Showing 1 words to 526 words out of 526 words

Chapter 1 - Mu Yi Dariya Zallah Hausa Novels 2025.txt

Yahya So   

22 Dec 2024

2276

😂Musha Dariya 😂
Wani Dan Nigeria ne yaje Kasar waje Sai 'yan Sanda suka Biyoshi zasu Kamashi. Sai ya shiga wani gidan Rawa, Suka rasa yanda zasuyi su kamashi. Sai wani Bature yace, " Kun San yanda Zakuyi?" Sukace " A'a. " Sai yace, " A kashe duk wutar dake wurin tayi kamar minti ukku." Sai kuwa aka kashe, bayan Minti ukku yace," A kunna. " Ana kunnawa abinka da dan Nigeria, Sai yace " Nepaaaa😀!!!" Baturen yace," Gashi can, Ku kama shi."😂😂




SHIN SHEHU JAHA NA WANENE?...


Sanannen suna na ban dariya a hikayoyin hausa ko? Haka ma a labaran gabashin duniya da Arewacin Africa wannan sunan ya ja zare na daruruwan shekaru, To ko wanene Shehu Jaha?
Jaha Gwarzon ban dariya a karni na 8 Miladiyya,wato Karni na biyu Hijiriya, fasihin wawa ne da babu wanda ya taba ganinsa sai a tatsuniya, amma har yau ana fafatawa kan mallakarsa tsakanin Tsohuwar Daular Farisa da Daulolin larabawan dauri inda kowanne ke cewa nasa ne. Sai dai masana halayyar tarihin al'adu sun fi zaton Juha dan asalin kasar Tatsuniyar Farisa ne, duba da cewa kafin hadewar Daular Farisa da Daular musulunci ta Larabawa, ba a san larabawa da hikayoyin ban dariya ba, sai yaki da soyayya, ta dalilin haka ne ma a adabinsu zaka rika jin Blockbusters na Sinimar zamanin su ne su Antaru dan Shaddadu wanda har dokinsa ma mayaki ne, da Irinsu Imru'ul Qais wadanda sukan kai ziyarar aikin Hajji garin masoyiyar da a mafarki suka hadu, kodayake su ma din ana zaton duk a mafarki suka faru....
Amma kuma ko da Juha baya dauke da fasfo din daular larabawa ba za a kwace wa larabawa Kokarinsu wajen kafa masa Industiri din da ta sa aka san shi a duniya ba, malaman hikaya larabawa sun wa Juha rawani suka sanya masa Alkyabba, sannan suka kara masa yawan labarai inda ya tashi daga Single film ya koma Series mafi tsayi, basu tsaya a nan ba wajen karrama wannan shahararren Sharukhan din ba sai da suka dora Subtitle a duk labaransa ta inda da ba dan larabci ba da Juha na can Farisa a matsayin lokal camfiyon iwa dan takarar NNPP, Sannan suka rika kai shi majalisar malamai da ta sarakuna yana diban nishadi a can babu me ce da shi Kanzil. Ina da tabbacin da Juha na duniya ko kuma an taba yinsa, zai fi zaben a ce masa Balarabe daga bafarise ko batirke, Don Aradu bagadaza ce Holiwud dinsa ba Santambul ko gidan Kisira ba....
Ba wannan ne abinda ya fi damuna ba, abinda ya fi jan hankalina shine yadda Juha ya warwasa a zamanin daular musulunci ba tare da an sami Malamai masu tsine masa ba kamar yadda takwarorinsa 'yan wasan kwaikwayo da masu kirkira na zamanin nan kullun ake hana su sakat ba. Darasin da nake iya dauka akan Shehu Juha Shine yadda yake nuna min cewa a zamanin da Musulunci ke da daula, addinin bai zama Dodo ba sai yanzu da ba shi da daular ne wasu tsiraru ke son mai da shi addinin da babu raha, babu walwala, daga tsoro sai tsarguwa ba.
Allah Ya jikan Hikima da Fasahar Musulunci me fama da kisan gilla

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login