya ce.