Showing 1 words to 3000 words out of 8322 words

Chapter 1 - KOGON ANNOBA Complete Document By Mansur Usman Sufi.txt

09 Dec 2024

1429

KOGON ANNOBA






















MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
Littafinyaki.com.ng
08137237071










©️ Haƙƙin Mallaka
Mansur Usman Sufi
Shekarar bugu:- 2024
Website:- littafinyaki.com.ng




GARGAƊI


Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu zuwa ga hukuma a kiyaye.
Ko kuwa zuwa ga babban mai sakamako Allah (SWT).


Sako daga
MANSUR USMAN SUFI






GODIYA


Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken KOGON ANNOBA.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama da iyalanshi tsarkaka.




SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya.




Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo Kano state Nigeria.
08137237071










BABI NA ƊAYA




Ƙananan yara ne mace da namiji kyawawa na gaban kwatance ke ta faman tsala matsanancin gudu babu sassauci, saboda matuƙar gudun da suke yi idan ka gani sai ka yi tsammanin za su fita daga duniyar ne.
kai duk sa'adda suka waiga bayan su idan suka yi arba da abin da yake biye da su, sai kaga sun ƙara ZAGE DAMTSE ƙarfin gudun su ya ƙaru ainun fiye da ɗazu.
Babu abin da zai bawa
mutum mamaki face idan ya ga yadda suke gudun sai ya rantse ya ce ba su kasance bil'adama ba, kallo daya zakayi masu ka fahimci cewa sun kasance 'ya'yan wani hamshaƙin attajiri ko BASARAKE, saboda tufafin da suke sanye da su masu tsadar gaske ne.
Haka dai suka cigaba da gudu domin tsira da rayukansu daga sharrin abubuwan da suka biyo su babu alamun tsoro ko firgici a tattare da fusakunsu, har suka iso wani ƙasaitaccen birni
ai kuwa sai suka kunna kai ta cikin wata yar mitsitsiyar taga ba tare sa sun jira masu gadin ƙofa sun buɗe masu ba.
Lokacin da abubuwan suka biyo yaran suka
sauka a birnin nanfa jama'a suka dinga guje-gujen gami da iface-iface kafin ka ce me gari ya kaure da ihun jama'a mutane suka dinga rugawa izuwa gidajensu suna ɗebo
makaman yaƙ.
A wannan lokacin sarkin dake mulki a birnin yana zaune akan karagarshi ta mulki fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatu nau'i daban-dabam dangin zinare da azurfa har da ma abin da ido bai taɓa gani ba. Duk inda ka duba a fadar kawunan jama'ane rututu tamkar dandazon kiyasai babu masaka tsinke.
A gefe guda kuwa sarki SIYAMUL-AMSAR na zaune akan ƙasaitaccen karagar mulki
yana sanye da doguwar alƙyabba akan shi yana ɗauke da KAMBUN MULKI da aka sana'anta shi da zallar zinare da lu'u lu'u.
Sarki SIYAMUL-AMSAR ya kasance dogon mutum mai ƙirar samudawan farko yana da kyakkyawar fuska da ɗan siririn gemu mai tsawon kamu biyu wanda shine ya ƙara tona asirin kyawun surarshi.
kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON JARUMI. 'Yan majalisar sarki na zaune a bisa shimfiɗu na alfarma waɗanda
idan mutum ya taka su saboda matuƙar taushin su sai ya ji tamkar ƙafafuwanshi za su nutse a ciki a wannan lokaci babu abinda kunne ke ji face guje-gujen jama'a da kuma shirun da ya wanzu a fadar tamkar mutuwa ta gifta, daga can ga dakaru masu tsaron ƙofa sun shigo fadar hankulansu a tashe.
Koda ganin halin da suke ciki sai sarki ya dube su ya ce ''shin me ke faruwa ne ?
Cikin rawar murya ɗaya daga cikin dakarun ya buɗi baki daƙyar ya ce ''ya shugabana muna cikin gudanar da ayyukanmu na tsaron ƙofa sai ga su yarima NAZMAR sun janyo mana wata gagarumar masifa, ban tsammanin cewa akwai wata halitta da ta tsira da rayuwarta, mu kanmu tsananin razana ya hana mu mu tantance wace irin masiba ce''.
Kafin badakaren ya gama rufe bakinshi sarki SIYAMUL-AMSAR ya zare sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi ya sare mashi wuya, nan take kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jiki jini ya yi tsartuwa ya kwaranya a ƙas.
kawai sai sarki SIYAMUL-AMSAR ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin, sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da saƙon mutuwa. Nan take ya yi umarni aka busa ƙahon yaƙi kafin wani lokaci MAYAƘA sun yi cincirindo a Ƙofar gidan sarauta. Shi kuwa sarki sai ya shiga izuwa gidan sarauta jim kaɗan sai gashi ya fito cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Jim kaɗan da faruwar hakan sai ga boka ZULWAL ya bayyana cikin alƙalumman sihiri, sanye yake cikin shigar yaƙi irin ta manyan hatsabibai.
Kawai sai ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa sarki
ya dube shi cikin matuƙar fushi
yana mai dakamashi tsawa ya ce ''shin kana ina ne masuba ta tunkaro birnina? Ina so ka gaggauta nemo mana mafita domin tserar da rayukan al'ummata".
Cikin ladabi boka zirwal ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa mafita ɗaya ce, shine mu fita mu tari wannan masuba tun kafin ta iso gare mu ina mai tabbatar maka da cewa zamu samu nasara''.
Gama faɗin hakan ke da wuya
sarki ya kaɗa linzamin dokinshi ya shige gaba boka Zirwal ya mara masai baya, take miliyoyin dakarun yaƙi suka yi koyi dashi




Babi na biyu




Sarki Siyamul-amsar ibn Fannas ya kasance mashahurin BASARAKE kuma GAWURTACCEN attajiri da babu tamkar a kaf nahiyar Baitul-Wahid.
Yana da matar aure guda ɗaya hal! Wata kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BINTU SHA'ARAN.
A rayuwar Siyamul-amsar babu wani rayuwar jin daɗi da ya nema ya rasa face rashin haihuwa, duk da irin tarin dukiya da ƙarfin mulki da yake da shi ya tashi a banza domin ba shi da wanda zai gaji karagarshi.
Aƙalla ya ziyarci manyan bokaye sama da ɗari akan wannan matsala ta rashin haihuwa amma abu ya ci tira, a wata shekara ne ya ziyarci wani boka a can birnin ƘUFA mai suna Zirwal.
Lokacin da sarki Siyamul-amsar ya bijirowa da boka zirwal da buƙatar shi ta samun haihuwa, sai kawai boka Zirwal ya bushe da dariyar mugunta har sai da ya faɗo ƙasa tim! Daga kan kujerar da yake zaune kuma idanunshi suka ciko da ƙwalla.
Al'amarin da ya ɗaurewa sarki Siyamul-amsar kai kenan kuma ya fusata shi ya dakawa masjid tsawa ya ce da shi ''shin ina dalilin wannan dariya taka? Cikin nutsuwa da biyayya boka Zirwal ya koma kan kujerarshi ya zauna ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana a karo na farko da shaƙaƙƙiyar muryarshi mai kama da kukan jaki yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya sarkin sarakunan masu isa kayi sani cewa ba komaine
ya sanya ni wannan dariya ba face bisa ganin yadda ka wahalar da kanka wajen faɗin bukatar da take tafe da kai, bayan cewa ka zo gaban uban bokaye, ya sarki mai cikakken iko ka yi sani cewa tabbas a halin yanzu matarka
na ɗauke da juna biyu nan bada daɗewa ba zata haihu, kuma ina mai farin cikin sanar da kai cewa 'ya'ya biyu zata haifa mace da namiji sai dai inda gizo ke saƙar shine 'ya'yan da za a haifa maka za su kasance hatsabibai marasa jin magana waɗanda sune zasu zamo ajalinka.
Yayin da boka Zirwal yazo nan a jawabin shi sai hankalin sarki siyamul-amsar ya dugunzuma fiye da kowane lokaci ya dubi boka Zirwall ya ce ''ya sarkin bokaye shin babu wata hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa ya zamto ba su kasance hatsabibaiba?
Zirwal ya nisa ya ce sannan ya ce ''ai bakin alƙalami ya bushe lallai wannan al'amari haka zai kasance''.
koda jn wannan batun sai sarki Siyamul-amsar ya sunkuiyar da kanshi ƙasa yana mai zurfafa cikin kogon tunani.
Abu na farko daya faɗo mashi a rai shine yanzu babu wata mafita face kayi murna da waɗannan yara da za a haifa maka domin sune zasu gaje ka bayan ranka tabbas ba ka da nadama koda sun zamo ajalinka ai da a ce wani ne zai gaji karagarka gwara a ce jininka ne. Can kuma wata zuciyar ta ce ka cigaba da bincike ya za ayi a ce 'ya'yan mutum sune zamto ajalinshi. Lokacin da sarki yazo nan a tunaninshi sai ya ɗago da kanshi ya dubi boka zirwal ya ce ''tabbas na amince 'ya'yana su zamo ajalina matuƙar za su gajeni bayan raina''.
Gama faɗin hakan keda wuya sai sarki ya ɗebi dukiya mai tarin yawa ya bawa boka Zirwal, saboda tsananin murna sai da Zirwal ya dinga birgima a ƙasa tamkar
wanda ya samu ciwon hauka, domin tunda yake a rayuwarshi bai taɓa samun dukiya mai yawan ta ba kuma dama yana da wani babban buri akan adukiyar yana son ya haɗa wansanadarin tsafi da ita.
Tun daga wannan rana
sarki Siyamul-amsar ya kasance cikin tsananin farin ciki kuma ya zamana cewa dare da rana baya rabuwa da uwargidanshu Nuzra yana bata gudunmowa wajen rainon juna biyunta har ta sauka lafiya
ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa mace da namiji aka raɗa msu suna NAZMAR da HULAISA.
Murna a wajen sarki kuwa ba a cewa komai domin a wannan rana ya dinga rabon dukiya da 'yanta bayi da barori sannan sai da aka yi kwanaki ashirin ana shirya walimar farin ciki, manyan sarakunan duniya sun sauka a birnin domin taya shi murna. Hakan ya sanya a lokaci ko ƙasa mutum ya kasa sai an siya saboda kawai ana farin ciki kuma
ya zamana sarki ba shi da wani abokin shawara face boka Zirlwal.
Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, sai gashi kwance tashi yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa sun shekara uku a duniya kasancewar yanayin jikinsu irin na mahaifinsu ne sai ya zamana idan ka gan su lokacin da suka shekara uku sai ka ce sun shekara biyar da haihuwa.
Tun suna waɗannan shekaru suke nuna hatsabibancinsu domin basa iya zama waje guda ko an kulle su a daki sai sunyi dabaru sun fita, a wasu lokutan idan suka rasa hanyar da za su bi su fice daga gidan sarautar sai su haɗa rigima tsakanin dakarun dake tsaron su sannan su sulale su fice daga gidan sarautar,
Domin akwai wani lokaci da suka je
suka tsokano wata qatuwar damisa ta biyosu har cikin gari ta dinga hallaka mutane sai dakyar da sidin goshi aka samu akayi maganin damisar kai in takaice maka
kafin Nazmar da Hulaisa su shekara shida sun janyowa birnin masifu guda talatin
kuma duk
lokacin da hakan ya faru sai an samu salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma
wani abu da zai baka mamaki shine tunda aka haifi su yarima Nazmar
arzikin kasar ya kara bunkasa amma sai dai mutane basu da kwanciyar hankali domin har kullum gani sukeyi su Yarima nazmar zasu janyo masifar
da zata zamo ajalinsu ko asarar dukyarsu duk irin dakarun da sarki Siyamul ansar zai sanya domin tsaron su Yarima amma
cikin hikima da basira sai Yarima nazmar sun samu nasarar gudowa shi kasansa sarki duk lokacin da ya tuna cewa su
Yarima nazmar ne ajalinsa sai takaici ya turnuke shi har ya zubar da hawaye duk cikin mutanen birnin walau yan majalisa
babu wanda ya iya kawowa sarki korafi su Yarima nazmar saboda ganin irin soyayyar da akeyi musu kuma babu wanda yake kaunar su domin ta sanadin su attajirai sun zamo talakawa wadansu sun zamo marayu.
Duk lokacin da sarki ya samu labarin su Yarima nazman sun janyo wata masifa sai ya kara sanya matakan tsaro aturakarsa domin hanasu fita daga gidan sarautar.
Lokacin da sarki Siyamul ansar da dakarun yakin suka fita daga kofar gari sai sukayi arba da wadansu irin jibga jibgan tsuntsaye
sude wadannan tsuntsaye sun kasance suna da jiki irin na zaki amma kawunansu sun kasance na rakumin dawa suna dauke da kafafuwa guda shida akalla girman
kowannensu yakai na qatuwar giwa fuka fukansu manya manya ne masu dauke da wadansu irin gashi mai kama da takobi
awajen kaifi da tsini hakika ba karamin jarumi bane zaiyi arba wadannan tsutsaye face sai ya razana ainun yayi nadamar wamzuwarsa agaban kasa koda tsuntsayen
su kimanin dubu sukayi arba da su sarki Siyamul ansar sai suka saki fukafukansu suka sauka aturba lokacin da dakarun sarki Siyamul ansar sukayi arba da wadannan tsuntsaye
sai suka razana ainun da yawa daga cikinsu basu san sa adda suka saki fitsari a wandonsu ba kuma suka yunkura zasu koma da baya sai sarki Siyamul ansar ya daka musu tsawa
suka tsaya cak jikinsu na tsuma gaminda karkarwa shi kansa sarki Siyamul ansar sai da yaji tsoro da razana sun darsu
a zuciyarsa domin a iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko jin labarin tsuntsaye masu tsananin girma da ban tsoro
kamarsu ba nanfa dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda tsananin dimauta
su Yarima Nazmar kuwa lokacin da wadannan tsuntsaye suka biyo suka shiga birnin suka wuce kai tsaye izuwa turakarsu suka fara sharar bacci abinsu kai kace
babu wani abu da ya faru agaresu al amarin da ya bawo kuyangi da barorin gidan sarautar mamaki kenan har wadansu
suka raya zuciyarsu cewa anya kuwa su Yarima nazmar mutanene ba aljanu ba?
ita kuwa mahaifiyarsu sai hankalinta ya dugunzuma ta kasa tsaye ta kasa zaune
kawai sai ta dinga kai komo cikin turakar hawaye na zuba daga idanunta.
Lokacin da aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Siyamul ansar da wadannan jibga jibgan tsuntsaye sai ya zamana babu wanda yayi yunkurin afkawo abokin gabarsa
awannan lokaci gaba daya mayakan dake wajen hankalinsu atashe yake shi kansa sarki Siyamul ansar hankalinsa atashe yake fiye da kowa yayi karfin hali ne na irin masu manyan sarakuna koda sarki Siyamul ansar yaga tsuntsayen sunki yunkurin afka musu sai ya umarci wasu dakaru dari biyar da su dana bakarsu su harbawa tsuntsayen take dakarun sukabi umarnin suka dana bakarsu suka harbawo tsuntsayen yayin da kibiyoyi guda dari biyar suka sauka akan tsuntsayen sai akaga tsuntsayen sun tsaya cak ko gezau basuyi ba hasalima idan kibiyoyin suka sauka akansu sai dai tartsatsin wuta ya tashi kibiyoyin su zube kasa saida dakarun suka karar da kibiyoyinsu sannan tsuntsayen sukayi wani irin kuka mai firgita manyan jaruman duniya suka afka musu da yaki take tsuntsayen suka yanyame miliyoyin dakarun kamar yanda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro duk inda ka duba sune birjik babu abinda suke face hurowa dakarun wata dunkulalliyar wuta abakinsu ko su hallakasu da wadannan tsinin gashin dake fukafukansu masu tsananin kaifi da tsini. Cikin kankanin lokaci waje ya cikada ihun mazaje gamida karar karafkiya karafe gamida haniniyar dawakai mutuwar sadaukai ta cigaba da yawaita awajen nanfa aka kacame da azababben yayi tsakanin kowane bangare har yazama an shafe tsawon rabin sa'a su sarki Siyamul ansar basu samu nasarar kashe ko daya daga cikin tsuntsayen ba sai dai kaga tsuntsu ya wangame bakinsa ya hurawo badakare wuta sai dai kaga nan take badakare da dokinsa sun kama da wuta sassan jikin dakarun ya dinga shawagi a sararin samaniya kura ta turnuke kamar hadari ya gangamo akece da ruwan sama mala'ikan mutuwa ya wanzu yana shawagi asama dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu kai duk inda daya daga cikin tsuntsayen ya sanya gaba sai dai kaga dakaru suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agonar auduga sarki Siyamul ansar ya wanzu yana kare kansa yana saran tsuntsayen cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka. Yayin da yaga yanda dakarunsa ke hallaka sai takaici ya turnuke shi ya takarkare ya kwarara uban ehu ya dire daga kan dokinsa ya tari wani tsuntsu guda daya suka kacame da yaki idan tsuntsun ya wangame bakinsa ya huro masa wuta sai kaga sarki Siyamul ansar ya kaucewa harin cikin bakin zafin nama idan wutar ta zuba a kasa sai kaga wajen ya haddasa wani wawakeken rami

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login