Showing 75001 words to 76231 words out of 76231 words

Chapter 26 - Shiryayyar Kaddara Part 1 Complete .txt

maka to?”
“ya kirani ne ya sanar dani har ma sun tattauna maganar shi da su ya Ubaid, Abbah da ya Tahir ɗin ne kawai ya rage basu sanarmawa ba,amma yace zuwa gobe zai sanar da su dan a san yaushe ya kamata a sa bikin na su,amma fa nayi mamakin da ban taɓa lura da suna soyayya ba duk abun Noor ma bata taɓa sanar dani ba” tunda ya fara magana mom fatilah ta shiga binshi da wani kallon rainin wayau,Noor saukowarta kenan taji abun da dadyn nata ke furtawa,da gudu ta nufi ɗakinta ba tare da ta ko kawo masa glass ɗin da yace ta ɗauko mashi ba.




“gaskiya naji daɗin haka,kinga kafin mu tafi sai a tsaida ranar Auren na su zuwa bayan sallah sai ayi bikin,yara nata ƙara mana daƙon zumunci,saura Yazdan fatana shima ya daina wannan shashanci ya zama mutumin ƙwarai kinga sai mu haɗa su shi da Yumnah” kallon mom fatilah yayi jin tunda ya fara magana ƙalla ba tace ba






“naji kinyi shiru ba kice komai ba,magana nake kana Auren Noor f...” saurin katse shi mom fatilah tayi
“dan Allah dakata Dr,wallahi sam ba zai yiwu ba”
da mamaki yake kallonta bai taɓa tunanin wannan ce kalmar zata fito daga bakinta ba.




“fatila kin san mi ki ke faɗa kuwa?”
“na san mi nake faɗa kuma ina cikin hankalina,wannan haɗin sam bazai yiwu ba ni ba hajiya halima bace ko salima da ku ka nunama fin ƙarfi akan ƴaƴan su,ku ka nuna basu da right ɗin zaɓarma ƴaƴan su abokan zama,ni sam bazan ƴarda da wannan ba,babu ƴaƴana babu ƴaƴan Zulaihart period”




kallonta kawai uncle mutallaf keyi cike da mamaki,ko a mafarki bai taɓa tunanin wannan amsar daga gareta ba,yayi matuƙar mamakin ta duk da ya san ba su jituwa da matar yayan nashi.


“wallahi babu ƴaƴana babu ƴaƴan Zulaihart,haka kawai kuyita kwasar mana ƴaƴa kuna ba ƴaƴan Zulaihart sai kace ita kaɗai ke da ƴaƴa, gaskiya ni ban amince ba”




“amma nayi mamakin jin haka daga gareki,banyi tunanin za ki yi haka ba,miye laifin Zulaihart ne da zaki ƙi son haɗa alaƙa da ita,ai ko dan ya Tahir da farin cikin ƴarki kin amince”


tashi tayi daga inda take zaune cikin ɗaga murya tace
“wallahi bazan amince ba,haɗa dangantaka da Zulaihart wallahi bazan yi ba,ai da Noor ke faɗa man na ɗauka shashancinta ne ai ban san abun da gaske bane da wallahi tuni nayi ma tufkar hanci,haka kawai kuyi ta haɗa mu da dangin yahudawa, wallahi tun wuri kace ma ƴan uwanka baka amince ba dan Noor bazata Auri Irfan ba” ta kai ƙarshen maganar tana huci




“kin gama” uncle Mutallaf ya faɗa yana tsareta da idanu
“ban gane na gama ba,haka kawai sai inƙi faɗin ra'ayina,kowace yarinya sai ku ɗauka kuba ƴaƴan Zulaihart haka akeyi,idan su hajiya halima sun amince saboda kwaɗayin abun duniya ni wallahi bazan amince ba”




“Fatilah ina so ki san wani abu Noor da Irfan are my kids, ke baki isa ki sa na fasa abunda nayi niyya ba,Aure tsakanin Noor da Irfan Kamar anyi an gama ne in dai ni ne ubanta ba wani daban ba” ya faɗa a kausashe




“lallai Dr zaka tafka babban kuskure in dai kace sai ta Auri Irfan”
“kwarai kuwa,kije kiyi duk abunda ki ke ganin zaki iya amma Aure tsakanin Noor da Irfan Kamar anyi shi angama,ke baki isa kisa na zuba ma ƴan uwana ƙasa a ido ba,yanda aka yi na Naeem da Adnan lafiya haka za'ayi na Noor da Irfan sai dai kiyi duk abunda za kiyi”




Kwashewa tayi da wata irin dariya“haka dai kace ko,za kuwa kaga abunda zan aikata” sosai saɓani ya shiga tsakaninsu akan wannan maganar.




Noor lokacin data nufi bedroom ɗin ta,wayarta ta ɗauka tayi dialing number Irfan,har Kiran ya katse baiyi picking ba, sake kira tayi sai a na biyun ne yayi picking
“hey beb, what's up?” ya faɗa daga cikin wayar


“am really happy dear,yau dai ka cika alƙawari, i really really love u irin billions ɗin nan,i wish kana kusa da na baka warm hug of happiness”ta faɗa tana sakin dariya


daga cikin wayar tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya “I would like that baby,but wait farin cikin mi kike?”
“ban gane farin cikin mi nake ba,kana nufin baka sani ba?”
“am serious dear ban sani ba” ɓata fuska tayi tana turo baki


“bana son wannan wasan yaya”
“am serious Qanwata ban sani ba”
“yaya yanzu maganar Auren namuce baka sani ba” ta faɗa tana wani murguɗa mashi baki kamar irin yana kusa da ita ɗin nan
“maganar Auren fa,a ina ki ka ji?”
“yanzu naji dady na waya da Uncle Ahmad yana sanar dashi” ajiyar zuciya taji ya sauke


“Alhmdllh, gaskiya naji daɗin jin haka,am really happy dear” dariya ta saki
“wai da gaske ba kai ka faɗa mashi ba”
“da gaske nake,i think Waseef ne ya sanar dashi”
“amma naji daɗi ya Waseef ya faranta man shima Allah ya faranta mashi”
“Ameen,yanzu shikenan beb mun kusa zama husband and wife”
“yeah very soon we became husband and wifeee” ta faɗa tana jan wife ɗin,dariya su ka yi gaba ɗayan su, faɗawa tayi saman bed ɗin ta
“gaskiya dole nayi ma ya Waseef kyauta yayi abunda ka kasa tsawan shekaru”




a shagwaɓe yace “beb Ni fa kyautar”
“taka special ce husband to be”
“beb,Ina so mu haɗu Please” ya faɗa yana wani shagwaɓe murya kamar ƙaramin yaro
“ka zo gida mana”
“No beby kunyar uncle nake ji,kina so yace daga faɗa mashi har na fara mashi Zarya a gida”
“kunya fa yaya,shi fa dady ba ruwanshi”
“ni dai bazan iya zuwa ba beb,kawai ki nema mana inda zamu haɗu”
“please Ni dai ka zo, ko a compound ne sai ka tsaya ba saika shigo ciki ba”
“ok let me see idan zan iya zuwa”
“zaka iya dear”




cike da farin ciki su ka cigaba da waya,daga yanayin yanda su ke wayar zaka tabbatar suna cikin farin ciki,hayaniyar da taji ne yasa tayi saurin ce mashi tana zuwa, rejecting call ɗin tayi,da sauri ta sauka daga saman bed ɗin ta nufi ƙofar fita zuwa parlor,anan ta samu dadynta da momynta suna saɓani saboda Auren su.




cikin parlorn ta ƙarasa,fashewa tayi da kuka “momy mi yasa za kice haka akan ya Irfan,gaskiya ki daina man wannan wasan”
“sai na mareki idan ba kiyi man shiru anan ba shashasha”turo baki Noor ɗin tayi hawaye na bin cheek ɗinta


“kowa na farin ciki sai ke ce zaki tsiro da haka,ni gaskiya ya Irfan nake so kuma shi zan Aura,haka kwai burinda na daɗe ina jira zaki wani ɓ...” bata ƙarasa ba saboda saukar marin da taji,da gudu ta nufi dadynta tana fashewa da kuka.




“shashashar banza wacce bata san inda ke mata ciwo ba,ai da duk a zatona kina da hankali ashe sakaryace ke ban sani ba”




“dady dan Allah karka bari ta rabani da ya Irfan” ta faɗa tana kuka
“yi shiru Noor,karki wani tashi hankalinki ni ne dai dadynki ba wani ba,babu wanda ya isa rabaki da Irfan sai Allah,Irfan shine zaɓi na” tsaki mom fatilah taja
“zaku sha mamakina daga kai har ita” tana faɗar haka ta nufi sama,hannu yasa ya shiga goge mata hawayen dake zuba.




“yi haƙuri kukan ya isa haka,where is my glasses?” bedroom ɗinta ta nufa da sauri, glass ɗin ta ɗauko mashi,amsa yayi yana ɗan shafa kanta
“karki damu kinji” gyaɗa mashi kai tayi,ficewa yayi daga parlorn ita kuma ta koma bedroom ɗinta ranta duk a jagule bata taɓa zaton haka daga momynta ba...




*Uhmmm mom fatilah yada haka*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login