Showing 3001 words to 6000 words out of 8322 words
Chapter 2 - KOGON ANNOBA Complete Document By Mansur Usman Sufi.txt
mai zurfin gaske Lokacin da tsuntsun yaga ya kasa samun nasara akan sarki Siyamuk ansar ta hanyar kone shi da wutar bakinsa sai kawai ya dinga kai masa yakushi da zaqo zaqon paratan hannunsa da nufin yayi fata fata da sassan jikinsa. Faruwar hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya fara gano lagon tsuntsun domin yanzu takobinsa ya fara tasiri akan tsuntsun dan ayanzu takobinsa na samun nasarar yankar jikin tsuntsun duk inda takobin ya sara ajikin tsuntsun sai dai kaga ya dare jinina kwaranya. Abangaren boka zulwal kuwa yana iyakar kokarinsa wajen yakar tsuntsayen amma babu abinda ya daure masa kai sama da yadda karfin sihiri baya tasiri ajikin tsuntsayen face tsagwaron karfin damtse duk inda mai kallo ya duba ba abinda zai gani face gawarwakin dakaru fululu kwance cikin jini wasu a babbake suna kauri jini kuwa ya cakude da kasa babu kyan gani ana cikin wannan yaki ne wannan tsuntsu ya samu nasarar yankar sarki Siyamul ansar da faratansa a cinya take inda ya yanke shi ya haddasa wani qaton rauni jini ya kwaranya saboda zafi da zugin da sarki Siyamul ansar yaji bai san sa'adda ya sandara uban ihu ba ya saki takobin dake hannunsa cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle daga inda yake tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan wuyan tsuntsun ya sanya hannayensa biyu ya kama kan tsuntsun ya murde iyakar karfinsa nan take wuyan ya karye ji kake rukuss sarki Siyamul ansar ya daka tsalle karo na biyu ya sauka daga kan tsuntsun take tsuntsun ya fadi kasa yiff tamkar an jefar da giwa ko shurawa baiyi ba. Yayin da tsuntsayen sukaga abinda ya faru ga dan uwansu sai gaba dayansu suka tsaya cak da yakin kawai sai suka bude fuka fukansu suka luluka sararin samaniya suna masu daukar gawar dan uwansu da sarki Siyamul ansar ya kashe koda bacewar tsuntsayen sai akaga sarki Siyamul ansar ya sulale kasa sumamme cikin tsananin kaduwa boka Zulwal ya ruga inda yake ya umarci dakaru su dauko shi aka shigar dashi cikin gidan sarauta bisa wani kasaitaccen keken doki lokacin da masu magani suka dukufa akan sarki Siyamul ansar domin ceto rayuwarsa sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ba tareda anga yayi wani kwakkwaran motsi ba al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin masu maganin da boka Zulwal kenan kuma hankalinsu yayi mummunan tashi babu abinda yafi dugunzuma hankalinsu sai bisa ganin yanda raunin ciwon sarki Siyamul ansar din ke zubar da jini da ruwa mai doyin gaske kamar kurji yana zubar da mugunya duk kuwa da kasancewar masu maganin sunyi iyakar kokarinsu wajen bawa ciwon kariya da wadansu magunguna. A bangaren Nuzura kuwa lokacin da su yarima Nazmar suka farka daga baccinsu sukayi arba da mahaifiyarsu tana kaikomo acikin turakar hawaye na zuba daga idanunta sai suka rugo izuwa gareta suka fada kirjinta cikin matukar damuwa suka hada baki sukace ya ummanmu shin ina dalilin zubar da wannan hawayen naki koda jin wannan tambaya sai Nuzura ta kara kankame su ajikinta ta fashe da kuka a karo na biyu koda ganin hakan su Yarima Nazmar suka fashe da kukan sai da suka dauki tsawon lokaci suna cikin wannan hali sannan Nuzura ta janya jikinta daga nasu ta dube su cikin tsananin damuwa tace yaku 'ya'ya na kuyi sani cewa ba komai ne ya sanya ni zubar da hawaye ba sai bisa takaicin mugun halin da kuka jefa jama'ar wannan kasa da mahaifinku aciki kunsan cewa ba wannan ne karo na farko ba da hakan ya taba faruwa koda jin haka sai hawayen bakin ciki suka zubowa Nazmar da Hulaisa dukkaninsu suka budi baki sukace ki gafarce mu ya ummanmu tabbas mun aikata babban kuskure kuma munyi nadamar abinda muka aikata kafin su gama rufe bakinsu Nuzura ta tari numfashinsu tace wai shin ma in tambaye ku wane laifi kuka aikatawo wadannan tsuntsaye ina son ku sanar dani idan kuka boye mini gaskiya zan gudu in barku in tafi wata nahiya in cigaba da rayuwa har ajali ya riske ni. Yayin da su Yarima Nazmar sukaji abinda mahaifiyarsu tace sai idanunsu suka zazzaro suka shiga damuwa fiye da ko yaushe alamun rashin gaskiya karara ya baiyana a fuskarsu har Nazmar ya bude baki da nufin yace wani abu sai aka jiwo ihu da kururuwar sarki ta cika gaba daya gidan sarautar al amarin da ya sanya gidan sarautar ya hargtse da guje guje da iface ifacen jama'a Nuzura da su Yarima suka fice daga cikin turakar da sauri suka rugo izuwa turakar sarki cikin tsananin tashin hankali koda isowarsu izuwa turakar sai sukayi arba da sarki Siyamul ansar akwance cikin mawuyacin hali raunin cinyarsa na zubar da wannan ruwa mai doyin gaske koda shigowar su Yarima Nazmar sai kawai akaga sarki Siyamul ansar ya mike tsaye zumbur ya ruga inda suke ya rungumesu a kirjinsa al amarin da yayi matukar bawa masu magani mamaki kenan bisa ganin irin mugun raunin dake cinyarsa amma har ya iya taka kafarsa ba tare da an bawo masu maganin umarni ba suka fice daga turakar boka Zulwal yabi bayansu ya zamana saura su Yarima Nazmar da sarki Siyamul ansar kadai koda ficewarsu sai sarki Siyamul ansar ya kama hannun su Yarima Nazmar ya jasu har inda gadon sarautarsa yake ya zaunar dasu suka fuskanci juna sannan ya juya ya dubi uwargidansa Nuzura yana mai kura mata idanu yace ya abar kaunata bazakiyi farin ciki ba da 'ya'yanmu suka kasance cikin farin ciki da koshin lafiya. Koda jin wannan tambaya sai Nuzura taje ta zauna a bisa lumtsattsiyar kujera da take fuskantar su sarki Siyamul ansar ta dubesu cikin nutsuwa tace ya uban 'ya'yana kayi sani cewa ba komai ne ya sanya ni cikin halin rashin walwalaba sai bisa tsoro abinda su Yarima Nazmar suka janyo mana yanzu gashi sunyi sanadin yi maka mummunan rauni mutane da yawa sun rasa dukiyoyinsu da rayukansu ya zama wajibi ka tursasa su Yarima su sanar dakai laifin da suka aikatawa wadannan tsuntsaye sannan kuma a gano shin wanne irin tsuntsayene da matakin da ya kamata a dauka koda jin wadannan tambayoyi sai idanun sarki Siyamul ansar suka ciko da kwalla sannan ya budi baki cikin karfin hali yace tabbas maganarki gaskiyace ya uwargidana amma ki sani cewa matukar su Yarima na cikin koshin lafiya bana nadama don na rasa wata gaɓa ajikina har kullum tunanina shine wacce hanya zan bi domin ganin su yarima sun gajeni to amma idan su Yarima suka cigaba da janyo masifu a wannan birni hakan zai janyo rushewar birni gaba daya a doron kasa a kundin tarihin duniya Nuzura ce tayi wannan furuci ga sarki Siyamul ansar cikin tsananin damuwa shiru ne ya mamaye turakar na tsawon lokaci shigowar boka Zulwal itace ta kade shirun da ya wanzu a tsakaninsu boka Zulwal ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya dago da kansa cikin kakkausar murya yace ya shugabana kayi sani cewa bayan na fice daga wannan turaka na gudanar da bincike bisa halarar tsafi nan take na gano wani mummunar al amari cikin firgici sarki Siyamul ansar yace me ya faru ya dodon bokaye boka Zulwal ya hada fuska yace ya shugabana kayi sani cewa ba komai ne al amarin da nagani ba sai gameda wadannan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance mallakin wani hatsabibin boka da ake yiwa lakabi da suna JABARUL SIHIR bokayen duniya sunyi ittifakin a wannan karshen qarni babu wata halitta mai tsananin zafin nama gamida karfin damtse tamkar wadannan tsuntsaye babban burin boka Jabarul sihir shine ya tsafance wani sihirtaccen kwai wanda daya daga cikin tsuntsayen ta haifa wanda da zarar kwan ya kyankyashe kansa zaiyiwa duniyar juyin mulki da wannan tsuntsaye bincike ya kara tabbatar mini da cewa maganin da zai warkar da su Yarima Nazmar yana cikin gidan Jabarul sihir wato ma'ul diya'u lallai ya zama wajibi a tura Yarima Nazmar su maidawa tsuntsayen abinda suka dauko musu domin ina mai tabbatar maka da cewa tsuntsayen zasu dawo wannan birni namu nan da wadansu kwanaki kasani cewa babu wata halitta da zata tsira daga cikin jama'arka matukar suka dawo. Koda jin wannan jawabi daga bakin Zulwal sai hankalin sarki Siyamul ansar ya dugunzuma ainun ya tashi ya dubi boka Zulwal yace shin kanada tabbacin cewa zamu iya zuwa gidan boka Jabarul sihir har mu debo ruwan ma'ul diya'u? wadanda zai warkarda su Yarima su daina rashin jin da sukeyi? boka Zulwal yace akwai wani jarumi mai suna HUZAIFAL BN MASNUR ma abocin addinin musulunci lallai kashe gari ya kamata mu gudanar da tafiya domin mu ziyarce shi domin ya amince da bukatarmu da wannan nakeyi maka bankwana na barka lafiya ya shugabana koda boka Zulwal ya gama wannan jawabi sai ya shafi kasa da hannunsa na hagu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen take sarki Siyamul ansar da Nuzura suka cika da farin ciki mara misaltuwa.
****
BABI NA UKU
Kamar yanda boka Zulwal ya fada haka al amarin ya kasance wato tun da dukun dukun safiya sarki Siyamul ansar da su yarima Yarima Nazmar sukayi shiri bayan sun rabu da mahaifiyarsu suna masu zubar da hawayen rabuwa
da juna suka dauki hanyar tafiya tare da dakaru masu yi musu rakiya mutum dubu biyu tafiyar sa'a uku sukayi suka iso wani daji mai tattareda kayan ni'ima nau'i nau'i daban
daban koramai na gudana acikinsa atsakiyar dajin akwai wani dan madaidaicin gida shi dai wannan gida da zallan duwatsun wuta masu kwarin gaske da isowarsu bakin kofar gidan
sai sarki Siyamul ansar ya sauka daga kan dokinsa yaje ya kwankwasa kofar gidan wanda ta kasance mai tsananin tsawo da kaurin gaske saida ya kwankwasa sau uku
ba tare da yaji motsin alamun za a bude taba koda ganin haka sai su yarima da boka Zulwal suka sauko daga kan dawakansu suka
tako har izuwa kofar gidan suna masu yin cirko cirko domin suga an bude kofar tsawon dakika dari biyu shiru ba aji sautin bude kofar ba al amarin da yayi matukar dugunzuma
hankalin sarki Siyamul ansar ya dubi boka Zulwal yace ya sarkin bokaye shin yanzu me nene abinyi? har boka Zulwal ya budi
baki da nufin yace wani abu sai kawai aka hango wani kyakkyawan saurayi mai cikar kamala da annurin fuska ya tunkaro
kofar gidan kallo daya zakayiwa saurayin ka fahimci ya kasance gwarzon mayaki mai karfi na Allah ya isa saurayin yana sanye da
kayan fata riga da wando takalmin dake kafarsa anyi shine da patar damisa akafadarsa yana dauke da wata qatuwar zakanya.
Koda isowarsa inda su sarki Siyamul ansar ke tsaye sai ya bisu da kallo cike da mamaki ba tare da yace da dayansu uffan ba yasa hannu daya ya tura gofar gidan ta bude ya kunna
kai izuwa ciki yayin da sarki Siyamul ansar da tawagarsa sukayi arba da qatuwar zakanyar dake dauke akafadar saurayin kuma sukaga yadda ya bude kofar gidan da hannu
daya wanda sai karti majiya karfi mutum ashirin sun taru sannan zasu iya bude kofar sai suka cika da tsananin mamaki domin basu taba gani ko jin jarumin da yayi wannan jarumtaka ba suna nan atsaye a kofar gidan sai
sukaga saurayin ya fito daga cikin gidan ya tako da kafafunsa har izuwa inda suke ya dubesu cikin nutsuwa yace aminci ya
tabbata agareku yaku wadannan baki shin menene ke tafe daku izuwa gareni koda jin wannan tambaya sai sarki Siyamul ansar yayi
gyaran murya yace yakai jarumi Huzaifal bin masnur kayi sani cewa ba komai
ne ke tafe dani izuwa gareka ba face wata muhimmiyar bukata bukatar kuwa itace inaso kayi mana jagora izuwa
gidan boka Jabarul sihir domin nemowa wadannan 'ya'yan nawa maganin da zai warkadda su larurar dake damunsu ta rashin
jin magana kuma har su mayar da abinda suka daukowa wadansu tsuntsaye
wadansu tsutsaye inason ka fadi dukkan abinda kake bukata da ya danganci dukiya da mulki ni kuwa zan baka shi. Koda jin wannan
jawabi daga bakin sarki Siyamul ansar sai.jarumi huzaifal yayi shiru yana mai sunkui da kansa kas ya shiga dogon nazari daga
can sai ya dago kai ya dubi su Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa sannan ya dubi sarki Siyamul ansar yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa fiye da shekaru goma ubangijina ya baiyana mini cewa zakazo gareni da wata bukata
na amince zanyi maka wannan aiki amma sai dai bisa sharadi guda daya jal wanda sai ka 08137237071amince dashi zanyi wannan gagarumar tafiya
da jin haka sai sarki Siyamul ansar yace fadi sharadinka ya jarumin kwarai Huzaifal yayi gyaran murya a karo
na biyu sannan yace sharadina shine bayan na samu nasarar debo ruwan ma'ul diya'u wanda shine zai warkar da su
Yarima zaka yarda kayi imani da ubangiji kai da jama'arka baki daya idan ka daukar mini wannan alkawari
shikenan ka biyani dukkanin aikina ba tare da ka bani dinare da ko wani yanki na masarautarka ba koda jin wannan
batu sai sarki Siyamul ansar yayi shiru duk tattaunawar da akeyi tsakanin Jarumi Huzaifal da sarki Siyamul
ansar boka Zulwal da su Yarima Nazmar suna sauraro koda Boka Zulwal yaji sharadin da jarumi Huzaifal ya gindayawo
sarki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya tabbatar idan sarki Siyamul ansar yayi imani cewa zai karbi addinin
musulunci duk shirinsa zai tarwatse na son mallakar birnin SARIRUL AIWAN da ya dade yana muradi yana cikin wannan hali ne wani tunani ya fado masa tunanin kuwa shine
tunda sarki Siyamul ansar umarninsa yakebi bana jarumi Huzaifal ba lallai akwai tabbacin burinsa zai iya cika sa'adda yazo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki a ransa sarki
Siyamul ansar ya kada shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar bude baki yace yakai jarumi Huzaifal hakika na amince da wannan sharadin naka matukar 'ya'yana zasu
daidaita yanda nake bukata amma kuma wani hanzari ba guduba menene batu a gameda cewa su yarima sune zasu zamo ajalina da jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa jarumi Hullzaifal har fararan
hakoransa suka baiyana farare qal ya dubi sarki Siyamul ansar cikin annurin fuska yace kada ka damu ya shugabana kasani cewa matukar kana tare dani kuma kayi imani da ubangijin musulunci mahaliccin sammai
da kassai da abin dake cikinsu babu yanda za ayi 'ya'yanka su zamo ajalinka yanzu dai abinda za ayi shine ku biyoni izuwa
cikin gidana kudan shakata kafin abinda ya kamata ayi tunda na lura cewa kun gaji ainun kuma a tsarin addininmu ubangiji ya
umarce mu da mu girmama ma'abota mulki matukar basu hana mu bauta masa ba. Koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal ya juya ya shige gaba yana mai.kunna kai izuwa
cikin gidan yana mai yafito su sarki Siyamul ansar na hannunsa ba tare da bata lokaci ba sarki Siyamul ansar Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa boka Zulwal ne a karshe suka suka biyo
bayan Huzaifal yayi musu jagora har izuwa cikin gidan da shigarsu izuwa cikin gidan sai suka cika da tsananin mamaki abinda
ya basu mamaki shine yadda aka tsara gidan bisa tsari da kayatarwa gidan yana dauke da manyan dakuna guda uku masu girma da fadi suna da kofa ɗai ɗai da tagogi guda
biyu a wani daki ne dake kallon yamma cikin gidan jarumi Huzaifal ya sauki su sarki Siyamul ansar aciki dakin cike yake da kayatattun
kujeru kuma an shimfide kasansa da kilisai masu taushi wani daddadan kamshi ya mamaye turakar bayan jarumi Huzaifal ya sauke
su acikin turakar sai ya fice daga cikin dakin jim kadan sai gashi ya dawo dauke
da wani dogon paranti cike da nau'in kayan marmari da gasasshen naman zakanya
gamida tatacciyar madarar shanu ya ajiye agaban su sarki Siyamul ansar a bisa wani dan madaidaicin tebur na katako a tsakiyar turakar yana ajiye abincin ya dubesu yace ai sai ku
dan kimtsa cikinku ko yana gama fadin hakan ya fice daga dakin sarki Siyamul ansar da boka Zulwal suka bishi da kallo cike da matukar mamaki tayaya akayi har ya sarrafa
naman zakanyar da ya farauto acikin kankanin lokaci haka kuma a inama ya samu wannan tatacciyaro madarar shanun al halin babu wata dabba dake rayuwa acikin dajin saida suka kammala kimtsa cikinsu suka
huta sannan aka dunguma gaba daya suka fice daga gidan har jarumi Huzaifal suna ficewa ya mayarda kofar gidan ya rufe ta ruf kawai sai suka ga ya kusanci wani
bangare adajin mai tattare da sarkakiya sai gashi ya janyo wani ingarman doki fari sol mai kyawun launi bayan ya hau dokin ne
kowa ya hau abin hawarsa sai aka nausa cikin daji aka fara tafiya dakaru masu rakiya na biye dasu ana fara wannan tafiya ne
jarumi Huzaifal yaki yarda ya jera da kowa face Yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa yana mai satar kallonsu fuskarsa
cikeda annuri ana cikin hakan ne Yarima Nazmar ya dube shi yace yakai wannan jarumi a dazu da kuna magana da abbana
naji kace akwai wani ubangiji da kake bautawa wanda ya halicci sama da kasa bayan abin bautarmu. Koda jin
wannan tambaya sai Huzaifal yayi murmushi ya dubi Yarima Nazmar yace tabbas akwai ubangijin da ya halicci duniya da
abinda yake cikinta kuma yake aiwatar da duk abinda yaso da ace zaku gwada neman taimakon ubangijin nawa da kun
kasance jarumai kamar yanda har kullum kuke muradi sa'adda Yarima Nazmar yaji amsar wannan tambaya sai ya cika da mamaki yace wacce hanya zanbi in samu taimakon
ubangijinka Huzaifal yace ai abune mai sauki kawai duk sa'adda wani abu ta taso maka kace kana neman taimakon ubangijin gaskiya ubangijin da yayi rana da wata yayi mutum da aljan dabba da tsuntsaye ruwa da iska
ubangijin da babu wani ubangiji bayan shi a ranka ba tareda ka furta wani yaji ba lallai kai da yar uwarka inason ku boye mini wannan sirri dake tsakanin mu Yarima
Nazmar da yar uwarsa sukace ai kuwa babu wanda zaisan da wannan sirri har sai gaskiyar abinda kake gaya mana ya baiyana daga wannan kuma Huzaifal ya shiga basu daddadan labarai masu sanyaya nishadi da annashuwa
haka dai aka cigaba da wannan tafiya babu sassauci ana cikin tafiyar ne kwatsam ba zato