Showing 1 words to 1088 words out of 1088 words
80-85
Cikin sauri ya mike tare da shiga bathroom ruwa mai zafi ya hada acikin tube bath sannan yaxo
ya dauketa cakk wadda bata motsi ko kaɗan" saka ta yayi cikin ruwan dumin anan ta saki wata
ajiyar heart nan ya cigaba da gasata bakaramun kuka taciba nan ya sake nadota ya fito da ita
akan sopa ya ajeta sannan ya nade bedshit din ya saka a lundry basket sannan yaxo ya
shiryata riritata yake kamar ƙwai a wannan ranar ko abincima da kansa yake bata.
Duk wanda yaxo gidan" aranar baya barinta fita sabida ciwon daya ji mata" sati guda yayi yana
jinyarta sannan ya koma fagen fama babu ji babu gani dan harkar tasa babu daga kafa kullum
suna liƙe har wajan two weeks" idan ka kallesu dukkan su kowanne su yayi kyau yayi fresh
abinsa.
Satin su uku ya daga da ita fatacoaut aka bar zara anan sabida ta koma aikinta" acan babu abin
da suke se soyayya da ririta juna anan khadija ta tabbatar da irin son daya ke mata domin ko
kuda baya barinsa ya hau jikinta.
Ya mallaka mata gidan sa dake unguwar ƴan majalissu sannan ya bata kujerar maka sannan ya
sai mata mota acan ake koya mata.
BAYAN SHEKARA.
zara taki kwantar da hankalinta tun da taga khadija ta sami ciki shinefa ta dage ta daga hankalin
kowa da kanta ta nemi daya sawwake mata agan su abbi aikuwa atake anan ya saketa saki
biyu acewarta zataje ta auri wanda ze mata ciki ta haihu haka ta hada kayanta tai maiduguri.
Babu abin da khadija ta nema ta rasa a rayuwa su umma tuni ya sai musu wani gidan anan
kasan su babbane mai kyau suna dawowa daga saudi suka tare acan yanxu haka cikin khadija
wata biyar wanda yayi dai dai da bikin kannanta amman fafur yaki barinta zuwa arewa wai
acewarsa kartai masa bari" ranar ba karamin kuka taciba" aykuwa nan ya susuce cikin dare yayi
musu booking na jirgi suka taho da asuba suka sauka a kaduna gidan hajiya suka wuce can
ban garansa.
Tunda suka sauka take faman kelaya amai wanda seda aka kara mata ruwa leda shida kuka
kawai yake yana dana sanin bin ra,ayinta kamar ze maida ita ciki haka yake jida ita.
Duk shagalin da akai na biki babu wanda taje hatta ga tariyar tana gidan hajiya na ririta ta
kamar ƙwai lokacin dasuka tashi tafiya hajiya kin barin ta tai tabishi haka ya gama haukansa ya
wuce kamar ze mutu.
Da ya dauki gaba da ita sabida yana ganin kamar itace taja masa amman daga baya sukaxo
suka jone.
Bayan wata tara tun safe aka kaita asibiti karfe sha biyun rana ta haifo ƴaƴan ta mace sa namiji
zokuga murna gun wannan family.
Ranar da aka gaya masa kamar zeyi hauka haka ya dinga rabo wanda bai san adadin abinda
ya rabar ba sanann ya hado kayansa yayo arewa.
Tunda yaxo ya kafa ya tsare ya hana kowa taba masa ƴaƴa shikadi zesaka ƴaƴansa agaba
yayita kallo.
Ranar suna na zagayowa aka radama yara sunan abbi da hajiya.
Fadin irin shagalin da akai ma bata bakine nidai mutum daya na hango tana ta sabga lomar
tuwo wato maman nana" fatima umar adams itace mai rabon take away fatima ali itace mai
wawar dambu har ina mata tsiya haka akai taro lafiya aka gama lapiya
Kula mai kyau hajiya take bawa khadija ranar daxatai arba'in haka tasha gyara na ban mamaki"
fafur ya hanata xuwa gidan kowa wai acewarsa kar yayan sa susha rana.
Da ƙyar ya barta taje gidan kannanta hakam gidansu ya barta tai kwana ɗay jall sannan
washegari sukai mai duguri gidan mallam suka yada zango.fadar irin karramawar da akai
musuma bata bakine kamar za,a maidasu ciki.
Kwanan su uku suna zaga dangi kafin su koma kaduna" acan ma sun danyi ziyara agidan
amina suke jin labarin zara tai aurenta yanxuma haka ciki gareta" murmushi yayi yana cewa
lallai rabon wani shike kisan wani.
Washe gari suka hada kayansu sukai fatacoaut. rayuwa mai kyau suke gudanarwa a garin yan
hka idan ka gansu baxaka shedasu ba sunyi kyau na ban mamaki.
Wata ranar asabar umma ta kirata bayan sun gaisa umma take cemata Allah yayiwa bashir
rasuwa sanadin cutar kanjamau ɗin daya kwaso taji mataukar tausayin sa nan tai masa addu,a.
Yana dawowa take bashi labarin rasuwar bashir shima yaji manta abin anan take gaya masa irin
artabun datasha kafin ya saketa wani abun yayi dariya wani abun yayi murmushi.
Haka rayuwa ta kasance musu wanda cigaban rayuwa yay ta zuwar musu yanzu haka suna da
shekara biyar da aure ƴaƴan su huɗu soyayya shaƙuwa ce take gudana a tsakanin su inda wani
baya son ganin bacin ran wani.
TAMMAT BIHAMDIHI.
Allah nagode maka daka bani damar kammala wannan labari lafiya ayau juma'a 17/sep/2020 at
1:37pm abin da na rubuta dai dai rabbana ka bani ladansa abin da na rabuta ba dai dai ba
rabbana ka yafemin.
ALLAH NAGODE MAKA ALLAH NAGODE MAKA ALLAH KA ƘARAWA ANNABINMU DARAJA
AMIN.
Waɗan da suka sai littafin nan har sukai hakurin bina tun daga farko har xuwa karshe ina
matukar yi muku godiya Allah yasaka muku da alkairi Allah yabar zumunci.
Abin da yake dai dai na darasi acikin wannan littafi kuyi amfani dashi abin da yake ba dai dai ba
kuyi watsi dashi.
Wannan labari akwai soyayya acikin sa amman jigon sa darasine ga ɗaukar ƙaddara ga ɗan
adam" zakaga kana son abu kana ganinsa mai saukin samuwane agareka amman se ubangiji
ya jarabceka da abin cikin wahalar samuwa gadai mu'azzam da khadija waya taba tunanin zasu
sami kansu cikin wahala amman gashinan seda Allah ya jarabcesu ko wanne yayi aure sannan
ya dawo ya kuma hada su akaro na biyu.
Darasin lami kowa ya gidan ramun mugunta karshan sa tabewa gadai karshan lami da ƴaƴanta
shiyasa bawa ya rike Allah ya isar masa komai.
Darasin bashir kowa ya dauki damarar sabawa ALLAH to karshan sa tabewa da ladama bashir
ya dauki'zina ado gashinan dai karshan sa yadda ya kare Allah yay mana tsari.
Ga labarin nan dai wani abun tabbas yana faruwa a gaske amman wani abun kawai na
kirkireshine domin karawa labarin armashi.
Nagode readers.
Allah ya bar soyayya.
Se mun haɗu a zazzafan novel ɗina mai suna..