Showing 1 words to 1335 words out of 1335 words

Chapter 1 - KAR KA DARA Sabbin Labaran Ban Dariya.txt

Yahya So   

22 Dec 2024

1567

Labari Mai Cike Da Nishadi Gamida Ilmantarwa Ga Masoya.


Sunyi aure ne bayan kyakkyawan lamarin soyayya, kuma bayan sati biyu sai mijin ya farka zuwa aiki. Ya shiga bandaki don wanke fuskarsa, a cikin madubi ya ga fuskarsa cike da zane-zane launuka daban-daban. Matarsa ƙarama ce, yarinya ce, kuma tana da zuciya marar laifi. Ta dago a fuskarsa yayin da yake bacci, kuma ta yi hakan ne da matukar kauna, da za su yi dariya da safe.


Mijin ya wanke fuskarsa yayin da yake cikin bacin rai, ya tafi kicin don shan kofi wanda yawanci yake yi kowace safiya. Bai sami kofi ba, sai ya kara damuwa, ya tafi wurinta.


Murmushi tayi domin tana tunanin zai mata dariya, kuma ya fadi wani abu na soyayya.
Amma ya mare ta har sai da ta fadi, sannan ya daka mata tsawa yana cewa: "Ban aure ku ba don in yi wasa da ku, ni mutum ne kuma ba karamin yaro ba. Na aure ku ne don ku kafa iyali ku haifi yara, ku zama mutum a idanun kowa. Shin kuna son rayuwa labarin soyayya na fina-finai da waɗancan littattafan da kuke karantawa? Ku farka, waɗannan labaran ba sa yin gida, ba sa samar da abinci, kuma ba sa renon yara.Yau zan gayyaci abokaina don abincin rana, ina son komai ya kasance a shirye idan na dawo. Shin kun fahimta? "


Ya fita sai ya ga kansa a matsayin maigidan gidan. Ya bar ta ta karye, tana kuka sosai har ta kasa numfashi da kyau.
Ba ta da lafiya in ta yi kuka sai ta kusan fashewa.


Sannan ta yi sauri ta tafi don shirya abincin rana, kuma hawaye ba su bar kumatunta ba.


Mijin ya je ya gaya wa abokinsa abin da ya faru yayin dariya: "Suna ganin cewa aure duk so ne da soyayya. Wannan shi ne yadda ya kamata a bi da mata, abokina, in ba haka ba ba za ta taba koyon aiki ba. Ba za ta zama uwa ta gari ba. Dole ne ta sani cewa aure ba kamar yadda ta gani ko karanta shi ba ne, wadannan labarai ne kawai don samun riba. Suna bukatar su koyi cewa aure ba wasa bane ko almara. "


Amma yayi sa'a abokin nasa ba kamar shi bane, bai barshi ya gama tattaunawar sa ba, ya yanke shi yana cewa: "Wane irin mutum.




NISHAƊI TIME


Ƙarashen Labarin Jiya.....


.....Nace mata abin mamaki fa kin santa, kuma kema zaki yi mamakin cewa zata iya aikata hakan.


Abinka da mata duk abin nan da nake faɗamata hankalinta ko alama bai nuna mata cewa da ita nake ba, domin a tunaninta babu yadda za a yi in samu labarin abin da ke faruwa a makarantarsu😀.


Sai na ce mata, abokin nawa ya kawo mun hotonan budurwar tashi tare da wancan sabon saurayin nata, zan baki ki duba, idan kika duba sai ki ajiyemun hotunan a wurinki zan karɓa daga baya, ni kuma yanzu zan je in bashi shawarar da kika bayar kawai ya saurara mata tunda lamarin ya zama yaudara ce kamar dai yadda kika faɗa🥺.


Na sa hannu aljihu na fito da envelope na miƙa mata, ban tsaya jiran ta zaro hotunan ba, kawai na juyo abina na tafi.


Bayan na bar ƙofar gidansu, daga nan na wuce wani gidan bread da ke unguwar, zan kai kimanin Awa ɗaya, amma wallahi dana dawo hanyar gidansu zan wuce gida na hange ta a tsaye inda na barta, bata tafi ko'ina ba, envelope a hannunta, ga alamu mamaki take ta yaya na samu wannan labari har na samu hotunan, abin ya yi matuƙar ɗaure mata kai. Ni dai na ƙara gaba na tafi abin na.


Washegari ta aiko neman na, nace ai ba wannan magana. Na bai wa zuciyata hakuri na fita sabgar ta.


Bayan kwana biyu ashe rigima ta ɓalle da ita da wancan gayen, akan tana zargin shi da yaɗa hotunan da suka yi, ashe bisa yarjejeniya aka yi hotunan kada a fitar da su, iya tsakaninta da shi ne kawai. Shi kuma can ɓagaren gayen ya yi tunani iya tunani ya rasa ta yadda aka yi hotunan suka fita.


Abokin nawa shi ke zuwa can wurinsa yana cigaba da shaƙo mana labari a can unguwarsu.


Ta shiga matuƙar damuwa, domin a unguwar kowa na ɗaukarta irin matan nan masu kunya da mutunci, yanzu kuma ga hotunanta da saurayi sun fito, bata san iya inda hotunan suka je ba, tsoronta watakila har gidansu hotunan zasu iya kaiwa.


Haka dai aka yi ta buga wuta tsakaninta da wancan saurayi akan dalilin da yasa ya fitar da hotunan, ga shi yana so ya ɓata mata suna. Shi kuma a rikice yake bai san yadda aka yi hotunan suka fita ba, saboda copies da ke hannunshi suna nan intact.


Kai, saboda pressure ana cikin hutu amma sai da aka je Kaura aka nemi mai hoton aka tuhume shi da cewa ko shine ya wanka wa wani hotonan. A nan ma mai hotu ya sha aradu bai san da wannan zance ba.


Gari ya yi mata zafi sosai domin tana tsoron kada ace hotunan sun fita wani wuri. Ta yi juyin duniya mu haɗu, ni kuma na ce Allabaran babu wannan magana.


Aka rubuto mun wata zungureriyar takarda cike da ban hakuri da labaran Aku wai ba saurayinta bane, course mate ne kawai, suna mutunci shi yasa har aka yi hotuna, ita bata san lamarin zai koma haka ba. Inda take shiga ba nan take fita ba. Wai don Allah in yi haƙuri in yafe.


Nima na rubuta mata takarda cewa maganar cigaba da alaƙa tsakaninmu a gaskiya na haƙura, amma ina mai bata tabbaci cewa hotunan nan suke nan copies dana bata, idan ma tana tsoron ko zasu fita wani wuri ne, to ba haka bane. Daga ƙarshe na rufe wasiƙa ta da 'Asha Soyayya Lafiya'


To gaskiya ga alamu akwai sauran soyayyar tawa a zuciyarta, ba mamaki shi wancan an so a riƙe shi saboda ana tatsar ɗan abin hannunsa, domin ta shiga damuwa sosan gaske, to amma saboda sanin haƙiƙanin zuciyar mace sai Allah, hakan ya sa na shafamata lafiya.


Tabi duk hanyar da take iya bi, akan mu dawo mu cigaba kamar inda aka fito to amma Hausawa na cewa Idan maciji ya sareka to a gaba ko tsumma ka gani to ka arce kawai. Wannan ya sa ban koma ba.


Shi kuma gogan naka tsakaninsa da ita lamari ya ƙi daɗi, ashe dama sun yi alƙawari da ita cewa bata so aga hotunan, wato dama ta shirya yadda zata ci duniyarta a tsinki ba tare da lamarin ya fita ba, ko ya kawo kunnen na. Ikon Allah ne kaɗai ya sa zance ya fita.


Shi kenan nakama gabana na fita sabgar ta, duk da cewa muna haɗuwa a unguwa ana gaisawa amma dai babu wata alaƙa. Kamar zance ya mutu. Ashe shi wancan gayen sonta ya yi matuƙar kama shi don haka baya so alaƙa ta yanke tsakaninta da shi, yana can yana binciken ya aka yi hotunan suka fita.


Da bincike ya yi bincike, sai ya samu labarin ai wannan abokin nawa da ke zuwa wurin shi, ashe tare muke, kuma ya tuna cewa lallai ya nuna masa hotunan nan a baya, ai lamari sai ya dawo sabo, wai gogan naka har da kai ƙara ofishin ƴan sanda wai an yi masa sata. Case fa rigigi, to amma fa ba hujja, saboda hotunansa suna nan intact a wurinsa, aka buga aka raya ba hujja😀. Ƙarshe dai dole case ya mutu.


Ita kuma ta rabu da shi saboda abin ya taɓata sosai, nima na rabu da ita, don haka a lokacin sai kuwa ya koma ya dasa sabuwar shuka wani wurin😀


Amma fa har yanzu da nake magan ina da record na wasiƙun da aka yi ta kaikomo a lokacin suna nan a cikin adakata, wani lokaci nakan yi boshiyo in ɗauko wasu daga ciki in karanta in yi ta dariya abina.


Duk da ya ke bayan tsawon lokaci mun dawo muna mutunci da ita matuƙa, ana zuwa neman shawara da tattaunawa wasu matsaloli na rayuwa, amma dai soyayyar aka jawa layi😀


To kun ji yadda zancen ya kaya, ita ta yi laifi kuma ta yankewa kanta hukunci😀😀.

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login