Showing 3001 words to 6000 words out of 19708 words

Chapter 2 - BAFULATANA Book Complete Hausa Novels BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

2796

so gida ,,, a qofar gida suka hadu da Rabe dan tunda ta dawo taqi shiga Gidan ta tsaya jiran moddibo
Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke , ba tare da ta kula da mutumin dake bayan saniyar ba tayi gaba da qar moddibo ya kwanto shi daga jinkin saniyar Yayi hanyar dakinsa dashi, suna shiga ya kwantar dashi akan tabar marsa ya mike ya dakko boronsa dayake sa magani ya ajiye ya sake dakko wata qarya ya ajiye qaho ne a cikin qwaryan da kuma aska take moddibo ya yage rigar dake jikin matashin subahanallah abinda ya firta Neman sabida yanda yaga jini ya taru a gefan qirjinsa na dama da alama seda aka dake shi sannan aka sareshi
A nitse ya dauki askar ya daidaici gurin da bakin jinin ya taru sannan ya yanka gurin nan da nan wani bakin jini ya fara fita a hankali ya shiga goge mai seda ya gama gaba daya sannan ya shiga samai magana a jikin raunukan bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwadama Laure kira, jiki na rawa ta qaraso tace gani mlm
Yace maza ki kawo min ruwan zafi jiki na rawa ta tashi ta hada wuta ta Dora ruwan zafin
[8:48PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 5*


Ta dan dauki lokaci kamin ta kawo ruwan zafin sabida sha'anin itace se'a hankali, dakyar ta samu wutar ta kama ba'a jimaba ruwan ya tafasa
Qwarya ta daukko ta juye masa ruwan a ciki ta nufi dakinsa dan ta kaimai ruwan. Sallama tayi sannan yay mata izinin shigowa ta shiga
Ya karbi ruwan sannan ya dakko wani farin saki yasa a cikin ruwan sannan ya dakko wani garin magani ya zuba a cikin ruwan ita dai Laure banda kallon moddibo ba abinda takeyi bakinta fal tambayoyi amma ta rasa ta inda zata fara yimai Tambayar. Suna cikin haka ne Rabe ta shigo dakin da sallama da fara'arta take kallon moddibo tace bab wannan shine mijin daka samo min din
Cike da damuwa ta qarasa maganar sabida se a lokacin ta lura da raunin dake jikinsa moddibo be damu da ya bata amsa ba sabda shi gaba daya hankalinsa yana kan wannan matashin
Kamar zatayi kuka tace baba amma wannan baqo ne ko? Ciwo yaji ? A lokaci daya rabe ta dinga jefo masa tambayoyi
Ba zato Laure ma ta jefo tata tambayar mlm a ina ka samo wannan yaron? Kai yanzu baka jin tsoron daukko shi ya zame mana masifa nan gaba?
Moddibo ya dube ta cike da murmushi yace haba Laure shin kin taba ganin inda taimako ya zama masifa? Tayi shiru batace komaiba, daya ga bata da niyar magana seya cigaba da maganarsa tin daga Hauwarsa da yaron har zuwa dakko shi da Yayi be boye musu komai ba
Nan da nan idon Rabe ya fara zubda hawaye dama su Rabe da arahan hawaye lol
Ita ko Laure ko a jikinta balle ma tausaya masa , dataga abin ya isheta ma seta fice daga dakin tana ta bambami wai moddibo ze ja musu bala'i
Shidai be kulata ba sema cigaba da gogewa matashin jiki da ruwan maganin daya hada yakeyi
Cikin muryar kuka Rabe tace baba, ya dago yana kallon ta sedai bece komai ba a hankali tace dame zan Iya taimakon ka?
Moddibo Yayi murmushi yace so nake kullum ki dinga yi masa adduar samun lfy kinji? Ta daga kai alamar gamsuwa moddibo ya share mata hawaye da hannunsa sannan yace ta tashi ta wuce daki ba musu ta mike ta tafi dakin kamar yanda yace mata
Ranar dai Rabe bata samu zuwa makarantar allo ba
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau matshinnan ya cika sati biyu a gidansu Rabe amma ba abinda yake motsi a jikinsa sedai kawai alamar numfashi, tun suna sa ran tashinsa har suka fara cire ran farkawar sa nan kusa
Yanzu Rabe CE take kula dashi itace ke zuba masa kunu a baki da ludayi tin baya shiga bakin har yazo ya fara shiga kadan kadan
Kallo daya zakayiwa matashin ka fahimci ya rame sosai akan ranar da moddibo ya kawoshi Gidan , tun ranar da aka kawoshi gdan Laure bata qara leqowa dakin ba dan acewar ta idan masifar ta zo ta afkawa moddibo da Rabe, hmmm su Laure akwai bakar zuciya lol
Wasa wsa Rabe ta shafe kwanaki bata zuwa makaranta ko kiwo bata zuwa, amma Sam hakan baya damunta sabda tsa a ranta taimakon mutum yana daya daga cikin dabi'u masu kyau
Mlm iro yazo yafi a qirga kan ta dawo makarantar ayi suka da ita amma fir taki yarda ta koma dan a ganin ta idan ta fita ko qofar gida waye ze bawa bako abinci?
Hmmm kuji fa Rabe da qarfin hali
Moddibo ne ya shigo dakin hannunsa riqe da wata saiwa ya mika mata yace maza jeki tafasata ki kawo min kinji
Da sauri ta karba taje ta hado qirare ta bada wuta ta Dora maganin ba'a dau lokaci me tsayiba ruwan ya fara dahuwa seda mutar ta mutu sannan ta juye maganin a qwarya ta kaiwa moddibo da murna ya karba yana sa mata albarka seda maganin Ya fara hucewa moddibo ya dago kan matashin ya shiga zubawa matashin abaki, dikda cewa ana zubawa wani na zubewa ansamu wani ya shiga cikin nasa, bayan ya gama ne ya shiga goge masa jiki da sauran maganin
Kullum haka suke masa har aka shafe wata ba wani ci gaba, gashi Rabe bata da aiki se kuka ga jarabar Laure ga kuma ciwon bako hakan ne yasa dik tabi ta rame se hanci da idanu
Abin yana dagawa moddibo hankali to amma bashida yanda zeyi illa kawai yayta addu'a
Laure CE ta Shiva dakin moddibo da sallama ya amsa mata da sakin fuska a dakile tace yame jiki ya amsa mata da sauqi
Moddibo ya sake murmushi a karo na biyu yace hala fita zakiyi? Da fara a tace ae dan dama ta rasa ta India zata fara tambayar sa cewar zata fita, a takice yace mata seta dawo ta gaida su iro da gwaggoji. Bata amsa ba tayi gaba bayan fitarta ne wani yaro hamisu yazo yay sallama da moddibo kan cewar mahaifin sa ba lafiya shine yace ya kirashi moddibo be bata lokaciba ya fito suka wuce har sun fita ya dawo yace Rabe ta koma dakinsa sabda maralafiyan
Da sauri ta mike tare da yi masa Allah kiyaye ta koma dakin ta zauna tunda ta zauna ta zubawa matashin ido ba tare da tace komai ba se hawaye cikin muryar kuma ta fara magana, wai kai yaushe zaka tashi ne?shin kasan yanda mukeji a ran mu? Dan Allah ka tashi ko hankalin banana ze kwanta!
Ta jima tana suru tanta kamar wata zararriya sannan tayi shiru ta cigaba da kukanta fukarta dik tayi ba idanunta suka kumbura abin ka da far in mutum
[8:49PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 6*


Ta jima tana kukan sannan bacci ya dauke ta
A hankali matashin ya fara motsa hannunsa daqar ya Iya daga hannun sa ya maidashi qirjinsa, jin da tayi kamar motsi ne yasa ta bude idanunta daqar ta maida kallon ta gareshi, ayko seta qara bude idanunta sosai alamar mamaki
To ya akai hannunsa ya koma qirjinsa? Tambayar da take mata yawo a zuciyarta Kenan
A nitse ta maida kallonta kan fiskarsa, ta jima tana kallon sa kamar bazata dena ba kamar a mafarki taga yana motsa idanun nasa ai seta qara zaro idanunta ๐Ÿ˜ณ cike da mamaki
A hankali ya fara bude idon har ya gama bude shi gaba daya a kan fuskar Rabe
A firgice ya fara qoqarin tashi yana so ya ja baya sabida tsoratar dayayi
Yana ja baya ya saki wata qara sabida wani azababben zafi dayaji a gadon bayan sa , bashiri ya koma ya kwanta yana maida numfashi, da sauri rabe ta sake matsowa kusa dashi sosai sannan ta fara magana cikin harshen fulatanci take cemai kayi a hankali sabda jikin ka akwai rauni!
Tunda ta fara magana yake kallon bakinta har ta kai harshen maganar ta dikda cewa be gama fahimtar abinda take fada sosai ba hakan be hanashi qare mata kallo ba tana gama maganar ta sakar mai murmushi tare da mikewa ta fita daga dakin ,
Tana fita daki ta nifa ta dakko wani rufaffen kwano sannan ta dawo ta sake zama dab dashi ta zauna ta kuma sakar masa murmushi a karo na biyu sannan tace masa ya tashi, dataga be gane me take nufi ba setai mai nuni alamar ya tashi
A hankali ya kuma yunqurin tashi a karo nabiyu amma kuma seya kasa ze koma ya kwanta tai masa alamar a'a, da taga bashi da niyar dena kallonta seta mike ta koma bayan sa wai zata dagoshi,, cike da mamaki yake kallonta tare da mamakin qarfin hali irin nata, jibeta 'yar qarama da ita wai zata dagashi, lallaima yarinya nan yana cikin zance zucin da yake ne yaji ta cakume shi da sunan zata dagashi, ayko seya sake sakin qara sabda zafin dayaji na ciwon dake bayan sa bata damu da ihun dayeke ba har seda ta zaunar dashi,
Daqar ta Iya zaunar dashi har tana zufa
Tana zaunar dashi ta zube a gurin tana mayar da numfashi,
Dakyar ya Iya dago idon sa da suka fara canza kalah dan azaba ya kalleta lokaci daya itama ta dago ido suka bada ido,
Suna hada ido gabanta ya fadi, da sauri tayi qasa da idonta a nitse Takai hannunta kan kwanon da ta dakko a daki ta bude fura ce da nono ta miqa msa tace yasha, ya gane nufinta a hankali ya fara dago hanun amma kuma seya kasa
Data fahimci hakan seta mike daga inda take ta dauki kwanon ta matsa kusa dashi ta zauna sannan tasa ludayi ta juya ta debo ta miqa masa kusa da bakinsa, ya jima yana kallon ludayin sannan ya maida kallonsa kanta,
Tambayar dayakewa kansa itace wai shin inane nan?
Kuma wa'yannan su waye?
Wannan yarinyar wacece ita?
Waze tambaya ya bashi amsoshin wannan tambayoyi nasa?
Data ga bashi da niyar bude bakin ne seta sake miqa masa ludayin har yana taba lips dinsa , sa'a sannan ya dawo daga duniyar tinanin da yakeyi, a nitse ya bude bakin ya fara seeping, se kuma ya kauda kansa da sauri kamar Wanda ya tina wani abu,
Daqar ta samu ta lallabashi ya sha sosai.
Bayan ya gama sha ne ta dakko masa maganin sa shima ta bashi yasha , tunda ta bara bashi maganin yake mamakin yarinyar
Badan komai ba se yanda take dawainiya dashi, harga Allah ya jinjinawa jarumtar yarinyar, tana gama shafa mai maganin ta taimaka masa ya kwanta yana kwanciya moddibo ya shigo da sallamar sa aiko Rabe da gudu ta nufeshi ta rungumeshi tana fading baba ya tashi wllh ya tashi,
Kana kallonta zaka fahimci tana cikin barin ciki๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ
Tunda ta fara magana moddibo yake kallonta da murmushi yace to yanzu kuka ya qare ko?
Da sauri ta rufe fuskarta da zarazarn hannayenta tana dariya,
Tun shigowar moddibo matashin yake kallon su har zuwa sanda Rabe ta rungumeshi, se kallon su yake cike da burgewa da alama mahaifin tane ya fada a zuciyar sa, sabda suna bala'in kama da juna!


Wai shin wanene wannan matashin??????


INA MIQA SAQON TA'AZIYAR SURAIYYAR surayyah ga Uwar dakin kuma aunty na Khadeeja candy
inayiwa sauran 'yan uwa ta'aziyar wa'yanda suka rasa fatan Allah ya gafarta mana gaba daya๐Ÿ‘(CIBADO TAKU A KULLUM๐Ÿ˜˜)
[8:49PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 7*


A nitse moddibo ya qarasa kusa da matashin ya sunkuya da murmushi a fuskarsa yace sannu da jiki kaji
Cikin harshen fulatanci moddibo Yayi maganar, ido kawai matashin yake bin moddibo dashi sabda Sam besan me yake fada ba,
Moddibo ya fahimci matashin baya jin fulatanci shiyasa yay murmushi sannan yace dashi sannu cikin harshen Hausa
Matashin ya bude baki da nufin ya amsawa moddibo amma sedai muryanshi bata fita sosai sabda mura data kamashi ( abinka da Wanda be saba da wahala ba lol)
A nitse moddibo ya fara magana kamar haka
Yaro nasan zuciyarka a cike take da tambayoyi akan mu , ko?
Kuma nasan zakaso kasan meye dalilin zuwanka wannan gurin?
To magana na gaskia itace ina hanyar dawo wata daga kiwo ne Allah ya hadani dakai kana kwance a cikin jini !!
Na Dade bana bin hanyar amma dayake Allah ya qaddara semun hadu dakai seya nufeni da bin hanyar Ashe rabon in taimake ka ne,
Safari nazata ma ka rasu amma Dana tabaka sena fahimci kana numfashi haka mukaita kula da rauni kan jikin ka har Allah ya amince mana ka tashi,
Nan da nan idon matashin ya kawo ruwa ba komai ne yasa shi hawaye ba se irin karamcin da moddibo yay masa,
Yanzu babbar damuwarsa yanzu be San halin da dadynsa yake ciki ba!
Cike da kulawa moddibo ya dafashi yace kayi haquri yaro nasan dole zakayi kewar gida amma ka qara haquri jikinka ya qara qwari seka tafi ko ? A nitse ya amsa tare da yiwa moddibo godia,
Har moddibo ya mike se kuma ya sake sunkuyowa yace da matashin yaro ya sunan ka??
A nitse ya firta Muzaffar Abdulwahab
Moddibo yay murmushi yace dakyau, dik wannan hiran da suke Rabe na jinsu a nitse ta qaraso kusa da matashin da murmushi a fiskarta tace sunan ka dama zafar ne?
Muzaffar yay murmushi a karo na farko yace muzaffar nace ba zafar ba,
Tun daga lokacin da zafar yay murmushi har zuwa sanda ya gama magana take kallon sa ,
Ba komai take kallo ba se tsabar kyau irin nasa bata tabbatar da shi kyakkyawa bane seda yay murmushi,
Mutane dayawa suna fadar tana da kyau amma yau taga Wanda ya fita kyau da tsarin halitta,
Nima kaina seda na dan tsorata da kyansa lol)
Seda moddibo ya dafata sannan ta dawo daga duniyar tinanin da take,,,
A daburce tace baba yaushe za'a kuma bashi abinci?
Harga Allah ba abinda tayi niyar fada ba kenan tsabaragen daburcewa ne yasa ta fadi haka, sosai moddibo ya fahimci halin data ke ciki amma kawai seyay murmushi, ya fita daga dakin
A hankali muzaffar ya dago kansa ya kalleta yace ya sunan ki? A taqaice tace masa Rabe
A hankali ya kuma maimaita sunan, a taqaice yace mata thanks for everything.
Daga haka ya koma ya kwanta,, ta jima tana juya kalmar a ranta dikda cewa bata San meyace ba amma setaji Kalmar tayi mata dadi,,
Be sake cewa komaiba har yamma
Moddibo ne ya shafa masa magani sannan yasa Rabe ta Dora masa ruwan zabi ta kawo masa tana kawowa tayi waje abinta, moddibo ya tashi ya nufi inda muzaffar ke kwance a hankali ya fara kiran sunan sa,
A nitse muzaffar ya bude idanunsa a fiskar moddibo,
Murmushi Yayi masa sannan yace ka gyara zan goge ma jikin ka , a nitse ya fara qoqarin tashi amma kuma seya kasa tashin moddibo ne ya taimaka masa ya tashi zaune, wani farin saki moddibo ya qara dakkowa ya tsoma a cikin ruwan ya fara gasawa muzaffar jikinsa, dik da cewa jikinsa nayi masa ciwo sosai hakan be hana moddibo gsa masa ba
Yana gamawa ya dakko maganin shafi ya shafa masa sannan ya taimaka masa yayi alwala, sannan ya shiga rama sallolin da ake binsa ya Dade yana yi dik da cewa besan adadin kwanakin daya zauna a qauyen ba,
Seda ya dau lokaci me tsayi sannan ya idar, moddibo ne ya tai maka masa ya kwanta sannan ya dakko wani zanin saki ya lullube shi ba dau lokaci ba bacci yay a won gaba dashi




Kuyi haquri da wannan bana dan jin dadi ne๐Ÿ‘
[8:50PM, 2/6/2018] โ€ช+234 813 272 6929โ€ฌ: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


*BAFULATANA*
_True life story_


*_Written By Cibado๐Ÿ˜˜_*


_Dedicated to Khadeeja Candy_


*Page - 8*


Ban garen Rabe kuwa tunda ta fita bata sake dawowa dakin ba
Sallah ta gabatar sannan ta fito ta gabatar da aiyukan da ta saba na yau da kullum seda ta gama tsaf sannan ta koma daki da nufin ta gabatar da sallar ishsha'i, bayan ta idar ta jima tana adduo'inta sannan ta shafa,
Da sauri ta mike ta cire mayafinta ta nufi katifar ciyawarta dan ta kwanta sbda sanyin daya fara busowa,
Kamar daga sama taji an banko mata cikin dakin aiko da sauri ta miqe sabda sanin ko wacece ta shigo, dan inda sabo yaka mata ace ta saba da halin Laure,
Masifa fal ranta ta shigo dakin tare da yi mata kallon wulaqanci tace to 'yar gatan gata rere to fito kiyi min ayki dakike qoqarin kwanciya, ai wllh baki isa kiyi bacci yanzu ba
Bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login