Showing 24001 words to 25591 words out of 25591 words

Chapter 9 - Kwai Cikin Kaya Book 1 By Billyn Abdull .txt

23 Nov 2024

2344

kuma a kwance cikin kujera.
Sam babu wanda a cikinsu yaji sallamarsa balle motsin buɗe ƙofa.
Taku yake a hankali har gaban kayan kiɗan yasa hannu ya kashe, tsitt falon yayi.
Gaba ɗayansu a firgice suka maido kallonsu gareshi, kafin kace mi an fara ƴar reran gudu ta ƙofar kichin, wasu kuma ta ƙofar falon.
Shahudah da ke kwance ta ɓata fuska tana masa kallon takaici.
Koda suka gama fita baice mata uffanba, kallo ɗaya yay mata yay hayewarsa sama inda zai iske ɗakinsa.
Tundaga hawowarsa step ɗin farko ya fahimci Batool ko Nabeelah wani yazo yay gyara, hakan saiya ɗan rage masa fusatar da yayi.
Ɗakin barcinsa ya zarce kai tsaye, yana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da murza key dan karma Shahudah ta shigo.
Ɗakin yay ƙal saboda gyaran da ya samu, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi ga iskar hadari da ke bada ƙamshin ƙasa.
Tamkar jira ake ya zauna ruwa ya fara sauka a hankali.
Yana zaune a bakin gado yana zame takalminsa yakejin bugun ƙofar da Shahudah ke masa, baiko kalli ƙofarba balle tasamu darajar kulawa yay shigewarsa bayi bayan ya cire komai na jikinsa, sai ƙaramin wando da ya bari.
Gaba ɗaya yarasa wane irin mataki ya dace ya ɗauka akan Shahudah ne ta dawo hankalinta, shi yama fara tunanin ko bata da isashshen hankaline, dan sam baiga abubuwan masu hankali tattare da ɗabi'unta ba, ko ada can yasan bata da kirrki sam, amma zaman watanni bakwai da sukai a tare ya sake fahimtar dashi sanin da yay mata a baya ƙaramine ashe.
Rai a ɓace yay wankan harya gama ya fito, baiji motsinta ba, hakan yasashi gane tayi fushi, ya taɓe baki irin na rashin damuwa da hakan.
Zuwa yanzu ruwa ake zugawa sosai, hakan yasa yay sallarsa ta magriba a ɗaki, bayan ya idar mai makon ya zauna tunani sai ya ɗauki Qur'an ya hau karatu cikin nutsatstsuyar muryarsa.
Bai matsa a gunba har sai da aka kira isha'i, har sannan kuma ruwan saman ake zugawa.
Wayarsa dake ring tun yana salla ya ɗauka, ganin Umma Bara'atu ce sai yay murmushi (Umma Bara'atu ƙanwar mahaifiyar Jawaad ce, karku manta a labarinsa ya nuna mana tana da ƙanne har uku duk mata).
Cikin girmamawa ya gaisheta, da ga can ta amsa masa cike da kulawa.
Bayan sun gama gaisuwarsu take tambayarsa koya ga abinci?.
Murmushi mai sauti yayi, wanda har tana jiyosa, ya kwanta rigingine a gadon ƙafafunsa na ƙasa, “Yanzu nan Umma bazaki daina walar da kanki wajen aikomin abinciba kamar wani ɗan primary ”.
Dariya tayi daga can, cike da son tsokanarsa tace, “Yo miye banbancinka dasu Jawaad, ni a gurina ai tamkar tata kake, bama ni na aiko da abincinba, ƴar uwarka ce tayisa shine tabama Nabeelah da taga zatazo tace ta kawo maka, sai kuma Nabeelar ta iske bama ka gidan ka fice”.
“Ayya, ALLAH sarki Sister, na gode mata kuwa, ALLAH ya bata miji na gari wanda zai kulamin da ita, wlhy kiran gaggawa na samu da ga Office Umma shiyyasa na fice bata iskeniba”.
“Aini wannan aikin naka dan banda yanda zanyine, amma da ga ni har Auta da Amina bama sonsa sam, sai dai muna maka fatan alkairi a cikin, tunda kullum baba shi baya ganin laifinka”.
Guntun dariya Jawaad yayi, da gani kasan hirar ta sakashi nishaɗi, dan a ransa ji yake tamkar yana magana ne da mahaifiyarsa, “Karku damu Umma's ɗina, addu'arku ita nafi buƙata, harma kinsa na tuna da Tsoho, insha ALLAH da safe asubanci zan masa naje shan saurar furarsa”.
“Ja'iri, zaka fara ko? To sai anjima”.
Sosai Jawaad ya ƙyalƙyace da dariya, ya shiga faɗin, “Haba Ummana karmuyi haka dake, tsaya kiji......”
Ƙitt ta yanke wayar da ga can itama tana ƙyalƙyata dariya.

Sumbatar wayar Jawaad yay a hankali yana kuma faɗaɗa murmushin fuskarsa dajin ƙarin ƙaunar ƙannen mahaifiyar tasa, masu ƙoƙarin share kukansa a koda yaushe.






_______________________
BILKEESU
________________________




Naji daɗin shigowa gida na iske su Jazuga basa nan, ɗakinsa a rufe.
Firdausi kawai na iske a ɗakinmu, Inna ta fita maƙwafta yin barkar haihuwa.
Tagumin da Firdausi tayine na janye, ta ɗago a firgice tana kallona, ganin nice sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya.
Murmushi nayi ina faɗin, “Matsoraciya kin zata waye da?”.
“Ƴan ta'addan gidanmu mana, wlhy wannan rayuwar ta fara gundirata Bilkisu, nifa yanzu ko shakkar banzan nan banayi balle tsoro, dan nakula ibilis ne kawai ya rikiɗa a mutum ya shigo mana gida”.
Ido na zaro waje ina waige-waige, a tsorace nake magana ƙasa-ƙasa, “Firdausi bar irin maganarnan dan ALLAH kar wani yaji”.
Baki ta taɓe tana miƙewa tsaye, “Ai kunji tsiyar, wannan tsoron naku shike ƙara masa karsashi da jin ya isa, wlhy inhar a haka za'a cigaba da tafiya to lallai akwai babbar matsala, dan kuwa sai kunkoma bayinsa tamkar a ƙarnin farko”.
Tsayawa nai kawai ina kallonta, dan na fahimci ranta a ɓace yake, hakan yasa nai shiru, sam banason zancen yay tsawon da har wani zaiji, duk da Jazuga baya nan za'a iya samun wani ɗan neman gindin zaman a gidan namu ya sanar masa.
Itama jin nayi shiru sai taja tsaki ta fice ta barmin ɗakin, murmushi kawai nayi ina girgiza kaina, na cire kayana sannan na ɗauki abincinmu da nasan Firdausi bata ciba tana jirana na fita, nasan bazata wuce tana soro ba zaune.
Ilai kuwa acan na isketa, dan haka na zauna kusa da ita ina ajiye kwanon tasar abincin a gabanta.
Cikin sigar lallashi nake faɗin, “Haba dai tawan, wai fushi kikayi? To kiyi haƙuri kinji, taho muci abinci, dan da gaske da yunwa na dawo mai katse ƴan hanjin ciki”.
Hararata tayi tana ƙokarin matse dariyar dake neman kufce mata, (haka muke sam bamu iya dogon fushi da juna).
Munacin abinci muna ƴar hira jefi-jefi, sai ƙokarin kauda firar da Firdausi ke ɗakkowa ta Jazuga nakeyi gudun kar'a samu matsala, a haka har muka gama na sake ɗaukar kwanon abincin na maida cikin gida.


★★★★★★★


Kwanaki huɗu kenan cif Jazuga baya gidan, da alama dai yayi nisan kiwo, kallo ɗaya zakaima gidanmu ka fahimci akuyoyin ɗaure sun samu sake, dan harmun fara sakin jikinmu muna rayuwarmu tamkar ta baya.
Sai dai kash a ranar cikon ta biyar murna ta koma ciki, ɓeraye suka koma wasan ɓuya da kuliya🤣, dan kuwa da yammaci kwatsam saiga Jazuga da zugarsa sun dawo, tsit kakejin gidan ya koma tamkar mala'ikan mutuwa ya shigo.
A ƙofar shigowa soro ya tsaya, sai da ya karema gidan kallon kamar yau ya fara shigowa, sannan ya tako zuwa ciki, tafiya yake kamar zai tsinke saboda rashin ƙiba
Dan sam Jazuga bashi da jiki, gaba ɗaya wiwi ta gama kalace dukkan wata tsokar jikinsa sai ƙashi data bar masa da fata
Amma a hakan akejin tsoronsa tamkar mutuwa, ga jiki duk yabi ya zane da tatu, daka gansa kaga ainahin hatsabibi mai matuƙar haɗari da rashin imani, dan tsaf zai iya tsarwatsa kwalwar kanka da bindiga ba tare da ya damu ba.................✍🏻
















*_ALLAH ka gafarta.a iyayenmu_*😭🙏🏻


********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels






Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ ***************************

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login