Showing 36001 words to 39000 words out of 50413 words

Chapter 13 - RIBAR UWA COMPLETE DOCUMENT BY Azizat .txt

Azizat   

29 Nov 2024

2791

to the extend sai da Uwar ta yi hawaye


Da ido na naga Uwar da matar ɗan ta ke walaƙantata


Da ido na naga Matan 'ya'yan wata Uwa sun haɗu suna zaginta su na kiranta Munafuka Annamimiya wai tana haɗa faɗa tsakanin su (lets say hakan ne tanada irin halin amma a matsayinta na uwar miji a gaban jikokin ta da gaban jama'a ku sata a gaba kuna zagi its totally bad)


Da ido na naga Uwa tana kuka saboda 'ya'yan ta sun kasa biya mata buƙatun ta.


Da ido na naga ɗa ya ce wa Uwar sa "dalla Mama ki yi mana shiru"


Akwai wata 'ya da aka bawa kifi mai yawa tsaraba ta kaiwa Uwar ta. Wannan 'ya ta cinye kifin nan ba tareda ta kaiwa Uwarta ba ba tareda ta kuma gayawa Uwarta maganan kifin ba. Kar ku manta kifin nan an bata nata kafin aka ba da na mahaifiyarta amma haka ta haɗa ta cinye duka. Bayan kamar sati wacce ta tura kifi ta kira dan ta tambaya ko wannan Uwa ta ji daɗin kifin da ta aiko. Uwa ta ce ba ta san maganar kifi ba, da aka kira wancar 'yar sai ta fara kame-kame, Ya Allah! Uwar da ta haifeka. (Dan Allah mu cire mentality na cewa iyayen mu sun tsufa ba za su ci daɗi ba. Indai ba wai abunda zai taɓa lafiyar su ba ne to mu bar su su ci daɗi. Wata tsohuwar kwaɗayin da ba ta yi a ƙuruciya ba sai tsufanta sai ta fara kwaɗayi amma a hakan ka ji 'ya'yanta na zaginta ko su dinga yaɓa ma ta magana, "kai Mama ba dai kwaɗayi ba". Wani lokaci kaya Uwa za ta sa 'ya'yanta su ƙwace su ce ta tsufa, wata takalmi Uwarta ta siya idan ta zo gidan sai ta ɗauke shi. Mu a tunanin mu sun tsufa da saka abu mai kyau ko amfani da abu mai kyau)...


Akwai misalai da dama na yadda 'ya'ya ke walaƙanta iyayen su musamman UWA.
I'm sure a cikin gidan ku ko a family ɗin ku, ko a anguwar ku ko a garin ku kun ci karo da wata Uwa mai irin 'ya'ya kaman na Innayi ko da 'ya'yanta ba su yi exactly irin abinda 'ya'yan Innayi su ka yi ba, za ka ga sun yi shigen sa. Lokaci ya kawo mu Uwa za ta haifi 'ya'ya goma amma kaga an rasa mai kula da ita yadda ya kamata cikin su, ko kuma kaga cikin goman nan baifi biyu ba ne ma su tausayinta a ciki.
Idan ma kina hantarar mahaifiyar ki ko Uwar mijin ki to kiji tsoron Allah ki dena domin akwai ranan da za ki kwanta ki mutu a tuhume ki ayyukan da ki ka aikata a rayuwar ki.


Wallahil Azim idan ka zamo mai yawan yiwa iyayenka alkhairi to ko ku talatin ne a gaban su za su fi sanyaka cikin addu'o'in su. Ba wai sai kana da kuɗi za ka kula da su ba, ba sai kana da aure za ka musu abin arziƙi ba. Yau ko lemu ka siya ka bawa Uwar ka za ta ji daɗi ta sa maka albarka balle you can do more than that. Idan ba ka da komai to ka yawaita ziyartar su ko ka kirasu a waya ka gaishesu saboda su ma addu'a, ba wai sai kana da buƙata za ka kira ko ka je ka ce a ma addu'a ba. Ko kira kayi ku ka gaisa idan kun gama magana sai ka ce " To Mama a sa mana albarka"
Wallahi addu'arta works like magic.


Ga wanda iyayen su suka rasu, ku yawaita yi mu su sadaka da addu'a, a duk inda su ke za a isar mu su. Tunda manzon Allah ya ce addu'ar 'ya'ya ga iyayen su da su ka rasu tana isa garesu, haka idan sun yi mu su sadaka ko sun musu wani aikin alkhairi.


Allah ka gafarta ma iyayen mu da mu kan mu baki ɗaya Amin...


***
Mutuwa dai ɗaya ce, kullum darasi ta ke ƙara zame mana a rayuwa, kuma idan aka yita ɗanya ta ke komawa.
Nasabarka, Arziƙin ka ko Talaucin ka baya hana ka jin raɗaɗin ta, matuƙar lokacin ka yayi to dole sai ka ɗanɗanata.
Allah ya sa mutuwa ta zamto darasi garemu, mu gyara ayyukanmu su zamto abin kusanci ga Mahaliccinmu Amin.


Damuwar mu a yau shine mu samu duniya. We want all the glitters in this world, komai na yayi shi mu ke so, komai na jin daɗi shi mu ke so. Ba mu san kowa ba sai kawunan mu, ma su ɗan sauƙi sauƙi su ne za su iya jawo kaɗan daga cikin 'yan uwan su na kusa su ci daga arziƙin su.
Saboda yadda mu ka bawa duniya mahimmanci shiyasa kowani motsin da za mu yi to na neman duniya ne. Hakan ya sa mu ke bin tafarkin ƙarya duk dan mu samu duniya.
Abun ya kai ga idan ba ka bi bokaye da malamai ba to za ka tauye hakkin mutane ka ci dukiyar bayin Allah. Wanda ya ke neman halal ɗin sa kuwa zai rufe ido ya kasa yin sadaka ko kyauta, ko ma ya taimaka wa wani ta hanyar da zai samu ya rufawa kan sa asiri. Abinda ya sani kawai shi ne ya ci shi kaɗai wai yana gutun talauci.


Shin mun manta duniyar gaba ɗayanta mai ƙarewa ce, yadda mutanen kirki su ke gushewa haka na banza ke gushewa, amma hakan baya taɓa zama mana izina.
Mutuwa aka ce rigar kowa ce. Ko ba daɗe ko ba jimawa wannan rigar za ta hau kan ka ko kan ki. Dukkan mu mutuwa mu ke jira kuma babu wanda ya san gaibun randa zai mutu ko kuma sababin mutuwar sa.


Ina Manzanni da Annabawa wanda su ka fi mu daraja da ɗaukaka a wajen Allah? Su ma fa sun mutu sun tafi sun bar mu.


Ina Sahabbai da Salihan Bayi? Su ma anyi zamanin su ya shuɗe.


Ina manyan kafirai, ƙangararru wanda su ka yi fice a zamanin su kuma har yau sunan su na yawo a doron ƙasa?
Kamar Fir'auna, Hamana, da Ƙaruna etc Sun fa halaka tun zamanin da ya shuɗe.


Mu gangaro zuwa zamanin mu na yanzu.
Manya- manyan celebrities a kowani ɓangare na rayuwa da duniya ta yi yayin su. Yau ina su ke? Ba sa nan fa.
To idan har sun shige suma fa na yanzun za su zo su shige ta yadda wasu ne za su maye gurbin su.
Amma majority ɗin mu yanzu mun mai da celebrities idol ɗin mu. Rayuwar su mu ke bibiya, rayuwar su mu ke kwaikwayo.


Idan ma mutane na ƙwarai ne su ma anyi su sun shuɗe kuma wanda su ka maye gurbin su ba jimawa za su yi ba za su zo su shuɗe a sake maye gurbin su da wasu.


Mun maida rayuwar mu daga wani kaya zan saka zuwa wani jaka ake yayi. Mun maida rayuwar mu daga tunanin nawa ne a account ɗina zuwa taya zan ƙara samun kuɗi ta kowani hali.


Muna aikata saɓo, muna aikata laifuffuka daga ƙananun har manyan. Amma ba mu damu mu dinga yin ƙananun abubuwa na lada wanda za su kawar mana da saɓon da mukeyi na yau da kullum ba.
Ke ce hantarar 'ya'yan kishiyoyin ki
Ke ce hana mijinki kula da 'yan uwan sa
Ke ce ha'intar maƙotan ki ko ƙawayen ki
Ke ce ke hana ruwa gudu a wajen aikin ki da kuma cikin 'yan uwan ki
Ke ce yiwa miji asiri
Ke ce hana 'yar uwar ki ko ƙawarki samun miji
Ke ce bin malamai saboda kasuwan cin ki ya ɗaukaka...


Kai ne butulci tsakanin matan ka
Kai ne ka ke walaƙanta matar ka
Kai ne watsar da 'yan uwan ka a lokacin da ka samu buɗi
Kai ne lalata yaran mutane, kana zina da yaran da sun kai ka haifesu
Kai ne munafukin anguwa mai haɗa guri
Kai ne mai ha'inci a kasuwan cin ka
Kai ne za ka ɗale kujeran siyasa ko wani muƙami ka cinye dukiyar jama'a
Kai ne malami mai gurɓata tarbiyyan yaran mutane
Kai ne neman kuɗi ta hanyar asiri
Kai ne neman matsayi a wajen bokaye da malaman tsubbu...


Da mu yi mai kyau da kar mu yi, daga ƙarshe dai babu wanda zai tsallake mutuwar sa.
A sa mu a kabari a bar mu daga mu sai halin mu. Duk yadda mu ka ji daɗin rayuwa muka yi abun da mu ke so za mu ga sakamakon daga lokacin da Malakul Maut ya ziyar ce mu.


A koyaushe mu dinga tunawa cewa akwai ranan hisabi, ranan da babu mai wani iko ko gata ko muƙami, ranan da kowa ke nafsi-nafsi, ranan da Allah kaɗai ne Sarki mai ɗaukaka mabuwayi, wanda zai saka mana gwargwadon abinda mu ka aikata.
Idan ka kwatanta daidai ka bi duniya a sannu, Aljannah tana nan an tanada ma ka. Idan ma rayuwar shaƙiyanci, gadara da mugunta ka yi, wutan Jahannama na nan an tanada wa kafirai, mushrikai da munafukai da ma su mugayen hali irin na ka.


Mu yawaita tuna wannan:


shin mi muka tsinana a rayuwar mu?
Shin yau idan mu ka mutu mi muke tunanin za mu tarar a ƙabarin mu?
Da mi mutanen duniya za su tuna da mu?, da mi za ayi shedar mu idan muka mutu?
Wani aikin alkhairi mu ke yi da mu ke tunanin Allah zai gafarta mana saboda shi?
Shin shekarun mu nawa a duniya yanzu? Kuma ko muna da sani gameda iya shekarun da aka ɗeba mana. Mun kusa mutuwa ko kuma dai da saura?
So nawa ka ke neman istighfari a rana?
So nawa ka ke karatun Qur'ani a rana?
Nafila nawa ka ke yi a rana ko a sati?
Yaushe rabon da ka yi sadaka ko kyauta?


Allah ka bamu ikon gyarawa Amin...




Akwai ayyuka guda uku da ladan su baya shiga mizani a ranan alƙiyama saboda girman su:


1- YIN AFUWA GA MUTANE: Allah yana cewa "Duk wanda ya yi afuwa kuma ya kyautata to ladansa yana ga Allah"


2-HAƘURI: Allah bai faɗi iyakar ladan da zai ba wa masu haƙuri ba. "Haƙiƙa ana bai wa ma su haƙuri ladansu ne ba tareda lissafi ba"


3-AZUMI: shima Azumi Allah bai faɗi adadin ladan da zai bayar wa ma su yinsa ba.


Manzon Allah ya ce a ranan Alƙiyama wani Mala'ika zai yi kira ya ce " Ina mutanen nan waɗanda ladan su ke wajen Allah?"


Nan ta ke ma su haƙuri da ma su afuwa da ma su Azumi sai su fito su tafi wajen karɓan sakamakon su.




*Ya Allah ka ƙara mana haƙuri da juna, da haƙuri da ƙaddara da kuma haƙurin biyayyarka. Ya Allah ka sanya mana taushin hali mu dinga yafiya ga junan mu, ka karɓa mana Azumin mu da dukkan Ibadunmu. Amin*




Ribar haƙurin Innayi da afuwan ta ga 'ya'yanta yana wajen Allah.


A nan na kawo ƙarshen labarin Innayi amma akwai 2-3 pgs da za su biyo baya da za mu ga yadda rayuwan 'ya'yan Innayi ya koma bayan rasuwan mahaifiyar su.


*Dan Allah mu daure mu dinga kyautatawa iyayen mu, yanzu da su ka girma ne su ke buƙatan mu, su ke buƙatan tausayinmu da jin ƙan mu. Mu nemi karanta fassaran suratul Isra'i musamman aya ta 23,24,25 da Allah yai magana akan Iyaye*












*RIBAR UWA*




*Na...Azizat*
*Wattpad@000Azee*






Chapter 13
(Free book ne)




*condolence*








Dogon suma Raudha ta yi dan duk taimakon gaggawa da ya bata dan ta farfaɗo ba ta farfaɗo ba hakan yasa ya ɗauketa ya wuce da ita wajen motar sa yayinda Emilia ta bi bayan sa saboda itama ta biyo bayan Raudha ne dan ta bata jakarta da kuma wayarta da ta baro shine ta ga abinda ya faru.
Bayan ya shimfiɗa Raudha a kujerar baya yai wa Emilia nuni da ta shigo gaba, ba ta ɓata lokaci ba ta shiga ciki da sauri...


A asibitin ma sai da ta kai kusan awa uku kafin ta farfaɗo, bayan wasu daƙiƙai da farfaɗowan ta ta kama kuka. Kukan ne ya ja hankalin Emilia da ke zaune gefenta tana latsa waya. Ta yi ta yi ta sanar da ita abinda ya faru amma ba ta gaya ma ta ba illa cewa da ta ke yi "i want to go home"
Emilia ta ɗau wayarta ta kira wanda su ka zo tare. Sallah ya fita yi amma da tare su ke zaune da shi a ɗakin. Bayan ya sanar da ita yana hanya ne ya sa ta kashe wayar ta cigaba da kallon Raudha da ke kuka, ba ƙaramin tausayi ta ba ta ba domin ta san duk abunda zai sa Raudha kuka haka to ba ƙaramin abu ba ne.
Ba wai sun shaƙu da Raudha ba ne sosai amma watan da ya wuce da ƙanwar Emilia ta mutu ta je ta ma ta ta'aziyya har gida ita da Azhar hakan ya sa ta ke ƙara ganin Raudhan da daraja, wannan ya sa su ka fara ƙawance.


Kafin Prof Bamalli ya iso Raudha ta cire ruwan da aka ɗaura mata wanda saura kaɗan ya ƙare. Ƙoƙarin tashi ta ke yi Emilia ta tareta.
"Emilia please let me go" ta faɗa da dasasshshiyar murya


Emilia ta girgiza kai. Raudha ta fara ƙoƙarin tureta amma ina Emilia ta fi ƙarfinta. "Rodha calm down, professor Bamly is coming"


Ta girgiza kai tana cigaba da tureta, da ƙyar Emilia ta samu Raudha ta nitsu ta zauna a bakin gado ta cigaba da kuka.


Turo ƙofar da aka yi ya sa Raudha ta ɗaga idonta ta kalli wajen ƙofar. Professor Bamalli ne ya shigo tareda sallama, ba ta iya amasawa ba sai ma kawai ta sunkuyar da kanta.


Emilia ta kissing goshin Raudha ta ce "take care dear, i'll call you later"


Bayan Emilia ta fita ne Prof Bamalli ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar Raudha.


"Raudha" ya kira sunan ta a hankali. Ta ɗago ta kalleshi na ɗan daƙiƙu kafin ta sunkuyar da kai ta cigaba da sheshsheƙar kuka.


"Na san ke musulmace Raudha, kuma kin sani yarda da ƙaddara yana ɗaya daga cikin cika-ciken musulunci. Saƙon mutuwa akwai ciwo, musamman idan wanda ya rasu makusancin ka ne. Sai dai Allah da ya haliccemu shi ya tsara wa kowa adadin lokacin da zai yi a doron ƙasa, hakan ya sa idan lokaci yai ko second ɗaya ba za ka ƙara ba"


Raudha ta ɗan sassauta kukan na ta tana sauraron sa. Prof Bamalli ya cigaba.


"Innayi mahaifiyar ki ce ko?"


Maimakon ta bashi amsa sai ta kifa kan ta a gwiwowinta tana ƙara sautin kukan ta wanda ke ratsa zuciyar mai sauraro.


"A maimakon kuka Raudha addu'ar ki ta ke buƙata yanzu, ki daure ki yi ma ta addu'a"


Ta ɗago ido da sauri ta ce "Sir ba ka san Innayi ba ne, ba ka san irin wahalhalun da ta sha a kan mu ba. Bai kamata ta mutu ba, bai kamata ta tafi ba tareda na cika alƙawurran da na ma ta ba. Bai kamata ta tafi ba tareda..."


"Manzon Allah da ya fi kowa daraja ya bar duniya Raudha. Babu wani da zai rayu ba tareda ya ɗanɗani zafin mutuwa ba, kisa a ranki mutuwa ita ce hutu gareta. Iya lokacin da aka ɗibar ma ta kenan a duniya. Raudha a duk inda mahaifiyar ki ta ke Insha Allah tana cikin farin ciki" maganar sa ya katseta.


Hawaye kawai ta ke yi tana yi tana goge majina da bayan hannun ta. Hakan ya sa Prof Bamalli ya ciro handkerchief ya miƙa ma ta.
Nasiha ya cigaba da yi ma ta bayan ya lura ta ɗan nitsu. Ya ƙare da ba ta labarin na sa mahaifiyar.


"Ban tashi na ga mahaifiya ta ba. Ance ina ɗan wata goma ta rasu. Yayar Mahaifiyata da ke zawarci Baba na ya aura bisa shawarar 'yan uwan sa, a cewar su za ta kula da ni. Sai dai fa abun bai kasance yadda ake so ba domin tun lokacin da ta shigo ta ke hantara ta, Baba yai faɗan yai masifar amma shiru Umma ba ta kula da ni yadda ya kamata, yadda ta ke mini tamkar ba Uban su ɗaya da Mahaifiyar da ta haifeni ba. Haka na taso a walaƙance tamkar ba a gidan Ubana na ke ba, sai na fi sati ba a min wanka ba, sai Baba ya lura da dauɗan da ke jikina tukunna ya ma ta magana akan ta min wanka, wani lokaci ta yi wani lokaci ta ƙi yi. Ina shekara huɗu ta haihu nan kuwa duk wani kulawa ya koma kan ɗan da ta haifa sai kuma Adama da ta zo da ita gidan. Akwai lokacin da Baba yai yunƙurin ƙara aure saboda ko zai dace a samu wacce za ta riƙe ni amana tunda dai Umma Habiba ta kasa riƙeni amma magana ta zo ta bi ruwa. A haka dai na taso har na kai shekara takwas ba na zuwa makarantar Boko sai dai makarantar Allo idan Umma ta ga dama. Ina girma ina sawa a raina ni ba ɗan gidan ba ne, Yaya ta Adama da ƙannena Sani da Amadu su ne 'yan gida shiyasa Umma ba ta so na. Ina shekara tara a duniya watarana Umma ba ta bani abincin rana ba, na fakaici idon ta na shiga ɗakin da ake dafa abinci na buɗe tukunya na fara ci, rabona da abinci a lokacin tun tuwon dare, dan ɗumamen safe ma ban samu ba. Ina cikin ci Umma ta shigo ta sameni nan kuwa ta hau duka na tana yi tana zagi na. Bayan kwana uku aka kaini wajen Baffa Saleh wanda ya ɗaukeni ya kaini Almajiranci a chan wani gari da ake cewa Yusufari da ke Yobe state yanzu. Ina chan ina karatu da daɗi ba daɗi haka, yadda ba na samun cin abinci da kyau a gidan Uba na haka wajen Malam ma ba na samu, wani lokaci ka samu abinci ka yi hani'an har ka godewa Allah, wani lokaci kuma ka wuni da yunwa. Banfi wata bakwai ba na fara rashin lafiya tun Malamin mu bai damu ba har ya damu ya sa aka fara yi min jiƙo ina sha. Wasa wasa sai ga cikina ya fara kumbura ta kai na kwanta ba na iya ko tashi, hakan ya sa aka kai ni asibiti. Da ganina nurses na wajen su ka yita yiwa Malam faɗa tareda cewa yai gaggawan kai ni Teaching Hospital da ke Maiduguri dan abin ya fi karfin su, idan ya barni haka mutuwa zan yi. Malam dai a tsorace ya lallaɓa ya kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login