Showing 6001 words to 7655 words out of 7655 words

Chapter 3 - ZAMAN DADIRO Book Complete Document Oum Aphnan.txt

dafe hannu "Wayyoh hannuna🥺hakan ya jawo attention din duk wanda suke dakin, fiddoh ta cika Nafsy da sauri, Adnan da sauri ya waigo ya kalli Farhaan
" Lafiya? Me tayi maka? "
Farhaan sarkin fadin rai, a fusace ya Mike tsaye yana maida kayansa "an fasa cin "
Da gudu tasa gwiwoyinta a kasa tana rokonsa yayi haƙuri ya ci ta" Ko bi ta kanta baiyi ba ya fara neme nemen kayansa zai tafi
"Aboki kanka daya kuwa? " Ban sani ba, in zaka yi ai ban hanaka ba amma ni wallahi na fasa... "
Fiddoh sarkin rashin kunya turo baki tayi " To wai me yasa? Ni wallahi sai na dandani dogon buranka, wannan ai bakin ciki ne saida ka sa mana rai"
"Ke! Kinsan ni wanene? Ina magana kina magana?! Yanzun nan zan maki dukan tsiya sannan in kira Jami'ai su tafi dake ki kare rayiwarki a gidan Yari... "
Yanda yake numfarfashi yasa Adnan hankalinsa ya tashi
"Ya Isah haka abokina mu je ko? " Ya tasa keyarsa yana rarrashinsa,saida yakai kofa ya waigo ya kalle su "bebs ku tura mun acc details dinku zan tura maku 1.5million kowannenku sai ta dauki 500k sai watarana ko? "


Tsaki sukayi ransu a bace nafsy tace "kinga tsiyan online date ko? Da Ace shi ya biyo mu da kansa ai da bai isa ya wulakanta ki ba wallahi, kamar ke? High valued din.... "


***
Washekari


Zainab bata fita aikin keke napep dinta ba, ta shirya tsaf cikin burgujejen riga over size na maza da wando cinos, ta dauko veil din abaya ta dan yafa a gashin kanta da yafi kwana dari ba kitso, yanzu ma ko tajeshi bata yi saidai ta cunkusa masa ribbom tayi gaba, neman kudi kawai tasa a gaba to sai yau kuma da ta fito neman lafiyalafiya
Tafe take a gefen titin GRA ɗin garin Kadunan, hannunta riƙe da sanda tana tafe tana caccaka sandar a ƙasa tana wasa dashi , ba jaka a tare da ita sai wayar salulanta ƴar ƙarama ta tsufa ko 5k baza a siya ba, ƴan canjin ta kuma suna cikin burgujejen aljihun wandon ta.


Babu zato taji Horn a bayanta “Ɓiiiiiiiii ɓiiiiiiii" Waigawa tayi bayanta taga wani kaftareren mota jeep baki wuluk yan dunfaro inda take tafe, tsaki taja ta cigaba da tafiyarta a tsanake tamkar ma bataji Horn din ba.
Farhaan a fusace ya cigaba da horning motarsa cikin ɓacin rai, zuwa yanzu ma Zainab ko juya baya ma takiyi bare ta san Allah yayi ruwan tsiruwansa


A hassale ya kashe motan daf da ita ya fito da sauri yana jaraba bakinsa kamar zai kama da wuta saboda yanda halshensa ke harɗewa cikin ɓacin rai.
"Ke kinga ya kamata kina mana yawo akan titi? "
Zainab soke wayarta tayi a cikin wando ta fara gyara hantsar wandonta kamar me shirin dambe.
"Ina ne hanyar? Nan gabana shine hanya ko anan.... Baka da hankali ne? Da zaka raɓo gefen hanya ka ishe mu da Horn to an ƙi a matsa ɗin"
Wangale baki yayi yana kallon ta kafin ya nuna ta da yatsa "ke jaka ne "
"Kai ne jaki ga ka nan babban Alade! "
Matsowa kusa da ita ya shiga yi yana buɗe mata ido "Ke ni kike ce ma Alade, jaki"
Sa hannu tayi a kirjinsa ta hankaɗashi "Ance maka Aladen, banza ɗan biri kawai"
"Ke ke ni kike taɓa da wannan ƙazamin hannun naki? "
Ɗaga hannunta tayi ta sake maka masa a kirji "An taɓe kan me zaka iya, nace na taɓeka"
"Ke Listen Listen, idan nayi Landing hannu na a kumatunki wallahi sai kinga farfatsin wuta"
"Bismillah shege ka fasa ɗan Halas se yanka, taɓeni in dagargaza motar nan" Tayi wani bata da gudu ta daggo zugegen zandarta a kasa ta dawo gabansa "Land it, kana Marina zan zuga maka sandar nan a gadon bayan ka"
Zare ido ya fara yi cikin tsorata, anya wannan mutum ce kuwa? Wawwaigawa ya shiga yi yaga babu kowa a hanyar abun ka da unguwar ƴan gayu.
Hankaɗata ya shiga yi "Je ki je ki dai you're animal"
Da yike Zainaba na ɗan jin Turanci ta sake harzuka "kaine babban Animal Bani ba dai... Ka bar animal a gida tana rainon kanninka"
"Ke ni kike zagin ma uwa? "
"Na taya ƴaƴa na kishina ne da ka zagan masu ni, shine na rama masu, in ma ka sake zagina ramawan zan yi banza ɗan shaye shaye"


"Gakinan ƴar ƙwaya ƴar kwata, ji ba kayan jikin ki kamar namiji, ji ba har da wani cire takalmi, to dawa zaki yi dambe? Wai ni na rantse saidai ki ƙare rayuwar ki a gidan Yari... "


"Karya kake yi wallahi kaine zaka mutu, bi iznillahi motar nan ita zata zama Ajalin ka... "
Ƙuuuu cikinsa ya karta, tunda yake ba'a taɓa masa mugun Alkaba'i ba sai yau "Iyeeeh ni kike ce ma haka? Yanzu nan zan taka ki da mota, kowa ya huta don na lura ke jarababbiyace in na kashe ki dangin ki sayi farin ciki"
"Wooohh ɗan yankan kai wooooh ɗan shan jinin mutane, kaina ƙwari gare shi na rantse Nafi karfin ka"
"Shegiya mahaukaciya matsa ki bani waje Ajjana kawai👹"


"Kaine nan Aljani me dodon tsafi wato kana so ka kashe ni ka siya sabon mota ko, ni ne nan zan tona maka asiri"


Juyawa yayi zai koma motan "matsa ko in hankade ki... Mahaukaciya kawai"
"Iyayen ka sune mahaukata bani ba kuma an ki a matsa din, zo ka taka ni"


Ta bishi har kofar motar, har da gudun sa ya kara ya shige motar ya ja murfin ya rufo bamm!
"Ballagaza kawai Get out! Get out" Sharɓa ma motarsa sanda tayi


"Kaine nan Doya Nonsense, Idiot banza kare me haushi... "


Fiyyy ya ja motar da gudu ya bar wajen, ita kuma ta wuce shi tana cigaba da zage-zage ta cire takalman ta ta riƙe su a hannu
***
Horoin Hospital


Tana shiga Asibitin ta fara rarraba ido kamar er ƙauye
Bin reception din tayi da kallo tana kallon wani abu a kafe kamar TV sai dai shi dogo ne tun daga sama har kasa, yana ta nuno office office din asibitin dasu Laboratory da cash office da wajen Awan ciki, live duk abinda ake kan yi a halin lokacin yake haskowa, bata ƙara tsurewa ba saida taga abun ya nuno ta a tsaye ita kadai a reception. Sosai ta zama er ƙauye ai da sauri ta matsa kusa da Nurse din da ta ɗan kwantar da kanta akan table din ta tana waya ta hanyar amfani da Bluetooth din kunnenta.
"Assalamu Alaikum"
Ɗaga mata hannu tayi irin bata da lokacin magana da ita din nan, kuma kanta a sunkuye ko arzikin ta dago ta kalle ta ma bata samu ba.


"Ina kwana"
Nurse din a kagauce tayi magana da wanda suke waya "Babe Sorry ok... Ke ki shiga can ki ce a nuna maki Dr salami,ki ce masa gakinan Dr Murja ta turo ki.... Babe kana da ban dariya oya gist me"ta cigaba da wayarta ba tare da ta cigaba da bi ta kanta ba


Jikin Zainab a sanyaye ta nufi hanyar da Nurse din ta nuna mata, ta shige Office din, ta ƙaddamar da sakon Nurse din da ta bata wato " Gata nan itace wanda Dr Murja ta aiko ta....... "
Hannu bibbiyu suka amsheta suka wuce da ita sloixe Room aka sauya mata kaya zuwa Blue sabo fil na asibitin mai kamar takarda na yin aikin tiyata,


Zainab dai duk abunda akace mata ta yi shi take yi, har aka gama mata procedure din tana mamakin wannan asibitin.


"Lallai likita bokan Turai, ban faɗi damuwa na ba amma sunyi mun komai su har sun san meke damuna... Yo ba dole ba mutanen da tun da ka shigo sun ma ganka ai wannan asibiti yayi! Saidai inda za ayi kan Bura uba dani shine wajen biyan kuɗi, don daga ni sai ɗari bakwai da sittin. .. Yau za ayi bala'i ni da likitocin nan, in kuma sadaka sukayi toooo... "


***
"Hi Good Morning" Surayya ta ɗaga ma Nurse hannu tana karkaɗe karkaɗe tasha bakin abaya qirar Qatar bakinta ɗau lipgloss sai tauna chewing gum take yi tana bin wajen da kallo tana yatsuna fuska


"Hi, Good Morning how can I help you? "


"Sunana Surayya nazo wajen Dr Murja ne for certain procedure! "
Raras! Gaban Nurse ya faɗi, shikenan yau na mutu, To in wannan itace za'a zuba ma Sperm din a mahaifa, to wacece kuma wancan da na tura?


Dafe kai tayi gamida cilli da wayarta da take kan charting "Wayyo Allah nana! ina zuwa " Tayi Office din Dr Salami da gudu.


Surayya binta tayi da ido gamida caɓe baki ta nema kujera ta zauna,ta harɗe kafa daya kan ɗaya.


Nurse Hurairah tn shuga isa office din Dr Salami akace yana procedure Room, office din Dr Murja ta nufa a furgice, bata yi knock ko sallama ba ta shige Office din
"Dr mutum nawa ne zaayima wancan procedure din? "
"Kamar ya ban gane ba? "
"Wannan Gynecological procedure din da aka ba Dr salami Sperm "
"Ban fahimta ba, you should wait lady din da za ayi mawa zatazo sunanta Surayya, beside yarinyar yayana ne ma"
Dafe hannu akai Nurse Hurairah tayi ta fashe da ihu "Na shiga uku na, Wallahi wata tazo na tura ta ayi mata kuma na je wajen Dr salamin ya riga ya fara aikin"


Daura hannu aka Murja tayi "ba kece da kuka ba ni ne da kuka Hurairah, kinsan kuwa waye me Sperm din nan? Kinsan waye Farhaan kuwa? "








Muje Zuwa💃
#Wai shin ma waye Farhaan??


#Wai ma shuni meye dalilinsa na barin gidansu ya zauna a gidansa shi kadai dukda bai da Aure?


#Tompa gashi dai maniyyin Farhaan ya shiga garari, shin an ɗure a mahaifar Zainab din ko ƙaƙa?


#Me zai biyo baya kuma daga nan? Karku manta bala'in dake tsakanin Zainab da Farhaan a haɗuwar farko.


*KARKU MATSA, LABARIN NAN AKWAI MURƊA MURƊA... AKWAI DIFFERENT SEX STYLES🍌💃👅YES NA MA'AURATA NE*




TAN TAN TAN ANAN KUMA PAGE DIN KYAUTA YA KARE KI BIYA KUDIN KI DON JIN YANDA ZATA KAYA


9065990265
OPAY
MOHAMMAD HASSANA


REGULAR 500₦
VIP 1000₦


MASU SON COMPLETE DOCUMENT 2000₦ NE
BYE💃💃💃💃💃💃🥰
Munje cin gin...... 😆🍌🍌🍌

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login