Showing 57001 words to 60000 words out of 184930 words
Chapter 20 - SHU'UMIN NAMIJI Book Complete by Phatyma Sardauna.txt
ba, kasan can akwai mata ƴan harka, amma ni gaskia nan a takure nake!" Abid yakai ƙarshen zancennasa cike da ƙosawa.
Kyakkyawan murmushinsa yayi haɗe da maida kallonsa ga wani kyakkyawan ruwa dake gudana a gefensu,
"Inason zaman Instanbul sosai Abid, domin yanayin garin yanasawa inajin shauƙin abar sha'awata!!"
"Bangane shauƙin abar sha'awan kaba? wai meke damunka ne? kusan tsawon watanni kenan dana fuskanci sauyawa a tattare dakai"
"Sha'awa nakeji Abid, matsanancin sha'awarta nakeji!"
Zaid yafaɗa cike da tsananin shauƙi.
"Sha'awa? wacece ita?" Abid ya tambaya cike da zaƙuwa, domin shikam yarasa wace irin macece Zaid ya kejin sha'awa'rta haka, ko da yaushe cikin maganarta yake, kuma ita kaɗai yakejin sha'awa.
"ZAHRAH NA!" Zaid yafaɗa cikin wata murya mai ɗauke da ma'anoni.
Dariya sosai Abid yasanya, hadda riƙe ciki, "Zahrah fa kace Zaid, wannan villager girl ɗin, koba sugar baby'nka ba?" Abid yatambaya yana ƙoƙarin gimtse dariyar da ta tasomai.
" Tana da matuƙar mahimmanci a wajena Abid, bantaɓajin irin abunda nakeji akanta ba, inason kasancewa da'ita a koda yaushe, inaso tazama ita ce mace guda ɗaya dazanna yin sex da'ita dare da rana, sha'awarta tamun mummunan kamu Abid, kasan yanda nakeji kuwa ?" Zaid ya tambayi Abid cikin sigar rashin wasa.
"Kokaɗan bansan ya kakejiba, amma kuma Zaid wannan ba sha'awa bane SO ne" Abid yafaɗi hakan da iya gaskiyarsa, domin shi abun da ya fahimta kenan.
Dariya sosai Zaid yashiga yi, haɗe da sanya hanunsa ya daki kafaɗan Abid.
"Shirmen banza, wai SO? menene SO Abid? kasan me kake faɗa kuwa, taya sha'awa zata zama SO, so fa kananufin wai inasonta ne, hahaha Abid ƙwaƙwalwarka ƙaramace, taya za'ayi nayi soyayya da'ita, sha'awace kawai kuma da zaran na sakeyin sex da'ita nasan komai zai wuce, tun farkoma danasan ban ƙoshi da'itaba, ai da banbari ta tafiba!!" yaƙare maganar yana mai ɗaga kofin giyarsa yakai baki.
Murmushi kawai Abid yayi, domin yafi kowa sanin cewa Zaid bayason gaskia, amma tabbas shikam anasa hasashen zuciyar abokinsa takamu da so, yana kuma da tabbacin idan har Zaid zaiyi sex da Zahrah sau ɗari, to wannan sha'awar bazata taɓa barinsa ba, saboda dama ba sha'awar bace So ne.
"Shikenan naji ba soyayya bane, sha'awa ce, amma kasan dai yanzu bazaka taɓa samunta ba ko, wataƙilama ta mutu, domin ina da tabbacin cewa baka shigeta da wasa ba"
"Dole zan sameta ne Abid, dole sai ta dawo gareni, kuma dole ta ƙara yarda da ƙudurina a karo na biyu, aure baya ɗaya daga cikin tsarina, amma idan taƙi yarda dani, saina aureta!"
Saurin kallon Zaid Abid yayi jin abun da yake fitowa daga bakin Zaid ɗin, "Aure kuma Zaid? Abid yafaɗa cike da mamaki.
"Ƙwarai zan'iya aurenta Abid, ƴan matan tana burgeni fiye da zatonka, inason komai nata, tana da kyau na fili dana baɗini, ni nasan mai naji a cikinta Abid, bakuma zanso nasake rasata ba, sha'awarta yasa koda yaushe cikin tunaninta nake, na kuma gama yanke hukunci, nan da sati ɗaya zankoma Nigeria, badon kowa ba sai don ita, nayi missing tattausan laɓɓanta masu zaƙi kamar zuma!!" Zaid yakai ƙarshen zancennasa yana mai lumshe idanunsa, da suka soma zama ja lokaci ɗaya.
Hangame baki Abid yayi yana kallon Zaid, "Anya kuwa ba aljana Zaid ya haɗu da'ita ba?" yatambayi kansa, tabbas baitaɓa ganin Zaid acikin hali makamancin wannan ba, gaba ɗaya Zaid ya sauya, yarage yawan yin sex da mata, a cewarsa wai bayajin daɗinsu, sannan kuma koda yaushe cikin tunani yake, to idan ba so ba meke da munsa ? Abid yakuma tambayar kansa.
A hankali Zaid ya buɗe idanunsa, haɗe da miƙewa tsaye kwalbar giyansa dakuma kofi ya ɗauka a hanunsa kai tsaye yanufi wani babban bene inda anan masauƙinsu yake, da kallo kawai Abid yabisa har ya ɓacewa ganinsa..
Yana shiga cikin ɗaki ya ɗaga kwalbar giyarsa ya kafa a bakinsa, saida ya shanye giyan tas kafun yayi wurgi da kwalba'r, kaitsaye ya nufi inda ma'ajin zane zanen sa suke, Caboard papers ne dayawa acikin wajen kuma duka ɗauke suke da hoton zanen fuskar Zahrah a jiki, wani ma iya bakinta kawai ya zana, wani ko iya idanunta ya zana, yana yawan yin zanen ne idan matsanancin kewa da sha'awarta ya da mesa, ɗaukan caboard paper'n dake ɗauke da zanen bakinta yayi haɗe da mannawa akan nasa bakin, wani irin zubawa yaji tsikar jikinsa tayi, domin kuwa ji yayi tamkar itaɗince da gaske, zamewa yayi ya zauna a ƙasa daɓas, haɗe da warwatsa caboard paper's ɗin akan jikinsa.
"Inakewarki Sugar Baby'na ,nayi missing komai naki, duk da cewa nasan kina fushi dani namiki da zafi, amma kiyi haƙuri wannan karon bazan miki da zafi ba, a hankali zan bi da ke tayarda zakiji daɗi har brain ɗinki, zakuma za ki saba da ni a sannu, na miki alƙawari zandawo gareki!, kina sona?" yatambayi zanen fuskarta dake jikin wani ƙaton caboard paper, "Nasan har yanzu kina sona ko Zahrah na?" still dai wannan zane yakuma tambaya, murmushinsa mai kyau yakumayi, haɗe da sanya hanu yashafi gefen kumatunsa.
" Kiyi murmushi Zahrah na, nakusa zuwa gareki, a yanzu zan iya sadaukar da komai na zuwa gareki, amma fa banso kina yawan fushi, duk da cewa idan kina fushi kinfi kyau !"
Haka Zaid yayita sambatun sa har bacci ya ɗaukesa a wajen.
Kwance take akan ƙirjinsa, yayinda fuskarta ke ɗauƙe da murmushi, a hankali ya matso da fuskarsa daf da tata, cike da matsanancin sha'awa ya kamo lips ɗinta na ƙasa yashiga tsotsa a hankali, cike da ƙwarewa yake cusa harshensa cikin bakinta, cike da soyayya ta soma tsotsan harshensa tana mai lumshe idanunta, a hankali yayi ƙasa da hanunsa zuwa ƙirjinta, cikin salo yashiga shafa breast ɗinta, yanayin yanda suke sucking tongue ɗin junansu, shiyasanyasu suka fice a hayyacinsu lokaci guda, ƙasa yayi da kansa zuwa ƙirjinta, yana shirin ɗaura bakinsa a kan nipples ɗinta kenan, taɓace masa ɓat, dai dai lokacin yafarka a hargitse, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe, duk da cewa sanyin A.C na aiki a cikin ɗakin amma shi gumi yake haɗawa, da ƙyar ya'iya miƙewa ya shiga bathroom haɗe da sakarmawa kansa shower.
ba yau yafara wannan mafarkin ba, amma maiyasa Zahrah take gudunsa acikin mafarki, takan ɓacewa ganinsa a daidai lokacin da yake matsanancin buƙatar ta....
*5/December/2019
*Voted,Comment, and Share please..... Follow me on Whatsapp and Wattpad @fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymerhsardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*Chapter 48 to 49*
Yajima tsaye a gaban shower ruwa na dukansa, mafarkinsa na yau ne yatsaya masa a rai, duk da kuwa cewa ba wannan bane karo na farko, daya fara yin irin wannan mafarkin. Koda wasa baiyi niyar komawa America a yau ba, amma yanzu yaji ajikinsa cewa komawarsa can ɗin yafi masa, domin kuwa mararsa har ƙullewa take saboda sha'awa, gaba ɗaya kwana biyunnan da suka shuɗe baiyi sex ba. A gurguje ya shirya kansa, bayan yasanar da Abid cewa shima ya kimtsa zasu wuce America a yau. Suna zuwa airport basu wani daɗe ba, jirginsu yaɗaga zuwa sararin samaniya....
Nigeria
Washe garin ranan da Dr yazo da dare yafaɗi muradinsa..
Tun tashinta takejin ƙunci a zuciyarta, hakanan take jin ta tsani komai na duniyar, badon lecture'n da zasuyi yau mai amfani bane, to tabbas da bazata je makarantar bama.
Doctor Sadeeq ne tsaye a tsakiyar ɗakinsa, yayinda hannayensa duka biyu ke sanye cikin aljihun wandonsa, shima kallo ɗaya zaka masa kafahimci cewa yana cikin damuwa, kallon sa yamaida kan agogon bangon dake saƙale ajikin bangon ɗakin na sa, ƙarfe 7 da rabi na safe kenan, tabbas yasan yau ƙarfe takwas suke da lecture, yanaji a jikinsa cewa yayi mata laifi mai girma, sannan idanunsa suna matuƙar son ganinta, to amma a yanda yakeji bazai iya zuwa gareta ba, "idan ma naje nace mata me?" yatambayi kansa. " Nariga dana furta mata abun dake cikin zuciyata, dole zanbata lokaci domin samun dawowar nutsuwar ta" yafaɗi hakan a bayyane, wayarsa ya ɗauka haɗe da kutsawa cikin dialing call ɗinsa, numbern drivernsa yashiga ƙira kai tsaye, ƙara biyu wayar tayi, drivern yaɗauki ƙiran, kasancewar driver'n yasan gidan su Zahrah, yasan ya kai tsaye, bai tsaya yi masa wani kwatance ba, yace masa yaje ya ɗauketa ya kaita makaranta, da "to" kawai driver'n ya amsa masa, katse ƙiran yayi haɗe da cilla wayar tasa zuwa kan gado,
"Yasan balallai ta yarda tabi driver'n ba, domin yanayinta da yagani jiya, kaɗai ya isa ya tabbatar masa da hakan, amma burinsa ne ya bata ingantacciyar kulawa, shiyasa baiyi ƙasa a guiwaba wajen sa driver'n nasa kaita makarnta, saboda baiso ta hau wani abun hawa bayan nasa....
Ko kwalli, yau bata shafa ba, balle kuma uwa uba fawder, zumbuleliyar doguwar riga ta sanya, haɗe da ɗaura ƙaton hijab akai, kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa tana cikin damuwa da ƙunci.
Koda tayi mawa su Baffa sallama, suma sun fahimci cewa yanayinta ya sauya, amma sai suka share babu wanda ya tambayeta.
Tana kai ƙofar gida zuciyarta tayi wani irin bugawa, sakamako'n ganin motar Dr Sadeeq, da tayi fake a ƙofar gidan nasu, tsayawa tayi cak ganin cewa driver'n sane yafito daga cikin motar, saɓanin shikansa Dr ɗin.
Cike da girmamawa Mudi driver ya ƙaraso inda Zahrah ke tsaye.
" Ranki shi daɗe barka da safiya! dama yallaɓoi ne yace nazo na kaiki makaranta, shi ba zai samu daman zuwa ba, wani aiki ne ya riƙesa, kawo jakar na karɓamiki" Mudi driver ya ƙare zance'n nasa yana mai ƙoƙarin karɓan jakar dake riƙe a hanunta. Saurin ja da baya tayi haɗe da fusge jakarta, cike da ɓacin rai tace.
"Kakoma kace masa bana buƙatar kulawarsa koda kaɗanne, ka kuma ce masa injini yafita a rayuwata, saboda bana buƙatarsa!" tanakai ƙarshen zancennata tasakai tayi tafiyarta.
Da kallo kawai Mudi driver yabita. "Uh ni naga bala'i, daga taimako kawai, to Allah ya kyauta" Mudi yafaɗa yana mai komawa cikin motar, key yayimawa motar haɗe da nausata kan hanya, tabbas zai koma ya shaidawa uban gidansa, duk abun da tace a faɗamai..
Cikin ikon Allah tana isowa bakin titi tasamu mai taxi, bawani ɓata lokaci tashiga yaja sukayi gaba, bayan ta sanar masa inda zai kaita.
Tun shigowarta cikin ajin, Husnah ta lura da mugun sauyawan da fuskar Zahrah'n tayi, domin kuwa kowa ya kalli idanunta, zai fahimci cewa tayi kuka har ta ƙoshi. kasancewar Zahrah'n na shigowa malami yashigo, yasanya Husnah bata samu damar tambayarta komai ga me da sauyawarta ta ba.
Koda aka fito daga lecture, kan dakalin da suka sama zama, yauma sukai mawa kansu masauƙi.
"Wai meke damunki ne Zahrah? gaba ɗaya kinsauya, bayan jiya ba haka muka rabu dake ba, sannan kuma na kula cewa, yau ba Dr bane ya kawoki, maike faruwa?" Husnah ta tambaya cike da kulawa, ga ƙawarta ta.
"Inacikin matsala Husnah! a she a yanzu babu wani, wanda zai taimakeka don Allah sai don biyar buƙatar kansa? na ɗauki yarda ta na basa, na ɗaukesa tamkar ɗan'uwa, na'aminta dashi, nayi saurin yadda haɗi da sakewa dashi, bantaɓa zaton haka zata faru ba, ashe shi abun dake cikin zuciya da ruhinsa daban ne, wani abune saɓanin tunani na!" Zahrah tafaɗa tana mai share ƙwallan daya gangaro daga cikin idanunta.
"Banganeba, kinsani a duhu, maikuma ya sake faruwa? ki faɗamin !" Husnah tafaɗi hakan cike da zaƙuwa, don ta ƙosa taji menene matsalar ƙawarta ta.
"Kinsan abun da yafaru dani Husnah, Zaid yaci mutumci na, ya ƙwaci budurcina da ƙarfin tsiya, ya halaka min rayuwa, shin kinaga akwai wani namiji dazai soni tsakani da Allah, bayan yasan abun da yafaru dani?" Zahrah ta tambayi Husnah.
"Haryanzu banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zaifi kyau ace kiwarwaremin komai!" Husnah tafaɗi hakan cikin rashin fahimta.
"Ba gaskiya bane Husnah, bai faɗawa kansa da zuciyarsa gaskiya ba, baizamanto gaskiya ba, soyayyar da yakemin ba gaskiya bace, Husnah bazan yaudari kaina ba, domin nasan babu tayanda za'ayi cikekken namiji mai aji da lafiya kamar Doctor Sadeeq, yace wai ni yake so ya aura! ina kokonto akan al'amarin !" gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska, lokacin da takai ƙarshen zance'n nata.
Nannauyar ajiyar zuciya Husnah ta sauƙe, domin kuwa sai yanzu ta fahimci inda matsalar ƙawartata take, dakuma abun da ke damunta.
"Doctor da kansa yace zai aure ki Zahrah?" Husnah ta tambaya, bayan ta aza hannayenta duka akan kafaɗun Zahrah.
Kai kawai Zahrah ta'iya gyaɗawa, alamar "eh''
"Ba wasa bane Zahrah kamar yanda kika ɗauka, haka kuma ba yaudara bane kamar yanda kike tunani, har yanzu keɗin mai kyauce, kuma haryanzu keɗin haɗaɗɗiyar mace ce abar so ga kowani irin namiji, ba'akanki a ka faraba, baikuma dace ki ɗau hukunci mai tsanani gawanda baiji ba bai gani ba, kina tunanin Doctor Sadeeq yaudaranki zaiyi ?" Husnah ta tambaya.
"Ƙwarai kuwa Husnah, ke kanki kinsani, namiji kamar Dr ba sa'an aurena bane, ko lokacin danake ɗauke da mutumcina yafi ƙarfina, balle yanzu danake fanko, inaso kisani wannan karanbani'n shi na tafka a karon farko, yazo yazamemin babbar matsala, domin kuwa nayaudari kaina, na sawa zuciyata soyayyar wanda har gaban abada yafi ƙarfina, yakuma yi mini rata, na yaudari kaina danaƙi amfani da tunanin cewa Zaid yafi ƙarfina, bazan taɓa yarda nasake aikata haukan dana aikata a baya ba Husnah!" Zahrah tafaɗa cike da raunin murya dana zuciya.
"So baitaɓa zama haukaba Zahrah, kada kicemin kin wulaƙanta Doctor saboda abun da Zaid yayi miki, kada ki yarda da tunaninki nacewa gaba ɗaya maza mayaudara ne, kowa da irin halinsa, kuma masu irin halin Zaid basa ɓoyuwa a kamanni da halaye, soyayyarsa ce kawai tarufe miki ido, har ki ka kasa hango mummunar manufarsa a kanki, yana da kyau ki nutsu kiyi tunani, inada tabbacin cewa Dr Sadeeq, ba zai taɓa cutar da rayuwarki ba, kema kuma yakamata kisan hakan, kada tunaninki ya gushe ki kasa tantance fari da baƙi, wlh ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq ba mutumin banza bane, bakuma zan ɓoyemiki ba, tabbas idan kika tsaya wasa da damarki, to zata miki mummunan suɓucewa, haƙiƙa Dr Sadeeq haɗaɗɗen gaye ne, wanda ko wacce mace zatayi fatan samunsa a matsayin mijin aurenta, nasan idan nace miki kiyi soyayya yanzu na haɗaki da babban aiki, amma zai kyautu ace ki koyawa zuciyarki soyayyar Dr Sadeeq, shawara nake baki Zahrah, idan kuma har kikayi amfani dashi, bazaki taɓa danasani ba, dan Allah ƙawata kiyi tunani mai kyu!" Husnah tafaɗi hakan cikin son ƙarfafawa Zahrah guiwa.
Hawayen dake zuba daga cikin idanunta ta sanya hanu ta share.
"Bazan iya ba Husnah, bazan iya taɓa sake son wani ba a cikin rayuwata, kada ki ga laifina, nasan Dr Sadeeq yafi ƙarfina, yana da asali, yana da ƴan uwa, yanada gata, yana da kuɗi, yanakuma da ƴancin da zai zaɓi matar aure wacce ransa keso, nikuma fa? idan kikayi dubi da tushena, to ban cancanta da zama inuwa ɗaya da shi ba, nifa yanzu banda wani ƴancin da zan iya zaɓin mijin aure da kaina, sbd akwai nakasa acikin rayuwata, dole sai mai tawakalli ne zai iya aure na, to maiyasa zansanya kaina a cikin wahala? balallai farincikin da Dr Sadeeq ke ƙoƙarin bani yakasance dauwamemmeba, nafaɗamasa yafita a rayuwata Husnah, a yanzu bana buƙatar kowani namiji, zaifi kyautuwa a gareni nayi rayuwata ni kaɗai, nayarda da ƙaddarata, amma kuma yazama dole na kiyaye sake jefa kaina a haɗarin soyayya!"
Rungume Zahrah,
Husnah tayi ajikinta, sosai tausayin ƙawarta ta ya kamata, haƙiƙa Zaid yacutar da rayuwar Zahrah, ya rabata da duk wani sukuni nata, amma a kwai Allah.
"Haƙiƙa dole zakiji ciwo Zahrah, amma yana da kyau ki zurfafa tunani, ni ina da tabbacin cewa Dr Sadeeq auren ki yakeso yayi bada wasa ba, amma abun da kikayi masa baki kyauta ba, ki basa haƙuri, koda kuwa bazaki auresa ba, yayi babban ƙoƙari acikin rayuwarki, kiyi nazari, amma kuka ba naki bane, kuma yana da kyau rama halacci da alkhairi !"
Gaba ɗaya Zahrah jitayi jikinta yayi laƙwas, take marin da ta shararawa Dr Sadeeq akan fuskarsa ya dawo mata, wani irin faɗuwar gaba taji, ko kaɗan batayi tunanin zata iya kai hanunta jikinsa da sunan duka ba, amma a daren jiya ɓacin rai yasanya idanunta rufewa, harta iya ta mare sa batare da tayi tunanin komai ba, tabbas komai yayi mata bai cancanci mari daga gareta ba.
Gaba ɗaya kasa sakewa a cikin makarantar Zahrah tayi a wannan ranan, dole ta tattara yanata yanata ta dawo gida.
Zaune take jigum akan tabarma yayinda hannuwanta ke dafe da ƙuncinta, idan da za'a ce za'a kasheta idan bata faɗi, tunanin me take ba, to tabbas da sai dai a kashetan, amma ita kanta batasan tunanin mai take ba.
Inna da fitowarta kenan daga bayi, hanunta riƙe da buta, kama ƙugu tayi, haɗe da maida kallon ta zuwaga inda Zahrah ke zaune tayi jigum.
"Wai lafiyanki kuwa Zahrah? meke damunki ne? tun safe haka kike sukuku, yanzu kuma kinyi tagumi tamkar wacce akamawa mutuwa, kodai halinki na da, kike son dawowa dashi ne? to wallahi bazan ɗau wannan iskancin ba, tun wuri ma kisani!" Inna taƙare maganar cikin faɗa faɗa.
"Ko ɗaya bahaka bane Inna, narasa taya zan ɓullowa matsala ta ne!" Zahrah tafaɗa cike da sanyin murya.
"Matsala! wace irin matsala kuma?" Inna ta tambaya cike da son jin gulma.
"Inna wai Likita ne yace zai aure ni !" Zahrah tafaɗi hakan cikin sarƙewar murya.
"Likita yace zai aure ki!" Inna ta maimaita maganan cikin ƙaraji haɗe da sanya duka hannayenta biyu ta dafe ƙirjinta.
Kai kawai Zahrah ta'iya gyaɗa mata domin zuwa lokacin