Showing 1 words to 3000 words out of 70697 words
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Ina farawa da sunan Allah azza wa jal, mai rahama mai jin qai.Allah ka taimaka na isar da
saqon alkairi kamar yadda nai niyya. Ameen
Wannan labari qirqirarre ne, ban yi dan cin fuska ko taba mutuncin kowa ba, zan yi domin
samun qyara a al'umma musamman ma ma'aurata, dan haka nake roqon duk wanda Allah yasa
ya karanta ya daure yai amfani da abinda yaji na alkairi a ciki, kuskuren daya riska , yai qoqarin
kauce masa. INA GODIYA DA DIMBIN MASOYAN NOVEL DIN WATA UWAR BAN FARA
WANNAN SABON BA SAI DA ROQO DA
KWARIN GUIWAR KU, INA ROQON KU DA KUCI GABA DA MIN ADDU'A ALLAH YA RABA
MU LFY DA MEDIA HAERMEEN HAMMAERH LOVE U ALL❤
Page 1:
Gidan malam Baballiya, gidane mai girma na qasa, a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi
mata biyu, Sarai itace uwar gida, sai Bilkisu, itace amarya, malam Baballe yana da yara guda
hudu dika mata, wanda yake ta burin Allah ya azurta shi da da namiji, mai albarka, wanda ko
bayan ba shi zai kula da wannan zuri'a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na
qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya
sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata yar ta tilo ba, dan haka in aka ji
rikicin ta to fa akan yar tane, ko shi ma ba zata tsaya aita bala'i ba , za dai ta tabbatar ta karbar
wa yar ta 'yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu,
Goggo Sarai nada, Suwaiba mai shekara 19, Saudat tana da shekara 18 wanda da watanni, sai
Salma me shekara 16, Mama Bilkisu na da Juwaira wadda take sa'a ce ga Salma kwana uku
ne tsakanin su, yanzu ta na dauke da tsohon ciki, wanda gashi nan haihuwa ko yau ko gobe.
Sai dai mui fatan Allah ya amsa adduar Abba Baballiya domin kullum fatan shi Allah ya dube shi
ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali amma yana iya qoqarin shi na ganin ya isa da
gidan shi, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan.
" wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje" da
sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita " Abba Maman mu na kiran ka,kai sauri
Abba bata da lfy kamar haihuwa zatai ina jin" da sauri ya shiga takalmin ma yaqi qarasa shiga
qafar tashi, " Subhanallahi Gimbiya, haihuwat ce?" ( yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi
na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai dadi sunna ne, inda yake kiran Goggo
Sarai Sarauta) " Malam taimaka min na samu na kai uwar daka bana son zama a nan na haihu
a rumfa" kamata yai ya kaita daki " amma mun shigo daka ko dai muje asibiti ?" Murmushi tai
sanin cewa qarfin hali yai dan ya kwantar mata da hankali ya fadi hakan ta san bai da kudin yin
hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwadayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo
Balki, dan yayan ta kyawawa inji ta da fada YAN ABUJA ne su sai mai kudi, dalilin wannan ne
yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa
samarin banza, amma sukai kunnen uwar shegu , da ya musu wuta2 kuma ya fara kulle sai ta
saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman
mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba daya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai
'ya'yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasara. Kukan jariri ne ya dawo da Abba
daga tinanin ina zai samo kudin kai ta asibiti ta haihu lfy? Da hanzari ya qarasa taimaka mata ta
haihun ya kuma gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida, "Juwaira doran ruwan zafi in ya yi ki
kirani" to Mamana sannu" cikin zumudi da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da
hushirya a saman su, fita tai taje dora ruwan taga ba iccen, amma duk da haka sai ta je ta
dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta aje, zata juya kenan ta ga
mahaifin ta na shigowa da icce a hannu da kuma leda, da hanzari ta isa ta karba, tana mai
sannu, komawa tai ta hada wutar ta dora shi kuma yai dakin, tsaki taji anyi a gefen ta, qin
juyawa tai dan tasan ba zai wuce daya daga cikin yan uwan ta ba" aikin banza sai rawar qafa
ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihu"
hmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika, to bari kiji yan baqin ciki, wannan karon
namiji Mamana ta haifa a cikin gidannan, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda"
wani uban ashar Salma ta saki ta tashi da hanzari zatai dakin su cikin rashin sa'a bokitin gaban
ta ya bige tukunyar da take dafa abu, ai ko tini ta zube nama ne na kaza cike da tukunyat
wanda yafi qarfin kaza daya, ko kulawa ba tai ba ta shiga dakin da gudu tana "Goggo ! Goggo !
Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?" Da saurin su suka fito dikkan su an
qule a daka ana hasafin kudin da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai
zancen auren su, " ke meye haka duk kin fadar min da gaba kamar Bilki ta haofi saurayi"
hmmmm ai kinji ashe ke kikai mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya
tabbata ai" damqo ta tai da qarfu cikin zare ido take tambayar ta" me kk nufi salma?" Ina nufin
Mama Balki ta haifu saurayin da kullum kk mana mugun baki akai" ai wurgi tai da ita gefe, ta
qume kai da hannun kujera sukai gaba ita da sauran yammatan nata, sai dakin Mama Balki" me
nake ji? Me nake gani? " Abba ne ya baje ma Mama Balki nama balangu sai shayi daya hada
mata da madara ta gwangwani da bred, "No i cant belive this, what is going on here, ina jaririn
yake?"A cewar Suwaiba yar boko kenan, don tana da NCE ita sai Saudat me kwalin secondary
a hannu wanda duk daya take da su Maryam sai dai Juwaira tana son ta cu gaba ba halin ne
yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, " Haba Sarauniya
ta ya zaki shigo daki haka ba ko sallama? Kuma bama ki tambayi ya ta haihu lfy ba? Aa
tambaya kuke ina jaririn?" Eh ban ga zan iya ba ne shiyasa ban ba, tambaya daya ko da zan yi
shine me aka haifa?" Na miji Allah ya bani, me zai faru? Allahn da ya ban ba wai dan ya manta
ki bane kema ai, in kin kwantar da hankalin ki kema naki na tafe, dan haka ku fita min a daki
tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba"Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi da na miji
shine zaki fara min kitifi ko, to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma yanzu wani
tinani ya wanken damuwa ta, Shi Uban yaran me ya ke da shi ya tara da zan damu raina akan
namiji? Bayan ga Yaya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Yarana kowanne namiji mai lafiya
ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba: bakin ta suwaiba ke
son rufewa tana" Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su, ko kin manta halin yan baqin ciki
ne?" Aa Suwai ba Banni na fada masu suji dan baqin xiki ya mutu, yarana guda biyunnan sun
samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin cewa
su turo magaba tan su a zo ai komai," hmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar
ko? Umarni kk ban akan mazajen auren si ko? Ba bincike ba komai kawai su turo b to bari ki ji
na fada maki zan ba yayan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina
ko? Fitsarartiya mara kunya mai raina mijin ta gaban Yayan ta dan su koya suma" ranshi bace
ya matsa kusa da Maman yana bata naman a baki" Shewa Saudat tayi tace " ikon Allah wai na
kwance ya fadi" dariya Suwai ba tai da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya,
can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai tai a ranta tace" Hmmmmm
to ai ku gama da yayana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan.
Bayan kwana arba'in da shida ne, anyi suna da kyar wanda ba wani tari da akai an sama yaro
Ammar, yaro kaykkyawa kamar iyayen shi, amma yafi kama da Juwaira, ba qaramin so da gata
yake samu ba a wajen su, musamman Juwaira din ma, yan zu haka wasa take mai ta shimfida
tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi, dakin su kuwa ba abinda ke
fitowa sai qamshin tirarwn wuta na tainke, Sallama Abban su yai shigo jikin shi a mace, amma
dik da haka sai da yai masu wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira ya shiga cikin dakin
Goggo Balki, kwalama Juwaira kira yai yace ta kira Mama.........
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: YAN ABUJA
BY HAERMEEBRAERH
Page 2:
Da isa da qasaita ta shigo palon, hakan ne yasa Abban murmusawa duk da qunan da ran shi ke
masa na abin da take yi mishi" Sarauta kenan yi ki qaraso mui abinda zamui na fita sallah"isowa
tao tana hura hanci ta zauna a gefen damar shi inda Mama Bilki ke zaune a gefen hagun shi,"
da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo man wannan rana danake ta buri, domin manema
auren yaran nan ne Suwaiba da Saudat suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe
cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwai ba kudin auren ta
sadaki, na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million daya da dubu dari biyu,
sai na Saudat Ita kuma Million daya, a gaskiya na so naqi karba saboda kudin sunyi yawa,
kamqr wanda zamu saida yayan?....... Abban su ina fatan dai bakai mana baqin cikin iyayen
zamani ka sa an rage kudin nan ba?" Ta fada tana cike da tsoron ko dai an rage kudin ?" Amma
dai na rasa me yasa baki da da'a wallahi? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina
ikirarin zan ma yayana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk na da kyau kuwa? Gaba
daya kin sa tarbiyyar yarana a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai
harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana,
ke kam na san da karuwanci zaki saka yayana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali
ba da Balki? Yarta daya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar t, ke
kuwa in ba Salma ba da tai sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani sui karatu mai kyau
ba, Salman ma gashi nan ne kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk,
ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni yasu,........ " Aa faaaa, bafa zaka sani a gaba
ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari,
Yaya dai nawe ni nai naqudar su na haifa, ba wanda ya taya ni lokacin danake qafa daya lahira,
daha duniya,ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura
ce bana so tammm, yanzu ka bamu kudin lefen da sauran dan musulunci bai yarda kowa ya
taba dukiyar auren yara ba sai su ehe" hmmmmm Sarai kenan to ai bari kiji iya kudin lefe zan
baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su, da ke a taki qaramar kwakwalwar sai
na dauku kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni
da biya da tashin hankali? To bazai yu ba" Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an
bata kudin, tashi yai ya kade rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke
cewa" Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy"
Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addua mai
dadi haka, dama ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen" sa kai tai ta fice ta shiga madafin
su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon
tazubar din su da sunan Islamiyya, " wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar
gida" hmmmm wannan sallamammen uban naku ne mana, an kawo kudin auren ku sun riqe
shida Balarabe, to wallahi ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin dika" Goggo
kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani" inji Suwaiba, daki suka shiga ta dakko mata
maqudan kudi.a jakar ta saida tai baya dan yawan su," waya baki wannan kudi haka?" Alhaji
Salihu mai tumbin Nera kk ji, cewa yai ga su ko zan qara wsu abubuwa a lefe yaso bayar wa a
can ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya
samu yar zuma, ( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat tai " Aaaaa
kice Adda Suwaiba Alhaji yaji zuma yau" dariya sukai dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin
ma da take ciki ta manta shi, ba sallah ba salati suna zaune ana maida tanda akai da yanda za
ai.
Juwaiirah ce na hangi goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta
saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah
zaibiya masa buqatar shi musamman a lokutan karbar addua wanda qarfe uku zuwa asuba
Allah na amsa adduar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, " Ya Allah kaine
masanin abin da ke zuciyata Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer
ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira" wannan addu'ar ce tafi daukan hankali
na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Adduar ta ta ci gaba wanda tai wa iyayen ta da yan
uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har
aka kira sallah ta gabatar ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta
dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara
gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana
son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin ta bane sai dai tai kwalliya sama2 kawai , ta
saka wata rigar ta doguwa ta atampa rigar na da fadi ta qasa unda ta sama aka dan tsuke ta da
dogon hannu yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah akwai shape mai kyau,
gyara gashin kanta tai da kyar dan yawan shi da tsaho, bayan ta gama ne ta kafa dauri me
kyau, ta samu tiraren ta ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta zata dau Ammar, Maman
ke tsokanar ta" Aa kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere diyar Mamanta" ni mama na ce
maki bana son Juwairere Allah dariya qawayena suke in suka zo sukaji kina fada musamman
Nafeesa" to in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau" kin ga
kuwa data tsokane ki sai ki murmushi saboda yarinta ce ba wani abu ba" dariya suka saka sosai
suke dariya saboda sarai ta san maman nata na tsokanar ta ne again, basuji sallama ba sai ji
tai an kama hancin ta," wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman
wannan Juwaiirahn da ta bude wannan qaramin bakin nata take cikawa mutane gida da yar
muryar nan ta ta"tsalle tai na murna ta kama hannayen shi dika" Yayana, wayyo Yayana kaine
da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? " Oh Juwaiiraah ko zama bai ba fa
wannan zumudi a bari ya dan zauna ya huta mana" Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing
din Juwairere na nai ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na" murmushi Mama
tai ta fita debo