Showing 30001 words to 33000 words out of 34154 words

Chapter 11 - Zubar Hawaye Part 1 Complete Hausa Novels by Billy Galadanci .txt

05 Dec 2024

2184

Maman Hanan: *********


Dakyar aka samu Ahmad ya farfad'o, yana bud'e idanun sa, ya sauke su akan Mahaifiyar sa, ya bud'e bakin sa dakyar da alamar ciwon kansa yafara tashi yace"Umma dagaske ba'aga Aysher ba, Umma suwaye zawu aika ta wannan mugun abun gareni, menayi musu ko kuma meye Aysher tayi musu?, na rantse da Allah zan iya rasa rayuwata, Umma zaku iya rasani daga yau zuwa ko wane lokaci muddin ba'a ganta ba, zan mutu Umma.




Ku kiramin Mudansir abokina nagari, zaije ya bincikamin inda matata take yau basai an kwana ba, kuka Ahmad yakeyi sosai duk wanda yake d'akin saida ya tausaya ma Ahmad, hawaye suke sharewa suma, dangin Aysher kana kallon su kasan suna tsananin tashin hankali......




Bakinsa Umma tarufe da sauri cikin k'arfin hali tace" kadaina fad'in haka Ahmad, kana k'ara tayar mana da hankali, zaka rayu da Aysher in Allah ya yadda dan kuwa tun da aka kawo ka suka fice dubo Aysher kuma muna saka rai za'aganta bi'izinillah, kayi addu'a Ahmad muma hankalin mu a tashe yake, likita ne yashigo yayima Ahmad alluran bacci wanda hakan ya sa bacci mai nauyi ya d'auke shi.




Umma suna zaune jugum-jugum kowa ya rafka tagumi, wajen k'arfe d'aya da rabi na dare Alh.Aliyu ya shigo d'akin da aka kwantar da Ahmad, Mudansir tare da wasu abokan Ahmad din suna binshi a baya, kowa ka kalli fuskar shi cikin su ba k'aramin tashin hankali suke ciki ba.


Umma ta mike da saura ta tari Alh.Aliyu da fad'in "Ya ake ciki kuwa Alh. Anganta kuwa?", kai Alh.Aliyu ya girgiza kafin yace" Ba'a ganta ba sai dai mu barma gobe idan Allah yakaimu amman kafin mu dawo asibitin nan, naje munyi report ma 'yan sanda muna saka rai za'a ganta in sha Allah, ya jikin Ahmad d'in ya farka kuwa?, Umma tace"ya farka....nan ta labarta ma Alh.Aliyu duk abinda yafaru bayan farfad'owar Ahmad".




Dariya Alh.Aliyu yayi (wanda kana ganin shi, kasan na dole ne) kafin yace"Ahmad d'an rigima na kenan, Allah ya kyauta ya kuma sa mudace, kuzo mu tafi, Mudansir zai kwana da shi mun gama magana, jikin kowa a sanyaye suka fice daga d'akin mudansir ya bisu dan yi musu rakiya.


🍒🍒🍒🍒🍒






Aysher tana cikin wannan hali batare da tasan tsawon lokacin data d'auka a haka ba, aka bud'e k'ofar aka shigo, cikin k'arfin hali Aysher ta bud'e idon ta kalli yarinyar (wannan dai budurwan ce data yaudari Aysher).




Cikin k'arfin hali Aysher ta mik'e ta kalli budurwan tana cewa" Baiwar Allah ki taimaka ki sanar dani abinda nayi muku, kuka yanke wannan hukuncin a gareni, kuma su waye ku? dan Allah ki sanar dani.


Yanzu kuwa zakisan ko ni wace ce "kamar yadda kika ganni ni sunana Ladidi REZA, bani da aikin yi sai dai asani aiki abiyani kamar yadda aka bani kwangilar satoki, wanda kika gani da safe sunan ta Feedo kuma ita budurwan mijin ki, sunyi alk'awarin aure yazo ya yaudareta sai samun labarin auren ku tayi ana sanarwa a kafafen yad'a labarai, dan haka bazaki koma ba sai anyi auren Uwar d'akina da mijin ki.................








MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/30, 12:37 PM] Zeetty: [10/30, 12:01 PM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*




Page 61-62




Iya wahala Aysher ta sha, a gurin su Ladi Reza da abokiyar aikin ta Ummi 'yar tsinke.


Bawani ishashiyar abinci mai kyau, kullum da safe alala ce dai da mai da yaji.


Ranar da Aysher tacika kwana uku a gidan, a wannan ranar Ladi tashigo ranta a 6ace tana fad'in"Ni feedo zata gwadama iskan ci da rashin cika alk'awari, toh billahil lazi zata ga abinda zai biyo baya, sai na tona mata asiri, sai tasan ta ta6o Ladi Reza, ke taso mu tafi (tafad'i haka tare da jawo hannun Aysher)."


"Ina zamu tafi? Kuyi hak'uri karku sake cutar dani, dan Allah ni wallahi na bar mata Ahmad indai dan akanshi ta kawoni gurin nan, ku mayar dani yola garinmu."


"Yimin shiru, ki wuce mu tafi police station zamu je mukai kan mu, dan idan ba haka nayima Feedo ba, baza tasan cewar nafita tantiranci ba, zan tona asiri uban kowa ma ya mutu dan ubansa."


Dakyar Aysher ta mik'e, Ladi Reza ta kamo hanun ta suka fice, tasaka Aysher a mota, dakan ta taja motar suka bar k'ofar gidan da sauri.
Tunda aka kai Aysher sai yau ta fito k'ofar gida, sai yau taga haske a idanun ta, dan haka dak'yar take bud'e idanuwan ta.






Fagge Division Aysher taga an rubuta, guri Ladi Reza ta samu ta faka motar ta, ta zagayo ta bud'ema Aysher, tare da kamo hanun ta, kai tsaye cikin police station d'in suka shiga.


Ladi ce tafara magana da d'an sandan da tagani a tace masa"Yallabai gani nakawo kaina, na kasance mai laifin sace wannan yarinyar........ Yi shiru ('Dan sandan ya katseta daga maganar ta)."


"Bari a fara rubuta statement d'in naki," biro ya d'auko daga aljihun rigar sa, tare da jawo wani babban littafi kafin yace"ina jinki meke faruwa"




Nan Ladi Reza ta fara bashi labarin yadda akayi da cewar" Wata rana Feedo ta sameni a Club tacemin zata bani wani kwangila ni da k'awata Ummi 'yar tsinke, tayi mana alkawarin kud'i mai tsoka amman da sharad'in zata fara bamu rabi, rabi kuma sai bayan mun kammala aiki, toh mukuma jin yawan kud'in yasa muka amsa mata, kwangilar kuwa shine wannan yarinyar za'a sato mata ranar da akeyin dinner ta, Feedo itace ta samo min hatta kayan da zanyi amfani dashi, wanda shine ankon gurin dinner, ni da k'awata 'Yar tsinke muka kammala had'a komai, na yadda za'ayi a d'auko amaryan dan Feedo ta bamu labarin saurayin ta ne ya yaudare ta bayan sunyi alkawarin aure, toh mun gama mata aikin komai hatta gidan da aka ajiye yarinyar nan (tafad'a tare da nuna Aysher) gidan mu ne, saida Feedo taga komai yayi dai-dai, yau kwanan yarinyar uku a hanun, amman Feedo tayi mirsisi tace bazata biya mu kud'in mu bai sai bayan ta shawo kan Ahmad sunyi aure, kaji rainin hankali Officer? Ni kuma akan kud'i zan iya komai Aradu, shine nakawo kaina, suma a nemosu, ga yarinya nakawo a sadata da danginta, ni ba bakuwar zuwa gidan yari bane (Ladi ta k'arasa fad'a tana taunar cingam d'in dake bakinta irin na gogaggun 'yan duniya)."






Shiru 'Dan sandan yayi, dan tabbas yanada labarin amaryan da aka saceta ranar Dinner, ya tabbata Aysher ce, dan haka tisa k'eyar Ladi Reza yayi zuwa bayan kanta, kafin yafara kiran wayar DPO.
[10/30, 12:37 PM] Zeetty: 🍒🍒🍒🍒🍒






Ahmad dai maraban shi da gawa numfashi ne kawai, saboda ko wane lokaci cikin zuga masa Alluran bacci nursing da doctor suke, dan yana farkawa zai fara tambayar anga Aysher kuwa? Idan daga nan Sai jiki ya rikice.


Dangin Aysher na yola duk sunzo hatta Yadikko tazo, zuciyar ta cike take fall da farin ciki, a zahiri kuma nuna wa take kamar tafi kowa bak'in ciki.


Kana kallon Baffa Usman kasan yana cikin damuwa, da labarin 6atar 'yar sa daya zo masa,




Suna zaune a asibiti cikin alhini da jimami, dan Ahmad ma yau ko farfad'owa baiyi ba ga damuwar rashin samun labarin inda Aysher take, wayar Alh.Aliyu ne yafara rurin neman d'auki, Alh.Aliyu ya d'auka tare da sallama.




"Hello! Wake magana?"






"Yauwa Alh.Aliyu ne dan Allah?"




"Eh nine, waye nawa?"




"Kana magana da DPO, na Fagge division, idan ba damuwa muna buk'atar ganin ka yanzu, kazo muna ganin kamar yarinyar da kuke nema ne, aka kawota yanzu......sai dai kazo kawai kaji sauran bayani."


Da sauri Alh.Aliyu yace"Ikon Allah! Alhamdulillahi DPO gani nan zuwa 'yanzu in sha Allahu, harda mahaifin yarinyar."


"Okay sai kunzo"


Ya katse wayar.

Su Umma ya kalla yace musu"Bari muje fagge da alamar Allah ya amshi addu'ar mu, anga Aysher"




Kowa ka kalli fuskar sa a gurin yana d'auke da annuri, sukayi musu fatan dawowa lafiya tare da dacewa.
***********


Rungume mahaifinta Aysher tayi tana kuka tare da fad'in "ita kam tafasa auren Ahmad, dan Allah Baffa ya taimaka a raba auren, dan ta wahala sosai", alama mahaifin ta yayi mata da cewar tayi shiru, nan aka zauna Ladi Reza ta k'ara bada labarin abinda yafaru.


Kowa a gurin yayi mamaki tare da Allah wadaran hali irin na Feedo, nan Ladi Reza ta bada kwatance na inda za'a samu Feedo da Ummi 'yar tsinke, take anan DPO ya tura 'yan sanda.




Aysher kuma sun yanke shawarar asibiti zasu kaita, dan tana buk'atar ganin likita itama.
Sun fito harabar Asibiti, wayar Alh.Aliyu tafara ringing, ganin number matarsa ya d'auka da sauri, kuka yaji Umma tanayi tare da fad'in" Alh.kazo asibiti yanzu dan Allah, Ahmad Allah yayi masa cikawa (taka'arasa fad'a cikin kuka)"




Ahmad ya rasu? Innalillahi wa'inna ilahi raji'un (Abinda Alh.Aliyu yafad'a kenan a bayyane).


Wani ihu sukaji Aysher tayi kafin ta yanke jikinta ta fad'i.


Cikin tashin hankali suka cicci6i Aysher, suka sakata a mota sai ZEEMAN'S CLINIC, hakika kana kallon wad'annan mutanen kasan suna cikin tashin hankali gwanin tausayi, kai tsaye A&E aka wuce da Aysher, Alh.Aliyu ko waiwayar inda aka kwantar da Ahmad baiyi ba, dan yasan tashi tariga ta k'are, saura aceto rayuwar Aysher (Baiwar Allah).


Nursing suka iso gurin da sauri, suka cicci6i Aysher dan d'orata a gadon marasa lafiya, HALIMA daman anan kike aiki? Baffa Usman ya ambata a rikice, wacce aka kira da Halima ta juyo da sauri kafin tace"Na'am Usman daman kana garin nan?"


"Yanzu ba lokacin wannan maganar bane Halima, taimaka ku shiga da ita ciki, ki taimaka ki ceto rayuwar 'yar mu"


"Kana nufin Aysher dana samu labarin bikinta itace a wannan hali? Yasalam kushige muje"


Da sauri suka tura gadon dan shigewa da ita d'akin bincike.






MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA.
[11/1, 6:26 PM] Zeetty: [11/1, 7:33 AM] Zeetty: 🍒
🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒
ZUBAR HAWAYE






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*






*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*





Page 63-END












'Yansanda sun kamo su Feedo da Ummi 'yar tsinke, iya wahala sun shata kafin su amsa laifin su, dan haka DPO ya tsaida ranar da za'a turasu zuwa kotu (wato kwanaki uku masu zuwa).






Ahmad ashe ba rasuwa yayi ba, doguwar suma ne, dan sanda aka fasa ihun mutuwar shi, basu kira likita ba, saida likita yazo ya dubashi, kafin ya sanar musu doguwan suma yayi.


Nan take daki yayi tsit suka saurara daga koke-koken da sukeyi, likita yakallesu tare da cewa"Kufita waje ku bani gurin zan dubashi dakyau", da sauri suka fice duk jama'ar cikin d'akin, hanyar cikin harabar asibitin duk suka nufa dan shan iska, fitarsu keda wuya suka hango Alh.Aliyu tare da Baffa Usman fuskarsu babu walwala, da sauri suka nufi gurin da suka hangosu.




Umma ce tafara magana bayan sun k'arasa da cewa"Alh. Lafiya kuwa muka ganku haka, kuns shigo asibitin baku k'araso dak'in da muke ba, Ina Aysher take?", duk wad'an nan tambayoyi Umma ta jerama Alh.Aliyu bata jira amsar shi ba, ta k'ara da cewa"kaji Ahmad d'in ma ashe doguwar suma yayi, rud'ewa mukayi shiyasa mukayi tunanin ya mutu, saida likita yazo tukunna yanzu haka ma doctor d'in yana d'akin Ahmad din."






Hamdala Alh.Aliyu da Baffa Usman sukayi a bayyane, kafin suka fara rokon Allah yatashi kafad'un Aysher.


"Meyafaru da Aysher kardai wanda suka saceta sun cutar da ita?". (Cewar Umma),


Alh.Aliyu yace" Kiran wayana da kikayi, tare da sanarmin rasuwan Ahmad, shine yasata suma amman ko badan hakan ba, daman muna da buk'atar taga likita".


Aunty Maryam (k'anwar maman Aysher) cewa tayi"Ikon Allah, wannan aure nasu akwai abubuwan Al'ajabi a cikin sa, Allah dai ya basu lafiya."


Gaba d'aya aka amsa da ameen yarabbi.




************


Suna zauzzaune cikin Alhini da jimami, wasu kuma suna tsaye, duk suna sauraron zuwan likita daga 6angare biyu na Aysher da Ahmad.
Mahaifiyar Aysher ce ta fara fitowa daga 6angaren Emergency, gurin su Alh.Aliyu ta nufo, kallon su tayi cikin murmushi kafin tace" Toh Alhamdulillah! Ta farfad'o, cikin ikon Allah ba'a sameta da wani matsala ba, kuzo mu k'arasa d'akin da take (takasa fad'in sunan Aysher, kasan cewar Aysher ce 'yarta ta fari, kuma guda d'aya tilo data mallaka, kunyace irin na fulani).






'Dakin da Aysher take suka nufa dukansu, sun sameta idanuwan ta a bud'e tana kallon sama, tana ganin shigowar su tafara kuka tare da tambayar su "Dagaske ya rasu?"




Fatima ce ta k'arasa gurin ta da sauri, hanun Aysher ta kamo tare da fad'in"Allah mungode maka, k'awata kece nake gani? Kwantar da hankalin ki, mijin ki yana nan da ranshi bai mutu ba, yi gaggawar mik'ewa ki tashi, saboda mijin ki yana buk'atar taimakon ki."
Gaba d'aya kunya tagama rufe Aysher, ta rufe fuskarta da hannun ta wanda ba'a saka mata k'arin ruwa ba, murmushi Aunty Maryam tayi tare da k'arasawa gurin ta, tanayi mata sannu, nan fa duk jama'ar d'akin suma suka d'auka fad'i suke "Allah yabaku lafiya".


Nurse ce tashigo da sauri tace" Alh.Aliyu ya k'arasa d'akin Ahmad Likita yanason magana dashi."


Dasauri suka fita daga d'akin shida Baffa Usman, kai tsaye 6angaren da aka kwantar da Ahmad suka nufa, Likita suka tarar a d'akin yana tsaye yadafa kan Ahmad, bayan su Alh.Aliyu sun k'arasa shigowa, likita ya dubesu kafin yafara magana"Toh Alh. Yaron kufa yana buk'atar addu'ar ku, sannan kuma yakamata aguji duk wani abu da zai sashi cikin damuwa, gudun kamuwa da wani babban cuta, kunyi sa'a ma jinin shi normal ne bai hau ba, ku matso kusa da shi idon shi biyu nayi masa magana, yak'i bani amsa.


Alh.Aliyu ne yak'arasa tare da fad'in"Tashi Ahmad mugodema Allah, Addu'ar mu ta kar6u, anga matar ka Aysher, yanzu haka tana cikin asibitin nan.
Zum6ur Ahmad ya mik'e tsaye kamar wanda aka tsikareshi, yana fad'in"Dan Allah Abba da gaske, ina take Aysher, suwaye suka aikata haka a gareta?"




Murmushi Alh.Aliyu yayi kafin yace"Koma ka kwanta, kaida baka da lafiya, zakaji komai idan kasamu lafiya."


"Lafiyata k'alau Abba, naji sauk'i, dan Allah Abba muje naganta."




Alh.Aliyu zai k'ara magana, likita ya dakatar dashi da cewa"Alh. ku rakashi ya ganta, hakan shine k'arin samun lafiyar shi, muje gaba d'ayan mu."




Dan haka Likita ya kamo hanun Ahmad suka fito daga d'akin da aka kwantar dashi.


********
[11/1, 5:06 PM] Zeetty: 🍒🍒
🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒
🍒🍒🍒🍒🍒






Bude k'ofar d'akin da Aysher take kwance akayi, Baffa Usman ne yafara shigowa, sai Alh.Aliyu, likita da Ahmad ne k'arshen shigowa.
Idon Ahmad kyam akan gadon da matar sa take kwance, dasauri yasaki likitan ya k'arasa gurin ta cikin sarsarfa, kamo hanun ta yayi wanda ba'a d'aura mata k'arin ruwan ba, yace"Aysher kece nake gani, waye ya aikata miki wannan mummunan abun?, hak'ik'a bazan ta6a yafewa ba, an zalunceni, an daga mana hankali."






Likita ne yabi 'yan d'akin da kallo, tare da yi musu alama da ido (ma'ana sufita daga d'akin), nan duk 'yan d'akin suka fice da d'ai-d'aya.






Goga kuwa Ahmad yama manta da wasu mutane a d'akin, shidai kawai matar sa, adai-dai wannan lokacin k'arin ruwan da ake mata ya k'are, Ahmad ya cire mata.




Tashinta yayi ta zauna ya kare mata baya da filo, kafin yace"Sannu my love, ya jikin naki?"


Shiru Aysher tayi masa, bai hak'ura ba ya sake tambayar ta, kuka ta sake mishi cikin shagwa6a tare da fad'in"Nidai na barmusu kai, na hak'ura kawai ka rabu dani tunda ban tare ba".




"Bangane abinda kike cewa ba, suwaye mutanen da kike nufi?"




Shigowar Aunty Maryam ne ya dakatar da komai tace"Abba yace kutaso, angama had'a kaya, ansaka a mota kuzo mutafi gida, an sallame ku."




Hanun Aysher Ahmad ya kamo, kamar bashi bane mara lafiyar nan dayake rai a hanun Allah ba, harabar asibitin suka fito Aysher kunya duk ya gama rufeta ganin fuskokin iyayensu a gurin, shi kuwa Ahmad ko a jikin shi, a haka suka k'arasa gurin da ake faka mota, aka bude kowa ya shiga, Ahmad fuska yayi, yak'i sake hannun Aysher har suka k'arasa motar Mudansir ya bud'e musu gidan baya suka shiga bawanda ya kulasu.


Kowa ya shige mota aka nufi gidan Alh.Aliyu wato Abba.

*******




Bayan sun k'arasa gidan kowa ya samu guri a falo, dan huta gajiya.
Ahmad da Mudansir kai tsaye 6angaren mudansir suka nufa, dan Ahmad yana buk'atar watsa ruwa a jikin sa, suna shiga falon band'aki Ahmad ya nufa, wanka yafarayi da brush kafin yafito jikin sa d'aure da rigar wanka, a nutse ya shirya cikin shigar shadda wanda ya d'inka su na musamman zaiyi angwanci da su.
Already daman akwatunan sa a shirye suke da kayan sa da zai tafi dasu gidan shi, wanda zaitare da amarya.


Mudansir tsokanan shi yadinga yi da cewa"gawa tak'i rami, mai cutar love"




"Naji din koma meye kafad'a ina son mata na" Ahmad yabashi amsa da hakan.




Idan ka kalli Ahmad yayi kyau cikin wannan shigar ta manyan (kaftan), kamar bashi bane wanda yayi rashin lafiya, sai dai 'yar ramar da yayi.






Abangaren Aysher ma, ruwan wanka aka had'a mata, tashiga tayi tare da wanko bakin ta, ruwan wankan nata kuwa yasha turarukan wanka wanda Umma ta bayar a zuba mata a ciki, Aunty Maryam ne ta shiryata cikin wani material mai tsananin kyau daga ganinsa yaja kud'i, daga cikin kayan fitar da Ahmad ya d'inka mata aka ciro, kwalliya mai sauk'i Aunty Maryam tayi mata, ta kamo hanun Aysher su fito zuwa falo amman Aysher tak'i fitowa a haka dole saida ta yafa gyale a jikinta.






Fitowar ta yayi dai-dai da shigowar Ahmad dan yaka tsummamun idanuwan sa ya zubo mata tare da murmushi mai isar da sak'on love, Idonta Aysher tayi saurin d'aukewa daga kallon sa, ta nemi guri ta zauna kusa da Fatima.






Addu'a Alh.Aliyu yafara yi, tare da mik'a godiyar shi ga Allah, daga nan ya fara bama 'yan falon labarin wa'inda suka d'auke Aysher da kuma dalilin su nayin hakan, salati duk jama'ar falon suka farayi daga k'arshe suka fara yima Feedo tofin Allah tsine.


Ahmad a fusace, yace"Zaisa a kulle Feedo, dan ya manta da itama kwata-kwata"


Alh.Aliyu ya dakatar dashi da cewa"tsuntsun dayaja ruwa........dan haka kawai abar Feedo da hukuma tunda sun shigo ciki, ajira danjin hukuncin da zasu yanke, daga nan yayima Ahmad fad'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login