Showing 3001 words to 6000 words out of 17000 words

Chapter 2 - UNCLE NE BOOK COMPLETE BY NIMCY SARAUTA .txt

13 Dec 2024

1883

ɗin gidan ya nufa yana zuwa ya shige cikin wata ash ɗin ferari ya murza mata key yay waje da gudu kasan cewar tuni Malam Habu ya buɗe gate ɗin.








Zulfa tafiya kawai takai a tsakiyan titin,ba tare data fahimci inda take sanya ƙafafuwanta ba,babu abinda yake ƙara hargitsa mata ƙwaƙwalwa wanda yake tunzurata ga gudun take irin kuka da gurnanin haɗi da wani ƙara da take jiyowa a bayanta,a duk sanda tayi niyar juyawa sai taji wani abu ya daki tsakiyan kanta hakan yasa cikin ƙaramin lokaci ta fice a hayyacinta gudu kawai take babu tsayawa,yayinda gaba ɗaya jijin hauhuwar ya gama jiƙa faffaɗar guduwar rigan dake jikinta,gaba ɗaya ta fice a hankali ta zama mahaukaciyar ƙarfi da yaji,musamman idan kayi duba da yadda yalwatacciyar sumar kanta ta hargitse ta bazo a bayanta tare da rufe mata gefen fuskarta,yadda gashin ya rufe mata fuska ne kuma babu tunanin ta gyarashi domin taga hanyar tafiya kai tsaye ta nufi tsakiyar makeken titin a kuma dai-dai wannan lokacinne wata tsaleliyar mota mai shegen ƙyau da kuma tsari ta kunnu kai,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un duk yadda drever'n motar yaso taka birki kasawa yayi,ƙyaƙƙyauwan magidancin dake bayan motar wanda dukkan alamu shiɗin babban mutumne ya fara salati cikin ransa kasan cewar bai fiya magana ba,amma tabbas ya shiga tashin hankali ba kaɗan ba,cikin dauriya da kuma zafin nama ya fara ƙoƙarin wara laɓɓansa wani zazzafan numfashi ya fesar tare da runtsa idanunaa da ƙarfin cikin daɗɗan muryarsa mai sauti yace "Ya subuhanallah!!" a kuma dai-dai wannan lokacinne drever'n yay gaba da Zulfa...










_Wannan labarin direct ta farkonsa muka fara, zai iya yi maku daɗi a haka wasu kuma ba lallai ba,amma tabbas wannan salon daban yake,cikin nutsuwa zaku fahimci wanene UNCLE ɗin mene yayi ko kuma mene aka aikata masa,na san in sha Allah za kuyi alfahari dani a Wannan littafin kamar yadda kukai a THE NEW EMIR,babu abinda nake buƙata irin *comments* sai share dan Allah dukkan wanda ya karanta ya share zuwa wasu grps koda ɗaya sabida suma su amfana da littafin😍just imagine over 300 messaged on one day masu yimin magana kuyi hqr in sha Allah zan duba ga dai number ta Whasapp 08119237616 a duk inda kuke zaku samu littafin UNCLE NE,masu wattpad kuma kuyi searching NIMCYLUV Thank you guys share share Please🤲🏻


_✨ UNCLE NE ✨_








https://www.wattpad.com/1073694982?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv&wp_originator=mevhPm7g3%2BBY6kjjW3lOcQab3cIv8D8nHmvVnjCDrhHk4t0XwF3ur1azv66d8V7BkCArOE5%2B3aQTAlH2%2BAXmY880JYZZRpZ2qCzrs%2F2ICX5nfNsNsgZ5M%2BazzcuVa2VZ














_✍🏼 NIMCYLUV_


*3-4*


















Ƙarar taka birkin motar da kuma ihun da Zulfa tayi shine yaja hankalinsa zuwa gareta,hannu yasa ya dafe saman goshinsa tare da runtsa idanunsa,cikin kuzari haɗi da sassarfa yasa hannu ya buɗe murfin motar,gaba ɗaya ƙafafunsa ya fito dasu waje tare da zuro da sauran jikinsa,lokacin har mutane sun cika a wajan sun yiwa motar ƙawanya,cikin natsuwa ya fara takawa har wajan da Zulfa ke ƙwance cikin jini,da dukkan alamu tayi muguwar buguwa a kanta domin shike tsiyayar da jini,ɗan tsaki yaja ganin tarin mutane amma babu wanda yay ƙoƙarin taimakonta.
Numfashi ya sauke tare da kallon drevernsa mai suna Joseph cikin jarumtar data rage masa yace "ɗauketa zuwa mota mana" yana faɗin hakan ya juya tare da nufar side ɗin baya ya buɗe,ɗan ja da baya ya bawa Joseph waje domin ya sanya ta a mota, bayan an ƙwantar da ita shi kuma ya kuma mazaunin mai zaman banza ya zauna Joseph kuma ya zauna mazaunin drever.
"Yallaɓai ina muka nufa ne?nasan dai babu maganar wani meeting yanzu saboda condition ɗin da wannan matar ke ciki,Nina gama kamar mahaukaciyace"
Tunda ya fara magana har zuwa lokacin da yay shuru mutumin daya kira da sunan YALLAƁAI baiyi magana ba,zuciyarsa ta tafi wani tunani nada ban,lallai mutum da yana sanin ƙaddarar da za ta samesa tabbas da yayi ƙoƙarin kujewa faruwarta,abinda ya kawo shi wannan garin da ban,amma abinda ya samesa da ban,wannan wanne irin abune.
Mene ya fito da ita? ina zata je?wanne jini kebin jikin?wannan sune tarin tambayoyin da suke zuciyarsa amma ya gagara furtasu sabida nauyin da labɓansa sukai masa.
cikin ƙosawa da maganar Joseph yace "muje UNITY MEDICAL CENTRE HOSPITAL dake nan IBADAN"
Cikin sauri Joseph ya joya motar da taimako map suka samu suka isa asibitin kasan cewarsu baƙi ne a garin.
Suna zuwa asibitin kai tsaye emagency aka shigar da ita,likitoci suka rufu a kanta,bin kican farko suka gano haihuwar da tayi da kuma ƙaruwa da tayi wajan haihuwar,hakan tasa suka yi mata ɗinki tare dayi mata allurar haɗi da sanya mata drip,suna gamayin komai suka fito daga cikin room ɗin da aka sanyata ciki,da sauri drever'n ya miƙe tsaye ya fuskanci babban likitan cikin sonjin abinda ke damun matar yace.
"Dr yaya jikin nata?ta samu lafiya dai?"
Jinjina kai likitan yay tare da juya ƙwayar idanunsa zuwa ga mutumin dake can gefe yana leƙa window,sosai yake mamakin mutumin domin ya hangu zallar damuwa da kuma tashin hankalin dake ƙwance a saman fuskarsa,yana ɓoyewa ne kawai sabida jarumtarsa, murmushi likitan yay kana ya kalli Joseph yace.
"Kada ka damu komai zaiyi dai-dai tasha wahala wajan haihuwa ne,ga kuma ƙaruwar da tayi, amma da yardar ALLAH zata samu lafiya amma ina babyn data haifa?kuma yana da ƙyau ace macace a wajan ta ba maza ba"
Sai a lokacin Mutumin ya juyo zuwa gare su tafiya kaɗan yay yace "Kace haihuwa ce ko?amma macen data haihu mai zai fito da ita kan titi? tabbas bayan haihu aƙwai wani ɓoyayyan tuggu a ƙasa.."
"kana nufin kace baka santa ba?kuma baka san asalin wacece ita ba?"
Dr ya tambaya shima cike da tashin hankali domin shima abin ya fara rikitashi "Amma yallaɓai mai zai hana idan ta farka ka tambaye ta sabida gujewar masu haihuwar cikin shege kuma su yadda shi,jinjina kai yay cikin gamsuwa da maganar Dr yace "ok amma sunana JABIR ba yallaɓai ba,zuwa yaushe zamu dawo muganta domin a gobe nakeson komawa birninmu" jin abinda Jabir yace ya sanya Dr yin murmushi yace "babu damuwa Jabir zuwa dare saika dawo ko?"da haka sukai sallama kai tsaye suka nufi Golden tulip hotel ɗin da suka sauka a cikinsa.


To abuba kamar wasa tun Alhaji Kabeer na ganin abun ƙarami harya shallake tunanin sa,duk inda zai bincika akan ɓatan Zulfan yayi amma babu labari,tun a hanyarsa ta zuwa wani gidan redio ya kira gidansu Zulfan ya shaida masu abinda yake faruwa,sai wajan magriba ya ƙarasa gidansa dake unguwar sango.
a babban parlour ya iske Mama wato mahaifiyar Zulfa da kuma Jawad ƙanwar Zulfa sai kuma Lamir yayan Zulfa daman su uku ne wajan Mahaifiyarsu,mahifinsu kuma ya daɗe da rasuwa.
cikin ɓacin rai Lamir ya kalli Alhaji Kabeer sannan yay tsaki tare da faɗin.
"Tabbas munyi kuskuren bawa ɗan kwararo auran tsatsanmu,amma wannan kuskuren na kine Mama da kuka nace a bawa Zulfa shi bayan koda wasa baku taɓa ganin danginsa ba, baku san waye shi ba, kawai kun ɗauki yarinya kun bashi,wama ya sani ko ɗan yan kan kaine,ko kuma masu kidnapping banda haka tayaya zai kalli ƙwayar idanunmu yace mana an rasa Zulfa kamar wata allura kai aƙwai wata a ƙasa.!!"
Lamir ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya haɗi da yiwa Alhaji Kabeer tsawa.
Mama da hanyar yanzu ta kasa cewa komai sai tasbihi take da salatin Annabi a cikin zuciyarta ta ɗago kai ta kalli Lamir tace.
"idan hankali ta gushe nutsuwa ce ke nemushi Lamir amma wannan abinda kake babu abinda zai sauya daga ƙudirar Ubangijin"
"Ohh! yanzu Mama kina nufin muyarda da maganarsa kenan ko?tayaya zai kawo mana zancen da bazai taɓa yiyuwa ba,tabbas wannan abun tuggu ne kawai,amma wallahi saika fito mana da Zulfa"
duk yadda Alhaji Kabeer yaso danne abinda ke ransa kasawa yay,tabbas yana da hakuri da kuma juriya da dukkan wani wulaƙancin da mutum zai nuna masa,amma a wannan karan ya kasa danne abinda ya keji yay,tabbas Lamir baiyi karya ba,shi kansa bai san wanene shi ba,ya wayi gari kawai ya gansa a wannan garin na ibadan,daga ina yake?wanene shi?mene Asalinsa?ina danginsa suke?duk babu abinda ya sani shi dai yasan yana rayuwa farin ciki ne kawai da iyalansa da burin ganin jininsa a duniya, amma wata rana yana tashi da kewa da kuma raɗaɗi a zuciyarsa, ƙwaƙwalwarsa nason tuna masa wani abu daya faru dashi a baya wanda bai san ko menene shi ba.
"Lamir yana da ƙyau kayimin kyakkyawan zato, wallahi ina son Zulfa fiye da kai da kake wannan maganar,ina son Zulfa fiye da yadda na keson nasan wanene ni,dan ALLAH kayi hakuri ka barni da abinda na keji a raina,ka barni da kuncin da kuma kewar farin cikina..."
"Kai malam nika isheni da wannan surutun na banza kawai kace ka tsaface mani ƙanwa ..." marin da yaji an sauke masa ne yasa yay saurin dafe fuskarsa tare da haɗiye sauran maganar da bata samu damar fitowa ba,cikin takaici ya kalli Mama yace "Mama akan wannan mutumin kika mareni? ƴar uwata yaje ya saida fa" cikin faɗa faɗa da kuma saurin maganar da take dashi ta fara magana "wallahi Lamir ka fita a idanuna tun kafin na bashi auren Zulfa na yarda da shi,tun kafin akai Zulfa gidansa nayi istihara akansa,na yarda da shi fiye da tunaninka har abada bazan taɓa yarda shine ya salwantarmin da ƴar ba,dan haka ba kinka ya kiyayi aibata mutum domin wata rana zakayi ladama"
baki ya buɗe da niyar yin magana babyn dake bayan Mameey ya fara kuka,cikin sauri ta sakkoshi daga bayanta ganin yana ƙoƙarin sanya yatsansa a baki yasa ta ɗauki dabino da zam zam ɗin data jiƙa masa ɗazo,a hankali ta sanya masa a ƙaramin bakinsa bisa mamakin ta sosai yasha,yana gamawa ta goge masa bakinsa tare da ɗora shi a kafaɗarta har sai da yay gyatsa,luf yay a ƙirjinta yana maida numfashi,Mama data zubawa babyn idanu tana hango zallar kamaninsa da Zulfanta tayi saurin goge hawayen idanunta tace "da wanne suna kayi masa huɗuba?" kansa a sunkuye dan baya so kuwa yasan kuka yake ya saki ajjiyar zuciya yace "MUHAMMAD JALAL" ma sha Allah Ubangijin ya rayasa bisa tafarkin addini,Mameey ce tace "Ameen"
shuru ne ya ziyarci parlour'n kowa da abinda yake saƙawa cikin ransa inda Lamir yake cike da kunci da baƙin cikin marin Mama tayi masa akan Alhaji Kabeer hakan yasa ya ƙara jin tsanarsa fiye da ko yaushe, Mama kam abubuwa da yawa ne sukai mata cunkoshe a zuciya domin rashin Zulfa a rayuwarta babban giɓine tana dannewa ne kawai sabida Lamir domin tasan halinsa,Jamal da tun ɗazo take kukan rashin yayarta ta tace "Mama yanzu shikenan mun rasa adda Zulfa?"shafa kanta Mama tayi tace "kiyi hakuri Auta muci gaba da addu'a Ubangiji ya kaita hannu na gari in sha Allah ba zata wulaƙanta ba"gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "in sha Allah"






Misalin 8 na dare Jabir da Joseph suka ƙarasu hospital ɗin direct office ɗin Dr suka nufa,sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ciki da murmushi Dr ya amsa sallamar tare da bashi waje ya zauna,bayan sun gaisa ne Jabir ya kalli Dr yace "yaya jikin nata?"shuru Dr yay kafin ya numfasa yace "aƙwai matsala wallahi"lumshe idanu Jabir yay kafin yaja numfashi yace "tame kenan?"cikin nutsuwa Dr ya zare farin glass ɗin dake manne a idanunsa numfashi ya sauke kafin ya samu damar faɗin "bayan halin da take ciki na haihuwa da kuma jinjigar da yasu kamata Allah bai yi ba,a fahimtar kda nayi mata ɗazo na fahimci aƙwai juyewar tunani a tare da ita,ma'ana dai ta samu taɓin ƙwaƙwalwa,babban tashin hankalin bata magana sannan kuma taƙi yadda kowa ya taɓa ta,da kayar akai mata wanka aka sauya mata kayan jikinta"wani gumi ne ya fara karyowa Jabir gaba ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, cikin Hausar sa da baya fita sosai yace "innalillahi ya subuhanallah meke nan hakan?" Joseph ne ya amshi zan can ta hanyar faɗin "yallaɓai kawai mu sallami Dr muyi tafiyarmu mene za muyi da mahaukaciya wacce bamu san a salinta ba"ɗan tsaki Jabir yaja cikin tashin hankalin da yake ciki yace "Dr mene matsalar daya haukata ta? jinjina kai Dr yay tare da faɗin "shine abinda har yanzu bamu gano ba,duk abinda muka bincika a jikinta yana nuna komai normal only God know what happen to her"


miƙewa Jabir yay kana yay waje abinsa ganin hakan yasa Joseph da Dr suka mara masa baya,kai tsaye room 12 ya nufa inda aka ƙwantar da ita,a sanyaye ya ɗura hannunsa a saman handle ɗin ƙofar tare da ɗan turawa kaɗan tura kansa yay cikin ɗakin haka kawai ya samu kansa da faɗuwar gaba,runtsa idanunsa yay kana ya fara karatu addu'ar da yazo masa,a ƙwance ya sameta ta rufe idanunta gaba ɗaya tulin sumar dake ganta ya baje saman pillow'n da aka ɗura mata kanta "ka ganta ko? tun ɗazo a haka take ko tea taƙi sha" jinjina kai Jabir yay kana yace "tafiya zamuyi" jin haka yasa Joseph zaro idanu cikin halshan turanci yace "tayaya ne zamu shiga BIRNIN NUFAR da MUSULMA bayan kaima kasan ba zaman daɗi kake ba sabida musuluntar da kayi" wata harara Jabir ya watsawa Joseph hakan tasa yay shuru bai ƙara faɗin komai ba "Dr tashe ta"cikin dabara Dr ya fara bubbuga pillow'n da take kai a zabure ta miƙe zaune tare da ƙanƙame pillow'n a ƙirjinta haɗi da jijjigashi,gaba ɗaya zuba mata idanu sukai suna kallon ikon ALLAH,a hankali kuma ta tura hannunta cikin riga ta fara ƙoƙarin fito da Nonon ta da duk alamu a tunaninta wannan pillow'n kallon babynta take masa,ganin hakan yasa Jabir yay saurin faɗin "keee mene haka"duk da irin tsawar da yake mata amma ko a jikinta,ganin da gske fito da nonon take sonyi yasa yay saurin ƙarawa inda take zaune,yana zuwa yasa hannu ya fincikota zuwa gabansa hakan kuma yay dai-dai da fitowar...




free pages dai babu😝😝 yawa domin da wuri na keson mu fara shiga cikin labarin na ko dako ɗaya ba muyi ba 08119237616
_✨ UNCLE NE ✨_
















_✍🏼 NIMCYLUV_


*5-6*














Wani baƙin hayaƙi daga cikin bakinta zuwa sama,few minutes jikinta ya saki numfashi ta ya tsaya cak kamar ɗaukewar ruwan sama,numfashi Jabir yaja and he trying to control his self, tabbas abinda yake tunani ya zama gsky she lost her mine,numfashi yaja tare da ƙare mata kallo musamman yadda ta ƙwanta jikinsa,cikin ƙasa da murya yace "i most go with her definitely" ganin har yanzu haƙin yaƙi daina fita daga bakinta yasa ya kalli Dr yace "do something Please" dan bai san mene zaice mata haka kuma bai san ta ina zai fara ba,gaba ɗaya yaushe ya rabauta da shiga musulunci, ya ilahi help me,what should i do? jin Dr ya fara yi mata addu'a tare da Tofa mata a kunne yasa shima yay shuru yana sauraransa haka nan yaji karatun yay masa daɗi,sosai yay mata har aka samu hayaƙin ta tsaya nan da nan wani zufa ya fara feso mata a saman forehead nata,kallon Jabir Dr yay kana yace "sai dai a tafi da ita haka,dan indai idanunta biyu babu wanda ya isa ya fiddata daga cikin room ɗin nan bare hospital ɗin,jin jina kai Jabir yay alamar gamsuwa gaba ɗaya yay abinda ya dace na biyan kuɗi da kuma kuɗin nurse ɗin data kula da ita, and they give them her medicine,rasa yadda zaiyi ya ɗauketa zuwa mota yay hakan yasa ya kalli Joseph yace " take her into the car"sosai Joseph lamarin uban gidan nasa ke bashi mamaki ba tare da yace komai ba ya ƙarasa inda take ƙwance flat like corps,harya kai hannu zai ɗauke ta yaji ance "No!! stop" cikin nutsuwa Jabir ya ƙarasu inda take ƙwance kana ya naɗa hannu suit ɗinsa, bisimillah yay kana ya lumshe idanunsa sosai yay mamakin rashin nauyinta,cikin nutsuwa ya ƙarasa da ita zuwa compund na hospital ɗin tare da sanya ta a back side ya ƙwantar da ita, Joseph shima mazaunin drever ya zauna tare da yiwa motar key yana jin Jabir ya shiga, Jabir side ɗin mai zaiman banza ya zauna yana zama Joseph yaja motar da gudu suka nufi hotel ɗin da suka sauka a cikinsa,gaba ɗaya hankalinsa ya gama yin gida ga ɓangare na zuciyarsa yana fargabar shiga da Zulfa cikin birninsu,dawa zata zauna?wane zai yarda da ita? tayaya zata zauna a cikin mutumane irin na birninsu, Joseph ne ya tari numfashinsa yace "oga You need to think,amma aƙwai haɗari a zuwanta birnin NUFAR hatta shugaba ba zai yadda ba,kai zai iya kasheta fa akan dai ya zauna da mai saɓanin addininsa"jinjina kai Jabir yay yace "i knew,but he is my father dole nasan weakness nasa,dan haka you don't have to worry, a cikin wannan daren suka gama komai na tafiyarsu yadda gari na wayewa zasu ɗauki hanya, Zulfa kam hanyar yanzu bata san a duniyar da take ciki ba,duk irin a.c'n dake kaɗawa a ɗakin hakan bai yana jikinta zubar da wata zufa mai yawan gaske ba,fita sukai daga ɗakin suka kama na kusa dashi domin he never sleep with a women in the same room ba hakan tasa yabar mata ɗakin ba tare da sanin abinda zai iya faruwa cikin dare ba.


Bayan tafiyar su Mama Alhaji Kabeer miƙewa yay tare da nufar upstairs har yaje last tsep sai kuma ya dawo da baya zuwa inda Mameey ke zaune tare da Jalal,ba tare da yay magana ba yace "bani JALAL" kallonsa tayi tace "tayaya zaka iya kula dashi bayan kasa a koda yaushe zai iya neman a abinci?"ganin tana wasting time ɗinsa kawai ya sanya hannu ya amshi JALAL dake ƙwance cikin showel yana bacci,a haka ya nufi saman bene dashi yana zuwa ya nufi part ɗinsa dake farcing part ɗin Mameey, direct can bedroom ɗinsa ya shige yana zuwa ya ƙwantar da Jalal a saman bed ɗin kana shi kuma ya shige bathroom,taken shower yay tare da ɗaura al'wala domin sai lokacin ya tuna bai sallar isha'i ba,cikin saurin daya rage masa yay shirya cikin farar jallabiya tare da fesa parfume ɗin da yake fesawa yayin sallah,paryer mat ya shimfiɗa ya gabatar da salla sosai yay addu'a tare da roƙan Ubangijin Allah ya bai yana masa Zulfa cikin kwanciyar hankali da kuma ishasshiyar lafiya,lumshe idanunsa yay hakan ya bawa hawayen dake maƙale a cikinsu damar fitowa,abubuwa da yawa sun haɗe masa ba tare ɗaya san menene silar faruwarsu ba,tabbas a ace yasan wanene shi babu shakka da a yau zaije ga danginsa amma rashin sani ya zauna al'umma na jifansa da kalamar marasa daɗi da kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login